YAR MAFIYA 1 TO END Complete Hausa Novel

YAR MAFIYA   1 to end



👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*



  ☠☠☠☠☠☠
        'YAR MAFIYA
            ☠☠☠☠☠☠
     _Gajeren labari_

 *Part 1-5*


© 🤴🏻 *KING BOY ISAH*  ✍🏼


 *Bissmillahir rahmanur rahim*
Godiya ga Allah madaukakin sarki da ya bani lafiya kwanciyar hankali.


*Tsira da amincin Allah*
Su kara tabbata ga shugaban mu annabi Muhammad S.A.W


*NA SADAUKAR DA WANNAN GAJERAN LABARIN GA YAN GROUP DIN. (KING BOY ISAH NOVELS) INA MATUKAR JI DAKU INA ALFAHARI DAKU*




*KARSHEN PAGEN BAYA*

~......................~
_*L*abarin ya fara ranar wata laraba da yamma. Ranar ina cike da bacin rai sosai ba. Duk duniya tayi min kunci. Sosai nake nadamar auren tallaka a rayuwa ta.  Saboda tsabar talaucin mijina a gidan in nayi tuwo yau shi zamuci da da dare. Da rana kuma garin kwaki. Da dare ma tuwan jiya zamuci haka da safe. Kasancewar mu biyu ne kadai a gidan, Shekarar mu 4 Allah bai bamu haihuwa b Sau tari ina kai kara gidan mu, Daga naje sai su fara min wata nasiha dake shiga ta kunnen dama tana fita ta kunnen hagu. Ya kasance duk sanda nakai karar a kan talaucin mijina sai Mamar mu tace, "Me yasa baki da hakuri Nusaiba. Shin baku san arziki na wajen Allah bane? Haba  me yasa kike abu kamar marar ilimi? A rayuwa in kana duba na sama da kai bafa zaka taba gode wa Allah ba. Amma a duk sanda kayi duba i zuwa na kasa da kai, Zaka gode wa Allah. Allah nasan masu godiya a gare shi. Kuma yana kara musu. A duk lokacin da sukayi godiya a gare shi".  Duk sa'ilin da Mamar mu ta fadi haka ni kuwa sai ince "Mama har a kwai matalauta na kasa da mu? Karfa ki manta kwana biyu muke bamu dora tukunya ba. Kullum cikin zarya nake daga gidana zuwa shagon sai da garin kwaki". In mum taji haka sai tayi murmushi tace, "Nusaiba kenan. Safiya a duniya akwai wanda basa samun abincin Safe, Rana, Dare. Wasu suna cin na Safe da dare ne kawai su tsallake rana. Wasu kuma sukan ci da Safe da rana shikenan suyi hakuri kuma sai gobe.  Sannan kuma duk wannaj cin abincin da nake gaya miki ba lalai ne suna ci suna koshi ba. Nusaiba akwai garin da ake samun gidan da Ba a dora girki sai sati-sati._



 _Sai dai su sha fura safe rana dare. Nusaiba ki gode wa Allah da ya bawa mijin ki halin saya miki garin ma. Kuma ki roki Allah da ya karawa mijin ki arziki. Domin talauci da aziki ba mutumin da ke zuwq da su duniya. Kowa a duniya yake sama kuma ba wayo ke bada su ba. Ko mako, ko Dabara. Aa Allah shi yake bayarwa ga duk wanda yaga dama". Duk da nasan maganganun Mama gaskiya ne amma bani daukar ko daya a ciki. Dan ni babban gurina shine in auri hamshakin mai kudi in ringa watayawa da walwalata.  Amma ba talaka ba irin mai gidana. Ni dai in zanci mai kyau in sa mai kyau. In rike faskekiyar waya. A samo min yan aiki da driver to fa ni ban damu da taya aka samu kudin nan ba. Ni kam har kisa ina iyayi saboda kudi. Bansan wacce kaddarar ce ta hada ni aure da Malam bala ba.  Kamar kullum haka yauma ya miko min naira Arba'in da zai fita wai kudin abincin rana ne. Ban ko kalle shi ba. Ya dade yana miko min amma naki karba. Da ya gaji sai ya wullar da su a nan ya kama hanya ya wuce kasuwa wajen dakon shi. Daki na shiga na kwanta ina tunanin rayuwata. Ina ta sake-sake ina wassafa yanda rayuwata zata kasance da ace ina cikin dola. Ana cikin haka barci ya kwashe ni ban tashi ba sai bayan la'asar.  Ai kuwa na tashi da masifaffiyar yunwa. Har wani jiri nake ji yana debata domin rabona da abinci tun tuwan safe. Ina fitowa daga daki mukayi ido hudu da 40 din da mijina ya wullo min. Tsaki naja a zuciya nace "Yo me 40 naira zata wa mutum. Ni kam gaskiya na gaji da gari da sugar". Hayaniya naji a makwabtan mu. Hakan yasa na tuno da cewar ashe fa Maryam ta haihu yau da safe. Makwabciya ta. Ai kuwa na dauki gyale na yafa na fito zuwa gidan a tunanina baza a rasa abinci ba ko kunu.  Bayan na shiga mun gagaisa da mutane. Na shiga baza ido ko zan ga abinci. Abun haushi ko loma daya banga wulginta ba. Sai faman hira suke ba abunda yasha musu kai. Ji nayi yunwa na neman sabautani da sauri na baro gidan na zo na tsince 40 din na fito na jawo gidan da nufin zan je shago in sayo Gari da suga. Tafe nake cike da bacin rai duk duniya tayi min kunci. Saboda bakin talaucin da ya min kanta. Cik! Na tsaya ina duban kasa. Ina kara kurawa wajen ido. Murje idanuna nayi domin tantamar nake anya kuwa abunda suke nuna min gaske ne. Tabbas gaskiya ne naira duba ce sabuwa fal! A kasa. Wani farinciki da jin dadi ne suka ziyarci zuciyata lokaci guda. Ji nayi kamar an bani kyautar million. Nan da nan na fara sake-saken abunda zanyi da ita. Lokacin da na waiga hagun da dama naga ba mai kallona na duka na kai hannu da niyar in dauki dubun.Da kai hannuna na bace Bat! Sai tsintar kaina nayi a wani daki._




_Sama da kasa na kalle dakin ni kam a duk tsawan rayuwata ko dakunan kawayen na matan masu hannu da shuni da nake ziyarta ban taba shiga daki mai kyau irin wannan ba. Glof din dakin kadai bana kananun kudi bane. Sai kyalli yake. Tsoro ne ya lulube ni nan take na fara karkarwa. Gefena na kalla wasu mutanen ne mace biyu namiji daya. Dukkan su ba ramamme. Dan dayar macen ma naga kibarta har  tayi ovar. Hannun na dora a kai, cikin kukan da ba hawaye nace, "Wayyo Allah na na shiga uku ni Nusaiba. Dan Allah ina ne nan kuka kawo ni. Dan Allah ku mayar dani gida". Dariya namijin ya gagabe da ita, Daya daga cikin matan ta kalle ni tace, "Baiwar Allah nan gida ne da kullum sai yayi baki amma duk bakon da ya shigo baya fita. Nan gida ne wanda ran dan adam ba a bakin komai yake ba. Nan gidan ne da  suka dauki kashe mutum kamar kashe sauro ko cinnaka. Yar uwa nan gida ne da bana tunanin zaki taba kubucewa daga cikin sa.  Bari in fayyace miki nan dai GIDAN YAN MAFIYA NE".  Ra! Ras! Gabana ya fadi jikina ya dauki kyarma. Dan tsabar tsoro. Matar taci gaba da cewa. Kin ganmu nan da mu biyar ne, jiya da shekaran jiya aka yanka sauran. kiwan mu ake kamar dabbobi. Dukan mu lokacin da muka shigo gurin nan bamu kai haka kiba ba. Naman mutane shine abincin mu shi yake hura mu muke hawa haka  ba wuya". A tsorace nace "Naman mutun?, to Wallahi ni bazanci ba". Murmushi tayi tace....  ..   ................................._



😰

Autan writers ✍🏼🤴🏻









👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.


  ☠☠☠☠☠☠
        *'YAR MAFIYA*
            ☠☠☠☠☠☠
     _Gajeren labari_

 *Part 5-10*


© 🤴🏻 *KING BOY ISAH*  ✍🏼




.     ~KARSHEN PAGEN BAYA~  .
*Naman mutane shine abincin mu shi yake hura mu muke hawa haka  ba wuya". A tsorace nace "Naman mutun?, to Wallahi ni bazanci ba". Murmushi tayi tace.*

*T*ana murmushi tace, "Dole kuwa kici, domin akwai wanda muka iske a nan da yaki cin abincin haka suka kyale shi har ya mutu a nan basu bashi abinci ba balle ruwa. To bari kiji in gaya miki jini shine ruwan shan mu". Cikin razana nace "Na shiga uku, Jini fa kika ce". Matar tace "Tabbas jini kuma yau za a zo a dauki daya daga cikin mu a yanka. Shiyasa kike ganin mu duk a firgice, Dan bamu san wanda za a dauka ba a cikin mu". Kuka na fara ina fadin na shiga uku na lalace".

 Ba wanda ya sake kulani har na gaji da kuka na nayi shiru. Ana cikin haka mukaji karar murda kofa. Nan take muka mika hankulan mu kofa dan ganin wanda zai shigo.  Wasu murda-murdan gardawa ne suka shigo.karti ne madaka maza. Fuskarsu ba alamar murmushi balle kasa ran zai maka dariya. Bayan sun gama kare mana kallo suka nufi wajen matar nan mai kiba.


Da ganin haka ta fara kuka tana kara makalkalewa jikin dayar mai bani labarin nan. Basu wani jira ba suka sunkuce ta ta rike dayar matar da kyar aka kankare ta. Ita kanta dayar matar kuka take haka shima namijin kwalla ta cika mai ido duk a tsorace suke.

Ni dai kallan su kawai nake nima duk nabi na rude.  Bayan kartin nan sun fita da matar cikin kuka dayar ta dube ni tace,

"kinga fa yanda ake mana dauki ba dadi. Yanzu shikenan sun tafi da wannan yau ita zasu yanka".

Na kalle ta fuskata dauke da tsantsar mamaki.

"Yankawa fa kika ce".

Ta kara fashewa da kuka murya na sarkewa tace, "Ba yankawar ba kadai yau namanta shine abincin mu. Jininta shine ruwan shan mu. Haka gobe ma wani zasu zo su dauka a cikin mu".

Wani gumi naji ya karyo min lokaci guda naji ina karkarwa. A zuciya nake cewa. "Anya kuwa wannan da gaske take?"...

Ba wanda ya sake cewa komai a cikin mu. haka shiru ta ziyarci mu. Kusan awa guda kowa na ta sake-sake muna tuno irin rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki. Ni dai kam kwadayi na ya jawo min. Wasu zafafan hawaye suka kwaranyo daga cikin idona. Bude kofa akayi a karo na biyu, muka zura idanu dan ganin wake shigowa.


Wasu mata ne suka shigo guda biyu. Daya dauke da tray mai dauke da soyayyen nama. Daya kuma jog ne wanda nake tunanin ruwa ne a ciki ko lemu. A tsakiyar mu suka ajiye ba tare da sunwa ko mutum daya magana ba. Abunda na gani a tran ne yasa gabana yayi mummunan faduwa. Jikina ya fara makyar-kyata kamar mai jin sanyi. Kunnen mutum ne da yatsotsi na gani a soye rumus da wasu ma sassan jikin mutum. Wanna ya tabbatar min da cewa naman mutum ne. Ban karashe firgicewa ba sai da naga Dayar matar ta bude jog din ta fara tsiyaya jini a kofuna. Ashe ba abunda na tsammata bane. Wato ruwa ko lemo.

Cikin rudu na fara ja da baya in fadin...

"ku wanne irin marar imani ne. Yanzu da gaske yankata kukayi?.

Har sai da na karasa jikin bango na kankame jikina da sai rawa yake ganin jini da naman mutum a soye.  Bayan matar ta gama cika kofunan glass guda uku da jini. Sai ta mika wa kowa a cikin mu kofi daya. Ina ganin an miko min jini na kwalla ihu! Bansan lokacin da nasa kafa na shure kofin ba. Nan fa jinin ya fantsala duk ya bata wannan matan duk da bakakken kaya ne a jikinsu.



Hade fuska tayi sosai alamar ranta ya baci. Tana huci tayo kaina  sai da ta wanka min lafiyayyen mari tukun tace,

"Matsiyaciya kawai kin zubar da ruwan da zaki sha a yau. Kuma in bakici sa a ba gobe za a yanka ki". 


Da jin haka na fara karkarwa ina bata hakuri, Nace

"Dan Allah baiwar Allah ki taimake ni ki fitar dani a nan gidan. Wallahi tallahi bazan kara daukan kudi a kasa ba in na gani.. Dan Allah Wallahi mijina na can na jira na".


Kallona tayi ta kwashe da Dariyar mugunta tace,

"Nan gidan duk wanda ya shigo ya zama nama".

Nace..

"Dan Allah ki taimaka ki  kawo min abinci Wallahi yunwa nake ji..kuma ni bazan iya cin naman mutum dan uwana ba".

Bushe wa sukayi da dariya. Sun dade sunayi daga bisani dayar tace, "Naman mutune shine abincin ku in kinga dama kici, In bakiga dama ba karkici".
 Tana fadar haka suka juya suka fice.

  Ana cikin haka mukaga wasu yara biyu sun bullo ta cikin bango. Dayan sai kuka yake kasancewar  babba da karami ne. duk cikin su ba wanda yayi 10years. Tausayin ne ya kamani ganin yara kananu amma wai yanka su za ayi.  Zuwa can dare aka kara kawo wani abincin Again naman mutane ne da jini a kofuka. Nan aka rarabawa kowa har yaran suma dake suna jin yunwa suka karbi naman suka zakal-kala. Ni kuwa fur naki ci nace "Wallahi sai dai in yunwa ta kashe ni".  Wanda aka turo ya kawo mana abincin ne ya fita. Bai jima da fita ba kuma ya dawo ya kira ni. Wai inje mai gidansu na kira na. Jikina yana bari na tashi nabishi ina waiwayan baya. A zuciya nace watakil kallan bankwana nake musu. Tafe yake ina biye da shi, in ban manta ba sai da muka ratsa ta dakuna wanda ba komai a ciki kusan 20.


Kafin muka karasa wani katan falo. Mutane ne sanye da jajayen kaya, Sai wani guda daya mai sanye da bakakken kaya..wanda nake kyautata zatan cewa shine ogansu.
 sun kewaye wuta sai wani maganganu suke wanda bana fahimtar yaren. Fuskokin su duk sunyi wani irin zane da wani farin abu. Falon cike yake da kwarangwal, da kuma kawunan mutane wanda aka rartaya a sama.



Sosai na firgita da ganin haka. Gabansu aka ke ni na fuskanci mai gidan nasu. Sai lokacin na lura da idanunsu a rufe suke, Tsuro nayi ina sauraren ogan nasu jin ya dawo hausa, Idan ya fadi magana sai suma duk su maimaita. "Kudunbur!" Ya fada da karfi, yayin da suma sauran mutane sukace "Kudunbur!. Yaci gaba da cewa. "Munyi alkawarin zamu shayar dakai jini, mu kuwa muna bukatar kudi". Nan take suka mai-maita kamar yanda shima yayi. Ni dai ina nan nayi zuro ina kallo. "Zamu baka jarirai". Nan take suma suka fadi hakan.




"Kudunbur!. Kudunbur! Kudunbur!  Wajen ya kaurade da fadar sunan abun da nake kyautata zatan cewa Abun tsafin su ne. Shiru ce ta ziyarci wajen na wasu mintuna, daga bisani kuma mutumin dake sanye da kaya wanda zai kai kimanin shekara 50 ya bude idanun sa da suka yi jajur gasu kulu-kulu. Ni da farko har tsorata ni ma yayi. Cikin kakausar murya yace dani, "Ke ce mai taurin kai ko? Wato kinki cin abinci da rana haka yanzu ma kinki ci so kike ki mana asarar namanki da jinin ki ki mutu a banza ko?".



Jiki na rawa a tsorace nace da shi, "Dan Allah dan annabi kuyi min rai. Ni matar aure ce kuma ni ba mayya bace shiyasa banci naman mutum ba". Hhhhh ya kwashe da dariya daga bisani kuma ya murtuke fuska cikin tsawa yace, "Keeee! Ki daina kira mana Allah a wajen nan. Duk da kasancewar mu muslmai amma in muka shigo nan bama kiran Allah". Jin ya fadi haka da sauri na matse bakine. Ina mamakin jin yace wai su musulmai ne. Yaci gaba da cewa "To ki sani cewa duk wayan ki da dabarun ki bazaki kubuta daga hannun mu ba. Zabi biyu gare ki.  Na daya ki amince ki shigo kungiyar mu. Ko kuma yanzu a yanka ki a bawa Kudunbur jinin ki. A soye naman ki  a cinye".  Jin ya fadi a yanka ne ban ko san lokacin da bakina ya fadi cewa "Na amince zan shiga kungiyar ku" ba. Da jin haka suka kwashe da Dariya. "Kin kyautawa kanki Kuwa kuma kunyi ban kwana da talauci. In dai kudi ne har filo zaki iya yi da su. Kalli can". Ya nuna min wani bangare da yatsar sa. Dum! Gabana ya fadi kudi ne jibgi guda, yan dubu-dubu kamar wasu takardun banza. Nan take na gaskata maganganun mutumin. Ji nayi koma miye zan iyayi in dai za a bani kudi ni kam. 



"Duk tarin kudin can da kike gani da yawa. Zasu koma tankar kwandala a gurin ki in dai kikayi join namu". Cikin kaguwa nake fadar cewa "Ayi sauri a rantsar dani. A gagauta yallabai". Jikina har rawa yake naga kudi. Wani mutun ne ya taso hannunsa rike da wata hula baka mai walkiya. Yana zuwa ya zagayo ta bayana ya cire min dan kwali. Ko juyawa banyi ba ni dai, Hular ya dora min. Lokacin naji kaina na wani irin juyawa. Lokaci guda naji zuciyata ta kekashe. Ji nayi yanzu bani da imani ko kadan. Ji nayi a yanzu zan iya kashe mutum ba tare da fargaba ko tausayin sa ba.



Bayan kai na ya dan dai na juyawa ne aka miko min wata kwarya, jini ne a ciki aka ce insha. Nayi mamaki yanda na amsa kai tsaye na kafa kai sai da na shanye shi gaba daya. Raf! Raf! Raf! Mutanen wajen suka kama tafi. Ana tayani murna wai na shigo kungiya. Mutumin yayi dariya sannan yace, "Yanzu shikenan kin shigo kungiya. Dokokin kungiya uku ne. Na daya, in ka shiga kungiyar mu ba fita sai ranar mutuwa". Dum!  Naji gabana ya fadi.  "Na biyu duk wanda aka kama ya kwashi asirin kungiya ya fita da shi, shima a nan take zai mutu. Dodon mu ne Kudunbur zai shanye masa jini. Dan haka kisa wa bakin ki linzami. Na uku, Aikin ki shine sato mana jarirai duk sati jariri daya duk satin da baki kawo ba kuwa. Bazaki kara kwana a duniya ba".   Zuciyata ce ta harba sau uku da sauri. Ji nayi kaina na juyawa. Ni kuwa ko uban me yasa na amshi wannan tayin ma. Yanzu dai gashi na hallaka kai na.............................



