↫ NI DA FATALWA! ↬
{gajeran labari}
Part {1}
@KINGBOY ISAH
NOTE:
IN KASAN KANA/KINA DA TSORO KARKA/KI KARANTA. DOMIN LABARI NE MAI CIKE DA ABUBUWAN TSORO DA NA DARIYA. IN KUWA KA KARANTA KAYI MAFARKIN FATALWA BA RUWAN KING.LOL
"Habib da gaske wai fita zakiyi ka barni ni kadai? Wallahi na gaya ma akwai fatalwa a gidan nan, ni fa na ganta da idanuna dan Allah in dai fitarka ta zama dole to ka barni in tafi gida da yamma in ka dawo daga wajen aikin sai ka biya ka dauko ni kaji angona tsoro nake ji". Tsaki naji yaja abunda bai taba mun ba tun kafin ma muyi aure balle yau da na zama amaryarsa yau duka kwana takwas nayi a gidan nasa. "Khadija naga alamun so kike ki bata mun rai kuma nima in bata miki. Wai ku mata me yasa komai sai kun canfa shi ne? Shegen tsoro ne ya miki yauwa amma ba wani fatalwa a gidan nan, ni a rayuwata kwata-kwata ma ban yarda cewa akwai fatalwa ba. Ni zan tafi kuma wallahi in kika yarda kika sa kafa kika fita daga gidan nan ko? Zakiyi mamakin hukuncin da zan yanke". Yana fadar haka ya shige motar sa ya fita sannan ya dawo ya rufe get din. Da sauri na karasa bakin get din na zukulkula kubobi hade da kule get din. Zuciyata cike take da tsoro amma ya na iya? zaman aure ya ja mun. Shima Habib sai da nace ya nema wani gidan- ya nema wani gidan amma yaki gida kusa da makabarta ai dole ma fatalwa ta takura ma. Tsaye nake tsakar gida ni kadai nake zancen zuci. Ta wutsiyar idona na hangi kamar wani farin abu ya shigar mun daki. Hakan tasa na nufi dakin a tsorace na bude labule. Sai da na leka ko'ina a falon naga ba kowa sannan na sauke ajiyar zuciya. Domin bana mantawa sau biyu naga fatalwar nan kuma fararen kaya ne a jikinta. Jikin socket ma naje na ciro wayata na bude data na kwanata kan kujera sofa, na shiga whatsapp na fara chat da kawayena domin shi ne kadai nake tunanin zai deben kewa. Message naga ya shiga na bakuwar number nayi saurin shiga hoto ne aka turo ba sallama ba komai. Na sa hannu na danna kan hotan don ya bude. Ihu na kwada hade da yin wulli da wayar. Domin kuwa hotan wannan fatalwar ta jiya ne na gani. Da gudu nayo waje daga cikin dakin. Fitowata yayi dai-dai da sallamar wata mata. Turus na tsaya ina maida numfashi ina kare mata kallo wani dogon farin hijabi ne dogo a jikin matar gata doguwa. Girman idanunta kadai abun tsorone gata dattijuwa. Cikin tsoro muryata na rawa na amsa sallamar. Sai ji nayi tace "Sunana Indo ni makwabciyar ki ce ga gida na nan gaba da gidan ki. Gani nayi an kawo amarya yau har kwana takwas nace bari na leko mu gaisa". murmushin karfi da yaji nayi cikin karfin hali nace "Bismillah to mu shiga ciki". Gabana ne ya fadi da na tuna cewa na fa kulle gidan nasa kubobi da jamuluck amma ta ina matar nan ta shigo anya kuwa ba fatalwar bace? na tambayi kaina da kaina tambayar da bata da amsa. Sofa na nuna mata nace ta zauna ni kuma na daukko mata juice a cikin kofin glass a tsorace na kawo gabanta na ajiye sananan na koma Can kuryan falon kan archair na zauna domin a matukar tsorace nake da matar nan. "Amarya banga angonba ko ya fita ne". abunda matar nan tace kenan da muryarta marar dadin saurare. "Eh dazun ya fita office". Na bata amsa. "Kina nufin ke kadai aka bari a gida? bakisan akwai fatalwa a gida nan ba". Tuni tsoro biyu suka farmake ni. Ga tsoron matar nan ga kuma ta kara tabbatar min da zargina."Fatalwa kuma Inna Indo? ashe da gaske akwai fatalwa dama sau biyu ina ganinta na fadawa Habib amma yace wai tsorata nayi". "Ba tsorata bane bari kiji na baki labarin gidan nan". Na kara gyara zama hade da mika hankalina gare ta, ta fara da cewa, "gidan nan gida ne mai hatsari nan baya da shekara biyar aka gida shi. kinga ai katanga daya ta raba ku da makabarta ko". Nayi saurin girgiz kai Alamun eh. "To da nan gidan da kike ciki makabarta ne an taba binne wata mata ce a saitin gidan nan. Matar nan kuma itace take fatalwa taki barin a zauna a gidan nan. Fatalwar nan tana da matukar hatsari gata da siffofin tsoro na tabbata mijinki ma bai san cewa haka gidan nan yake". Wani sabon tsoro ne ya sake ziyartar zuciyata lokaci guda, na daga kai ina kare wa gidan kallo. A raina nace ko habib yana so ko baya so wallahi sai ya canza min gida. taya zan zauna a gida Ni da fatalwa?...................
Autan writers ne...
https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/
↫ NI DA FATALWA! ↬
{gajeran labari}
Part {2}
@KINGBOY ISAH
note;
Mai tsoro kar ta karanta!...
