ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 7

 




🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️


*ALJANAR FATIMA BOOK 2*


🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️



By *Kingboy Isah* 


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*Zamani writers Association*

•••••••••••••√••••√••••••••••••••••

_$$ Free book but support us read in our site $$_


https://youtu.be/jEISNufi6_E


Join Aljanar Fatima 2 Fans group 


https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N



*^ Part 7 ^*



Haka dai suka gama maganganunsu Fatsuma bata tamka ba haka itama Mairo bata ce kala ba. Da dare ma haka Fatsuma ta kukuta ta nemar musu abinda zasu ci da dan sauran canjin hannnunta tunda a gidan horon yunwa ake musu. Bayan sallar la'asar Habiba ta shigo gidan da murnarta hannunta rike da littafai. A tsakar gida ta samu su Kubura suna ta gulmace-gulmacensu da suka saba. Ta gaishesu suka amsa a wulakance kai tsaye ta nufi dakin su Fatsuma tana ta murna suka gaisa da Fatsuma tace "A'a su Habiba yau kam farin cikin me kike haka". Habiba ta washe baki hade da cewa "Ai dole inyi murna kalli abinda baban su Salame ya kawo min daga kasuwa". "Ah masha Allah littafan ne har an sayo". 


Fatsuma ta fada hade da karban littafan, kawa'idi ne da juzi'i dan izo biyu "To kinga yanzu karatu zai fi tafiya dai-dai sai mu koma baya ma in fara koya miki tun daga alifun ba'un". Ba karamin dadi Habiba take ji ba nan take ta zauna suka fara ita dai tana son ilimi ba karamin burgeta matan birni da yaransu suke ba. Ba don komai ba sai don ilimi da suke da shi na boko da na islamiyya, su kauyen nan ba abinda suka sani sai gulmace-gulmace da hada annamimanci ga asirce-asirce har na innalillahi, yaran kuma ba zaka taba jin wata kalma mai dadi ta fito daga bakinsu ta bangaren addini ba sai shegen ashar kamar jikokin maguzawa. 



Suna cikin karatu Laure da Kubura suka lallabo kamar munafukai suka labe kofar daki suna jin abinda ke faruwa, burun! Kubura ta fada dakin hade da kare musu kallo, "Ashe malama muka samu a gidan bamu sani ba, ai na zata gulmarmu kuke da kuka zo kuka wani shige daki kamar bakin bokaye". Cewar Kubura yayin da tayi tsaye kan Habiba da Fatsuma dake karatu. Laure tace "Kwarai fa mun sama malamai a gida nan gaba kadan za'a fara yi mata layi ana zuwa neman taimako daga garuruwa". Kubura tace "Au karamar bokanya zata zama ashe". Suka kwashe da dariya hade da tafawa, su dai su Fatsuma basu tamka ba suka cigaba da karatunsu.



Kwana biyu da Habiba take zuwa gidan ta fahimci cewa Fatsuma na fama da rashin samun abinci musamman da dare don taga ba'a bata ko kuma sai suna karatu taga sai hamma take. Hakan yasa ta yanke shawarar zata rika kaiwa Fatsuma abinci bayan ta tambayi mijinta. Kullum idan zata je wajen karatun sai ta debarwa Fatsuma abinci ta tafi mata da shi, dake a tsakar gidan take wuce su Kubura abun ba karamin kona musu rai yake ba don haka lokacin horon yunwar da ake wa Fatsuma na hanata abincin dare har ya wuce amma suka ce ba zasu cigaba da bata ba tunda Habiba na kai mata. Ana cikin haka suka lura Fatsuma bata damu ba don haka sai suka fito da sabon salo da zarar sunga Habiba ta kawo abincin tana shiga dakin Fatsuma sai suje da kwano su raba abincin biyu su bar mata rabi wani lokacin ma wanda suke bar mata baya kaiwa rabi, Ita dai shiru take bata tankawa 




Ita kuwa Habiba abun na matukar ci matar rai tabbas tasan bakin hali irin na su Kubura amma batayi tunanin abin ya kai haka ba, haba ace ku hana mutum abinci dan wanda ake kai masa ma ba zaku bari ya ci ba, don haka tace zatayi maganinsu. Washe garin ranar da zataje gidan sai ta zuba abincin a kula yar doguwa mai maruka kuma ta sa katon hijabi don haka ta gabansu ta wuce suna tsakar gida kamar mayu suna jiran zuwanta. Ko kadan basu ga alamar ta riko abinci ba, Laure tace "Yaya naga kamar yau Habiba bata kawo abincin da ta saba kawowa Fatsuma ba". Kubura tace, "Kai anya sai dai in batayi ba amma ni zumbulelen hijabin nan ban yarda da shi ba don haka bari a dan jima su sakankance kawai sai mu fada dakin mu gani". Habiba kamar ta san haka zata faru shiyasa ma da ta isa dakin bata bawa Fatsuma abincin ba littafai ta ciro kawai suka cigaba da karatu



Suna cikin karatun kamar daga sama sukaji fadowar Kubura da Laure ko sallama babu, su Fatsuma suka daga kai suna kallonsu yayin da su kuma suke karewa dakin kallo basu ga alamar abinci ba. Sun juma a dakin ba tare da sunce uffan ba suka tashi suka fita, Habiba kuwa murmushi kawai tayi sai da ta tashi tafiya tukun ta fito da abincin daga hijab dinta ta bawa Fatsuma, washe gari ma hakan Habiba tayi, Bayan sati biyu suna zazaune tsakar gida suna gulmace-gulmacen matan gari. Kamar kullum Habiba ta zo ta wuce bayan ta gaishesu sun karba a wulakance. Laure tace "Ni fa wallahi bana son zuwan matar nan gidan nan, ga dukkan alamu akwai wata hanyar da take bi tana kawowa Fatsuma abinci don na lura kwana biyu bata jika garin kwakin da ta saba jikawa in mun hanata abinci". 