King boy yace, San kudin ki ne ya kai ki ga hallaka.lol







👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

        *'YAR MAFIYA*
            ☠☠☠☠☠☠
     _Gajeren labari_

 *Part 10-15*

© 🤴🏻 *KING BOY ISAH*  ✍🏼


👨🏻‍💻 *NAYI MISTAKE PAGEN DA YA KAMATA NASA 5-10, SHINE NASA 10-15*


 _*DEDICATED TO KINGBOY ISAH NOVELS*_
👨🏻‍💻✍🏻
Ina ji daku 👌🏼 Ana mugun Jone 🤝





.     ~KARSHEN PAGEN BAYA~  .
~Bazaki kara kwana a duniya ba".   Zuciyata ce ta harba sau uku da sauri. Ji nayi kaina na juyawa. Ni kuwa ko uban me yasa na amshi wannan tayin ma. Yanzu dai gashi na hallaka kai na~

_"Toh kinji dokokin mu, sauran kinji a gaba".  Da ga mai kai kawai nayi, Alamun Eh  "Yau yaushe?"._

_Ya tambaya, lokacin da ya kwalalo min idanu.  "Laraba".  Na bashi amsa a takaice, "Ranar asabar zaki fara kawo jarirai". "To" na furta ba tare da wata fargaba ba. Yace, "Jiki ki deba kudi san ranki, kunyi bankwana da talauci". Tashi nayi na nufi wajen kudin ba tare da fargabar komai ba. Ban wani dauka da yawa ba gudun kar inyi zari mijina ya gano.  Bayan na dauka na dawo gaban mutumim. Wani kwando ya daga ya fiddo wata alewa (Sweet) ya miko min guda biyu. Bayan na karba nace "Wannan fa". Dan murmushi yayi kafin yace, "Bazaki taba iya fita daga gidan nan ba tare da kinsha wannan sweet din ba. Kasancewar ki bakuwa. Amma in kika yi nisa a cikin mu zaki iya fita da shigowa ba tare da ita ba. Kuma in kina so zaki iya gwada fita ba tare da kinsha ba ki gani".  Haka kawai naji ina san in gwada din. Juyawa nayi ina kare wa falon kallo, kofofi ne barkatai  can daga bangaren gabas na hangi wata makekiya na nufi ta  a zatona itace ta fitar. Ina bude kofar nayi sauri nayo baya. Saboda wani makeken rami da na gani marar iyakar zurfi. Suna ganin nayo baya dafe da kirji sai suka hau dariya. Bayan na dan dai-daita natsuwa ta sai kuma na sake nufar wata kofar. Lokacin da na bude sai naga hanya ce a mike doguwa duk kwayaye sun haske gun. A zatona nan ne hanyar juyowa nayi. Na masu murmushi tukun na shiga dakin na fara tafiya.  Dakuna ne gife hagun da dama kamar wani hotel. Sai da na wuce kusan biyar a na shidan na fara jin kukan jariri ban tsaya ba gaba kawai nayi. Ina zuwa saitin daki na takwas naji an kwalla iho ta gefan dama. Ihun mace ne mai karfi har sai da na razana na kulle kunne na.  Kunnuwana a toshe na wuce ba tare da na bude dakin naga mai ihun ba. Kafin in karasa daki na shabiyu naga wani abu mai kama da dodo ya fito daga dakin bangaren hagun ya shiga na dama da gudun._


 _Ai bansan lokacin da na kwalla ihu ba. Hannuna na karkarwa na fido alewar  da sawata baki nabace bat!  Sai gani a kofar gidan. Mamaki ya cika ni sosai lokacin da na juya na kalli gidan. Gidane da akayi shi tun baya da shekara uku. Amma mutane basu taba zama a cikin sa ba. Gidan ya tsaru sosai bene ne hawa biyu. Mutanen anguwar kansu suna fadar cewa tun da masu ginin suka gama suka kulle har yau ba a taba bude shi ba. Kuma a san mai shi. Nasan gidan sosai kasancewar layi biyu ne tsakanin mu da layin. Gidan na nufa ina tafe ina ta tune-tune ta wani bangaren ina tuna shikenan burina zai cika a rayuwa na zama malonia. Wani bangaren kuma tunanin ina zan samo jarirai nake. Wani mai doya da kwai na gani a hanya na ciri dubu cikin kudin da na daukko nace ya ban ta dari biyar. Da sauri ya amsa ya zubo min tili guda a leda. Ya kullo yaji daban a farar leda. Zai miko min canji nace ya rike kawai. Nakarbi doyar na kara gaba. Dan murmushin jin dadi nayi hade da cewa. "Haba yanzu ne lokacin jin dadi da more rayuwa. Yanzu sai ince abunda raina ke so. Inci insha in rike babbar waya ni da tuwo sai dai kallo, balle ma wani abu wai kwaki". Dariya nayi lokacin har ta  dan fito fili. Ina ganin gida a bude na tuno ashe lokacin da na tafi ban ko rufe shi ba. Ina shiga naga dakin da hasken fitila alamun mai gidana na ciki. Tsaye nayi a tsakar gida ina tunanin wace amsa zan bashi in yace dani daga ina nake. Na dade a wajen amma na kasa samo amsa guda. Kamar daga sama naji ance "Sai yanzu kikaga damar dawowa daga yawan naki?". Dum! Gabana ya fadi. Juyawa nayi na kalle saitin da maganar ta fito. Mai gidana ne rike da buta ya fito daga ban daki._


_Ta gabana ya zo ya wuce cike yake da bacin rai daga ka kalle shi zaka gane hakan ba sai an fada ma ba. Dan murmushi nayi a zuciya nace "Duk fushin nan nashi fa dubu biyar kacal ta isa ta bashi hakuri.  Kai kudi kenan shiyasa nake sanku. Zan kuma iya yin komai a kanku".  Kudin dake rike a hannuna na manna wa kiss tukun na zari dubu biyar na boye sauran a kirji wasu kuwa a habar zane. Dan dama ban debo wanda zasu fi karfina ba.  Da sallama cikin sasanyar murya na shiga dakin a bakin gado na iske mai gida na._


_Zaunawa nayi a ta gefan sa na dama na ajiye ledar doyara a gefe na. Ba tare da ya kalle ni ba yace, "Ki fara fada min daga ina kike tukun. Da kuma dalilin da yasa ki yin tuwo. Alhalin kuma kinsan yau ranar da zan ayi tuwo ne. Ki mun sahihin bayani, dan in  ban gamsu ba wallahi yau bazaki kwana a gidan nan ba".  Gabana ne ya fada lokaci guda naji na fara gumi. Dan murmushi nayi na mika mishi dubu biyar din hannuna. "Kudin miye ne wannan?". Ya tambaye ni yana kallan kudin ba tare da ya karba ba. Cikin murmushi nace, "Mai gida kai dai ka rike mana".  "Nusaiba ni fa bazan karbi kudin nan ba ba tare da nasan ko ba mine ne ba". Nace, "Mai gida bafa wani abu bane Hajiya Talatu ce ta dawo daga saudi arabia dazun nan suka sauka ita da mijin ta amma shi ya juya ya koma. Zata yan kwananaki ne taga yan uwa tukun su koma. Wannan kudin kuma cewa tayi na kawo ma a matsayin tsarabar ka kasan su yan gayu basu cika riko kaya da yawa ba".  Ni kai na bansan taya na kirkiro wannan karyar ba.  Nayi mamakin ganin mijina ya hauta ya zauna. Bayan ya karbi kudin ya tusa aljihh ne ya juyo yana mun dan murmushin jin dadi hade da cewa, "Kai amma fa naji dadin rashin sayo tsarabar nan. Ana samun dubu biyar a tsaraba ai wallahi ko gobe bazan yi fatan a sayo tsarabar ba". Dariya nayi nace, "Kai mai gida to kasan irin tsarabar da zasuyo ne. Watakil ai da suka sama damar yo tsarabar da sai ta baka mamaki. Domin fa mijin ta babban likita ne a can Saudi arabia din. Kai gaskiya tana cikin dolah". Tambayar da mai gida ya watso min ce tasa naji kamar komai ya rushe, cewa yayi_

_"Nusaiba wannan ita kuma wace ce. Ko 'yar uwar ku ce? Ni ban taba sanin ta bama". Sai da na tattara natsuwata tukun nace,  "Mai gida ai ba lalai kasan Talatu ba domin tun kafin mu fara soyayya da kai sukayi aure. Kuma mijin ya dauke ta suka tafi can sai bana suka dawo. Yar kawuna ce".  Gudun kar ya kara jefo wata tambayar, yasa na jawo ledar doya nace.  "Mai gida kaga harda doya tasa aka sayo mana yau dai ba cin tuwo". Dariya yayi yace, "Kai amma wannan mata Allah ya saka mata da alheri".  Murmushi nayi hade da cewq amin. A zuciya nace, "Lalai wannan ya kamu".  Doyar mukaci muka koshi har mukayi saura. Bayan yayi sallah nima nayi tawa har da ramuwa._

A ranar kwana nayi cikin tunanin inda zan ringa samo jarirai..........

👨🏻‍💻 Kije gidan su..... Anyi sabuwar haihuwa 😛

Autan marubuta ✍🏻




👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

        ​*'YAR MAFIYA*​
            ☠☠☠☠☠☠
     ​_Gajeren labari_​

 ​*Part 15​-20*

© 🤴🏻 ​KING BOY ISAH​  ✍🏼



 ​​DEDICATED TO *Zamani writers*

👨🏻‍💻✍🏻
Ina ji daku 👌🏼 Ana mugun Jone 🤝


            *KARSHEN PAGEN BAYA*

~"Kai amma wannan mata Allah ya saka mata da alheri".  Murmushi nayi hade da cewq amin. A zuciya nace, "Lalai wannan ya kamu".  Doyar mukaci muka koshi har mukayi saura. Bayan yayi sallah nima nayi tawa har da ramuwa.​  A ranar kwana nayi cikin tunanin inda zan ringa samo jarirai..........~



Washe gari da safe kayan tea mai gida ya sayo na hada mana kayan break wanda aka dade ba aci ba a gidan.  Muna zaune ina cikin cin abincin na fara jin wata irin murya na kiran suna na. "Na'am". na amsa ina waiga bata ba kowa mu biyu ne a dakin.  Mai gidana ya dau kofi zai kai baki jin na amsa kira yasa ya fasa.... "Nusaiba waya kira ki da naji kina cewa na'am?.. 


"Wallahi ji nayi kamar an anbaci suna na baki ji bane kai?".   Yace, "Aa ni kam banji ba wallahi. Gaskiya inaga dai kunnen ki bai ji dai-dai bane".


Shiru nayi ban tanka mai ba naci gaba da cin abinci na... "Nuuussaiiibaaaa".    Naji an kara kira, Firgigita na juya ba tare da na amsa kiran ba. Banga kowa ba. Mai gida na na kalla naga shi kam hankalin shi bai ko kawo gun ba. Wannan ya tabbatar min da cewa shi bai ji kiran ba.


"Kiyi sauri kizo muna jiran kiiiii".  Na kara jin anyi magana  wannan ya tabbatar min da Yan mafiyan nan ne suke kira na. Kasancewar na lura da mai gida na baya jin maganar. 


"Kiyi saurrri faaa!  Domin muna bukatar ganin ki yanzun nan ba sai kin wahalar da kanki ba kawai ki dauki halewar nan ki sa a bakin ki".    Ni dai ina jin ana magana amma naki tankawa dan kar mai gida na ya gano ni.  Mikewa nayi da sauri na nufi wajen jakata na laluba na daukko alewar nan. Tukun na sabi gyale. Duk a rikice nake. Har na zura kafata waje zan fito naji mai gida na yace.

"Ina kuma zaki je naga kin sabi hajab?".  Juyowa nayi ina murmushi nace, "Nan gidan su Maryam dan dan leka naga lafiyan jaririn".   Cewaya yayi "Ok ki duba min shi kuma kice mata ina mata barka kin san ban hadu mai gidan nata ba ma balle na mai barka". 


Juyawa nayi na fice hade da cewa. "To zata ji".  Na kusan kawo bakin kofa kenan na bare alewar nan da jefawa baki sai gani a tsakiyar falon nan.  Yauma kamar jiya.mutane ne sunyi kuri dukan su sanye da jajayen kaya. Sai dai na yau basu kai na jiya yawa ba.  Ogan nasu na kalla fuskar sa a murtuke ya wani bata rai.  Cikin ladabi na dan duka..


"Barkan ku da safiya oga. Ina zaune ina kari naji ana kira na".

Tsawa ya daka min hade da bude  min kwala-kwalan idanunsa wanda suka kara fito da muninsa.

"Kee! Nusaiba. Kin karya dokar kungiya da kika fara cin wani abu ba jini ba. Ko dan laifina ne da ban sanar dake ba jiya. Ki sani cewa duk dan kungiyar mu da safe da jini yake fara karyawa tun kafin ya ci kuma kuma jinin mutane".    Kwabe fuska nayi kamar wace zatayi kuka.  "Jini fa kace oga. Ko ka manta cewa  bani kadai bace a gidan ni da mijina ne fa". Hahahahaha ya kyal-kyale da dariya. Kafin ya fara nuna min wasu mata dake zaune a wajen.


"Kinga wadan nan duk da auren su kafin su shigo wannan kungiyar. Dokokin mu suka sa su kashe auren dake suna san kudi. Ke ma yazama dole ki kashe auren ki. In dai kina san kudi"..  Ya karashe maganar cikin dariya.




Dururum! Naji gabana yayi wata irin faduwa mai kama da saukar aradu. A zuciya na fara magan. "Mijina kuma ? Kai wallahi ni bazan rabu da mijina ba. Zan iya komai saboda kudi amma fa banda rabuwa da mijina. Saboda ina matukar kaunar sa. San bana tunanin zan yi wa wani d'a namiji irin san da nake masa".



Jin shirin tawa tayi yawa ya sake daka man tsawa!!. "Ke dake fa nake magana kin wani yi man shiru".   Dagowata nace "Wallahi bazan iya rabuwa da mijina ba sai dai komi ma zai faru ya faru. Zan ma iya hakura na fita daga kungiyar nan na hakura da kudin in dai kuka takura a kan cewa sai na rabu da mijina".   


Heheheheh
 Ya wani langabe kai yana kallo na yana wata irin dariya wacce da kagani kasan dariyar mugunta ce.  Murya irin ta mugayen mutane mai kama da ta tausaya wa ya fara cewa. "Nusaiba kenan.. Nusaiba nayi tunanin ke wayayya ce wacce zata iya yin komai saboda kudi.  Kuma nayi tunanin cewa ke nusaiba kin tsallake shan kaifin wukar mu. Ashe dai zaki sha ta". 




Yana fara maganar wuka naji jikina ya har rawa.. Nan fa na fara tunanin cewa kwanakin da aka rubuto zanyi a duniya sun cika ne yau.   Murtuke fuska ya karayi A karo na biya. Tukun ya kalle wasu rikakkun gardawa wanda da ka kalle fuskar su zaka gane ba imani  a tare da su balle tausayi.


"Ku kama min wannan yarinya ku yanka min ita yanzu nan. Tunda naga tafiyar mu bazata zo daya ba. Irin wannan sune masu tonawa mutane asiri ma".  Da fadar haka naga wasu karti sun nufo ni daya ya zare wuka.   A firgice na waiga baya na domin neman matsera.  Abun mamaki ko kofar da na gani jiya ban ganta ba yau.


Ganin sun nufo ni da wuka tsirarar ta yasa na juya na nufi wani bangare na dakin a guje. Ai kafin nayi nisa tuni naji an cafke ni.   Dayan ya tade kafafuna na fadi kasa rigijif.  Mai wukar ya zagayo ta gabana. Yayin da gudan kuma ya haye kaina ya dadane min hannuwa.  Tabbas na murkusu domin ko motsi kasa yi nayi.  Dan kamar ya taushe sanyi haka ya min. Kuka na fara ina zubar da hawaye ina ihun neman dauki. Cikin mutanen nan ba wanda ya kula balle ya kawo dauki. Illa iyaka idanun da suka kwalalo min.   



Wuka gardin nan ya dora........................................



😱😳 Shikenan an yanka wata 😰


 *Autan marubuta* ✍🏻










☠☠☠☠☠☠
        *'YAR MAFIYA*
            ☠☠☠☠☠☠
     _Gajeren labari_


 *Part 20 -25*



© 🤴🏻 *KING BOY ISAH*  ✍🏼

'          👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com




.     *KARSHEN PAGEN BAYA*  .

 ~Tabbas na murkusu domin ko motsi kasa yi nayi.  Dan kamar ya taushe sanyi haka ya min. Kuka na fara ina zubar da hawaye ina ihun neman dauki. Cikin mutanen nan ba wanda ya kula balle ya kawo dauki. Illa iyaka idanun da suka kwalalo min. Wuka gardin nan ya dora.~





Yana dora wukar na rufe idona wanda hawaye suka kwaranyo daga ciki, a zuciya nace "shikenana tawa ta kare". Kafin yaja wukar dip! Muka ga duhu ya mamaye  dakin lokaci guda. "Karku yanka ta tana da amfani a wajen mu".  Wata murya mukaji ta ambata haka. Dajin muryar kasan ba mutum bane yayi wannan maganar saboda amon ta  ga karfi. Kai in ma mutum ne to yayi amfani da sufika.  kuma sai hasken dakin ya dawo nan take mutanen suka dauki wani kara wanda bansan ko me suka fada a ciki ba.




Shugaban nasu ya kalle ni ranshi a bace yace, "Kinci sa'a kudunbur ya ce ce ki". Wata ya kalla daga cikin matan nan, ba tare da yayi mata magana ba.  naga ta mike ta nufi wani dan daki. ba a dade bana naga ta fito hannun ta rike da kofi na glass da jan abu a ciki wanda kuwa nasan a gidan nan duk wani abu da ya shafi ja in dai ruwa ne to jini ne.  Tana zuwa ta miko min. Ba gardama na  amsa hade da cewa me za ayi da shi?. Ogan yace "Shanye shi,  yanzu nan".  Ba tare da nayi gardama ba na kafa kofin a kai empty na ajiye kofin ina kallan shi.  Wasu kudi ya miko min bandir biyar. Na tashi daga inda nake a zaune naje na karba. 



"Wannan kudin da kike ganin su duk wanda ya taba su ko baban ki ne sai ya koma kaza ko doya ko pure water".  Da sauri na zubar da kudin kasa na binsu da kallo ina kuma jinjina maganar tashi. "Yace kowa ya taba su sai ya koma wani abu to ni ya akayi ban koma ba?". Maganar shi ce ta fizgo ni daga koramar tunanin da na afka. 



"Ke ma kanki badan jinin nan da kika sha ba da yanzu kin bace kin koma daya daga cikin abubuwan da na lissafa".  A zuciya nace "Oh! Shiyasa".  Yaci gaba da cewa. "Ki debi kudin nan kije ki ya yarda su a wurare daban-daban. Da zarar mutum ya dauka zai koma daya daga cikin abubuwan da na gaya miki. Ke kuwa sai ki biyo baya ki dauke ki saka a jaka. But ki kula domin in aka kama ki bazata miki da kyau ba".




Jin wannan mutumin na neman jefa ni cikin hadari da sauri nace, "Oga wannan ai yayi hadari da yawa ina wannan irin wanda ake bace wa. In an dauki kudin? A bani irin shi yafi". 



"Wannan da kika gani sabon sihiri ne da ba kullum yake aiki ba. Dan haka yanzu da wannan muke aiki. Duk mutum daya da kika kawo za mu baki 2 million sanan karki manta da maganar jarirai domin wanna  a zaune takee duk satin da baki kawo ba ke za a cinye a mamakon sa".