Maganar matar nan ce ta dawo dani daga tunanin da nake, "Shin kinsan me ya faru da matar da ta fara zama a gidan nan kuwa?". Na kada kai alamun Aa. "Itama amaryace kamar ki tun ranar da aka kawo ta gidan nan fatalwa ta fara firgita ta. Wata rana da daddare mijinta baya nan ya tafi wajen aiki bai dawo ba har dare wajen magariba. Tana zaune a falo ita kadai tana kallon tv kawai sai gani tayi wuyar dakin ta dauke, nan take fanka ta fara wulwulawa da karfi. Yarinyar nan tsoro ya kamata kawai gani tayi TV ta kawo ciki kuwa wata doguwar mata ce mai dogayen faracina domin farcen ta na hannu har kasa yake tabowa gashin kanta kuwa baki ne wulf amma yana da tsayi sai hakora zako-zako abun tsoro". Ina jin haka tuni na makalkale kafafuna kan kujera na kame waje daya kamar ni ce naga fatalwar. "Kina ji nan take sai fatalwar nan ta cikin TV ta kyalkyale da dariya mai firgitarwa yarinyar nan ta kwalla ihu ta yunkura zata tashi amma sai taji kamar an daure ta. Fatalwar nan ta daka mata tsawa tace "Ina zakije? ko ina zaki ba zaki guje mun ba sai kin gaya mun dalilin da yasa kuka shigo mun gida. Yarinyar nan ta fashe da kuka tace "Dan Allah kiyi hakuri wallahi bansan nan gidan ki ne ba" fatalwar nan ta bushe da dariya kawai yarinyar nan sai gani tayi fatalwar ta zuro hannu daga cikin TV zata kama ta kawai sai ta sulale kasa a sume". A firgice nace "Wayyo Allah na Fatalwar ta kashe ta?". Matar tayi murmushi tace ai ita bata kashe mutum sai dai ta basa wahala domin tana ganin yarinyar nan ta suma sai ta barta. shi kuma mai gidanta wata rana yayo dare karfe goma ya nufo gida sai sauri yake domin shi kanshi tsoron unguwar yake kasancewar dare yayi ga kuma duhun dare. yana cikin tafiya kwatsam sai ganin wani abu yayi fari tass a gaban shi. Da ya lura da kyau sai yaga kamar mutum ne a kwance cikin fararen kaya hakan yasa ya tsaya cik ya fara cewa "Waye a nan? waye ne". amma sai yaji shiru hakan tasa ya dan rabe da nufin yabi ta gefe ya wuce bai sani ba ashe fatalwa ce, Ya kusan wucewa kenan ta mirgina ta rike masa kafa a lokacin ta dago fuskarta abun tsoro da gashi baja baja ta fashe da dariya marar dadin saurare. suna hada ido kuwa ya kwallah ihun neman agaji amma ina ba wanda ya kawo mai dauki domin kowa yasan halin unguwar nan ba a zuwa da dare daga bakin isha'i duk wanda ya fito to ba shakka sai ya hadu da fatalwar nan". Ai tuni jubi ya kwaranyo min. naji tsoro ya dabai baye ni. Nace "To Inna Indo ya kike ganin za'ayi domin nima na ganta wata abun tsoro mai fararen kaya jini na zuba a idonta". Wata irin dariya naji Inna ma'au ta kyalkyale da ita wacce har sai da ta ban tsoro ma. "Kwarai yarinya kin ganta domin nima ina ganinta sosai jarumta nake kawai ina nuna mata rashin tsoro. Yanzu dai mafita daya ce ku tattara ku bar gidan nan in ba haka ba komai zai iya faruwa daku kullum kina cikin tsoro ne da fargaba. Yauwa yar nan ni bari na tashi na shiga gida gobe ma zan zo in dan debe miki kyauwa". Inji Inna Indo ta fadi haka hade da mikewa ni tuni tsoro ya kamani ita kanta tsoronta nake domin hijab din jikinta yayi kama da likafani gashi fari har kas. Tana tashi tayo waje nima na dau wayata na biyo ta da sauri domin in rufe kofar gidan. Wani sabon tsoron ne ya kara ziyarta ta domin gani nayi Babu Inna Indo gashi banji karar bude gida ba haka kuma na duba naga kubobi a makale kamar yanda nasa su dazun. Bansan lokacin da kuka ya kubce mun ba. da sauri na kira number Aunty na Hauwa. dake tana gida sun sama sabani da mijinta. "Hello amarya kinsha kamshi sai yau aka tuno damu wata amarci yasa an manta da mu ma". itace mai fadar haka kuka taji na fashe da shi ina fadin "Aunty Hauwa Dan Allah kizo yanzu akwai matsala wallahi". "Kuka kike khadija? Me ya faru ne? Innalillahi gani nan zuwa". Daga ji hankalinta ya tashi amma kin kashe wayar nayi domin tsoron da nake ji ya baci. Ban koma daki ba ba dadewa sai gata ta iso a napepk nayi sauri na bude mata kofa ta shigo tana tambayana. ban mata magana ba sai da naga mun shiga falo nace "Aunty Hauwa Wallahi gidan nan akwai fatalwa. Ni na ganta da ido n kuma yanzu wata mata ma ta shigo itama abun tsoro, take bani labarin akwai fatalwa. A gidan nan shiyasa na kira ki dan wallahi bazan iya zama ni kadai ba. dama sai da nace wa Habib ya barni na tafi gida yaki". Aunty Hauwa ta kwashe da dariya ta dade tana yi na tambaye ta me take wa dariya? wai ni take wa dariya domin ita ma wai bata yarda akwai fatalwa ba ni kuwa na kyale ta nace naji din. Haka muka wuni duk inda tayi ina biye da ita bana bari ta bace mun a gani ko kadan. Da yamma Habib ya dawo daga aiki suka gaisa da Hauwa bayan sun gaisa ne take bashi labarin zuwana da kuma irin tsorona nan fa suka hadu su biyun sukai ta mun dariya ni kam kallon su kawai nake domin ni kadai naga abunda na gani. Aunty Hauwa tace zata tafi gida na kuwa tashi hankali nace wallahi bazata tafi ba sai dai ta tsaya a nan in yaya habib ya tafi aiki ta ringa taya ni hira. Da kyar na samu na shawo kanta ta yarda da hakan a kan zata tsaya ta kwana din. Wani irin dadi naji da kaina naje na gyara mata dayan daki wanda dama saboda baki aka tanade shi. Da dare bayan munci abinci mun dade a falo muna hira sai wajen sha daya tukun muka shiga daki nida Habib Aunty Hauwa kuwa mayyar kallo tace sai ta tsaya ta idasa kallon wani indian film da ake a bollywood wani irin kuka kuka kamar na jariri ta fara ji kafin wutar dakin ta dauke dif lokaci guda kuma sai ta dawo. Wata irin firgita Aunty Hauwa tayi da ta tuna cewa Khadija ta fa gaya mata akwai fatalwa a gidan nan.................
ZANCI GABA
https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/
↫ NI DA FATALWA! ↬
{gajeran labari}
Part {3}
@KINGBOY ISAH
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
[WARNING; MAI TSORO KAR TA KARANTA. IN KUMA TSORON BA SOSAI BA TO KI KARANTA DA RANA]