Kubura tace "Barni da su kawai nima na lura da cewa akwai wata manakisa da suke kullawa a tsakaninsu ba iya karatun ba amma kawo kunnenki kiji". Laure ta mika mata kunne me ta fada mata oho suka kwashe da dariya hade da tafawa, bayan kwana biyu da dare suna zaune tsakar gida su kuma su Habiba suna daki suna karatu Bukar ya shigo gidan, da ganinsa Kubura da Laure suka rushe da kukan munafurci, nan take ya nufe su yana tambaya me ya samesu. Cikin kukan karya Kubura ta fara "Dole muyi kuka mana, yanzu abun na Fatsuma wuce gona da iri, bayan irin cin mutunci da take mana a gidan nan yanzu kuma ta fara debo mutane har gida suna shigewa daki suna gulmarmu". Laure tace "Da kunnuwana naji suna gulmarmu abun bai tsaya iya nan ba cikin gulmace-gulmacen nasu harda kai a ciki shiyasa ma mu ka yanke hukuncin sanar maka in dan ta mu zamu iya jure duk irin munafurcin da zasu kulla mana dan kar mu tabata aita yawun yamadidi da mu a gari ana cewa muna zalintarta". 



"Ita Fatsuma din ce take tara mutane a gidan nawa?". "Kwarai yanzu haka suna ciki ita da Habiba sun fake da sunan karatu amma ba abinda suke sai gulmarmu". Cewar Kubura, da sauri ya karasa kofar dakin ya leka tabbas karatu yaga sunayi amma ba zai yada maganar Kubura ba. "To Allah ya tonu asirinku munafukai, yanzu ke Fatsuma abun naki har ya kai ki rika debo mutane ana zuwa har cikin gida ana ci muna mutunci ni da iyalina?". Fatsuma da Habiba kallon juna sukayi cike da mamaki domin su basu ma fahimci inda ya dosa ba, don haka Fatsuma ta daga baki ta fara da cewa "Baban Zubairu me aka ce ma nayi wallahi karatu muke ba wani abu ba ga Habibar nan zaune". "Rufe mun baki munafuka ai an fada mun, to bari kiji in fada miki wallahi ba'a gidana ba idan ma gulmace-gulmacen zakuyi ki bita can gidanta ba dai a nan gidan ba" Ya kalli Habiba "Ke maza tashi ki tafi gidanki". Su Kubura dake gefe suna jin abinda ke faruwa duk dadi ya kumesu murnars ce ta koma gefe jin ya ba Fatsuma dama ta bi Habiba gidanta, sunsan cewa idan har Fatsuma zataje gidan Habiba domin koya mata karatu to fa ba zatayi yunwa ba.



Don haka da sauri Kubura ta ruga wajen har tana tuntube "Aa Bukar kamata yayi kawai a rabasu na har abada kar wata alaka ta kara shiga tsakaninsu balle ma har ta bita gidanta, karka manta da dare ne fa kar wani abu ma yaje ya sameta". Bukar yace, "Wani abun ya dade bai sameta ba, ko kwana ta ga damar yi a can taje ta kwana ni fa da ita da babu duk daya suke a wajena. Don haka ko mutuwa tayi ni abun farin cikine a wajena". Da fadar haka ya kada kai ya tafi. Fatsuma kuwa banda kuka ba abinda take, Habiba na lalashinta. Tabbas abin da ciwo ace wai mijinka ne ke maka fatan mutuwa yake kuma kwatantaka matsayinka da babu. 


Laure ta ja tsaki hade da cewa "To malama ai sai a tashi a tafi gida ko karatu ya kare kuma". Habiba tashi tayi ta tafi hade abincin ma bata yarda ta ba Fatsuma a lokacin ba sai da taje gida ta ba Mairo ta taho mata da shi. Bayan kwana biyu Lado mijin Habiba ya roki Bukar a kan ya bar Fatsuma ta rika zuwa gidansa tana koyawa matarsa Habiba karatu shi kuwa yace ba ruwansa ai ya bata dama in taga dama taje amma a gidansa ne dai bai yarda a rika tara mai mata ana gulmace-gulmace ba. Don haka da suka hadu a wajen rijiya Habiba ta roki Fatsuma domin ta ware lokaci ta rika zuwa gida suna karatun, kuma ta kara tabbatar mata Lado ya nemi izinin Bukar a kan hakan. Ba tare da gardama ba Fatsuma ta amince ta rika zuwa, domin ko ba komai dai tasan akwai tarin lada ga shi kuma itama zata rika bitar karatun riba biyu kenan............



Muje zuwa 

Comments