 Wannan alewar ya miko man na karba na kwashe kudin nan na kasa. Ba abunda nake hange sai yawan kudin da naje ance za a na bani. Alewar na bare nasa a baki sai ganina nayi a tsakar gida na. Dakina kulle da kwado wannan ya sheda min mai gidana ya fita. Waje na samu na ajiye kudin kafin na fito na zagaya gidan Maryam makwabciyar mu. Bayan mun gaisa na duba jariri na amso makulle na zo na bude daki.  Katuwar handbag na dauka hade da katuwar dark blue din hijab dita wace in nasata har kasa. Ban jira komai ba na dauki yan kudin kashe wa na fito na kulle dakin na kwashe kudin tsafin nan na zuba a jaka na fito na jawo gidan.




Ina fitowa bakin layin mu naga wani dan adai-dai ta ba kowa a ciki hakan yasa na tsayar da shi. Na hau "Gara zaka kai ni".  Na fada lokacin da nake kokarin gyara zamana. "Malam ya zaki shiga bayan bamu gama cini ki ba". Ya fada cikin gadara.




 Ya bani haushi sosai domin a yanzu gani nake na wuce a min wulakanci a kan kudin.  A zafafe nace. "Wai ku me yasa kuke da rashin kirki ne. Duka napep din nawa take da har zaka nemi gaya wa mutane magana a kan an shigo ba ayi ciniki ba".  Da sauri ya juyo yace, "Ai dan na isa da ita ne shiyasa kinga malam fita kawai ki nema wani ai bani daya bane".  Yayi matukar kule ni domin yanzu har iri  girman kan nan na masu dukiya ya fara shigata. A zuciya nace nasan maganin ka. A fili kuwa cewa nayi, "Kaga yi hakuri ja muje ko nawa ne zan baka".  Yana gunguni ya napepk din ya nufi gara. Wani dan kauye ne  gaba da garin mu kadan ba nisa.




 Jan burji ne hanyar dake sadaka da garin mutane jefi-jefi ke giftawa yan mashina da yan napepk. Ko da naga mun kusan zuwa gari kuma wajen ba mutane sai nace "sauke ni nan". Tsaki yaja ya faka gefan hanya a zuciya nace zaka ci uban ka ai. Cikin kudin tsafin nan na fiddo Dubu daya na miki mai ta baya ba tare da na fito ba. Nace "Amsa dauki kudin ka ka bani canji". Juyowa yayi yana sa hannu da niyar karba. Bat! Ya bace ya koma doya. Zabura nayi hade da yin dan kara.




Domin na dan tsorata. Kai na fara jinjinawa a raina nace "Tsafi gaskiyar mai shi".  Ta famar set din napepk din na zura hannu domin in dauki doyar dake kan set din.  Kamar daga sama naji ance. "Ina mai napepk din nan tafiya zai yi". Dum! Naji gabana yayi wani
Da sauri na juya na kalle wanda yayi maganar. Wata mata ce ta yafa gyale tana rike da wata Yarinya.





 "Eh... Ahha  baya nana yanzu ya kawo ni kuma ya kuma gida daukko wani abune ya dawo".  Na fada lokacin da na dauki doyar ba tare da kwokwanto ba na tura cikin jaka. Na fito a napepk din, Na kalli matar nace ina yini.  Ta amsa lafiya lau muka gaisa. Nace, "Yaje ya dawo ne zaku iya shiga ciki ma ku zauna ku jira shi.  To  ta fada yayin da ta kama hannun Yarinyar suka shiga ciki suka zauna. Ni kuma da sauri na nufi cikin kauyen nan.






Har yanzu gaba na faduwa yake bama kamar da naga wannan matar na min wani irin kallo. Kasancewar bansan kowa a garin ba kurum haka nan na kama yawo ina zagaye gari ina zubda kudin nan ta cikin hijab.  Wani wajen in yarda  bandir wani gun kuma in yarda dubu guda..............................


😳😮 Su oo banda ganin kudi a kasa a dauka













👨🏻‍💻👩🏻‍💻 ​*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​


        *'YAR MAFIYA*​
            ☠☠☠☠☠☠
     ​Gajeren labari​

 ​*Part 25-30*

© 🤴🏻 ​*KINGBOY ISAH* ✍🏼


.                👨🏻‍💻👩🏻‍💻        .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com






. *DEDICATED TO BESTYN NANAH...*


👌🏼 Na gode da lalubo gyara...

Readers ku gafarce ni nayi mistake na fara da sunan Nusaiba na koma Nusaiba 🙊 Wannan ya faru ne sakamakon wannan ne littafi na daya da na fara tafiya da irin wannan salon. Na jarumi ya dinga bada labari. 😔 Zanci gaba da tafiya da Nusaiban kawai👏🏼




*KARSHE PAGEN BAYA*
~Har yanzu gaba na faduwa yake bama kamar da naga wannan matar na min wani irin kallo. Kasancewar bansan kowa a garin ba kurum haka nan na kama yawo ina zagaye gari ina zubda kudin nan ta cikin hijab.  Wani wajen in yarda  bandir wani gun kuma in yarda dubu guda.~


Haka na ci gaba da zubda kudin har kusan bayan gari. Inda naga ba mutane sai jefi-jefi suke giftawa.  Da dai naga na yarda kudaden da yawa kawai sai na sama waje dan lungu a bayan wani rumbun hatsi na zauna kawai na zuba ido ina kallan ikon Allah. A raina nace, "Allah ya kawo mai tsautsayi". Na jima a wajen amma banga gifcin ko mutum daya ba kasancewar garin kauye ga rana da ake kwadawa ya bazara. Hakan yasa kowa na gida a inuwa. Tun ina jin dadin abun a ganina in mutum  ya zo ya dauka ko kaza ya koma bazai min wahalar dauka ba.




 Har kuma na fara jin haushi ina tunanin ko dai tashi zanyi in nufi wani yanki na garin. Wani sabon tunanin ne ya fado min wanda ya saka ni cikin farin ciki. Af! Wai ni yanzu ni ke shirin zama maloniya nan take na fara tuna abubuwan da zanyi, zan canzawa iyaye na gida na musu dankareran gida. Nasa a rushe gidan mu a maida shi bane. Tunowa nayi a duk fadin garin kazaure ba bene mai hawa uku nace to ni in na tashi hawa hudu zanyi.





In saya wa mijina mota dankareriya in kuma bude mai katan shop wanda babu irin sa ko a cikin kano. Balle nan kazaure.  Makwabciyar mu ce ta fado min a rai, domin duk da muna mutunci da ita tana nuna min banbanci, wato mijin ta yafi nawa hali. Yar dariya nayi irin ta farin ciki naci gaba da tunanin irin abubuwan da tayi min a baya domin ranar da ta tashi rashin mutuncin ta kanzo take kankarowa na tuwo ta miko min ta katanga. nan take maganar da take min in ta miko abincin ta fado min  a kwanya.






 "Nusaiba ga kanzon nan kisa mai ko gishiri ne ki kwada nasan cewa jiya bakuyi abinci ba". Bata rai nayi duk da ba yanzu take fadar maganar ba amma ji nayi kamar yanzun take. A raina nace wannan wulakancin da take min yaseen sai na rama, domin a yanzu da dola ta samu sai...




Surutun wasu yan mata su biyu ne da suka tawo rike da hannun jina. Kallo daya zaka musu ka gane cewa cikakkun yan kaye ne duk da kasancewar su ba wasu bakake ba.   Sanye suke da riga da zani a tamfa amma ko wanne ware-ware ne. Kafafun su takalmi silifos dayar kan takalmin ma ya tsinke sai kaba aka sa aka daure.  Da ganin yaran na farin ciki ya rufe ni ganin kuma hanyar nan suka biyo kuma ba kowa a hangun da dama.   Kamar hadin baki naga yaran sun ruga da gudu a tare.





 Lokacin da suka hangi kudin. Ko wacce dubu ta nufa a kusan tare suka kai hannu domin dauka. Bat suka bace daya ta zama kaza daya kuma pure water. Da ganin haka na taso cike da farin ciki na wawaiga banga ko wulgin mutum ba. Hakan yasa naje da sauri na dauki pure water din na jefa a jaka. Kazar ma bata wani bani wahala ba na kamata na rike a hannu cikin hijab. Sai da na wai-waiga naga ba mai kallona tukun da sauri na dau hanyar gida.






 Tafiya nake cikin sauri da ka ganni kaga marar gaskiya. Lura da in naci gaba da tafiya a haka za a yi gano ni ne tasa na dan natsu na ringa tafiya da sauri amma cikin kunciyar hankali. Haka na ringa ratsa wa ina wuce mutane a inuwoyi suna hutawa. Duk in da na wuce sai naga sai kallona ake, amma ban wani damu ba naci gaba da tafiya da nazo saitin napepk din nan sai da na kalle ta a zuciya nace, "To ita fa wannan napepk din ko ya za ayi da ita? Ko gwabnati ta dauke ko kuma barayi su dauka.  Oho dai ni dai na dauke mai ita nayi kudi da shi".




 Tafiya nake muna kiliya da mutane jefi-jefi. Ban sama napepk ba sai da na kusan zuwa titi tukun na sama. Ina hawa nace ya kai ni magama.
Har bakin kofar gidan yan mafiyan na  ya kai ni. Ina fitowa kuwa na bashi dubu guda. Dari biyar kadai na karba nace ya rike canjin.  Sai da na duba naga ba mai kallo na tukun na bare alewar na saka a baki. A tsakiyar falon na bayyana. Wannan karan ba kowa  a falon sai ogan.





Yana ganina fuskar shi ta fadada da murmushi. Ganin kaza a hannuna, nima murmushin na taya shi. Kafin naje gaban shi na bude handbag din na fiddi doyar nan hade da pure water guda sai kaza.  Dariya yayi kafin yace "Lalai za aje dake. Nusaiba. Kinyi kokari matuka, domin a yanzu yara na wasu da kyar ma suke kawo mutum daya. Sai gashi ke tashi farko kin kawo har uku".





Murmushi kawai nayi hade da cewa "Ai zan koma in kawo sauran ma. Domin na zubda kudade da yawa a wajen". Yar dariya yayi kafin yace, "To ai kudin nan amfanin su ya kare yanzu ko kinje wajen bazaki ga komai ba. Domin su haka suke, daga wanda ya yarda su ya danyi nisa bacewa suke yi".  Shiru nayi ina nazarin maganar shi.  Tashi yayi ya dauki kayayakin da na kawo ya nufi wani daki da su. Dan jimawa kadan ya fito da wata leda gari yayi zafi. Yana zuwq ya miko min yace, "Ga kudin ki nan million uku chif! Ki kara himma zaki zama mai arziki nan da dan lokaci kadan".





Karba nayi na bude kudi ne yan dubu-dubu sababbi kal! Dadi ya cika ni na kalli duk yawan kudin nan wai nawa ne. Jaka ta na bude na zuba su ciki. Ogan yace naje gida gobe zasu neme ni. Mukayi sallama da shi. Lokacin kuwa waccen Alewar ma ban idasa shanye ta ba. Ba tare da na da bude wata nasa a baki ba bullum na ganni a waje. Ba tare da shakkun komai ba na tsaida dan napepk nace ya kai ni bakin titi. A saitin shagon wani mai sayar da su shinkafa nace ya tsaya in fito. Na shiga ba tare da bata lokaci ba na sayo buhun shinkafa da jarkar mai ga katan din taliya da macaroni.




 Yaran shagon ne suka jido kayan suka kai min napepk
Bayan na biya kudi nazo na shiga napepk  a hanya na kara tsayawa na saya mana kayan miya har da nama. Sanan muka karasa gidan ba kowa hakan yasa na bawa mai napepk din umarani ya taimaka ya shigo min da kayan. Bayan ya shigo min da shu dubu daya na bashi nace ya kawo dari biyar, da duk zan barmai sai kuma nayi tunanin zargi. 





Hijab dina na cire na shiga daki na fara nazarin inda zan boye kudin nan. Can kuma sai na tuno ba inda ya kamata na ringa tarawa sai karkashin katifa domin mai gidana baya daga katifar.  Nan take na daga na juye kudin bandir daya na rage na boye a fili.   Fitowa nayi na fara kokarin yi mana abinci. Bayan na gyara kayan miyan na samu yaro a waje ya kai min markade nazo na hada girki shinkafa da miya da nama wanda raban mu da cin irin sa tun amarci. Bayan na kamala komai.







Nayi wanka na share gida na kimtsa komai. Lokacin magariba tayi tunda naji an fara kiran sallah mai gidana bai shigo ba na san cewa sallah ya tsaya yi. Alwala nayi naje   kabbara sallah. Fayau! Naji an wanke ni da mari ba tare da naga mai marin nawa ba. Dafe kunne nayi ina waige-waige.


 "Keee! Ki sani cewa kungiya ta haramta yin sallah. Saboda haka daga yau karki kuskura ki sake kokarin yunkurin yin sallah..in kuwa kika yi to ki kuka da kanki".    Nan take jikina ya fara kyarma.



 Cikin kuka-kuka nake cewa. "Haba ace mutum musulmi bazai yi sallah. Wallahi ni sai nayi neman kudi ai ba hauka bane".





 Sake matsawa nayi na dai-dai ta a kan sallayar tawa na daga hannu da niyar yin kabbara kenan naji an hangiza ni baya da karfi. Nayi tagal-tagal zan fadi kenan na tokare da bango. Lokacin mai gidana yayi sallama ya shigo dakin......................................




😳🤔 Turkash! Lalai kun daukko babbar magana



🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀

Ku biyo Autan Writers abokai dan jin wannan kasaitaccen  👌🏼




👨🏻‍💻👩🏻‍💻 ​*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​


        *'YAN MAFIYA*​
            ☠☠☠☠☠☠
     ​Gajeren labari​

 ​*Part 30-35*

© 🤴🏻 ​*KINGBOY ISAH* ✍🏼


.                👨🏻‍💻👩🏻‍💻        .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com



*DEDICATED TO MASOYAN KING BOY*  😛 _Har ma da makiyan in inada_


☺👏🏼 Assalamu alaikum yan uwa kuma masoya da abokanai yayyai da kannai na masu bibiyar littafin *'YAR MAFIYA*.   Ina mai sanar daku tare da baku hakurin  cewa littafin ya tashi daga *'YAR MAFIYA*  ZUWA *'YAN MAFIYA*.  Kasancewar korafi yayi yawa akan cewa Aunty *Rashkardam* tayi 'Yar mafiya shekarun baya 👌🏼

Fatan zakuci gaba da kasancewa da Autan Writers domin jin yanda zata kwashe tsakanin Nusaiba da 'YAN MAFIYA.






    *KARSHEN PAGEN BAYA*

 ~Sake matsawa nayi na dai-dai ta a kan sallayar tawa na daga hannu da niyar yin kabbara kenan naji an hangiza ni baya da karfi. Nayi tagal-tagal zan fadi kenan na tokare da bango. Lokacin mai gidana yayi sallama ya shigo dakin.~


_*M*ai gidana ya shigo dakin ranshi a bace duk ya wani murtuke fuska. Bayan ya zauna a gefan gado ya watso min harara hade da tambayar ina naje a wunin yau. Dan murmushi nayi tukun nace, "Mai gidana farin cikina kuma jigon rayuwa ta ka gafarce ni nayi ma laifi, amma nasan cewa wannan laifin ba laifi ne da zai bata ran mai gida na ba in dai ya tsaya ya saurare ni". Kallo na yayi yace, "Ina jinki". Nan take naji kwarin gwiwa ai kuwa na fara zabga karya nace, "Ina fita daga gidan nan ban ko shiga gidan Maryam ba Hajiya ta kira ni cikin tashin hankali take magana lokacin da naji tana cewa in taimake ta in zo da sauri zai kashe ta. Hakan   tasa na hau napepk nace yayi gudu ya kai ni gidan. Muna zuwa kuwa ban ko biya shi kudin ba na fita a guje na shiga gidan. Abun haushi da na shiga wai sai na iske Hajiya can ta kankame jikin ta can jikin bango. Na shiga dube-dube ko zanga mutum amma ban gani ba._





 _Haka  na kuma fara dudubawa ko maciji ne. Da dai naga ba komai sai na tambaye ta miye. Bude bakin ta cewa tayi "Kyankyaso" tana nuna min shi a kan gadon. Ai kuwa na kece da Dariya.  Mai gidana naga ya bingire da dariya har da kwantawa kan gado yana kyal-kyala dariya. Da ganin haka nace a zuciya "Yauwa ya kamu". Naci gaba da bashi labarin cewa bayan na dauke kyankyasan ne nace  wa Aunty Talatu zan tawo nan fa ta tashi hankalin ta wai bazan taho ba. Ba yanda na iya dole na tsaya na taya ta aiki yanzu ma da kyar ta barni na taho. Shine ta hado ni da wannan shinkafar da sauran kaya. Tace na baka hakuri kuma na gaya ma ita ta tsayar dani. Cike da mamaki mijina ya tashi zaune yana kallona. "Nusaiba kina nufin wannnan buhun shinkafar da macaroni da na gani a waje duk Hajiyan ta bani".   "Eh ita tace na kawo ma na kuma baka hakurin tsayar dqni da tayi". Nan fa ya kama murna yana sawa Hajiya albarka. Bayan ya danyi shiru ne nace. "Sannan hajiya tace na rokeka alfarma ayuka sun mata yawa bata saba ba. Kullum zan ringa zuwa ina taya ta aiki kafin su koma".  Nayi zatan zai hanani sai naji yace wannan ai ba komai bane dan Allah gobe ina so ki kai ni na wa hajiyan nan godiya". Da sauri na dago kai na kalle shi. "Nace haba dai da wuri haka ka dai bari in gaya mata tukun inji yanda zata ce"._





_Ban bari yayi magana ba na juya hade da cewa "Bari na kawo mana abince".  Da sauri na fita gabana na faduwa tsoran kar yace dole sai yaje yawa hajiya godiya._
_Abinci na kawo muka ci da isha'i ya fita domin yin sallah hade da cewa nima in tashi inyi. Nan take naji fargaba ta kamani, wai yanzu dai ana nufin bazan sake sallah ba. "Uhm neman kudi da wuya yake"._




_Tun kafin ayi kiran sallar fari naji ana tashina. Farkawar da zanyi na tsinci kai na a gidan yan mafiyan nan.  Nayi mamakin ganin duk mutanen a zagaye a gun kamar dai ranar nan yau ma jajayen kaya ne a jikin su fuskokin sun zazana farin abu, ga kuma wuta a tsakiyar su. Ogan ne yace dani in shiga layi. Cikin magagin barcina na tashi da kyar na hau layi.  Wani irin jini ne mai ja sosai aka fara bi layi-layi ana rabawa. Nan take na tuna da batun ogan wato da yace da jini ake fara karyawa. Abun mamaki duk wanda yasha sai naga ya bace bat!. Ana cikin haka har aka zo kai na nima ana bani nasha sai na bace. A gida kan gado na bayyana. Na juya na kalli mai gidana har yanzu barcin sa yake..._


_Da safe ma karin yan gayu mukayi harda su wainar kwai. Kamar yanda na kudurci niya kwano na daukko na juye dan sauran naman da mukaci jiya hada da yan kasusuwa na kuma dora dan guntun bire di ta katanga na mikawa Maryam duk dan taji haushi.  Mai gidana cewa yayi yau bazaije aikk ba domin jiya ma da ya fita kasuwa bai sama dako ba. Dan haka yace ni na shirya na tafi gidan hajiya shi hutu zaiyi. Naji dadin hakan sosai, kamar dai jiya katuwar jaka ta na rataya tukun na zura hijab nayi sallama da mai gida na na fita. Ina zuwa bakin kofar gida na saka alewar nan a baki dake dama can na bare ta. Tsulum na bayyana a GIDAN YAN MAFIYA. Ba a wani bata lokacin ba ogan namu ya fiddo wasu kudi dubu biyar ya mika mun yace yau ba kudin tsafin da yawa. Nan nake sheda mai alewar wajena ta kare. Tashi yayi shiga wani daki dake hagun din mu, ba a jima ba ya fito rike da wani kofin gilas ciki wani tsanwan abu ne. Yana zuwa ya miko min yace na shanye. Ba tare sa bata lokaci ba na kwankwade kasancewar naji abun shi ba zaki ba shi ba kumq salat ba. Bayan na shanye ne yake cewa "To daga yanzu in kika tashi shigowa ko fita kirjin ki kawai zaki dafa da hannun hagun kice, 'Kudunbur' kawai zakigan ki a nan"._