Ai tuni ta fara karkarwa, Kuuwwuuuuuu! karan da taji ya wuce shiff! ta gefan kunnenta kenan da sauri ta waiga sai bata ga komai ba. Tuni ta fara karkarwa amma tsabar maita taki hakura da kallon. Ji tayi an shafi bayanta da hannu. Bata san lokacin da ta saki dan kara ba. Karan yayi sanadiyar fitowar mu ni dai dama a tsorace nake ina kankame da Habib domin ko sanda muka shiga daki ma a like da shi nake kamar cingum. "Aunty Hauwa lafiya naji kinyi kara". Habib ya tambaye ta, Rau-rau tayi da ido ta hade tsoron ta hade da kakalo murmushi "Lafiya lau wallahi wani abu ne akayi a film din nan da ya burgeni shine fa nayi karar jin dadi". Habib yayi murmushi "Lalai aunty Hauwa ke ko gajiya ma bakya yi da kallo? Yanzu fa karfe sha biyu da rabi. Mu dai tuni mun kama gobe". Habib ya fada hade da komawa cikin daki. A yanayin da naga Aunty Hauwa na tabbata a tsorace take naje nayi mata tambayar duniyar nan amma tace wai ba tsorata tayi ba. na lurs dai bata so na gano ta tsorata watakil dan kar na rama dariyar da tayi mun. Tayi nayi na nufi dakina dama gidan falo ne sai dakuna uku wanda ko wanne akwai bandaki a ciki sai kuma kitchin. nace Aunty Hauwa in zaki kwanta dai kiyi addu'ah ni dai na gaya miki halin gidan nan". Aunty Hauwa tuni har jubi ya fara keto mata domin ta tsorata matuka kallon take amma bata fahimtar abunda ake yi ma. hakan yasa ta kashe TV din ta tashi ta nufi dakin baki inda Na share mata domin ta kwanta. Ta fara tafiya ta je tsakiyar falo kenan nepa suka dauke wuta dif hakan yasa ta tsaya cik! tayi saurin latsa switch off na wayar tana karkarwa amma sai wayar ta subuce daga hannunta ta fadi kasa. Aunty Hauwa tsoro ya kamata kamar zata fashe da kuka tsabar tsoro ta tsugunna ta hau laluban waya. Karar tafiya taji kamar anyo wajenta hakan yasa ta fara cewa "waye waye". amma shiru bata ji ance komai ba. "Me kike nema a cikin duhun nan". abunda taji an fada da muryar mace kenan a zaton ta ni ce hakan yasa tace "Khadija wallahi wayata ce ta fadi shine nake nema domin duhu yayi yawa bazan gane hanyar dakin ba". Dai-dai wannan lokacin nepa ta dawo fuw! aka kawo wuta bisa mamaki sai gani tayi bata ga kowa ba da sauri ta dauki wayarta ta ruga daki a guje tana shiga bata tsaya dubawa ba ta banko kofa jamuluck ya shiga. Juyawar da zatayi sai tayi arba da wata doguwar mata siririya wacce take sanye da wata doguwar riga fara sai wani mayafi da ta yafa a kafada gashin kanta duk ya barbazu a bayanta dake matar ta juya ne Aunty Hauwa bata ganin fuskarta. Nan take gabanta ya fara dukan uku-uku duk illahirin jikinta ya dau rawa. "Wace ce". Aunty Hauwa ta fada cikin muryar tsoro dake fitowa a hankula. Shiru taji Matar batayi magana ba. Ta sake maimaita tambayar har sau uku, a na hudun kawai sai matar ta juyo fuskarta fari fat kamar wacce ta shafagari amma kuma idanunta ko kadan ba fari a ciki baki kirin da su ga wani irin gashin gira dogo da Aunty Hauwa bata taba ganin kalarsa ba tunda take. "Ni ce Fatalwa Indo". Abunda matar ta fada kenan. "Wayyo Allah na dan Allah dan annabi fatalwa kiyo hakuri ban san nan dakin ki bane. Na rantse yanzu zan fita". Kulululu cikin Aunty Hauwa ya kada sai zawo kafin kace me tuni ta jika zanin ta da fitsari. Ita sam ta kasa yin addu'ah kamar an mantar da ita kuma ta kasa bude dakin ta fito a guje. Kawai sai ihu take. Fatalwar nan kuwa ba abunda take sai kyalkyala dariya. Ni da Habib muna daki har barci ya fara daukar mu muka jiyo ihun Aunty Hauwa can kasa-kasa. Dake ni na fara tashi nayi sauri na tada Habib nace ihu nake ji. Yace "kwarai kuma kamar a gidan nan ma". Da sauri ya tashi ya yo falo ni ma da nake a tsorace a guje nabi bayansa. Mukaje kofar daki mukayi mukayi Aunty Hauwa ta bude amma ta ki budewa ihu take har muryar na shakewa. Da gudu Habib ya koma domin ya daukko makolin dakin nima kuwa na bishi dan bazan yarda ya barni ba wannan yanayi. Muna dawowa mukaji Aunty Hauwa ta daina ihu. Habib na budewa muka tarar da Aunty Hauwa bakin kofa a yashe a kasa ga dukan Alamu dai suma tayi Habib ya debo ruwa ya yayyafa mata ta farko. Hade da sakin razanannen kara. Sai kawai gani mukayi ta tashi ta baza a guje ta fito daga dakin tayi hanyar kofa. Da sauri Habib ya riko hannuta. "Ina zaki Ke Hauwa lafiya kuwa". Habib yake yake tambayar ta cikin tashin hankali. Ita kuwa kokarin kwacewa take kamar mai aljannu sai kuka take tana fadin "Wayyo Allah ka barni in tafi gida fatalwa wallahi bazan kwana a gidan nan ba". Nima tambaya nake lafiya lafiya amma ina hankalinta ya matukar tashi ga dukkan alamu dai tayi matukar razana ne. Habib ya juyo yana tambayana wai ko tana da iskokai ne ai kuwa ta gallamai cizo a hannu dan dole ya sake ta ta ruga da gudu waje na bita a guje ina fadin ta dawo. Kafin ta kai gate naga taja wani uban birki ta saki razanannen kara. Ta juyo a guje, Nima ihun na saki na juya a millon sakamakon ganin abunda ta gani. Fatalwar nan ce zaune cikin fararen kaya tasa wani abu wanda shima kamar gawa ce dai cikin likafani sai dariya take hasken glof din tsakar gida ya haska mana ita. Sai gamu muna tsere da Aunty Hauwa da da take niyar bude gida ta gudu. Ina zuwa na rukunkume Habib ina fadin "Fatalwa Fatalwa". Aunty Hauwa ma da gudu ta zo ta makalkale ni. Habib yace "Wai ku wane irin mutane ne in ma fatalwar ce ba zakuyi addu'ah ba sai ihu?. oya ku sake ni naje na ga miye". Ai maimakon in sake sa ma kara rukunkume shi nayi.Aunty Hauwa da sai maida numfashi take hauwaye kam sun cika fuskar share-share. itama kara matse ni tayi kam. Nace "Dan Allah karkaje Habib Fatalwa ce". Tsaki yayi yace "Oya to muje dakin iyayen tsoro ku kama karanta ayatul qursiyyu. Ai tun kafin ya rufe baki Aunty Hauwa kamar an kunnata ta fara karantawa. A haka muka tafi daki kamar yara Ni ina rike da Habib Aunty Hauwa kuwa na rike da ni. Mukaje wajen kwanciya aunty Hauwa ta kwanta a kasa tace Alquran ba mai raba ni da ita. Habib yace to mu kwanta a kan gadon shi zai kwanta a kasa. Ni ma nace wallahi ba zan rabu da kai ba, ni da Aunty Hauwa ai duk jirgi daya ya kwaso mu tunda itama fatalwar ta rainata. Ba yanda baiyi ba a kan shi ba zai kwanta gado daya ba da Aunty Hauwa Amma abu yaci tura domin nima nace bazan rabu da shi ba itama kuma bazata rabu dani ba. ganin muna shirin yin kwanan zaune ga barci a idanunmu sannan ya aminta ya kwanta can gefan ni kuma na rungume shi aunty Hauwa itama ta kankame ni. ya zmana ni ce a tsakiya. Aunty Hauwa a jike take sharaf da fitsari amma tsoro baza zai barta ta canza ko nawa ne bama. rokon Allah kawai take gari ya waye ta bar mana gidan. Cikinta ne yayi kara kulululuuuu "Aunty Hauwa lafiya kuwa". Tace "Wallahi zawo ne kuma bzan iya shiga toilet ba ni kadai wallahi tsoro nake ji. g zawan ya matse ni"..............