_Dan sauya fuska nayi. Ogan na ganin haka yace "mine ne kuma?".   Nace "Jiya naje yin sallah aka hanani wai aka ce dokar kungiya ta hanani sallah daga yau". Dariya yayi tukun yace "Kwarai haka ne. Gaba dayan yan kungiyar nan ba mai sallah".  Nace, "Amma fa ni gaskiya da nasan haka kungiyar nan take da ban shiga ba".  Yayi dariya tukun yace. "Da kudi da sallar wanne kika zaba?".  Tsuru nayi ina tunani ban ce mai komai ba. Domin ciki ba abunda ya kamata na jefar. Jin nayk shiru da yawa yasa shi cewa. "Dake fa nake ina jiran amsar ki".  "A yanzu dai gwara kudin  domin zan iya komai a kansu". Na fada ina kallan shi, bayan ya kuma kyal-kyalewa da dariya yace, "Ai kuwa kinzo gidan kudi kibi dokar kungiya kawai in dai kudi ne har fillo zaki iya yi da su. Maza tashi jeki dan yau muna bukatar kawunan mutane da jini kuma"._




_Hannu na dora a kirji kamar yanda ya fada man  na kira sunan dodon tsafin nan su ai kuwa kafin kifta ido na ganni a waje tsaye bakin titi.  Mai napep na tsayar kamr jiya yau ma gara nace a kai ni.   Muna zuwa saitin napepk din jiya da har yanzu take a ajiye a wajen cikin rudu naga mai napepk din ya tsaya da sauri ya fito ya nufi napepk din yana lalekawa.  Can kuma naga ya fito ya nufo ni yana waya a cikin wayar naji yana ambatar Asp hakan ya sheda min cewa yan sanda yake kira.  Fitowa nayi a napepk din duk tsoro ya kamani da kyar na iya control din kai na ta hanyar karfafawa zuciyata gwiwa na daina karkawar tsoran da na fara. Na zagaya ta inda yake duk a rikice yake nace nawa ne kudin sa. Cewa yayi in daba ko nawa ne. Nan yake fada min wai tun jiya ake neman mai napep din nan an rasa. Ni dai ban tanka masa ba na zaro dari na bashi na wuce da sauri. Naje giftawa ta wajen wasu mutane a majalisa naji suna labarin bacewar Kande da zakiyya. Wanda kuwa nasan cewa yaran da na sata ne jiya.  Wucewa kawai nayi sai da naje bayan gari wajen jiya tukun na yarda dubu a can nesa na kara gaba na ajiye watq dubun. A wajen wata kwana ma na ajiya,Kusa da inda nake labewa._






_Ina labe zaune a inda nake a labe naga wani yaro ya fito daga cikin daji zai nufi gari. Yan ganin dubun nan kuwa da sauri ya nufe ta da niyar dauka. Ai kuwa yana tabawa ya zama pure water murna sosai nayi naje na daukko nasa a jaka. A cewata yau da wuri zan ci kasuwata na koma. Can an dan jima kadan na hangi wasu yara maza su biyu haka dai matasa yan kimanin 15 years sun nufo hanyar ai kuwa dadi ya kume ni. Kara boyewa nayi a inda nake duk da dai basa ganina wai ni tsoran kar su ganni suki daukar kudin dan tsintuwa bata yin dadi a gaban idan wani ko ba mai kayan bane.   Na juyo ina wannan tunani kawai sai ji nayi an kwalla ihu!. A hankali na leko ai kuwa naga ashe cikin yaran nan daya ne ya zama doya da alamar dai shi ya dau kudin. Nan da nan dayan ya tara jama'an inajin wani dattijo yana cewa, "tunda akayi haka to wanda ya sace su Kande shine ya hada wannan abun yaci gaba da cewa, yanzu labewa zamuyi nasan cewa tunda ya hada wannan abun zai dawo domin dauka yanzu mu samu waje mu boye yana zuwa sai mu cafke shi"._




  _Wani daga cikin matasan yace, "Mu dai gaskiya mun fi zargin wata mata mai dogon hijab  da ke wucewa. Bamu taba ganin ta a garin nan ba sai jiya. Haka kuma dazun ma ta gaban mu ta wuce duk yanda akayi ita ce mai wannan aiki".  Nan take mutane suka dauka haya-haya kowa na cewa ya ganta. Da jin haka  a zuciya nace yau fa in aka kamani mai kwatata sai Allah.  Ai kuwa na sulale ta bayan gari na ratsa cikin daji. Gudu-gudu sauri-sauri har na karasa bakin titi na hau napepk tsabar tsoro har fitsari nake ji. Muna isa gida bayan na biya mai adai-daita kudin sa na shida daki a kan gado na iske mai gidana yana kwance sallamar da ya amsa ta sheda min ba barci yake ba. A tsakar daki na ajiye jakata hade da cire hijab din shima na ratayi a kyaure. Sauri nake sosai saboda fitsarin dake neman kwabci min.  Sai da naje na yo fitsarin tukun na sama natsuwa. A hankali na nufi dakin ina tafe ina kallan kofar gidan tsoro duk ya cikani ga gabana na faduwa gani nake kamr mutanen nan sun ganni sun biyo bayana.  Ina shiga daki nayi tsaye cur! Ina kallan wani jan zakara dake kusa da jakata. Gabana ne ya shiga dukan tara-tara ganin mijina baya kan gado bayan yanzu na barshi a kan gadon. Ko dai shine ya taba kudin tsafin nan ya zama zakara?......................................._




🙆🏻‍♂😰 Kutt! Lalai akwai chakwakiya in mijin ki ne ya koma zakara..lolz


Autan writers ✍











👨🏻‍💻👩🏻‍💻 ​*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​


        *'YAN MAFIYA*​
            ☠☠☠☠☠☠
     ​Gajeren labari​

 ​*Part 35-40*

© 🤴🏻 ​*KINGBOY ISAH* ✍🏼


.                👨🏻‍💻👩🏻‍💻        .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com




'       KARSHEN PAGEN BAYA     '

_Cike da tsoro na nufi wajen jakar. Ina budewa kuwa naga kudin nan saura dubu daya. Wannan ya tabbatar min cewa mai gidana ne ya zama zakara.  Kuka na fara yayin da na kama zakaran ina kare mai kallo. Shima kallona yake. Ai kuwa cikin tashin hankali na dafe kirji hade da fadin sunan da ogan mu ya fada. Kafin kiftawar ido na bayyana a gidan yan mafiyan nan ina kuka. Wannan shine karo na farko da na zo ban iske ogan ba. Shiru falan ba kowa. Na dade a tsugune rike da zakaran da nake wa kallan shine mijina. ina kuka daga bisani naji kwaramniya na fitowa daga wani dan daki.  Da sauri na mike na nufi wajen, Sanda na ratsa dakuna uku ina bibiyar karar da nake ji tukun na karasa wani wargajejen kitchen. Matan da suka kai mana abinci a wancan ranar da aka kamani ne suke ta faman aikin dahuwa. Nadai ga jini kaca-kaca a ko'ina sai daga bisani can na hangi kawunan mutane har uku a ajiye. Idanu na rufe domin na gane cewa wanda aka yanka ne._



_Daya daga cikin matan ta juyo ta kalle ni fuskar ta ba wal-wala "Ke kuma me ya kawo ki nan? Daga shigowa kungiya shikenan aka gaya miki har an baki ikon shiga ko'ina ne a nan gidan?". Ta gefan ta dake rike da ludayi tana juya nama a tukunya tace. "Kawata rabu da ita, in dai tana shige-shige har ta kai kanta mahallaka in dai nan gidan ne". Kuka na kara rushewa da shi hawaye suka kara jike man fuska. Da sauri suka maido hankalin su gare ni. Sai yanzu ma suka lura da zakaran hannuna. Na gane hakan ne saboda jin da nayi daya a cikin su tace "Wannan zakaran fa. Ke kin samo kayan kudi miye kuma na kuka"._




_Cikin kuka nace, "Wannan da kuke gani mijina na ajiye kudin tsafin a daki ban sani ba yaje ya taba. Yanzu gashi ya zama zakara dan Allah. Ku taimake ni ku dawo min da shi in kunsan yanda ake dawowa da shi".  Maimakon su tausaya min sai naga sun kyal-kyale da Dariya hade da kashewa da hannuwa. Tsuru ni dai na tsaya ina kallan su. Bayan sun gama dariyar daya ta kalli dayar tace. "Asabe kinji wata sabowa inji 'yan ca-ca". Asaben tace, "Sahura wannan al'amari kuma ai mu saidai kallo ta jira oga ya dawo watakil ya kokarta".  Sahura tace, "Ke malam wama kike da suna? Nusaiba. Yauwa Nusaiba in gaya miki gaskiya kin rasa mijin ki kenan na har abada. Kawai yanzu abunda yafi shine ki koma gida ki mai sutura ko ke kaddaice ko mai sallah. Domin in mai gida ya dawo zaiyi wuya bai karbe shi yayi kudi da shi ba"._




_Wasu zafafan hawaye ne suka kara kwaranyo min daga idanu. Na tuna soyayyar dake tsakanin mu wai yau ace nayi sanadin barin shi duniya. Wani kukan na kara fashewa da shi.  Asabe ta daka min tsawa, "Kinga malam mu fa kin cika mana kunne. Mu fa da kike gani ba wai tausayin ki zamuji ba. Kawai malama kiyi farin ciki. Yanzu ba ruwan ki zaki sake yanda kike so a gidan ki".  Motsi mukaji daga waje. Nan da nan suka juya suna ci gaba da girkin su, Wai ogane ya dawo daga gidan.  Ina jinsu suna gulmar cewa wai oga baya zama sosai tunda matar shi ta kusan haihuwa din nan. Da sauri na fita wajen sa ina kuka. Yana ganina ya fara tambayar miye-miye?.  Gabanshi na zube ina kuka hade da ajiye zakaran a gabanshi. Cikin kuka na fara magiya ina rokon shi  kan ya taimaka ya dawo min da mijina._





_Ya kalle ni cikin rashin fahimta yace, "Banfa gane abunda kike magana a kai ba".  Nace, "Mijin na ne ya taba kudin tsafin nan ya koma zakara , ka taimaka ka dawo min da shi". Dan murmushi yayi kafin yace. "Wanne ganganci ya kai ki kika bar kudin nan har ya gani ya taba? To ki sani cewa duk wanda ya koma pure water doya ko kaza ya riga ya zama kudi kenan. Dan haka a shawarce ki bar min shi a madadin Million daya zan baki million biyar".  A zabure na dauki zakaran na mike cikin hargowa kamar na zautu na nufi Mutumin._




_"Wallahi tallahi baka isa ka mayar min da miji kudi ba. Ka dawo min da shi mutum ko kuma wallahi duk abunda ya faru dakai ku kuka ja".  Dariya yayi kafin yace, "Dama kin dangana kin karbi kudin ki. Domin kuwa mijin ki ya tafi kenan. Ko da kuwa baki bar shi a nan ba Sati daya na cika zai koma kudi".  Zuwa nayi na cakume shi ina jijigawa ina cewa sai ya dawo min da mijina. Matan nan ne suka fito a guje suka karkare hannuna a jikin shi. Dan shi abun bai sha mai kai ba dariya ma yake. Dan zakaran na dauka nace, "Tunda kuka ki maido min da mijina yanda yake to wallahi sai na tona muki asiri da yan sanda zan  hada ku. Kuma bazan kara sato yara ko jinjirai ba". Dariya ya sake kecewa da ita yayin da ya nuna min wata gawa dake can kwance bayan mu. Kallo daya nawa saurayin na gane shi. Dan ina yawan ganin shi a nan._



_Ogan yace, "Wancan da kike gani ya dade a kungiyar nan yana aiki. Aikin shi sato kananun yara ne duk sati, Jiya ne ya kamata ya kawo amma ba kawo ba. Kinga abunda ya faru da shi. Dodan nin mu sun shanye mai jini. Kuma ki sani cewa baza ki taba iya kai karar mu ba bama zaki gan mu ba in kika zo da wannan kudirin". Ina kuka na fice a gidan na koma gida nasa zakara gaba, Sai da nasha kuka har na gode Allah, Ni dai shiga kungiyar nan bai min rana ba"._



_Ganin da nayi zakaran ya kwalalo min ido yasa nayi tunanin ko yunwa yake ji. Kitchen na shiga na debo farar shinkafa nazo na zuba mishi a gaban shi. Hade da debo mai ruwa a wani dan kwano na ajiye. Amma ko kulasu baiyi ba. Nayi tunanin ko irin su ne baya so, hakan tasa na fita naje shago na sayo hatsi dan chabe na kawo na juye mai da yawa. Amma yaki ci.  Tsuru na zuba mai ido ina kallan shi kwalla ta cika min ido, Sallamar da akayi ne tasa nayi saurin  goge kwallar da ta cika min ido. Ganin masu shigowar yasa gabana ya dingi faduwa. Uwar mijina ce da kanwar sa.  Ji nayi jikina duk ba karfi domin kasa tashi ma nayi har sanda suka karaso wajena. Ganin sun kurace min yasa na kakaro murmushin karfi da yaji na mike. "Umma sannu da zuwa. Na shiga daki da sauri na daukko musu tabarma. Bayan sun zauna ne Umma take cewa. "Nusaiba yaushe kika fara kiwo". Nayi murmushi nace, "Ai jiya ya sayo min"._





 _"Kai Amma Bala anyi sakarai. Yo ya za ayi ya sayo miki zakara ke da kika so ki sama albarkar kiwo? Ai kamata yayi ya sayo miki kaza in san samu ne sai ya hado da zakaran amma ba zakara daya jall ba".  Hasu hawayen naji suna kokarin zubowa da sauri na juya na shiga daki, bayan na goge na dan natsu na daukko hijab da wata yar kula mai kyau. Na fito nace, "Umma bari na karbo muku abinci, Kunzo abincin ya kare".  Har sun fara cewa na bari ni kuwa ban ko saurare su ba na fice. Duk da yamma tayi ban rasa abincin saidawa ba a wani restaurant shika fa da miya harda nama.  Na kuma sayo lemun kwalba biyu da pure water._



_Naje na kai musu.  Tun da na durkusa na ajiye Umma take kallona nasan cewa kuma kallan mamaki ne. Gefe na koma na sama waje na gaishe da Umma, Salima ta gaishe ni, bayan mun gama gaisawa nace bismillah suce abinci. Umma ta kalle ni hade da kallan kofar daki tace, "Wai ni kam ina Balan yake ne? Shi fa yace in zo yana gida". Dum! Naji gabana ya fadi Murmushi nayi hade da cewa "Umma ku dai kuci abincin tukun, ni nafiso kuci abinci ku huta tukun"._




_Bata min gardama ba suka juya suka dukufa wajen cin abinci. Zakaran nan ne ya fara wani dan kuka yana kallan mu. Umma ta juya ta kalle shi tace,  "Nusaiba ko dai baya da lafiya ne naji yana wani irin kara ga kuma abinci a gaban shi ya kasa ci". Ta karasa hade da kai lomar shinkafa baki. A zuciya nace, "Umma yaran ki ne ya koma zakaran nan". A fili kuwa murmushin yake nayi lokacin da na kai dubana ga zakara nace. "Baya da lafiya tunda aka kawo shi, Gashi ma yaki cin abinci"  "Ina ga gwaida ce ta ke damun shi". Shiru nayi ina tunanin wace karya zan zabga wa Umma. Nayi zurfi sosai cikin tunani har suka gama. "Nusaiba! Nusaiba!". Naji ana kira na. Sai lokacin na dawo daga duniyar tunanin da na tsunduma. "Me kike tunani haka ina ta magana kin yi shiru"._



Autan writers ✍





👨🏻‍💻👩🏻‍💻 ​*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​


        *'YAN MAFIYA*​
            ☠☠☠☠☠☠
     ​Gajeren labari​

 ​*Part 40-45*

© 🤴🏻 ​*KINGBOY ISAH* ✍🏼


.                👨🏻‍💻👩🏻‍💻        .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com



DEDICATED TO 👇🏽
😍 *Eloquence writers ass...*

😍 *Pen writers ass...*


🤘🏼 Ba karamin ji zamani take da ku ba. Allah ya albarkaci kungiyoyin mu. Allah kuma ya kara mana basira da son junan  mu. A kullum mu zaman ganji kwari kamar karfe. Farin jini kamar yashi a gurin yara.  👌🏼☺

Up^ Up^

 *Zamani*

 *Eloquence*

 *Pen*
🤘🏼


'       *KARSHEN PAGEN BAYA*     '

~"Nusaiba! Nusaiba!". Naji ana kira na. Sai lokacin na dawo daga duniyar tunanin da na tsunduma. "Me kike tunani haka ina ta magana kin yi shiru". Cewar umma,~


Murmushi nayi kafin nace, "Ba komai inna kawai ina tunanin Yaya bala ne. Dazun muna zaune a daki aka aiko wai yaje ana kiran shi. Shine ya tashi ya fita, ya dawo yana sauri kp wayar shi bai dauka ba yace sallama yazo ya min. Wai abokin shi ne ya zo zasu tafi kano an samar musu aiki". Umma ta daga hannun sama tace, "Alhmdulilah na dade ina addu'ar nan dama. Na gaji da wannan sana'ar dakon da yake yi. Kai yanzu mutane ba taimako wani fa dubu dari kada ta ishe shi jari. Amma sai ta gagara kuma duk ga masu kudi amma bazasu taimaka ba. Naji dadi na gode wa Allah. Kuma Allah yasa wa aikin nashi albarka._




_Haba ai ko kema kya huta da cin tuwo, dan nasan kina hakuri sosai Nusaiba ba abunda zance saidai ince Allah ya biya ki. Domin samun mata irin ku masu soyayya dan Allah ba dan kudi ba yana da wuya".  Wasu hawayen naji sun taho da sauri na duke kai na dan kwalla ta cika min ido, gaba daya tausayin mijina da na uwarsa dama ni kaina nake yi. Umma tace, "Naga kamar kina kwalla ko tafiyar da yayi ne baki so ba".  Murje-murjen karya na kamayi nace wani abu ne ya fada min ido.  Nan dai muka dan taba hira tukun mukayi sallama na raka su har bakin titi. Ban basu kudi ba dan kar su zarge ni._



_Haka na dawo gida cike da bakin ciki. Na zauna nasa zakara gaba ina kallo. Tunani biyu ne ke min yawo a kwakwalwa. Na farko rabuwa da mijina. Na biyu kuma taya zan fita daga kungiyar nan. Gashi sunce in ban kai jariir gobe asbar ba sai na mutu. Gashi naga tabbas, dan dan cikin su ya mutu.  Wata shawara ce ta fado min a rai. Nan da nan kuwa na dauke ta da mahimmanci.  Da sauri na mike na koma daki na daukko hijab dina na fito.  Napep na tsaida na hau bai sauke ni a ko ina ba sai babbar police dake kazaure._




_Bayan na biya mai napep cike da kwarin gwiwar da zuciyata ke ban na shiga cikin police din. Kai tsaye wajen masu rubuta report na nufa. "Assalamu alaikum  barka da aiki". Na fada ina kallan dan  sanda. Bayan ya amsa ya dauki bero da fefa ya kalle ni yace, "Me ke tafe dake?".  "Yallabai yan mafiya ne a bayan layin mu".  "Mine? *'YAN MAFIYA* ?".  Ya fada a zabure.  Abunda ya ankarar da sauran kenan duk sukayo wajen mu suna sauraro na. Naci gaba da cewa, "Eh *'YAN MAFIYA* mutane suke suna ci kuma jini ne abincin su".  Dajin haka ba awani bata lokaci ba aka hadani da 'yan sanda wanda sunkai su takwas ko wannen dauke da bindiga suka duru bayan motar._




_Ni kuwa gaba aka ce na shiga.  Jiniya aka kunne muka hau titi a guje ina nuna musu hanya motoci sai gocewa suke suna bamu waje. Direban na kalla nace, "A shawarce zaifi dacewa a kashe wannan jiniyar muyi musu shigar sumame".  nan da nan ya aminta da shawara ya kashe. Ba a dau lokaci ba muka karasa benen da nake da tabbacin nan ne gidan, Domin nasha zuwa ba sau daya ba, ba sau biyi ba. Nan take muka sasako yan sandan suka firfito suka zagaye gidan cikin shiri kowa ya haka bindigar sa._



_Nan take biyu daga cikin yan sandan suka nufi kyauren gidan domin ba gate bane irin na bakin titin nan ne wanda tsakar gidan daga ciki take. Dokan kyauren suka fara yi dan jinshi da sukayi a rufe.  Wani dan sanda ne ya dauki amsa kuwwa, ya fara magana. "Muna umartar ku da ku mika kawunan ku, domin yau asirin ku ya tonu bazaku tsira ba. Gwara ma ku mika kawunan ku cikin laluma".  Wata 'yar yarinya ce ta leko. Tana ganin yan sanda sun zagaye gidan nasu da gudu ta koma falo ta shedawa mahaifan nata.  Uban bai yarda ba sai da ya leko ya gani. Ai kuwa da sauri ya dawo falo ya kashe kallon da suke, domin shine ya hana su jin abunda ke wakana. Da gudu ya saukko downstairs lokacin da ya karaso yaji ana kokarin karya mai kyaure. Matan nashi guda biyu suma a tsorace suka rufo mai baya dan suzo suga me ke faruwa._




 _Da karfi yawa 'yan sanda magana a kan su dakata ya bude. Ai kuwa nan take sauran yan sandan suka matso kofar gidan duk suka nuno ta da bakin bindiga. Hannayen su a kan kunamar, jira suke suga badai-dai ba kawai su bada wuta._





_Yana bude wa yayi saurin daga hannuwa sama. Dan gani da yayi ana kokarin harbe shi.  Fitowa yayi daga cikin gidan hannun shi dage, yana tambaya me ya faru.  Daya daga cikin 'yan sandan ne yace, "Dr Habib kai ne?".  Ya juya ya kalli dan sandan cike da sanayya hankalin shi a tashe yace, "Eh nine Fahad lafiya me nayi kuma". Wanda aka kira da Fahad din ta juya ya kalli Nusaiba yace, "Ke Hajiya nan ne kuwa?".  Nusaiba da duk ta rude kanta taji yana juyawa. Sai yanzu ta juya ta kalli layin gaba-da-baya taga ai ba nan layin bane bama. To amma kuma da farko nan na gani. Na kalli dan sandan ina rawar jiki nace, "Yallabai Wallahi ba nan bane, inaga nayi batan kai ne. Amma na tabbata can layin  ne. Na nuna wani bangare da hannuna"._



 _Nan fa tsaki ya fara fita daga bakunan yan sanda. Hakuri suka bawa Dr. Habib domin Fahad yace, Ya sanshi likitan shi ne.  Nan take suka dawo suka hau mota duk ransu a bace, ni ma shiga nayi._





_Abun mamaki kwatancin naga ya dawo min sabo fall! Nan fa naci gaba da nuna musu hanya har muka karasa. Gidan yan mafiya,  kamar dazun suka fito suka yi attack wa gidan,  dana fito sai da na kare wa layin kallo hade da gidan na tabbata gidan ne. Tukun  Babban cikin su yazo ya tambaye ni a kan cewa na tabbata nan ne? Nace masa eh. Nan take mai amsa kuwa ya shiga shelanta cewa mutanen ciki su fito su mika wuya. Ana cikin haka sai kawai muka ga mota ta faka,  mutane biyu ne suka fito sanye da kakin sojoji. Suka nufo wajen mu. Hade da tambayar lafiya. Nan take dan sandan ya fada musu abunda ya kawo mu.  Daya daga ciki yayi dariya yace nan ai gidan sa ne.  Kaina ne naji yayi wata irin kullewa naji wani hajijiya. Kafin kuma sai naji ni normal._



_Dan sanda cikin tsawa yace. "Ke nan ne ko ba nan ba?".  Juyawq nayi na kalli farko da karshen layin hade da gidan da na kawo su. Sai nagama ban taba sanin layin ba. Nan take na tuno da batun yan mafiya. Da yace ko na kira yan sanda bazan gane gidan ba. Nan fa na gane asirin su ne ya hanani gane gidan._





_Marin da aka gaura min ne yasa ni Dawowa daga duniyar tunanin da na lula. A zabure n bawa dan sandan dake tambaya ta amsa. "Aa Wallahi ba nan bane". Wani marin ya kara min cikin masifa yace raina musu wayo ne nake.  kuka na kama dan zafin marin.  Yan sandan  hakuri suka bawa sojojin suka turani mota kowa tsaki yake ana hararata har muka karasa office.  Nan take mukaje suka shedawa D.P.O duk abunda ya faru. Sama da kasa ya kare mun kallo yaga dai ni ba mahaukaciya bace. Ya tambaye ni na fada mai gaskiya.  Nan fa na hau rantse-rantse ina sheda musu Wallahi ba karya nake ba. D.P.O yace, to shikenan ya yarda inje in na tabbatar da gidan sai inzo in sanar da su. Yama kara da cewa in bar wani tsaro in na tabbatar da gidan dan kar in sake batan kai. Godiya nayi na fito duk an kunbura min kumatu da mari,  yan sandan basu so aka barni na tafi haka ba salun-alun.  Adai-daita na tsayar ya kai ni gida. Ina shiga gidan mukayi ido hudu da mijina dake a matsayin zakara. A yanda na barshi haka yake dai har yanzu. Ba alamar yaci abinci, sannan kuma a inda na barshi bai motsa ba a nan dai yake._



_Ajiyar nunfashi nayi cike da tausayin shi na dauke shi na shiga daki da shi.Rairan na kwanta a kirjina na dorashi ina kallan shi ina zubda hawaye, "Banzan taba mantawa da kai ba a rayuwa Yaya bala. Duk ni na jefa ka cikin wannan yanayi, laifina ne ka yafen yaya bala. Sanna...".  Hahahaha  naji gaba daya dakin ya kashi wata mahaukaciyar dariya..,......................................_



😦 Ni dai ina daga gefe ina kwaso muku labari. Wannan dariyar tasa nayo waje a guje 🏃🏻🏃🏻🏃🏻 gudun da nake ko yan Zamani da Eloquence bazasu iya kamani ba dan na tsora ta. 😆




Much ❤ Fans

Autan writers ✍







😘 *DEDICATED TO MY HEART PART*
I MEANING ZAMANI MEMBERS😍

Kun zamto ginshiki a gare ni. Wanda nake jin in har ba ku bazan iya takawa ba. Tafiyar ku da kasaita zamanawa mutum baya damun ku balle abun hannunsa ya tsokale muku ido 😚😉. Kun ringa da kun gagara dole ne ayi kurum da lamuran ku. Ikon Allah kuke tashin jirgi... 🤔 Ba mai daga ku saidai Allah.   Hakuri da juriya maganin zaman duniya. Komai da lokacin sa zamanawa. 😉 Wannan lokacin ku ne. Kuyi amfani da damarar ku wajen ankarar da al'umar ku yanda zasu zama masu alfahari daku.  😍 Ina sonku.. Allah ya kara mana hakuri da juna. Hadin kanmu shine abun alfahari na. I'm with u zamanawa duk rintsi insha Allah 👌🏼💪🏼
✍ Dan Autan ku king 👑

 °       *KARSHEN PAGEN BAYA*  °
~Ajiyar nunfashi nayi cike da tausayin shi na dauke shi na shiga daki da shi.Rairan na kwanta a kirjina na dorashi ina kallan shi ina zubda hawaye, "Banzan taba mantawa da kai ba a rayuwa Yaya bala. Duk ni na jefa ka cikin wannan yanayi, laifina ne ka yafen yaya bala. Sanna...".  Hahahaha  naji gaba daya dakin ya kashi wata mahaukaciyar dariya.~

_*S*osai na tsorata nan take na fara waige-waig dan ganin wanda ke dariyar amma ban ga ko dan tsako ba. Maganar da na fara ji anayi ita ta tabbatar min da cewa shugaban kungiyar mu ne. Muryara shi ce ba banbanci da ta wajen. Yana magana cikin dariya, "Nusaiba kenan, shin ban gaya miki ba dama? Ko kin dauka karya nake miki? To ya kamata wannan ya zama izina a gare ki ki kiyaye sabawa dokokin  mu. Yanzu babban abun da ya kamata ki maida hankali kuma ki kiyayye dan karki rasa ranki shine kawo jariri. Dan yanzu awoyin mutuwar ki ne aka fara kirgawa".  Dif! Naji shiru, maganganun sa sun girgiza ni matuka. Nace "Turkash! Wata sabuwa inji 'yan ca-ca. Wai in ban kai jariri ba mutuwa gobe, lalai da matsala"._





_Ina tunani ina shafa gashi  shafaffen mijina da aka mayar zakara, a haka har barci ya kwashe ni. Nan fa nata mafarkai barkatai. Ban tashi farkawa ba sai wajen karfe 8 na safe, gari ya waye. Jina nayi a cikin wasu takardu wanda sun cika gadon har zuba ma suke. Firgigit! Na mike a tsorace na  danko Takardun a hannu na gwale ido ina kallo. 'Yan dubu-dubu ne sababbi kar!.  Na juya na kalli gadon da tsakar daki duk kudi ne, iska ya kwasa ya war-watsa.  Jin dadi da farin ciki ne suka mamaye zuciyata. "Wannan kudin daga ina haka". Lokaci daya kuma sai murna ta koma ciki, nan take na dukufa neman zakara. Zakara yace dauke ni inda kika ajiye. Sama ko kasa na rasa zakaran nan har karkashin gado na duba amma ban ganshi ba. Na fito tsakar gida duk na lalleka inda nake tunanin zai shiga amma baya nan. Kuka na fashe da shi mai tsuma zuciya._



_Nan take na fara wasu tambayoyi da bansan wa nake tambaya ba, balle nasa ran za'a bani amsa. "Shin wai yanzu shikenan na rabu da mijina farin cikina masoyi na annurin zuciya mai haske idaniya ta?. Wai yanzu ana nufin mijina ne ya koma wadan can takardun da na guji mai su na aure shi saboda son da nake mai. Wayyo yanzu ya zanyi da rayuwa ta? Taya zan rayu ba babu kai? Ba ayi namijin da zan kalla a matsayin miji ba bayan kai yaya bala". Na sake fashewa da kuka.   Kamar daga sama naji ance, "Ba abunda rayuwar ki take bukata a yanzu sai ki cece ta. Domin a yanzu awoyi ne kike da su. Ki sa a ranki in baki kawo jaririn da muka bukata ba, yau shine wunin ki na karshe a duniya. Kuma nasan zuwa yanzu dole ki gaskata zantuka na domin kwararren hujjoji sun bayyana a gare ki kuru-kuru". Wani turirin turnukin bakin hayaki ne na bakin ciki naji ya cika zuciya ta. Wanda ya kunburata sumtum kamar ta fashe. Nan take na fara huci kamar mesa, a wannan lokaci da ace ina ganin shugaban 'yan mafiyan nan da ba abunda zai hana in kashe shi. Na tsane shi na tsani kungiyar na tsani mai san kungiyar. Ban san lokacin da na fara surfa masifa ba duk-da baya gani na. "Banaso-banaso baza a kawo jaririn ba ku kashe ni, marar imani kawai. Kuma Allah ya isa tsakanina daku bazan yafe ba, kuma duk kudin da kuka ban yanzu zan toya su, dan banga amfanin su ba. Kuma bazan kawo jaririn va ina jira ku kashe ni kamar yanda kuka kashe mijina"._






_Ina fadar haka na tashi a fusace na shiga daki. Wani buhu na dauka na fara dura kudin da niyar banka musu wuta na toya. Sai da na kwashe su tsaf, na zuba a buhu har na karkashin gadon ban bari ba. Nazo fitowa kenan naji magana a tsakar gida. Kuma maganar maza samari. A tsorace nayi baya na boye buhun kudin tukun na leka. Mai gidan da muke ciki muna haya ne ya gayyato 'yan daba, fuskar sa ba annuri ba haske balle ka nema murmushi ma a ciki.  Samarin su uku duk kattai ne majiya karfi madaka karti, sai hararena suke suna hura hanci. Na fito cikin sanyin murya nace, "Alhaji lafiya kuwa". A tsawace yace, "Ba lafiya ba,×  ai kin fini sanin me ke faru yau wata uku kenan mijin ki bai biya ni kudi na ba. Tun ina hakuri yau hakurin nawa ya kare. Dan haka ko ina yake ya fito ko dai ya bani kudi na. Ko kuma Wallahi in sa wannan matasan suyi facali da kayan ku out"._




_Hadiyar yawo nayi, sannan na kakaro murmushin karfi da yaji na shimfida a fuskata na dubi Alhaji nace, "Allah ya huci zuciyar ka. Hakika kayi hakuri matuka kuma alhmdulilah dama mai gida ya tanadi kudin ka yace in kazo in baka. Bari na daukko ma". Wani shegen kallo yake min ya zuba min ido da alamar yayi shiru ne dan ya kure karya ta.  Daki na koma na daga buhun nan na zaro kudin da bansan ma ko nawa bane. Amma kudin zasu kar dubu hamsin ko ma su fi. Na fita cikin fargaba  na mika mai kudin ina cewa, "Yace ka dauka iya kudin ka na wata ukun ka kawo na ajiye mai sauran".  Alhaji yana murmushi yaga kudi masu gidan rana. Ya karba ya lissafa. Daga bisani ya kalle ni yace, "Yarinya Allah ya taimake ki yau, ba dan kun biya kudin nan ba yau da kinga wulakanci irin wanda baki zata ba. Dan da sai nasa anyi daya-daya da kayan ki a layin nan". Bayan ya dan tsagaita yaci gaba da cewa. "Dan haka yanzu kin tsira kudin nan kuma na ciri na wata uku kuma na dauki sauran a matsayin na wata shida. Domin bazan yarda in bada canji ba yanda mijin nan naki ya iya fadar babu kamar wanda aka wanke wa hatimin talauci. In ya dawo kice mai na zo na karba Allah ya rufa muku asiri._






_Da fadar haka ya juya 'yan daban shi suka rufa mishi baya". A nan tsakar gidan na zauna kan kujera ina tunanin yanda kudi suka zamar mana bala'i a rayuwa. Kudi a wannan zamanin suna raba danganta raba aure raba uwa da uba. Kai kudi yanzu in sukayi yawa har mahaliccin ka suke raba ka da shi.  Godiya nayi ga Allah da yasa ban toya kudin nan ba. Da naga tashin hankali. A zuciyata sake-sake nake kawai ta ina zan rama abunda Shugaban 'yan kungiyar nan yayi min.  Dan har yanzu ban yanke shawara ba. Shawara biyu nake, in bari in ki kai jaririn  in mutu. Ko kuma in kai jaririn kuma in rama abunda akayi min na kashe man miji._




_Inyarrr! Inyarr! Kukan da naji yana tashi daga gidan Maryam kenan. Wato kukan jaririyar ta.  A guje na tashi na nufi wajen katangar dake tsayina baya isa in  gano ciki na dauki turmi da sauri na leka. 'Yar jaririyar ce  kwance cikin farin zani tana sanye da kayan sanyi. A tsakar gida kan tabarma kuma gidan naga kamar babu kowa.  Nan fa duk na rikice ina shawarar yanda zan sato yarinyar nan. Da gudu-gudu na nufi daki na sako katuwar hijab dina. Na fita sumai-sumai ina waige ba kowa a anguwar na shiga gidan maryam har yanzu dai yarinyar ke kuka kuma ba kowa a gidan. Ina zuwa nasa mata yatsa a baki ta zaci mama ne. Nan take ta yi shiru na kuwa sabo ta cikin hijab._










_Tafe nake ina waige-waige tafiya ce ta  munafurci da tsoro. Nasan cewa in aka kamani kuma aka gane kudirina to fa tawa ta kare. Bani da ta cewa, nasan in ma aka babbake ni da wuta an min karamin hukunci. Hakan tasa nake ta sauri, naje shiga gidana naji an kira sunana. Nusaiba!. Ban tsaya ba balle na juyo. Naji dai muryar mace ce. Ina shiga gidan na banka kyauren nasa sakata har biyu. Zuciyata sai bugon tara-tara take, lalai na cika mai karfin hali. Na jinjina wa kaina. Wayar dake makale a jikina na fiddo na kira. Duka daya ya dauka. Cikin azarbabi nace, "kayi sauri kazo gafa jaririn na sato". "Kai amma naji dadin wannan canza shawara da kikayi Nusaiba. Kin ceci kanki. Gani nan zuwa. Amma kafin inzo tunda a gidan ki kike ina so ki yanka jaririn". Dum!  Naji gabana yayi wata irin faduwa. "Yankawa?". Na mai-mai ta.  "Eh Nusaiba ba, haka na fada ki yanka shi". Jikina yayi sakalau na katse wayar._ 




_Wani gwabran nunfashi na sauke, Nan take na shiga sake-sake a zuciyata. Shin in yanka jaririyar nan ko kuwa?. Ta dayan bangaren kuma wanda ya kirani din nake tunani na dai ji muryar mace amma bansan ko wacece ba. Wata muguwar marar imanin zuciyata, wacce ta saba saka ni aikin asha! A wannan karan ma itace ta bani shawarar in yanka yarinyar dan gudun sabawa ogan kungiyar mu. Dake na saba yarda da shawarar wannan azzalumar zuciya haka yanzu ma na aminta nabi zabin ta. Kai tsaye na nufi kitchen na daukko dalleliyar wukata. Wacce ba a dade da waso min ita ba a kasuwa. Jaririn na dauka nasa a robar wanka gudun kar jini ya bata min gida asiri ya tonu. kujera na daukko na zauan a kai hannuna rike da wuka nasa robar jaririyar gaba ina kare mata kallo kamar wacce zata yanka kabewa ko fere doya. Kamar su daya sak! da makwabciyar mu Maryam. Duk da yau kwanan jaririyar uku da haihuwa but sai ka rantse kace tayi sati uku ko wata. Domin a koshe take bul-bul.  Kallan ta nayi zuciyar nan tawa ta kara tunzurani nan take naji wani sabon rashin tausayi da rashin imani sun ziyarcen lokaci guda. Ban yi wani tunanin halin da mahaifiyar ta zata shiga ba. Na daga wuka da niyar tsinke mata wuya.  Cik! Na dakata sakamakon jin ana kwankwasa kofar gidana da karfi........................................_



😱😱😱😱😱😱😱😚 Kunga asalin novel din status din nan



Autan Writers ✍
👑King boy👑







👨🏻‍💻👩🏻‍💻 ​*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​


        *'YAN MAFIYA*​
            ☠☠☠☠☠☠
     ​Gajeren labari​

 ​*Part 50-55*

© 🤴🏻 ​*KINGBOY ISAH* ✍🏼


.                👨🏻‍💻👩🏻‍💻        .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