ZANCI GABA
https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/
↫ NI DA FATALWA! ↬
{gajeran labari}
Part {4}
@KINGBOY ISAH
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
(*KUYI HAKURI JIYA KUN JINI SHIRU WAYA TA CE TA SA MAN HAWAN RUWA. HAR YANZU DAI BAI SAUKA BA*)
Nace "Aunty Hauwa ki daure ki matse shi wallahi ni dai in kika fita fatalwa ta kamaki ba ruwana" Karan tusa naji. Aunty Hauwa kaman tayi kuka "Wallahi ya matsen Dan Allah muje ki rakani na rantse in ba haka ba a wando zanyi". Da sauri Habib ya mike zaune yace "Khadija maza tashi ki raka ta". Na tashi zaune nace wallahi ni dai bazan iya zuwa ni kadai ba dole sai dai a tafi da kai domin nima tsoro nake ji". "Khadija kina da hankali bn dakin zan bi ku?. Dallah kinga ki tashi ki rakata muje na jira ku a kofa. Haka muka tashi a tsorace sai waige-waige muke. Aunty Hauwa na tura kofan ban dakin tayo baya da gudu. Habib yace "Miye kuma?" "Faa.... tall... wa". Ta fada cikin in'ina Habib da shima zuwa yanzu ya dan fara tsorata a hankali yaje ya tura ban dakin ya tura kafar haggun gaba ya dan like kamar marar gaskiya, ganin ba komai ya juyo yayi tsaki yace "Kawai tsorata kukayi amma ba komai a ciki". Da kyar aunty Hauwa ta shiga kusan sau uku tana shiga tana bazowa da gudu daga karshe dai tare muka shiga na juya baya nima tsorace tayi toilet din Habib na jiran mu a kofa sannan muk fito. Bayan mun kwanta wani irin kara muka ringa ji daga falo kamar kuka kamar dariya ba shiri na kara makalkale Habib Aunty Hauwa ta makalkale ni itama. A daren nan bamuyi barcin kirki ba. Kiran sallar fari Aunty Hauwa tace gida zata da kyar muka lalabata ta tsaya sai karfe shida Nima ban yarda an barni a gidan ba tare muka shigo mota aka kawo ta gida sannan muka koma. Wajejen karfe goma lokacin Habib tuni ya fita aikj zaune nake a Falo rike da waya ina chat da kawayena whatsapp amma sam ba a cikin natsuwa nake ba kallo daya zaka mun kq tabbar da hakan, "Salamu Alaikum" Naji ance durum! Gabana yayi mumunar faduwa Inna Indo ce ta shigo yau ma dai cikin dogon hijabinta fari har kasa. Fuskarta kam kallo daya nayi mata na kauda kai dan tsoro. Abun da ya dugunzuma hankalina shine ta ina matar nan ta ke shigowa bayan kuma yau ma na tabbata na makala kubabin gidan baki dayansu?. "Wa'alaiki salam" Na amsa sallamar hade da cewa ga waje zauna. Bayan ta zauna ne nace "Inna Indo naga na rufe gidan da kubobi ta ina kika shigo?". "Aa ni kuma ai a bude na ganshi leka ma ki gani a bude yake". Na tashi na dan rabe na wuce, abun mamaki kuma tabbas gidan a bude yake. bayan na dawo na zauna n naji tace "Ki daina barin gida a bude fatalwar nan da rana ma fa zata iya shigo miki gida". Nace "Wallahi nima na rufe". Sai ji nayi tace "Kin san me ya faru da matar da ta zauna a nan gidan ta biyu kuwa?". A dan tsorace nace "Aa". Nan take ta shiga bani labarin. "Bayan matar nan ta farko wacce aka tsorata ita da mijinta sun tashi. Sai wani mutum ya kama hayar gidan nan dan kasuwa ne shi sai karfe sha dayan dare yake dawowa gida. Yana da mata da yara biyu, Wata rana wajejen karfe sha dayan dare lokacin mijinta bai dawo gida ba yaranta kuwa tuni sunyi barci, Itama din ta kwanta har ta fara barci kawai sai taji kamar ana surutu a falo. To lokacin nepa basu kawo wuta ba. Fitila dayace kuma suke da babba. hakan yasa ta tashi ta sauko daga kan gadon ta dau fitilar nan ta nufi falo. Tana zuwa falo sai tayi curus sakamakon ganin wasu mutane biyu masu fararen kaya a zazzaune kan kujera sun juya mata baya wato bata ganin fuskarsu". Tuni tsoro ya rufe ni nace "Inna Indo kuma ba mijinta bane?". Tace "Tsaya kiji mana, Lokacin da ta gansu sai tsoro ya kamata cikin muryar tsoro tace "Su waye?". Maimakon taji an manta magana sai ji tayi su biyun sun gagabe da dariya, Tsoro ya rufe ta kamar zata ruga cikin daki a guje amma sai ta dake a tsorace ta kara furta "Su waye". Nan take taji sun kara fashewa da dariya kuma sai gani tayi su biyun sun mike tsaye a tare. Mata ne gashin kansu baki wul ya zuba kan bayansu kuma duk dogayen riguna ne farare ajikinsu. Matar nan taji sunyi shiru hakan yasa ta kara magana sai kawai gani tayi kawunan su sun juyo baya maimakon su waigo. Fuskokin su abun tsoro ba kyan gani domin sam ba irin fuskokin mutane ne da su ba. Wani irin dogon hanci ne lauyayye da shi bakin kuwa wangameme ga wasu hakora sun zuro daga ciki jini na zuba idanunsu kuwa jawur gasu da girma. Abun dai baya lissafuwa. ". Nace wayyo Allah na, basu kashe ta badai ko?". Tayi dariyar nan wacce tafi haushin kare ban tsoro hade da cewa "Ai tana ganin haka sai jikinta ya hau rawa ta koma daki a guje. Tana zuwa dakin ta iske wannan halittun a kan gado kusa da yaranta a kwance a nan wajen ta sulale kasa sumammiya. Lokacin da mijinta ya dawo ya tayarda ita kuwa ta hau rikici tace wallahi bazata kwana a gidan ba ta tashi. Ai kuwa haka akayi tun a daren ta kwashe yaranta suka bar gidan da safe sai canza gida mijinta yayi har yau bata ko yarda ta biyo ta nan kofar gida". Na sauke ajiyar zuciya hade da cewa "To ke kuma fa Inna Indo fatalwar bata taba tsorata ki bane halan". Tayi murmushi wanda ya karawa fuskar tata ban tsoro tace..................................
Zanci gaba
https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/
↫ NI DA FATALWA! ↬
{gajeran labari}
Part {5}
@KINGBOY ISAH
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
(KU CI GABA DA HAKUR DA NI DAI. KUNSAN WAYATA BATA AMFANI SAI IN AKWAI NEPA. JIYA KUMA BA NEPA SHIYASA KUKA JINI SHIRU Autan writers ne)
Hade da cewa "Innah Indo ke kuma fa Fatalwar bata taba tsorata ki bane halan". Ta yi murmushi wanda ya fito da jajayen hakoranta waje, Fuskar ta wani yamutse abun tsoro sannan tace "Watarana ina zaune a tsakar gida bayan isha'i na gama tuwo na da miya ina jiran mai gidana kurum sai ji nayi an yi sallama. Lokacin na dai ji ana cewa akwai fatalwa a nan amma ban taba ganinta ba hakan ne ma yasa bani da tsoro a sannan. Na amsa sallama. amma sai naji shiru ba a shigo ba.Aka kara sallama na kara amsawa ba a shigo ba sai da akayi sau biyar ina tambaya wacece amma ba cikakkiyar amsa sai dai naji ance ni ce. hakan tasa na mike hade da daukar torchlight dita na nufi zaure na hahaska ko ina amma banga kowa ba har kofar gida na haska banga kowa ba. Kawai ina komawa sai naga wani abu fari kamar mutum a zaune wajen da na taso. Nan take jikina ya fara karkarwa domin nasan ba kowa a gidan kuma yanzu na ta so, Hakan tasa na bude baki a hankali nace "Mine ne a nan?". Sai ji nayi anyi wata yar guntuwar dariya. Na kara cewa miye a nan?. Sai gani nayi abu ya mike sama wai ashe fatalwar ce. Na juya a guje na shiga makwabta. Ina zuwa zauren gidan ta mukayi karo da ita itama ta fito a guje wai fatalwa ta je ta kwanta mata a kan gado. Ba shiri muka fito a guje. A ranar dai ba irin wahalar da fatalwar nan bata bamu ba tsoro kuwa har suma sai da nayi. Bayan wannan ma cikin dare in na fito fitsari na sha ganinta da fararren kaya a zaune ko a tsaye a tsakar gida. Ranar nan munje gidan biki mukayo dare wajen karfe sha daya muka taho ni da Makwabciyata muna tafe a kasai tsoro ya cika mu sai sauri muke a saitin makabartar nan a muka ga fatalwar da bakar doguwar riga abun tsoron babu kai a jikinta. Muka kara sauri ni kam dan tsoro kamar in tashi sama. lokacin fa ban tsufa sosai ba. Kawai sai ji mukayi fatalwar nan tace kai ku zo nan". Cikin duhun dare ai kuwa sai muka zabura da gudun bala'i ai kuwa fatalwar nan ta biyo mu. babu kai a jikinta tana kiran mu tana dariya". Wani motsi naji a bayana ai kuwa na daka tsalle hade da kwada ihu. domin nayi matukar tsorata. Inna Indo ta bushe da dariya ni kuwa ido wuri-wuri na kama kallonta. ji nayi tace naje na dan debo mata ruwa. nace to abun mamkin kafin naje kitchen na daukko mata ruwan ina zuwa sai tararwa nayi falon wayam. na leka waje naga gida a rufe. a guje na koma daki na kulle. Wayata na dauka na kira Aunty Hauwa duka daya ta dauka. "Hello lafiya dai Khadija ya naji kina huci? ko fatalwar ce?". Nace "Eh wallahi wata mata ce take zuwa gidana mai wani hijab fari dogo. in kin ganta abun tsoro ni wallahi inaga ma itae fatalwar saboda fa sai na kulle gida amma sai kawai na ganta a cikin gida, Kuma in ta zo ba labaran da take bani sai na fatalwa wallahi na fara gajiya". "Shegiya mahaukaciya maza dai ki tsaya a gidan nan naki fatalwa ta kashe ki. Ai ni wallahi ko a mafarki naga na sake bin hanyar gidan ki sai na tashi na yi addu'o'i da nafiloli. Wai ke me yasa ba zaki dawo gida bane? Ya zaki tsaya gida sai ke da Fatalwa". Nace "Aunty Hauwa ke kanki kinsan halin Abban mu wallahi in na zo gida a kan wannan dalilin dan banzan duka zai yi mun kuma ya koro ni. Gashi shi kuma Habib yaki fahimta ta ni wallahi addu'ah nake ma Allah yasa shima fatalwar nan ta tsorata shi nasan a lokacin zai gaskata ni". Karan kwankwasa gida naji da karfi hakan yasa na mike a firgice. daga can Aunty Hauwa tace "Miye akayi". Nace "Wallahi gida naji ana bugawa watakil ma fatalwar ce". Dull sai ji nayi wayar ta katse. Na sake kira na dauka network ne ke rawa wai ashe Jin nace ana knocking watakil ma fatalwa ce yasa auntu Hauwa ta kashe wayanta. A hankali na fito daga falo bayan na gama leke-leke kamar marar gaskiya. A lokacin dan kwakkwaran motsi zanji kawai in ara a na kare. daga bakin kofa na fara fadin "Waye? Waye?" Shiru naji ba ayi magana ba an kuma kara kwankwasa gidan. A zuciya nace yau na shiga uku wai ni me nayi wa fatalwr nan ne da bazata bar ni in zauna lafiya ba?". "Waye ne?". Na kara fada da karfi cikin fada naji Habib yace "Dallah can sarkij tsoro ki zo ki bude gida waye zai zo yanzu in ba ni ba?". Shima a tsorace na karasa a hankali na bude sai da na leka naga shin sannan na bude sauran kubobin. Dariya yayi hade da cewa "To sarkin tsoro ni wani abu na manta na zo dauka"? Nayi murmushi hade da cewa "Ba zaka gane bane habib sai ranar da fatalwar nan ta makure ka". Yayi murmushi hade da cewa "Malama ba wani fatalwa kawai dai tsoro ne irin naku in ma fatalwar ce ai ina da addu'ah". A zuciya nace "Baka san lokacin da abun tsoron ya zo ji zakayi kamar an mantar da kai duk addu'o'in ba kenan. In takaice muku labari sati daya nayi a gidan Habib cikin tsoro da fargaba wataran kullum kuma Innaa Indo sai ta zo gidan nan haka kuma kullum da kalar salon labarin tsoron da take zuwa da shi. Tsakar dare kuwa daga inga fatalwa a tsaye sai inga Fatalwa kusa dani a kwance. mafarkai kuwa gasu nan barkatai ba irin wanda banayi. na taba yin mafarkin munje cikin makabarta ni da Inna Indo wai tace in shiga cikin kabarinta ni kuwa naki shiga kawai sai ji nayi an tura ni ciki da karfi. Ni tsoro ba irin wanda ba a bani ba. Wataran inga bakar mage da jan ido tana kukan gadawaa wataran inga mage na tafiya ba kai. Yau ma kamar kullum Inna Indo ta zo ta gama zazzaga labaranta na abun tsoro ta tashi ta tafi. Ina zaune a Falo naji shigowar waya kawayena ne su uku suka ce gasu nan zuwa zasu kawo min ziyara ne.................
Hhhhh yan kawo ziyara, Allah yasa dai ku fice lafita.lol
https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/
↫ NI DA FATALWA! ↬
{gajeran labari}
Part {8}
@KINGBOY ISAH
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_GABA DAYA PAGE NAKU KYAUTA NA BAKU. INNA INDO ZATA ZO TAYA KU MURNA.LOL_
*✧✦✩UMMIEY ZEE✩✦✧*
*✧✦✩AUNTY ASY INDIMI ✩✦✧*
___________________________
Yanayin dariyar da take yayi matukar firgita ni bansan lokacin da n fara karkarwa ba bakina na rawa na fara ja da baya ina cewa. "Inna Indo dan Allah kiyi hakuri ki yafe mun". Wata gigitacciyar dariya ta daga kai sama tanayi jini ya fara zuba daga cikin idanunta. yayin da ni kuma naje karshen bango a lokacin da nake ja da baya din. Sai ji nayi ta daka mun tsawq duk falon ya dauka
nan take sai gani nayi ta zama hayaki al'amarin da ya kara rudani kenan, hayakin nan ya baje a tsorace na tashi na fara kokarin bude kofar falo domin dawowa tayi ta rufe da karfi. Ina cikin jan kofar da nufin in bude in gudu sai ji naji an kyalkyalewa da dariya na juyo amm banga ta ina ake dariyan ba domin ko'ina a cikin falon amsawa yake sama kasa da ma ko'ina Tsulum sai ganin Inna Indo nayi a sama kan iska kusa da fankar dake sama, cikin wata irin bakar riga mai baza hayaki na fita a karkashinta. gashin kanta ma ya mike tsaye wani irin bakin hayaki ke fita a ciki. Fuskar ta bakyan gani abun tsoro domin idanunta jawur suke kamar danja haka suke fito da wani haske ja. Hakoran ta kuwa sun kara tsayi da tsini gasu suma bakakke fuskar ta jagule ta zama abun tsoro. Magana ta fara da wata irin murya mai tsananin kara da ban tsoro "Hahahahaha Tabbas kin aikata babban kuskure Khadija da kikayi kokarin kona ni Indo Fatalwa. Kin aikata zunubin da ba zan taba raga miki ba bazan kuma taba ragawa duk wani wanda yace zai zauna a gidan nan ba". Cikin firgin ina kukan tsoro sai karkawa nake nace "Dan Allah Inna Indo ki yafe mun zan bar miki gidan yanzu". "Hahahaha kinyi kadan domin nan gida na ne dama baki isa ki fita a cikinsa ba yau sai na kashe ki. A nan aka binne gawata sadda na mutu ana cikin haka kuka zo kuka gina gida a wajen kabarina. Da kun samu ina raga muku shine har kika sama damar yunkurin kashe ni? hahahaha ko kin manta dama can ni matatta ce? Kin taba ganin gawa ta mutu? to bazan mutu ba. kuma daga yanzu ba wanda ya isa ya kara zama a cikin gidan nan ko na minti biyar gida ya zama mallaki na. don haka yanzu zan hallaka ki kamar yanda kikayi yunkurin hallakani". Tana fadar haka sai kawai gani nayi ta bace tsulum ta bayyana a gabana da hannu daya ta shake mun wuya ta daga ni sama a haka, harbe harbe na fara ina buge bug hannuwan n kokarin banbare hannunta daga wuyana amm ina kamar karfe hannun nata. In banda wata mahaukaciyar dariya ba abunda take. ni kuwa tuni lumfashina ya fara kokarin daukewa. A zuciya na yanke shawarr yin kalmar shahada domin dai yau na tabbata kwana na y kare. Nan take na fara karanto kalmar shahada tun sannan naji Inna Indo ta kwalla uban ihu. Ta kalle ni hade da kara zazzare mun jajayen idanunta. "Kiii... daki.... na... kar.. karatun... nan". Haka ta fada cikin in ina tana kara shake wuyana ni kuwa tuni idanuna sunyi jawur lumfashi ya fara daukwa. Nan take na tuno ayyutul kursiyyo. Ina fara karantawa sai ji nayi Inna Indo ta kwalla gigitaccen ihu ba shiri ta sake ni ta fadi kasa. Ina ganin hka cikin juriya da karfin hali na juya na bude kofa falo na fito a million har sannan da karfi nake karanta ayyatul kursiyyu. Na jigata sosai amma ganin na fito daga wannan gida baisa na fasa gudu ba. kafafuna ba takalmi ko dan kwali babu shi a kaina balle hijab. Ko da naga nazo saitin makabarta sai na kara kaimi wajn karatun kamar dalibar da aka karawa karatu take yi dan karta manta.