😍🌹 _DUK TSAYIN PAGEN DA FADIN SA. HAR MA DA DADIN SA. NAKI NE KE KADAI BAN HADAKI DA KOWA BA._  *MUHIEVERT ER INDIA ER LOVE,*

😉 Zan shigo ajin nan domin nima na zama Hadadden masoyi. 😍 Ke din fa daya ce amma kinfi million wane dubu. 👌🏼 Takama kike da ikon Allah ba dai mutum ba sai dai Allah. Mahassadanki kuma fadawan ki. 👌🏼 Kin yi daban ko a cik.... Kai bari na gimtse baki na dan kam ban iya kirarin ba balle na miki. 👨🏻‍💻


•        *KARSHEN PAGEN BAYA*    •
~Ban yi wani tunanin halin da mahaifiyar ta zata shiga ba. Na daga wuka da niyar tsinke mata wuya.  Cik! Na dakata sakamakon jin ana kwankwasa kofar gidana da karfi.~

_Tunanina bai bani wani ba sai oganmu domin nasan cewa mijina baya raye ballema in zaci ko shine. Da sauri nace "Sir jira gani nan". Ina kokarin tashi.  Muryar da naji anyi magana da ita ta daga min hankali, Muryar maryam ce. Nan take jikina ya fara bari na shiga laluben maboya, mafaka a kwanyata. Da sauri na dauki wayan na kira oga. Nace masa karya zo domin ga uwar yarinya ta zo. Tsaki yayi ya kashe wayar, ni kuwa na tashi da sauri  na dauki jaririyar na mayar cikin zanin. Na zuba ruwa a cikin robar cikin hanzari na daukko kwandon wanka na ajiye a gun.  Jaririyara a hannu na nufi kofa ina cewa "Maryam dakata in bude mana karki balla mana kyaure". Ina bude wa naga Maryam din gabadaya yanayin ta ya sauya duk a rikice take, dan ko dankwali babu a kanta balle mayafi. Tana ganin  'yar ta a wajena sai ta sauke a jiyar zuciya. "Wash! Wallahi har naji wani irin sanyi mai dadi ya ratsa zuciya ta". Ta rike baki cikin mamaki da fargaba taci gaba da cewa. "oh! Ni Maryama. Yanzu da an sace Yarinyar nan me zai faru in baban ta ya zo. Nusaiba ashe ke kika daukko ta?". Sai lokacin na juya bakina daga galala da nayi ina kallan ta zuwa wata kagaggar dariya wacce bansan ko daga ina ma na lalubota ba. "Eh wallahi ni na daukko ta. Naji sai kuka take kuma na leka naga sai ita kadai, shiyasa ma naje na daukko ta". Na nuna saitin robar wanka da yatsa. Naci gaba da cewa, "Kinga wanka zan mata ma". Maryam tace, "Wallahi gudawa ce ta sakani gaba tun jiya, daga cin naman kai. Amma fa karki so kiga irin rudewar da nayi dan na dauka barayin mutane ne suka shigo suka dauke min ita. Bani ita". Na mika mata ina cewa "Wankan fa?". Tace, "Wallahi ban dade da mata wanka ba"._ 




_Dan murmushi nayi nace, "To shikenan. Amma dan Allah ba gudawa ba ko ma miye ki bar barin ta ita kadai a tsakar gida ba kyau". "To". Ta fada ta juya ta koma gida. Na dade a nan tsaye ina sauke ajiyar Zuciya. "Ni yau da an kamani da na shiga uku. Naga samu kuma naga rashi". Cikin gida na koma ina ta tunanin in bari lokaci ya cika in bi mijina in mutu ko kuwa in je in sato jariri inci gaba da rayuwa?. To ni in ma naci gaba da rayuwa masu tambaya ina mijina ya zance da su?. Ya zance da babar sa?. Wani kululun bakin ciki ne yazo wuyana ya tokare, nan take tsanar Ogan mu ya kara tsanan ta a zuciyata. Nan na yanke shawarar ci gaba da rayuwa ba dan komai ba dan in rama abunda ogan yayi min na kashe min miji. Domin ni shi na dorawa laifin. A gogon dake like a bangon dakin na kalla. Karfe tara  dai-dai. Wannan na nuna cewa ina da sauran awa sha uku ne kacal a raye in dai ban kawo jariri ba._





_Lalai yau komai a gagauce za'ayi sa. Da sauri na tashi na shiga bayi nayi wanka, nazo na zabi kaya masu kyau daga cikin kayayyaki na. Na dauki wata zumbuleliyar hijab na saka, na kuma dauki katuwar jakata hade da daukan kudi wanda yawansu zai kai dubu 60 ko sama da haka.  Na dauki waya na kira ogan cikin bacin rai kamar bana san yin maganar na tambaye shi, shin jaririn dole sai mai rai ko matacce ma suna so. Naji dadin amsar da ya bani cewa har mataccen ma.  Fitowa nayi na kulle gida. Ko sallama banwa Maryam ba. Na kama hanya na mike ni kaina bansan ina na nufa ba. Tafiya nayi mai nisa ina dube-duben gidaje. Wai ni so nake naga gidan da akayi haihuwa ko gidan suna inje in gwada sa'a ta. Karfe goma tuni nayi nisa a yawo na har ma na fita daga anguwar mu na kusa zuwa Bagara.  Jin nayi kafata kamar zata tsinke hakan tasa na tsaida wata napep da naga ta tun karo ni._






_Mata ne biyu wanda duk a cikin su ba sa a ta. Duk na girme su. Tun kafin na hau naji suna magana dayar na cewa, "Ni fa Wallahi dan dai kar muyi abun kunya shiyasa zanje wa Fauziyya barka. Kinga yau sauran kwana biyu suna. Da jin haka na kasa kunne ko ba komai rai na yayi fari duk dabarar da zanyi ni kuwa sai na bisu. Dayar ce ta fara magana "ke dai bari kubura. Lamarin na ai sai a hankali abun ya zama kamar bashi, in baka je ba shikenan kayi abun surutu. Ni fa cikin satin nan a busy nake wallahi ayyuka duk sun ishe ni ga bani da kudi. Da kyar Sade ya barni fa na ta ho. Dan yama kidaye min lokaci wai kar na yarda na wuce sha daya kinga kuwa ina zuwa naga jariri nasa albarka shikenan sai nayi sallama na fito abuna". Da sauri  kubura tace,  "Ki fito ko mu fito". Jin haka tasa nayi saurin shiga mai napep yana tambaya ta ina zai kai ni, nayi banxa da shi na shiga gaisawa da wannan matan.  Mai napepk ya gaji har ya fara ma tafiya._






_Can na nisa nace, "Sha'anin mu mata sai dai ayi kurum. Mun maida al'ada kamar addini, tunda akayi haihuwar nan yau saura kwana biyu suna, amma kullum sai an min masifa wai banje barka ba. Yau dai nace bari naje in huta". Kubura tace, "Sauran kwana biyu kika ce? Gidan wace zakije mu gidan Murjanatu zamu itama yau saura kwana biyu sunan ta".  Kamar da gaske na juya da sauri nace, "Lah! ai kuwa gidan murjanatu zani, ashe waje daya mukayi. Kai mai napepk waje daya zaka kai mu". Ummi tace, "Ashe gu daya zamuje. Kinga Murja kawar muce ta kut!-da-kut!". Sai da cikina ya dan kada ina dan zazare ido game da karyar da zan fesa Allah yasa ta hau, na ce. "Ai ni kawar yayar ta ce, to itace ma ta takura min wai dole in je barkar nan"._





_Kubura ta dafe haba alamun tunani. Daga bisani tace, "Dama murja nada wata yaya ne bamu sani ba?".  Dum! Naji kirjina yayi wata irin bugawa. Murmushi nayi nace, "Ai ba lalai ku santa ba. Zahra sunanta 'yan uba suke da Murja". Ummi tace, "Aiho! Ai yan uwan maman murja suna da yawa sosai". Nan take naji wani sanyi a raina. Bansan lokacin da na sauke ajiyar zuciya ba. Nan dai mukaci gaba da tafiya har muka karasa. Dan karamin gidane wanda na tabbata mutanen ciki basu da yawa domin kuwa irin gidajen amare ne. Bayan mun bibiya shi kudin gaba daya muka runkuta cikin gidan gabana sai faduwa yake. A hanya muka hadu da wasu 'yan barkar zasu fito. Muka gaisa tukun muka karasa ciki. Su biyu ne kawai a gidan. Daga Murja mai haihuwar sai kuma wata yar dattijiwar mata wacce nake tunanin yar uwarsu ce mai dan taya ta aiki  dan har muka shiga daki bamu ma san tana nan ba. Sai da tazo neman wani abu sanna muka gaisa da ita, ta kuma koma kicin tana hada abinci.  Ummi da Kubura sai da suka rungumi suja cikin daukin suka gagaisa. Yanda na ringa nuna kulawa har wajen gaisuwar sai ka rantse da Allah. Kace Murja 'yar uwar mu ce ko kanwata._




_Bayan mun gagaisa ta kawo mana ruwa tana wa su Ummi jaraba wai basu zo ba sai yau an kusan  suna, tace ai yaseen sai sun wuni. Nan suka ta zano mata matsaloli amma taki yarda fur wai ita sai sun wuni. Murja a tunanin ta tare muke da su Ummi. Suma kuma su Ummi yanda sukaga ina kulawa da ita da tsare-tsare suka gaskata lalai ta sanni. Domin Murja ta kasance mai sakin fuska sai balgata dariya take kamar gonar auduga baki yaki rufuwa. Yaro ne fari sal da shi kyakyawa ta miko mana. Su Ummi suka fara karba. Ya dade a hannun su tukun suka miko min. Nan naci gaba da rikon shi ina tsokalar  ina cewa yaro yayi kyau kai kace ta dade da sani na can dama._




_Su Ummi suka ce zasu tafi fur taki yarda. Da dai sukaga da gaske take bazata barsu su tafi ba. Sai sukayi karyar cewa zasu je nan baya gidan yayar kubura su dawo. Dajin haka nayi farat! Nace, "Yauwa kuje ku dawo sai mu tafi". Murja jin nasa baki kuma tana tunanin tare muke yasa ta kyale su suka tafi. Nan dai naci gaba da rikon jariri tana linke wasu kaya muna dan taba hira ina yabon kyan yaranta. Su Ummi kuwa shiru har yanzu. Tashi tayi tace, "Dan Allah kiyi hakuri bari na dan shiga toilet,naji cikina na murdawa". Murmushi nayi nace, "Ok to sai kin fito. Ni nag ka su Kubura sun ki dawo wa".  Tace, "Ai dole su dawo ko dan ke ma. Dan saboda ke ma na barsu  suka tafi nasan dole su dawo daukan ki". Murmushi kawai nayi nace, "Ai kuwa dai dan basu isa su tafi su kyale ni ina bakuwa ba"._






_Bata ce komai ba ta fita. Da fitar ta ba a jima ba na leko waje. Dayar matar na kitchen jajage take yi abunta hankalin ta ko kadan  baya nan. Ai kuwq da sauri na koma na tusa jariirn a jaka wanda sai barci yake. Na fito a sukwane nasa ta kalmina. Sauri-sauri gudu-gudu na bar gidan.  Ina fita kuwa na kwasa da gudu ina waigen baya. Ta wani dan lungu nabi kasancewar wajen bayan gari. Gudu kawai nake  tsabar gudun da nake ni ya jijiga jaririn nan ya tashi ya fara tsala ihu!. Ba shiri na fito dashi daga jakar na rike a hannu baci gaba da sauri ina jijiga shi. Har Allah yasa na kawo bakin titi. Da zuwa ban dade ba sai ga mai adai-daita, nan kuwa na tsayar da shi, wajen hawa na fito da yaron a dai-dai lokacin direban napep din ya juyo, yana ganin yaro naga ya sake juyowa. "Kai wannan kamar dana".  Dum! Naji gabana ya fadi. Dan  acikin hirar da su Murja suke. Naji tace, mijin ta ya tafi haya......................................................_



😳😰 Ni dai King doke in tsaya a nan in jinjina wa Nusaiba.  Sannan mu tsaya muga me zai faru tsakanin t da wannan mai cewa danshi ne



Autan Writers, Autan Zamani. ✍







👨🏻‍💻👩🏻‍💻 ​*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​


        *'YAN MAFIYA*​
            ☠☠☠☠☠☠
     ​Gajeren labari​

 ​*Part 55-60*

© 🤴🏻 ​*KINGBOY ISAH* ✍🏼


.                👨🏻‍💻👩🏻‍💻        .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


*DEDICATED TO OLL FANS*  😍 Ana tare

🙈 _*Ban san da wanne irin kalamai zanyi amfani wajen baku hakuri ba abokai.*_ 😔 _*Amma dai kuyi hakuri kwana biyu uzuri shine ya dace da kuyi min. Dan duk cikin satin nan busy nake. Anyi auren abokina ne, to ni kuwa in ba a nutse nake ba bana iya type shiyasa kuka jini shiru. Amma yanzu kam komai ya lafa. Zaku na jina. Sai dai ku taya ni addu'a kai na ciwo*_ 😫




•       *KARSHEN PAGEN BAYA*  •
~wajen hawa na fito da yaron a dai-dai lokacin direban napep din ya juyo, yana ganin yaro naga ya sake juyowa. "Kai wannan kamar dana".  Dum! Naji gabana ya fadi. Dan  acikin hirar da su Murja suke. Naji tace, mijin ta ya tafi haya.~

_*F*uskewa nayi na basar, na lulube tsoron dake a fuskata na shige napepk din na zauna bayan na mayar da yaron cikin hijab. Na danyi murmushi tukun nace, "Ashe kai ma an maka haihuwa? To Allah ya raya".  "Amin ya fada fuskar shi ba alamar gamsuwa. Dan naga yayi wani jim! Kadan yana nazari sannan kuma sai naga yayi gaba. "Ina zamu je". "Tsohon kafi". Na amsa da sauri. Dan tsoro nake ya kai ni anguwar mu kuma yaje ya duba dansa babu ya dawo. Bansan kowa a Tsohon kafi ba a bakin kofar wani gida nace ya sauke ni ga gidana nan. Bayan na biya shi kudin sa sai naga ya tsaya baya da alamar tafiya ma.  Ni kuwa ganin haka sai na tunkari gidan nan da ban san kowa a gidan ba, ni layin ma ko hanya bata taba biyo dani ba. A zauren gidan na labe wani lungu, inaji saida ya kwashi kamar mintuna biyu tukun ya tada napep dinsa a guje ya juya. Ai da jin ya tafi na fito da sauri na canza hanya na sama wani mai napepk din ya kai ni anguwar mu magama. Bayan na biya shi na wa-waiga naga ba mai ganina. Nan take na dafe kirji na kira sunan dodon tsafin nasu. Sai gani a tsakar falon rike da jariri. Ogan na ganina ya kama washe baki kamar gonar abduga ya taso ya nufo ni._





_"Nusaiba gaskiya ke jarumar mace ce, kinyi matukar kokari. Na zaci zaki ai kin zabi kibi mijin ki lahira ne. Ashe dai kina son ranki. Au! Na manta ya hakurin rashin mijinki, ni kaina banso kika rasa mijin ki ba, amma ya muka iya haka Allah ya so". Maganganun shi zafi suke mun a zuciya kamar ana zuba min jan garwashi. Kawai daure wa nayi na kuma dake, dan ji nake kamar na rukunkume shi na shake shi shima ya mutu. Sai dai bazan iya da shi ba, ko da kuwa ina da karfin ja da shi ai ga yaran shi cike da falon. Bance komai ba na mika mai jaririn dan fari da shi sai kallona yake a yanzu ya bar kukan. A karo na farko kenan da naji tausayin sa.  Ogan yana wata shu'umar dariya irin ta tsofaffin mugaye ya karbi jaririn yabi hanyar wani daki yace, "biyo ni". Ba gardama kuwa nabi bayan sa. Sai da muka ratsa ta dakuna kusan goma yan madai-daita wanda duhu ya cika su kai kace dare ne ba dan fitilun kwan da ke ciki ba da ko tafin hannun ka baka iya gani. Tafe yake cikin jar riga doguwa wacce har jan kasa take, kanshi ma ya daura jan kyalle. Hannun shi rike da jaririn ina biye da shi, har muka karasa daki na goma sha daya. Sosai dakin yake da abun tsoro dan haka kawai na ringa jin kamar ihu a baya na._




_Ga jikin bangon dakin duk wasu kasusuwa ne kwarangwal a dadaure.
Ga jikin bangon dakin duk wasu kasusuwa ne kwarangwal a dadaure. Wani carpet ya bude nan fa na tsura mai ido da naga kofa ce gurin. Bude wa yayi ya fara taka matatakalar yayi kasa tukun ya juyo yace min in taho. Cike da tsoro nabi bayan shi muka shiga wannan dakin kasan. Haske fau ko ina akwai fiilar kwai, Tun kafin mu karasa sauka kasa na fara hango kamar mutum a rataye a bango. Nan take na kara lekawa tun kafin mu isa wajen. Ihu na kwalla da karfi hada da toshe kunnuwa na. Yara biyu ne daya babba daya kuma karami. Karamin zaiyi shekara 5 babban kuwa zai kai akalla ashirin ko sama da haka dukan su ba kaya a jikin su._





 _An kwakware kayan cikin su. Jan jini kawai kake hange a gun. haka kuma idanun an cire su sai bakunan su a hangame  duk sun bubude. A fusace ogan ya juyo ya daka min tsawa yace,  "Kiwa mutane shiru ko yanzun nan dodon mu ya shanye miki jini".  Nan fa jikina ya hau rawa duk jarumta irin tawa sai na rana kaina domin na tsorata. Sai da ya karasa gafda wannan Yaran nan rataye ni dai ina binsa ina karkarwa sannan ya nuna karamin yace, "Wannan yaro na ne, ni na sace shi na kawo shi nan don biyan bukata ta. Babban nan kuma kanina ne. Daga kauye na daukko shi nace wa iyayen mu makarantar allo zan kai shi". Ni dai jinshi nake ina karkarwa ina binshi da "To-to!"._






_Yaci gaba da cewa, bari kiga abunda zai faru yanzu, idan aka zuba jinin a cikin su a nan za a barshi dodon mu zai ringa sha nan ne matsayin kofin shi. Idan kuwa muka bukaci kudi bari dai na nuna miki". Yana fadar haka naga ya nufi wani dan akwati dake kan wani benci a gefe. Ya bude naga ya zaro wata doguwar wuka sai kyalli take. Tsoro ne ya kamani nama zata ni zai yanka.  Gaban yaran  nan ya zagayo ya saita wuyan jaririn a saitin kwakwararren ciki  tsik! Ya fille mai kai ya fadi can kasa. Ni kuma ihu na kwalla. Hankali na duk ya fara ficewa daga jikina. Ban taba ganin marar imani irin wannan ba. Kan jaririn da ya fadi can kasa yana zubar da jini yace na miko mai. Cikin rudu da tashin hankali naje na durkusa na daukko hannuwa na na karkarwa.  Sai da ya gama tsiyayye jinin kaf! Sannan ya naga ya saka gangar jikin cikin wata roba. Ni dai duk tsoro ya kamani._