Ina karasawa bakin titi Allah ya taimake ni wani mai napep ya kawo kai na tsaida shi tun kafin ya karasa tsayawa na hau da sauri ina cewa muje muje. shima dai ya fahimci ba lafiya ba saboda irin figar napep din da yayi a guje. Muna cikin tafiya yace "Hajiya ina za'a kai ki? Da alama dai ba lafiya ba?". nace muje tawalala zaka kai ni. har a lokacin lekowa nake baya dan kar inje Inna Indo ta biyo mu. Muna karasawa tawalala a kofar gida ya faka a guje na fito na fada gida. Umma na zaune a bakin kitchen Aunty Hauwa kuma na cikin kitchen tana juya abinci. Ita ta fara ganina na shigo a guje na fada daki. Haba ai itama ihu ta kwala ta wullar da ludayin hannun ta ta fito dag kitchen din a guje kadan ta hana ta bige Umma dake zaune. Ina ban tsaya falo ba na tsallake sai dakin umm can kuryan gado na haye naja blanket na shiga. Aunty Hauwa ma na ihu ta fado ta shige cikin bargon. Banda haki ba abund nake. Umma ta fado dakin a rude "Kai miye wai? Khadija Lafiya". "Indo Fatalwa, Indo Fatalwa zata kashe ni Umma". Tambya take amma banda haka ba abunda nake cewa. kuma ban yarda na fito daga bargo ba. Aunty Hauwa kuw kar kudundunewa take. Umma ta fara addu'ah tana tofa mun da kyau na dai-daita na dawo normal. ina ji mi napep ya aiko aka karba masa kudinsa. Zaune nake gefan gado Umma a gefan damana tana mun addu'ah Aunty Hauwa a gefan hagun wai itama addu'ah tak na kuwa tabbata banda miyau ba abunda take watsa mun domin kuwa itama a firgice take. Kuka na fashe da shi na kwashe labarin duk abunda ya faru na gayawa Umma. Umma ta tafa hannu hade da yin salati. Na kara da cewa wllahi bazan koma gidan nan ba. Umma ta goyi bayan haka sai dai dady na take ji. Nima shi nak ji domin mutum ne mai tsatsauran ra'ayi. Har dare ba wani bayni bana rabuwa da Umma duk inda tayi ina biye da ita ina kuma karanta Ayyatul Qursiyyu dan ba dan itab da yau an kashe ni. Ina jin shigowar dady amma naki yardq ya ganni. haka mukaita wasan buya Umma ma bata gaya masa ba domin zai iya cewa sai na koma gidan Habib.
Misalin karfe biyar na asuba na farka sakamakon mummunar mafarki da nayi wai ga Inna Indo nan zata kashe ni ni da Habib. A gigice na tashi na yo falo a nan fa mukayi kicibus da Dady ya fito zai tafi masallaci. Salati yayi sannan ya kwalawa Umma mu kira. Tana fitowa yace "Me wannan ta zo yi gida naga alama ma a nan ta kwana da izinin wa? Mijinta ne ya kawo ta?". Cikin tsoro nace "Aa dady gidan ne da mtsala fatalwa ce a gidan shiyasa gudu zata kashe...". Tass! naji saukar mari ba shiri na hadiye maganar da ban karasa ba. Marar hankali da tunani kin dauka aure wasa ne da zaki fito daga gidan miji har ki kwana a wani waje bai sani ba? Oya shige muje ko masallaci bazan je ba sai na maidaki gida tukun kuma wallahi ki kuka da kanki in har na iske ran Habib a bace"..................................
_Kutt! Khadija ana maidaki Inna Indo zata sheke ki. Ko dan ai yanzu kin tuno da addu'ah_
https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/
↫ NI DA FATALWA! ↬
{gajeran labari}
Part {9} *Last page*
@KINGBOY ISAH
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_GABA DAYA PAGE NAKU KYAUTA NA BAKU. INNA INDO ZATA ZO TAYA KU MURNA.LOL_
*♡❥❥PHATEEMA ALIYU♡♡*
*♡❥❥AUNTY ZEETY♡♡*
_____________________________
Kuka na farayi ina rokon Abba yayi hakuri ya bar ni. Haka itama Umman mu tana masa magana amma kunnuwan shi kamar an toshe. Ya kama hannuna har cikin motar sa dake waje dama nan take kwana. Muna shiga yaja motar yayi gaba, Titin fayau mutane jefi jefi suke tucewa masu zuwa masallaci. Cikin dan kankanin lokaci sai gamu a kofar gida. A matukar tsorace nake har lokacin ban daina kuka ba domin nasan ba makawa Inna Indo ba zata kyale ni ba. Addu'ah na farayi yayin da dadi ya fara kwankwasa gida ya dan dade yanayi yaji shuru yana dan tura kyauren sai yaga ya bude ba a kulle yake ba. Bugon zuciyata ya karu tuni nq fara karkarwq a lokacin da Abban mu yace in shiga. Ayyatul kursiyyu na fara karantawa sannan na dan sama kwarin gwiwar shiga. Cikin sanda kamar barauniya haka nake tafe Abba na bina a baya. har muka isa falo. Abba yayi sallama kusan biyar amma ba muji an amsa ba. hakan tasa yace in je inga ko Habib din barci yake in taso shi. Tsuru nayi ina kallon dakin ina kallan dadi yayin da na fara in ina ina shirin yin kuka domin tsoron shiga nake. Sai da Abba ya daka mun tsawa sannan naci gaba da karatu na nufi dakin kirjina na dukan tara tara. tsoro ya dabai baye ni. Rufe idanuna nayi domin kar in bude dakin inga Inna Indo hankali na dora hannuna jikin kofar na murda a hade da tura kofar jin shiru yasa na bude idona ihu na kwalla da karfi na fara kiran Abba domin abunda na gani yayi matukar girgiza ni. Habib ne kwace cikin jini kamar matacce kanshi jini ke zuba haka jikinsa duk raunuka ne. Cikin hanzari Abba ya karaso da sauri ya karasa wajen shi. Kara kunnensa yayi a kirjin Habib din yaji zuciyarsa na bugawa. da sauri ya cicibe sa yayo waje ni kuwa banda ihu ba abunda nake zundumawa na bi bayan Abba. Ni na bude bayan motar ya saka shi sannan na shiga, cikin hanzari ya figi motar sai General hospital A nan Habib yake aiki Muna zuwa akayi gagawar yi da shi Emergency shi.Nan na durkushe a kofar banda kuka ba abunda nake. Abba kuwa ya rasa me ma zaiyi, Sai sintiri yake a kofar wajen da aka shiga da Habib din. Likitoci kuwa sai kai komo suke domin wasu duk abokan shi ne na aiki. Wajejen karfe shida da rabi wani dan gajeran doctor ya fito. Ni da Abba mukayi saurin tarbarsa dan jin ya jikin Habib. Ajiyar zuciya yayi sanan yace "To Alhamdulillah a gaskiya da ace kun yi jinkiri wajen kawo Dr Habib da an rasa shi. Amma yanzu masha Allah mun yi masa aiki in sha Allah ba wata matsala babban ciwon da yaji a kai ne sai dai anci sa'a abun bai taba kwakwalwarsa ba". Cikin kuka nace "Dan Allah ina so in ganshi". Dr din yace a yanzu ba halin ganin shi domin har yanzu akwai sauran likitoci a kanshi