_Gefe guda ya dawo ya kalle babban ya kira sunan shi,  nan take naga yan dubu-dubu suna fitowa daga bakin shi a guje.  Tsuru nayi ina kallo kafin kace me kudi sun cika mana gaba. Ogan ya kalle ni yaga mamaki karara a fuskata. Dariya ya kashe da ita sannan yace,  "Kwashi million biyar nasan kudin nan sun ma fi haka. Da sauri nace, "A a na yafe Wallahi". Dariya yake ya juya ya daukko jaririn tukun ya kama hanyar fita, da sauri na bishi. Har muka isa falo jikina rawa yake, Sallama nayi mai cike da tsanar shi nace gida zani. Wata mata dake zaune a gefe tace, itama yanzu zata tafi. Nace tazo mu tafi._





_A hanya na fara mata tambayoyi domin so nake na gano lagon Ogan nan dan nasha alwashin sai na dauki fansa. Nace, "Wai dan Allah da gaske mutum mutuwa zaiyi in bai kawo abunda kungiya ke bukata ba".  Matar tace, "Kwarai kuwa mutuwa har lahira in dai baka kawo ba. Dan akwai wata kawata mai suna Hadiza watan ta biyu da mutuwa yanzu kuma itama ta mutu ne ta dalilin kin kawo jariri"._





 _Ajiyar zuciya na sauke tukun nace, "Kenan yanzu ba wata mafita haka rayuwar mu zata ta walagigi duk asabar rai yana barazanar barin gangar jiki in har ba a sama jaririn ba".  Matar tace, "Ai kuwa dai, to ke in ma tambaye ki a ina kike samowa ne?"  Nace, "Ni ai wannan ne karon farko da na kawo kuma daga zuwa barka".  "Barka!". Ta mai-maita maganar tana jinjina kai, nace "Eh". "Lalai in kin tsira yau gobe ba tabbas ki tsira". Gabana ne ya fadi ras! Nace, "To a ina ake samowa?". Dan murmushi tayi "Kinga ni kawata wacce ta mutu aikin asibiti tke yi, shiyasa ma bata jin wani wuyar satowa a asibiti. Ni kam kinga ba aiki na ba kenan a kungiya amma da ace aikina sato jariri ne, da uniform din nurses zan dinka Wallahi in ringa shiga ina satowa"._




_Jim! Kadan nayi ina tunani.  naji shawarar ta kwan min a rai. Wata tambayar na sake jefa mata ba tare da na bi ta kan waccan maganar ba. "Wai yanzu dan Allah 'yar uwa, misali in kina so ki kashe ogan kungiyar mu ta wacce hanya zaki bi?". Murmushi tayi kafin tace, "Kashe shi ba karamin tashin hankali bane, domin shi din mugun matsafi ne. Barayi da yan daba sunsha yunkurin zuwa gidan sa sata. Amma da sun dau hanya sai gidan ya bace.kin ganshi nan takadiri ne baya jin bindiga balle wuka, wuta kadai ce zata iya cinye dan banza"................................................_




😫 Wayyo kaina ciwo! Ayi man afuwa Readers need ur prayer yaseen ina cikin damuwa 😔

Autan Writers, Autan Zamani. ✍






👨🏻‍💻👩🏻‍💻 ​*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​


        *'YAN MAFIYA*​
            ☠☠☠☠☠☠
     ​Gajeren labari​

 ​*Part 60-65*

© 🤴🏻 ​*KINGBOY ISAH* ✍🏼


.                👨🏻‍💻👩🏻‍💻        .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com

*__DEDICATED______*
*_____TO YOU_______*
🌹```KAMALA MINNAH🌹
🌹BAMAI A. DABUWA🌹
🌹ZAIDU MRZAID🌹
🌹MUBARAK MUBSON🌹
  🌿NABEELA 'ER AMANA🌿
🌿ZUWAIRA MADARA🌿
🌿'YAR MUTAN ARKILLA🌿
🌿AMINA AUTA CITTA🌿
🌿MMN NOUR🌿
🌿ACTION BABY🌿
🌿MARYAM SAI'D🌿
🌿SURUKA AMA🌿
🌿ZEETY🌿
🌿SHAXEE🌿
🌿ZULAIHAT RANO```🌿

👯 A daina batuna in baku. Cikin Whatsapp nace sai ku. 👯 Kun zamo jinin jiki na ni 👯


😁 *Abokai naji sauki in sha Allah zaku na jina. Na gode da Adduo'in ku*





•        *KARSHEN PAGEN BAYA*    •
~"Kashe shi ba karamin tashin hankali bane, domin shi din mugun matsafi ne. Barayi da yan daba sunsha yunkurin zuwa gidan sa sata. Amma da sun dau hanya sai gidan ya bace.kin ganshi nan takadiri ne baya jin bindiga balle wuka, wuta kadai ce zata iya cinye dan banza".~

_*A*jiyar zuciyar na kara saukewa ina tunani lalai fa na daukko babban aiki. Ashe gwara da ban yi niyar kashe shi da wuka ba. Matar ta tsare ni da kallo tana karantar fuskata duk na shiga damuwa da jin maganar ta. Ta danyi murmushi kafin tace, "Wai kashe shi kike san yi?". Da sauri nace "A'a". Gudun kar in je magulmaciya ce ta gayama. Tace. "Na zata kashe shi kike son yi. Da ince lalai kin dakko babban aiki, hanya daya ne nake ga mace kamar ke zata iya kashe shine toya dodon nan na falon nan. Domin na taba jin suna hira yana fada wa wani cewa, 'In dai aka toya dodon nan mutuwa zaiyi'. Kuma kinsan Eng. Mansur baya rabuwa da wannan gidan tsafin, in ba kwanan ba da matarsa ta kusan haihuwa. Kuma ma yanzu ya wakilta mataimakin shi a kan shi zai ringa gudanar da komai ij baya nan". Cike da mamaki na kalle ta nace, "Eng. Fa kikace, kuma yana da mata har ta kusan haihuwa?". Ta girgiza kai lokacin da mun daina tafiya muna tsaye a gefen titi. Tace, "Kwarai  ne. Sai dai yanzu da yaga ya wuce sananin kudi ya daina aikin ma". Nace, "Dan Allah yaushe zaki rakani gidan shi in gano matar sa?"._




 _Rike baki tayi da sauri tace, "Wa? Ni! Rufa min asiri yaga dan kungiyar nan  a gidan sa ai mutum ya kade. Kinsan fa ba wanda yasan yana wannan harkar to  in ya ganki a gidan sa sai ya zata ai zuwa kikayi tona mai asiri". Nace, "Tabb! Amma zanso naga wannan matar wai amma karama ce ko? Da har mijinta zai ringa kusan kwana a wani waje ta kasa gano shi". Murmushi tayi tace, "Bari ki ganta ai muna facebook da ita". Nan take ta shiga ta login account ta shiga nuna min photo. Ni kuwa ba hotan nake kallo ba sunan kawai nake nanatawa a zuciya dan kar na manta. (Mai Jidda Mansorr) nace, "Haba yarinya ce shiyasa. Yanzu haka wayo yake mata". Nan dai mukaci gaba da hira. Ni kam har na matsu mu rabu domin can kasar zuciya ta da kudirin da nayi._


_Sallama mukayi da matar ta kama hanyarta nima nabi tawa. Jibeer shopping na biya na sayo lemuka da cinci. A hanya na saya kaza daya tukun na wuce gida. Da shiga gidan naji gabana na faduwa, na shiga tunanin mai gidana. Hawaye suka kwaranyo min a fuska. Cike da takaici na bude dakin na shiga ina kallon jakar kudin nan, wanda wai mijina ne ya koma haka.  Kazar na ci da  dan cincin sai lemu da na kora ban bi ta kan sallah ba. Domin tun ranar da aka hanani na hanu na daina. Sai kuma na lula sabuwar duniyar tunani dan ni yanzu shirin da nake mai karfi ne. Ba dai sun ce in mutum ya shiga kungiya ba fita sai dai mutuwa ba. Ai kuwa su zasu mutu. Ina cikin sake-sake da yanda zan gudanar da plans dina barci barawo yayi gaba dani.  Washe gari ban tashi ba sai karfe bakwai domin jiya na gaji sosai._





_Na fito ina brush almajiri ya shigo yayi bara, na kirashi na rubuta mai abubuwan da zai sayo min a takarda kayan shayi ne da su kwai sai biredi.  Ba a dade ba ya kawo min komai dai-dai. Naira dari biyu na bashi nace yaje yaci abinci. Sosai naga yana murna kamar wanda na bashi million. Na girgiza kai a zuciya nace, "Allah sarki iyayen yara wasu ko katan basa da tausai. Sai su sako kanannu  yara su shigo gari suta gararamba da sunan suna karatu. To wai su garuruwan su ba makarantu ne?". N tambayi kaina lokacin nayi kwafa na tashi na shiga kitchen nan-da-nan na hada kayan breakfast dina. Shayi mai kauri sai wainar kwai gefe ga biredi.  A rufar kofar dakina na shinfida tabarma na zauna ina karyawa hankalina kwance._






_Sallama naji yayin da na dago kai ina amsawa. Salima kanwar mijina bala, ta shigo sanye da kayan islamiya. Kan tabarmar ta zauna bayan mun gaisa nace mata bissmillah tace dani taci tuwo a koshe take. Duk mai hankali in ya kalli Salima yaga irin kallon da take min yasan kallan zargi ne. Ganin shirun da tayi tana kallon abincin dake gabana yasa ni cewa. "Salima makaranta za a kenan? Ya su Umma da Abba?". Firgigit ta zabura kamar wacce aka tsikarawa allura tace. "Duk lafiyan su lau, dama Umma ce tace nazo naji meke guduna game da lamarin yay bala". Nayi murmushi nace, "Jiya ma wani abokinsu yazo ya kawo min waya mun gaisa da Umma kuma yace dan Allah tayi hakuri tafiyar ce ta zo mai kai tsaye".  Salima ta mika tace"To ni zan wuce, dama Makaranta zan wuce Umma yace nazo naji ya ake ciki". A dawo lafiya nayi mata hade da cewa ta gaida Umma in ta koma._





_Bayan ta fita nabi bayan ta da kallo dan kuwa ko ni na rasa gane wane irin kallo ne take min? Ko dan da dumamen tuwo ta sanni yau kuma gani da tea da wainar kwai?. Murmushi nayi naci gaba da cin abincina. Waje-jen karfe sha biyu na fita naje kasuwa. W2 sabuwa fil a kwali. Kasancewar ina da sim a tsohuwar waya ta katin dubu da dari biyar na saya tukun nayi cefanen abincin rana na koma gida. Da zuwa na hau laluben tsohowar Nokia ta rakani kashi. A can karkashin gado na samo ta tashi daurin kirji da roba yar bale. Ba carji a ciki domin ni a kalla tayi sati ban ko kula taba domin wannan sabon alamari da ya shigo rayuwa ta ba ta waya nake bama. A kan gado na zauna na cire sim din na bude sabuwar wayar nasa._





_Tukun na kunna na loda katin. Kai tsaye sub nayi na dubu daya. Tukun na shiga lalube a wayar. Can na hangi Facebook abunda nake nema kenan dama. Sai kuma na tuna ashe fa ban iya ba. Wayar ma ba komai na iya a cikin ta ba. Amma sai dai nace bari na gwada bude wa, domin ni zuciyata bata taba yarda da bata iya abu ba. Saidai in na gwada na kasa. Data na bude kamar yanda naga mutane nayi nan take na shiga Facebook app dake kan wayar. Cikin mintuna kalilan na bude account Facebook da suna. Kareeme baby,  ban tsaya wata-wata ba na nemi wajen search na rubuta sunan da na bude Facebook din saboda shi, MAI JIDDA MANSORR nan take kuwa naga hotanta wanda na gani a wayar matar nan jiya. Friend request tare da message na sallama._




_Bata online lokacin hakan yasa nace bari na jira ta. Na bar datar a kunne na tashi na fara gyara kayan miya na dora tukunya domin yunwa nake ji. Ina tsakar jajage naji wayar daga daki tayi wani kara alamun sako ya shigo da sauri na tashi naje dubawa. Tsaki naja ganin kamfanin layi ne suke min tallah. Nan na jefar da wayar kan gado na koma naci gaba da girki na. Kasancewar abincin gwangwani uku ne. Ban dau lokaci mai tsawo ba na karasa. Bayan na zuba a flat ina jira ya huce na daukko wayar ina duba Facebook din.  Groups masu amfani irin na mata wanda nake jin labarin su ana karuwa sosai na fara join. MANYAN MATA. GIRKE-GIRKE MUTUNCIN MACE, MACE TAURARUWA, MACE MUTUM, DAKE AKE. ZAMAN AURE A ADDINAN CE._





_Da dai sauran su haka tata join din groups din wanda duk na females only ne. Ina cikin yi naji karar shigowar message. Da sauri na bar abunda nake naje ina dubawa kuwa naga Jidda ce har tayi Accept ta dawo min da sallama.  Nan fa muka fara chat. "Yakike ya gida". "Lafiya lau dawa nake magana". Ni sunana Karima kamar yanda kika gani dai. Ni sabowa ce a Facebook to ina budewa naci karo da sunanki haka kawai naji ina so ki zama kawata shiyasa ma nayi add naki". "Kai gaskiya naji dadi a wane gari kike?". "A Kaduna nake ina da aure sai dai ban sama haihuwa ba har yau Allah baiyi ba". "Ayya ni kuma a Kazaure nake. 'Ya'ya na uku Babban cikin su ya bace biyun kuma Allah ya musu rasuwa. Amma yanzu kam ina dauke da juna biyu, haihuwa ko-yau-ko-gobe"._




_Sticker nasa mai alamar kuka sanan nace, "Ayya yar uwa na tausaya miki. Ace har yara uku amma ba ko daya yanzu. To Allah yasa dai a haife cikin lafiya. Kuma Allah ya bada da mai albarka wanda zai maye gurbin sauran". "Amin". Ta rubutu  hira muka sha sosai in kaga yanda muke wasa da dariya sai kace mun shekara uku muna abota. Wajejen karfe hudu muka rabu tace zatayi girki.  Ni kam dama tuni na kammala cin abinci dan ina chat ina ci ne. Na kwashe kwanukan na kai na ajiye wajen wanke-wanke tukun na kwanta a gado ina jin dadi tarkona ya kama kurciya a karon farko._




 _Yanzu saura tsari na biyu.  Ana cikin haka barci ya washe ni. Ban farka ba sai karfe shida. Tashi nayi nayi wanka na canza kaya na fito na shiga gidan Maryam domin duk yau ban shiga ba. Ai kuwa nasha masifa a wajen ta wai bani da kirki duk cikin satin nan na daina kula ta. Ni kam ban biye ta ba. Hira muka shiga yi da yan barka har dare. Dan abinci ma a nan gidan naci. Karfe goma nayi musu sallama na koma gida na kulle. Ina zuwa na dauki wayata na jona charji dan lokacin an kawo wuta. A zuciyata nace bari na leka Facebook naga ko zan iske Jidda._





_Ai kuwa ina shiga na ganta a online tayo replay din sakunan dazun. Wata sabuwar hirar muka shiga yi inda nake tambayar ta mai gida bai dawo bane?, dan naga har shadaya ta kawo kai?". Sticker mai murguda baki ta turo daga bisani tace, "Ke rabu da wannan mai gidan nawa kinsan fa matan shi uku ni ta hudun ce. In dai ba ranar kwana na ba a rana baya wuce yazo sau daya. Wataran waya ma baya yayi balle yazo. Yanzu haka yana can gidan sauran matan shi. Kinsan kwana bibiyu ne".  Dan murmushi nayi a zuciya nace lalai Jidda bata da isasshen wayo na gano hakan ne tun daga yanda take fallasa min sirrin mijinta ba abunda yasha mata kai. Ashe ita abunda yace mata kenan matan shi uku bayan kuma wajen tsafi yake kwana. Nayi kwafa nace, "Tabb! Sister ashe kishiyoyi gare ki. To ba gida daya kuke ba?"._






_"Aa ba gida daya muke ba. Nice fa uwar gida dan haka gidana daban. Su kuwa can bansan ko gida daya suke ba. Ko kuwa a hade suke oho dai. Dan ni ba taba zuwa nayi ba".  Dariya nayi sosai da lamarin Jidda.  Lalai mijinta yayi mugun raina mata wayo. Haka mukaci gaba da hira sai wajen 12 tukun mukayi bankwana na kashe data na kwanta abuna. Da safe barar almajiri ce ta tayar dani. Lokacin da na bude ido naga ashe har gari ya wayo. Da na kira shi nayi mamakin ganin almajirin jiya ne. List na sake rubuta mai na abubuwan da zai sayo min. Na kuma fada mai inda zai sayo min ya fita. Ni kuwa na  kama brush. Ina shirin shiga wanka sai gashi ya dawo. Kayyaykin na amsa na ajiye na bashi dari biyu kamar jiya. Har ya juya zai tafi sai na tuno da sauran abincin da na rage jiya. Nace, "Dan malam ga abinci can cikin tukunya dakko ka gani in kana so. In kuma ya lalace ka zubar a waje"._





_"To". Ya fada yaje ya daukko tukunyar ni kuwa na dauki ruwan wanka na wuce ban daki. Na fara wanka kenan naji ana masifa a waje da na saurara sai naji muryar Umma ce, tana cewa, "Kutumelesi! Dama abunda Salima ta fada min ashe gaskiya ne. Dubi abincin da aka ba almajiri nama zuku-zuku. Ga kuma kayan shayi har da su kwai da wannan tikeken biredin mai kama da katifa. Iyyeee! Lalai Nusaiba sai yanzu na gane baki da kirki ko kadai wato Bala  yaje can ya aiko kudi watakil ni ya aiko wa ma shine kika zo kina murkushe wa ke ga matar shi. Kai ina matar gidan". Ina ji tagi tambayar cikin tsawo. Almajiri  yace. "Yanzu ta shiga wanka". "Wanka? Bari kagani in sama kujera yau ko wankan canza fata ne ta fito ta same ni a nan"..............................................._




🤔🙄 Yo ai hikenan. In nene bazan fito ba ta katanga zan haura in ruga 😂😂😂😂🏃🏻



Autan Writers, Autan Zamanawa. ✍









👨🏻‍💻👩🏻‍💻 ​*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​


        *'YAN MAFIYA*​
            ☠☠☠☠☠☠
     ​Gajeren labari​

 ​*Part 65-70*

© 🤴🏻 ​*KINGBOY ISAH* ✍🏼


.                👨🏻‍💻👩🏻‍💻        .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com

*__DEDICATED______*
*_____TO YOU_______*
💐```Beauty Queen🌹
🌹Bestyn Nana💐
💐Aysha 🌹
🌹Hauwa Jidda💐
💐Hafsat amarya🌹
🌹Mmn Twix💐
💐Mmn Namma🌹
🌹Momin maryam💐
💐Nabeela 🌹
🌹Lawaiza kabir💐
💐Rahma🌹
🌹💐
💐Momin khairat🌹
🌹Momin hibba💐
_______^_____^________```

✍🏼 *Alkalamin King bazai taba gajiya da rubuto ku ba zamanawa. Kaunar ku a Qalbina take. Idan na kalle ku farin ciki da walwala na shekowa da gudu cikin zuciya na.* ☺

😔 Mutuwa kadai nake ji. Dan ita kadai data raba mu. 🚶🏻 Tunani nake yi in babu ku cikin duniyar net ya zana kara? 😔