sai nan da wani lokaci sannan. Ni da Abba mukayi sallah sannan ya kira Abban su Habib ya shaida masa suzo asbiti ba lafiya". Cikin kankanin lokaci sai gasu sun karaso a firgice Abban Habib sai Mamanshi da kuma Ibrahim kaninsa. Abban Habib ya fara tambayar Abban mu lafiya kuwa?. Abban mu ya kwashe duk abunda ya faru ya gaya masa.Da jin haka Umman Habib ta hau kuka. tana leka ciki inda Habib yake. Abban mu ya kira gida ya fadawa Umman mu sannan yace ta taho mana da kayan kari nan asibitin. Bayan mun kakarya har lokacin ba abada damar shiga wajen Habib ba. Ina jin su Umma suna hira wai a zargin su Yan fashine suka wa Habib haka.Ni kuwa ban kawo kowa a zuciya ta ba sai Inna Indo domin na tabbata ikirarin da tayi ba karya bane don nima kadan ta hana ta hallaka ni. Wajejen karfe biyu da rabi likitocin suka bada damar shiga. Muka shiga kowa kuka yake ganin irin mawuyacin halin da Habib yake ciki. Har lokacin bai farka ba balle mu san me ya faru da shi. A takaice Habib bai farka ba sai bayan kwana uku da faruwar abun. Ina zaune a gefansa Umman sa da Bintu kanwar shi suna zaune a kujeru banda tagumi ba abunda mukayi. "Wayyo Allah fatalwa". Abunda ya fara tashi da shi kenan. a gigice. ganin yana neman zare karin ruwan dake hannunsa yasa na fita a guje na kira wo doctor. har lokacin da na dawo ihu yake yana fadin fatalwa tayi hakuri karta kashe shi. Abun ya daure wa su Umma kai amma banda ni domin ni nasan komai. Allurar bacci akayi masa ba wuya ya koma barci doctor yace Insha Allah nan da awa biyu zai tashi. kuma zai farka ne cikin natsuwa. Sai a lokacin muka dan kwantar da hankali. Umma ta kira Abban shi ta gaya masa ya farka haka nima na kira gida na fada musu ance nan da awa biyu Habib zai farka. Kafin lokacin tuni Family din biyu an hallara. Kamar yanda doctor ya fada awa biyu na cika Habib ya fara bude ido a hankali. Sannan ya yunkurq a gajiya ya tashi zaune. yayin da su Abba suke taimaka masa. Waige-waige ya hau yi yana cewa bata nan karfa ta zo ta kashe ni". Abban shi yace "Wace ce kuma zata kashe ka din". Habib yace "Indo Fatalwa mana dan Allah kar ku bari ta zo". Abban mu yace "Fatalwa kuma? Habib lafiyan ka kuwa". Yace "Eh Abba a hayyacina nake da idona na ganta duk ciwukan jikina ita taji mun wallahi bata da imani". Kallon kallo mutanen wajen aka shiga yi kafin Habib ya fara bada labari yace........,..............
Koma dai me yace ni kam na gaji yaseen a nan zan tsaya. Tunda Habib aka sambada bani ba.lol
https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/
↫ NI DA FATALWA! ↬
{gajeran labari}
Part {10} *The end*
@KINGBOY ISAH
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
♥♡❥ ALFAHARI DAKU NAKE MASOYAN LITTAFAINA A DUK INDA KUKE. NA GAIDA MASOYAN ALJANA KURIYYA DA KANWARTA MARIYYA NA LITTAFIN MIJIN ALJANA. DA KUMA MASOYAN ALJANA SAFURATU TA LITTAFINA ALJANAR FATIMA. BAN MANTA DAKU BA MASOYAN SMASHER NA LABARIN ALJANA CE. GA KUMA MASOYAN FATALWA INNA INDO GAISUWA NAKE. KU KASANCE DA NAKU KING BOY ISAH MAI GURIN NISHADANTARWA FADAKARWA AND WA`AZANTAR DA KU A KO DA YAUSHE.❥♡♥
Habib ya fara da cewa. "Karfe shida da rabi na dawo daga wajen aiki. Abun mamaki ina zuwa kofar gida sai naga gidan a bude. bayan kuwa nasan Khadija da tsoro ba zata iya barin gida a bude ba. Bayan na saka mota cikin gida sai na shiga falo inata sallama amma shiru ba khadija. Hakan yasa na shiga cikin daki a zatona ko tana ciki ne amma sai ban ganta ba. Na tura ban daki naga nan ma a bud bata nan. Nan take zuciyata ta hau suya. Wato khadija har tana da ikon fita daga gidan nan ba tare da izinina ba? Lalai zata dawo ta same ni. A zuciya na fadi haka cike da kunar rai. Na ajiye jakar dake hannuna bayan nayi wanka na dawo falo Abun haushi har lokacin Khadija bata dawo ba dare kuma ya farari domin bakwai da rabi. Na fiddo wayata na kira number khadija amma sai ji nayi waya tayi ringing a kusa dani wato a nan ta bar wayar. na dauka hade da yin tsaki a zuciya nace yaushe Khadija ta fara bin gidaje yawo gashj har dare yayi bata dawo ba? Ni a zatona batayi nisa ba tundq ta bar gida a bude kuma ga wayarta ma a gida. Haushi da takaici suka ishe ni jira nake kawai Khadija ta dawo domin ta karbi hukunci. Dan kwanciyar da nayi ne barci yayi gaba dani. Ina fara barcin nan Kuwa na fara mafarka na abu tsoro kala kala. Ji nayi ana daddabata ana kiran sunana alamun tashina ake daga barci. Bude ido da zanyi sai ganin wata mumunar fuska nayi mai ban tsoro wata mace mai sanyi da bakakke kaya doguwar riga. hakan yasa na kwalla ihu kafin in tashi zaune na nema matar sama da kasa na rasa. Lokacin na lura da an kawo wuta. Kirjina yana bugawa domin na tsorata sai dai ina tantama matar nan a mafarki ne na ganta ko a farke. lokacin na kara kiran khadija amma sai ji nayi shiru kamar maye yaci shirwa. Na lashe wayata karfe tara da rabi. nan take haushi yq kara rufe ni. wato Khadija bata dawo ba har yanzu
Tashi nayi naje kitchen na dakko bredi da juice na zo na kunna kallo na fara ci. Ana cikin haka naji an bude kofar kitchen da karfi ina waigawa naga wani bakin abu ya shiga kitchen din a guje ya rufe kofar. Cikin gaggawa na tashi na bude kitchen din na leka ko'inq Amma banga kowa ba. Na fito yayin da na dawo sai gani nayi babu biredin da nake ci juice din dake cikin jug ma babu an dauke sannan na duba ni da nake kallon MBC 2 sai gani nayi an maida ni mbc Bollywood abun ya ban mamaki sosai. zaunawa nayi naci gaba da kallo ko minti biyu ba ayi da zamana ba naji ana kwankwasa gida da karfi. tun daga falo na fara fadin waye? waye jira a bude ma?. Ina zuwa na bude sai gani nayi wajen wayam ba kowa. Ana cikin haka naga wani abu baki kamar doki ya nufo ni a guje. ba shiri na mayar da gidan na kulle na koma ciki a razani. Naje wucewa kawai naji an tada mota ta ina lekawa naga wani a ciki na dauka barawo ne hakan yasa na dauki wani icce dake kusa dani kafin in zagaya na bude motar sai gani nayi ba kowa kuma motar ta kashe kanta. Ana cikin haka sai ji nayi an kure volume kallo da nake yi a falo da gudu na karasa ciki amma sai banga kowa ba. Na dauki remote na rage. Lokacin fa abun ya fara bani tsoro. Ina cikin kallo naji an dungure ni ta baya na juya da sauri banga kowa ba. Nan take kuma sai naji wani iska mai karfi ya shigo cikin falon ina jiyawa naga fankoki ne suke gudu kamar zasu cire. na tashi a rikice nakashe su. Kukan dan jariri naji a cikin dakin da muke kwana tsoro ya fara ziyarta ta a lokacin a hankali na nufi dakin ina lekawa naji shiru jaririn ya daina kukan. Kai in takaice muku labari ban sama hutu ba har wajen karfe dayan dare abubuwa ne suke faruwa na ban tsoro makamantan wannan. karfe biyun dare ina zaune a falo domin sam na kqsayin barci har kwantawa nayi amma sai naji ana kirqn sunana a falo. na fito kumq banga kowa ba. Ina zaune sai gani nayi kofar falo ta bude wani iska mai karfi ya shigo isakan ya farq rikita abubuwan daki marar nauyi irin su labulaye da sauran su. kujerar dake saitin kofa naga ta matsa da kanta kamar an ture ta. yayin da naga tayas din wajen ya fara banbarewa. bayan ya gama fashewq can sai gani nayi an zuro hannu ya hudo ta karkashin kasa. Tuni tsoro ya kamani na fara karkarwa. dayan hannun ya karq hudo kasa ya fito hannu ne mai dogayen yatsotsi gq farcina dogaye suma can jimawq sai gani nayi kan mace ya hudo mai matukar ban tsoro. Idonta daya ya kwakware gefan fuskar ya rube wasu irin tsutsotsi na yawo. Hakoran kuwa bakikirin sai wani abu yake zuba daga cikin bakin. Nan take matr nan ta kaure da wata irin dariya mai firgitarwa wanda gaba dayan dakin ne ke amsawa. Ni kam tuni na fara karkarwa sai dai kuma kamar an rufe bakina nq kasa yin addu'ah kuma na kasa tashi in gudu. Sai dq matar nan ta gama fitowa daga cikin kasa gaba daya sannan ta mike tsaye ta dage kai sama ta kyalekyale da dariya cikin muryarta marar dadi ta fara magana.
"Kai Habib ka sani kayi kuskuren kama gidan nan gidan haya domin yau matar ka ta jawo ma silar ajalinka. Ni ce nan *Fatalwa Aisha Indo* kuma nan gida nan ne. Ba wanda ya isa ya zauna a cikinsa. Yau matar ka khadija tayi yunkurin kashe ni sannan ta gudu. Na bita domin in kashe ta amma sai dai gidan da ta shiga akwai tsari shiyasa ban shiga ba. Tunda kuwa nayi alkawari bazan karya ba yau sai na kashe ka". Tana fadar haka ta bushe da dariya Na mike cikin karfin hali nace "Karya kike shedaniyar aljana ki sani kinyi kadan kuma baki isa ki kashe ni ba. Sannan yanzu...". Kafin in rufe baki sai gani nayi kan Indo yayi jawur alamun taji haushi tayi nuni dani da hannunta nan take wani haske ya fito ya dauke ni ya rada da kasa. Kafin in mike ta sake daga ni da asiri irin nasu aljannu ta kama wulwulawa dani tana dakani jikin bango. Ana cikin haka ne na ruga da gudu daki na samu sa'ah na rufe dakin. ina tunanin na tsirq amma sai gani nayi ta ratso ta cikin bango. Nan take taci gaba da wahaltar da ni har wajen karfe hudun dare. Sai sannan na samu na fara addu'ah da kuwa kamar bakina ya kulle na kasa addu'ah. Har tayi mun jina jina. Tana ji na fara addu'ah sai ta fara wani irin ihu ta farq daukana tanq bugawa da kasa. Tana cewa in daina addu'ah Amma naki a haka ne ta sa wani irin haske ya daga ni sama na rabu da kasa. Lokacin kuw na karanta ayatul kursiyyu da la'ilafi na tofa mata. Sai ji nayi t saki ihu wuta ta kamata sai ci take da wuta. Ni kuma ta sake ni a lokacin ne na fado kasa kaina ya fashe ban sake sanin a ina nake ba sai yau da na farka nq ganni a nan asbitin". Kowa na cikin hospital din yayi tsananin mamaki. nan take aka kama yi mana barka ni da Habib. Abba yace inyi hakuri da rashin fahimta ta da yayi. Nace ba komai Abba. Bayan sati guda Aka sallami Habib daga Asibiti domin yaji sauki sosai. Muna komawa gida yasa akaje aka kwaso duk kayana dake wancan gidan na fatalwa Habib yaje sukayi lissafi da mai gidan aka biyashi kudin wata goma domain bqmuyi wata biyu a gidan ba.
Da ya tashi kama mana gida sai da ya nema na tsakar gari sannan shima sai da ya tabbatar nan kusa da mu bq makabarta. Watarana muna hira nace "Habib ya labarin Inna Indo fatalwa shin ta mutu ne dq wutar ta kamata ko kuwa?". Harare ya watso min yace "please karki sake tuno min da wannan Indo fatalwa din". Da jin haka na bushe da dariya......
TAMMAT BI HAMDULILLAH..
A NAN NA KAWO KARSHEN LITTAFIN NI DA FATALWA. KUNJE YADDA TA KASANCE TSAKANIN INDO FATALWA DA KHADIJA AMARYA. ABUN TAMBAYAR A NAN SHIN INDO FATALWA TA MUTU NE TA BAR GIDAN KO KUWA TANA NAN? NI DAI BAN SANI BA AMMA DAI GIDAN YANA NAN WANDA YAKE SO ZAI YI SABON AURE ZAN MAI JAGORA HAR GUN KAI GIDAN DOMIN YA KAMA HAYA. KUNGA SHI ZAI GAYA MANA INNA INDO NA NAN KO KUWA.LOL
MASU JIRAN *FESHIN JINI* DA *NI DA YAYA SAIFI* IN SHA ALLAH BAZAN SAKE WANI NOVEL DIN BA SU ZANCI GABA DAYI TUNDA YANZU NA SAMA YAR AKWALAR WAYATA. LOL
MASU SAN FESHIN JINI KO NI DA YAYA SAIFI DAGA FARKO ZAKU IYA BIYO NI TA WHATSAPP DOMIN IN TURO MUKU AMMA DOCUMENTS NE. GA NUMBER WHATAAPP DINA 08096831009. AUTAN MARUBUTA NAKU KING BOY KECEWA A HUTA LAFIYA
https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/