🙋🏻‍♂ *Salma Queen*💅🏻💍 daga hannun. Albishir ce dani goro fari 😁


•       *KARSHEN PAGEN BAYA*   •
*~Ina ji tagi tambayar cikin tsawo. Almajiri  yace. "Yanzu ta shiga wanka". "Wanka? Bari kagani in sama kujera yau ko wankan canza fata ne ta fito ta same ni a nan".~*
_*I*na wanka gabana ba abunda yake sai dukan hudu-hudu. Dan bugun yafi uku-uku. Sake-sake na farayi a zuciya, ni kam ya zanyi da jarabar Umma? Dama can nasan Umma jarababbiya ce. Dama tana daga min kafa ne saboda ina zaune da danta duk talaucin sa. Haka dai na gama wanka na fito salo-salo jikina ba kwari.  Tun da na fito na kalle ta zaune take kan kujera. Fuskarta zata fara gaya ma ranta a bace yake. Harara kawai take bina da shi har na karasa wajen, gefe guda na tsugunna "Umma ina kwana". "In da ban kwana ba zaki ganni ne". Shiru nayi kaina a sunkuye. Domin bansan wacce irin amsa zan bata ba. "Tambayar ki nake. In ban kwana ba zaki ganni ne? Nusaiba yaushe kika zama munafuka? Da ina daukar ki yarinyar kirki, mutuniyar arziki. Ashe talauci ne can dama ke lalasa ki shiyasa kike ladabin karfi da yaji?. Wato yanzu Bala ya sama aiki ya fara turo kudi shine zaki ci ke kadai. Ga uwar sa ma bazaki bata ba wacce ta kawo shi duniya?".   Nan fa dai ta fara zuba tana surfa masifa. Ta inda ta shiga ba ta nan take fita._





_Da dai naga bal'in nata yayi yawa bata da niyar bari sai na mike na shiga daki. Ina ji tana kira na wai wato tana min fada shine zan tashi in shiga daki. Kudi na daukko dubu sha biyar. Na buye sauran kudin dake jaka a karkashin gado. Fitowa nayi na durkusa na mika mata. Hannu har karkarwa yake ta amsa tana tambaya na miye. Murmushi nayi nace, "Ai dazun wani abokin Bala dake aikin shikafa ya kawo dubu ashirij ne. Shine yace na dauki dubu biyar na baki sha biyar din". Sai lokacin naga tayi murmushi lokacin take tambaya to ya bala din fatan suna lafiya?." Nace mata "Kalau yake yace  gaida ku".  Bata dade ba tayi min sallama zata tafi. Yanda naga tana kallon kayan shayin nan na gane wani abun take so a ciki. Tun kafin tayi magana nace "Umma ina zuwa". Na gashi da sauri na daukko leda na raba kayan shayin biyu. Har madara peak guda daya na jefa mata. Na bata tayi godiya. Har kofar gida na raka ta tukun na dawo ina takai'cin Umma.  Kayan kari na hada na karya kafin na jawo waya ta na bude data na kuwa ci sa'a  na iska Jidda a online nan muka hau chat._





_Karfe sha biyu na shirya cikin kayana masu kyau na fita. Ko sallama ban wa Maryam ba. Asibitoci na kama bi daga wannan zuwa wannan. Duk ina lora da tsarukan su ne.  Da yanayin tsaron wajen. Domin wannan asabar a asbiti nake so na sata jariri.  Duk asibitocin naga ba fuska dakyar insha. Bama kamar asbitocin kudi da naga ba wani girma gare su ba. Ba wuya a kamani. General hospital. Na tari adaidaita ya kaini da sauka naji wajen ya kwanta min. Domin masu gadin gate din ma naga duk dattijai ne. Sai hira suke abunsu ba ruwansu da mai shiga da fice a  kasa. Ciki na wuce kai tsaye dakin haihuwa. Yanda naga abubuwa na tafiya duk sai naji dadi da farin ciki ya kamani. Na dai fahimci ko kadan sata a gun bazata bani wuya ba._






_Bayan na gama zagaye-zagaye na. Na gama kare wa aabitin kallo na fito abuna. Napep na sake tsayar wa ya kaini kasuwa atampopi da yadika kala-kala na sayo domin dai kaya basu wadace ni ba. Bayan na gama saye-sayen kaf! Na wuce gidan Binta tela. Nan na jibge mata su na kuma bata rabin kudi nace kafin asabar nake son su. Cikin kayan kuwa harda farin yadi wanda nace ta min Uniform na nurses. Har ta fara tambaya nq a kan na fara aikin asbiti ne. Nayi saurin taka mata birki. Na dau sauran kayana na fice daga gidan. Na fito titi ina jiran napep in hau y karasa ni gida. Can na hangi dandazon jama'a a can nesa dani. Wajen ya cika dankam sai hayani ya ake. Haka kurum naji zuciya ta na san zuwa inga ko me ya faru. Ai kuwa na nufi wajen da sauri. Na isa wajen sai dai duk mutane sun gewaye wani abu a tsakiya da bansan ko mene ne ba. Na leka dan gani amma ba sarari mutane sun rufe. Wata mata na gani a gefe na tambaya me ya faru a gurin. Matar ta dan girgiza kai alamar takaic'i tukun ta fara da cewa._





_"Kai Wallahi duniya ta zo karshe. Duniya ta gama lalace wa. Mutane so suke kawai su jawo mana masifa da bala'i hade da fishin Allah.  Wai ace zunace-zunacen da ake yi da garkuwa da mutane duk bai isa ba. Sai an hada da sace mutane ana tsafi da su. Kai Wallahi halin wasu mutanen ko kare aka bawa bazai ci ba".  Sororo na tsaya ina kallanta da neman karin bayani. Jin bangaren mu ta tabo wato YAN MAFIYA. Bayan na dan nuna alamun damuwa nace, "Wallahi na karanta wani labari a jaridar Aminiya  an tsinta gawar wani yaro ni ko a wane gari ne? Na manta amma duk an cire wasu sasa daga jikinsa. To mu dai Allah ya sawake mana wannan masifa kar ta shigo kazaure". Charf! Matar nan tace, "Wanne iri  kar ya shigo kazaure? Bayan abun ya zama ruwan dare a kazaure dama kauyuka. Ba afi sati bafa acan kauyen Gara. Aka sace yara har uku. Na hudun ne ma ya koma pure water mai satar bai sama dama ba".  Dum! Naji gabana ya fadi an tabo shafina. A zuciya nace, 'Kai wannan mata da masifar surutu take'. A zahiri kuwa nace, "Naji Wallahi abun ai ya taba zuciya ta. Nan me ya faru?"._





_"Leka kigani wani alhaji ne aka kamada ya maida wasu yara daya doya. Daya pure water. Allah ya tuni asirin sa akaga jini na fitowa daga jikin doyar shine aka gane cewa dan mafiya ne. Yanzu haka an masa lugu-lugu a kan ya maido dasu mutane amma yaki. Dan har barazana aka mai za a toya shi amma yace bazai ba sai dai a kashe shi".  Ajiyar zuciya nayi. A  raina nace, "Tashin hankali yanzu nima fa in aka kamani haka za ayi min ko? Tun da dai rana dubu ta barawo, daya tak ta mai kaya".  A fili Innalillahi na kama furtawa. Harda dafe kai alamun shiga damuwa kamar wani da gaske. Motar yan sanda da ta paka ne ta katse mana tunani muka bita da kallo. Nan take yan sanda suka  fito suna kora mutane da kyar suka iya ciro mutumin. Dan jama'a sunyi ca a kanshi wai sai ya dawo musu da yaran mutane. Kallo daya nayi masa na gane shi. Nasha ganin shi a kungiya. Da sauri na bar wajen ina kara tsanar wannan mumunar harkar. Shidai wannan karshen shi kenan inaga._|





_Bayan naje gida na ajiye kayan sayayya da nayo kai tsaye kungiya na nufa. Nan take na bayyana tsulum!. A falo kamar wata Aljana. Cike da damuwa na zazage wa oga labarin abunda ya faru. Ba dan komai ba sai dan inga wane irin mataki suke dauka in haka ta faru. Bayan ya gama saurare na ya kwashe da Dariya. Waccce ta sani tsayawa ina kallon sa.  Zuwa can ya dan tsagaita da dariya tukun ya dube ni yace, "Muna sane da duk abunda ke faruwa. Wanzu haka muna mishi kashe di ne  a kan karya kuskura ya tona asirin kungiya ko da za a kashe shi. Zamu lalaba shi ne zuwa dare kudunbur zai shanye masa jini ya mutu. Domin gudun kar ya tona asiri in yaji wuya sosai"._





_Tsuru na kura mai ido cike da takaici da haushin lamarin kungiyar nan. Dama haka al'amarin yake ashe. Idan aka kama mutum ba wani yunkuri da za ayi na ceto rayuwar sa. Sai dai ma a kama tsare-tsaren kashe shi, wai dan kar ya tona asiri. A lalai ya zama dole na bar kungiyar nan ko da kuwa zan mutu ne. Amma dai zan jaraba shirin da nake na tarwatsa su naga in yayi. In kuwa baiba to fa sai na bar kungiyar ko zan mutu. Maganar ogan namu ce ta katse ni daga tunanin da nake. "Yauwa Nusaiba dama muna so muji dalilin da yasa kike karya dokokin kungiya". Yamutse fuska nayi na kalle shi ba yabo, ba fallasa nace, "Ban gane ba wanne dokokin kungiya kuma?. Bayan jariri da kuka ce na ringa kawo wa da salla da kuka hana ni akwai wani abu ne kuma?"._





_"Kamar yanda kika fara da farko ai ana fita neman nama. Da kudin tsafi. Kwana biyu baki fita da shi ba kika kawo mutane. Sannan kuma fara karyawa da jini dokar kungiya ce. Kuma itama kwana biyu bakya zuwa. Kinsan kuwa kungiya bazata juri haka ba". Raina yayi matukar baci. Duk kwarjinin sa. Da tsafin sa dama duk mutanen dake zauna a gaban shi wand suka kwalalo min ido bai tsorata ni ba nace. "Malam tsaya fa kaji, ni tunda mijina ya mutu ta sanadiyar kungiyar nan na tsane ta. Ni bama kungiyar ba yanzu gaba daya kudin ma bana so. Da zaku dawo min da mijina mu kari rayuwar mu cikin talauci da shi nafi so. Dan haka maganar fita da kudin tsafi na daina bazan kuma ba. Haka kuma karyawa da jini, tunda dai in ban karya da shi ba ba mutuwa zanyi ba. To a kyale ni banzan ringa yi ba. Kuma ma Wallahi sallah zan dawo yi. A kan me zaku hana mutum sallah? Wato ku dai shiga kungiyar ku kamar shiga wuta ne ko?. To baza a je wuta dani ba  abu biyu nasan zan kiyaye game da ku. Sato dan jariri sai kuma fita a kungia wanda nasan wannan biyun ne in banyi ba zan mutu. Sauran in kunga dama ku kashe ni amma bazan ba". Ina fadar haka na juya  na wuce. Ran oga Mansur in yayi dubu ya baci. Mutanen wajen ma baki kawai suka saki suna kallona. Ina ji yana kirna lokacin da juya amma nayi banza da shi._





_Kai tsaye gida na wuce. Raina a matukar bace, na rasa inda zansa raina. Kwadayi na neman kai ni ga hallaka. Na tsani kungiyar nan sosai kamar annabi da kafuri. Ina zuwa gida na haye kan gado domin na gaji sosai. Har barci ya fara debata Maryam ta aiko ana kirana. Sai lokacin ma na tuno ashe fa gobe ne suna.  Na fito  da waya ta na kulle gidan na shiga gidan Maryam. Mita ta shiga min wai kwana biyun nan na cika yawo wai tun dazun take aikawa a kira ni gidan kulle. Saida nace mata gida nake zuwa tukun ta daina mita. Sai lokacin nake nuna mata wayata sosai tayi murna hade da tambaya waya saya min. Ba ko fargaba nace mai gidana. Har zatayi magana kuma ta fasa. Wayar ta karba tana buga game sai ihu take wa mutane kamar wata yarinya. Ni kuma na fita domin taya mata aiki._





_Maryam kam a ranar hauka ta kama wa mutane. Game din da take subway daga an kamata sai tayi kara duk tabi ta ishe mutane. Yanda take abu kamar yar kauye.  Yaron ta ya kama kuka amma taki kula shi. Kasancewar sa dan fari, sai da aka sani na karbe waya ta tukun Maryam ta dauki danta. Bayan munci abincin dare muk dora wani sabon girkin kuma na suna. Muna yi na bude data. Na shiga dube-duben muhimman post a Facebook din. Can kuma sai ga Jidda nan muka sha hira. Har ta kara gayan wasu groups din mata zallan na koyan girke-girke da kwalliya hade da kissoshi. Sai wajejen 12 muka gama abincin shinkafa fara cike da tukunya lamba talatin. Muka juye a kuloli miyar ma haka. Kasancewar Mijin Maryam yace sunan tuwo waje ne ba sunan masallaci ba._





_Bayan an gama komai kowa ya watse. Sai ni da Maryam da ta amshi wayata a yanzu ma take game. Na warce abuna dan nasan in nace ta bani sai ta tsaya ja min rai. Nayi mata sallama. Tana mita wai  na kwace wayata. Zaman mutunci muke da Maryam tamkar yan uwan juna. Duk da na fita amma bana wani nuna mata banbanci.  Alarm nasa a waya ta tukun na kwanta. Dan ya tayar dani da suba. Haka kuwa akayi asuba nayi wayar ta ishe ni da kara dole na na tashi ba dan naso ba domin baccin yayi min dadi.  Alwala naje na dauro domin nayi niyar ci gaba da sallah abuna.  Bayan na dawo daki na daidaita a kan sallaya zan tada kabbara kenan naga dif!. Nefar dakin  na ta dauke. Kafin in tayar na juya tsakar gida naga da hasken nepa. Ban damuba na juya cikin duhun da niyar kabbara sallah. Kamar dai ranar nan, yauma da karfi aka hangiza ni baya...................
....................._



🏃🏻 *Duhu yayi yawa a dakin gashi na tsorata hakan yasa na fita a guje. Gobe in rana tayi zanje na gano muku abunda ya faru* ☹


Autan Writers, Autan Zamanawa. ✍










👨🏻‍💻👩🏻‍💻 ​*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​


        *'YAN MAFIYA*​
            ☠☠☠☠☠☠
     ​Gajeren labari​

 ​*Part 70-75*

© 🤴🏻 ​*KINGBOY ISAH* ✍🏼


.                👨🏻‍💻👩🏻‍💻        .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com

*__DEDICATED______*
*_____TO YOU_______*
💐BIGBOY ISAH NOVELS🌹

👯 Kun shiga raina kun sama waje kun zauna. A-a-a zana rike ku hannu biyu alkawari zan muku gata. 👯👯
Ina ji daku ana mugun tare 

✍🏼 Kurarren lokaci ne da na zano ko goma ne a cikin ku. *Kingboyisah novels*







•       *KARSHEN PAGEN BAYA*     •
~Kafin in tayar na juya tsakar gida naga da hasken nepa. Ban damuba na juya cikin duhun da niyar kabbara sallah. Kamar dai ranar nan, yauma da karfi aka hangiza ni baya.~

_*K*adan ta hana kai na ya budu da bango. Wata murya marar dadin ji naji ta fara dakar dodon kunne na. "Nusaiba.... Muna ja miki kunneeeee karki yarda kici gaba da salllah. In ba haka ba....". Ayyatul kursiyya na fara karantowa. Abunda ya dakatar da maganar kenan. N kuwa da naga haka sai na kara himma wajen karanta kursiyyun. Ba a dade ba kuwa naga wutar dakin ta dawo. Ba tare da wata fargaba ba, Na tada sallah. Har na idar ba abunda ya kuma faruwa. Haka na kwanta ina tunanin kar wani abu ya biyo baya ko da dadare su zo su kashe ni. Ina cikin tunanin barci ya kwashe ni. Washe gari tun asuba nayi wanka na shirya na tafi gidan suna._




 _Munsha shagali aka radawa yaro suna Iliyasu. A raina nace, "Lalai Iliya kai din rabo ne. Da yanzu tuni ka dade da shan wuka". Ranar wuni mukayi a gidan sunan muna aikace-aikace. In kuwa na dan ganni a free sai na bude data na fara chat. Da dare sai bayan da kowa ya watse tukun nima na koma gida. Nayi jira har na gaji Jidda bata hau online ba. Nan take na tuno da wannan matar wacce naga username  din Jidda a gunta. Har na shiga wajen search da niyar in nemo ta sai kuma na tuna ashe ko sunan ta ban sani ba. Nan take kuma sai na tuno ashe naga duk abokan Jidda a Friends nata. Kai tsaye can na nufa ko Allah zai sa na dace na gano ta. Ai kuwa banyi nisa ba naga hotan ta. Hajiya Safara'au, naga user name nata. Nan take na tura mata friend request. Banyi zatan tana on bama dan dare yayi. Sai kawai naga notification tayi accepted._





_Sallama na aika mata ba a jima ba ta dawo min da shi. Nan muka gaisa nake fada mata Nusaiba ce ta kungiyar su na mafiya. Tayi mamaki sosai take tambaya wai a ina na sama Username nata. Kuma taga sunana Karima ne. Nace, Basaja nayi. Hirar duniya muka sha sosai da ita. Kafin mukayi sallama kowa yaje ya kwanta.   Safiyar yau ta kama alhamis kullum cikin zullumi nake asabar ta tunkaro ni. Tsoro nake inje asibiti satar jariri a kama ni. Na gaji da zaman gidana da ma na Maryam da muke shiga muna hira. Yau na yanke shawarar zanje gidan mu ziyara. Wanka nayi nazo nasa sabun leshi na wanda jiya-jiya Binta tela ta kawo mun si har ta gama dinki wai da taga kudi hannu.  Les din yayi mun kyau sosai. Yar simply makeup nayi. Nawa Maryam sallama na kulle gidana na._





_A tsakar gida na iske Mamar mu na tankaden garin tuwo. Tana ganina fuskar ta ta fadada da murmushi tana min sannu da zuwa.  Nima murmushin nake da sauri na kara nace ta kawo tankaden nayi amma ta hana wai nasa sababben kaya kar na bata. Ba yanda banyi ba amma ta hana dole na hakura na shiga daki na daukko tabarma na zo na shimfida na zauna. Bayan na gaishe ta ba a jima ba sai ga Baban mu ya fito daga ban daki na gaishe shi. Ya tambayi ya maigida. Da har nayi shiru kuma sai na dago da sauri nace ai yayi tafiya tun wancan satin. Nan fa Umma ta hai ni da fada wai me yasa ban gaya mata ba. Ai da ta turo min wata wacce zata na taya ni kwana ko a makwabta ne. Da sauri nace "Aa Umma ba wani matsala a bar ni ni kadai nafi jin dadi"._





 _Lokacin tuni dady ya fita Mum ta kalle ni tace, "Nusaiba naga sabon danki a jikin ki yau fa ba salla ba. Kuma ban san kina da ciki bama balle ace haihuwa kikayi yau suna". Dariya na kyal-kyale da ita dan maganar  Umma ta ban dariya. Ashe ta riga tayi min fenti bana sa sababbin kaya sai ranar sallah. Nace "Umma yau ba sallah bane amma ai Umma kinsan komai dan lokaci ne. Juyin zamani ne". Umma tayi tsuru tana kallo na kallo mai dauke da alamar tambaya. "Ban gane ba Nusaiba. Me kike nufi?".   "Umma bala ne fa ya sama aiki a kano. Shine ya aiko min da su. Kala uku ne ma". Murmushi tayi tukun ta shiga min nasiha. Wai ai dama duniya haka take naga ranar hakuri. Dama talauci Allah ne ke dorawa bawansa dan ya jaraba imanin sa._





_Ni dai sauraren ta kawo nake taita kora min wa'azi a kan cewa hakurin da nayi ne na zama da mijina duk talaucin sa shine yanzu Allah ya buda mai. Kusan tare mukayi tuwan duk da tana hanani amma naki hanuwa. Dama wasu ayyukan da na taya ta na mata. Bayan sallar magariba Adamu (kani na) ya shigo gida. Muka gaisa cike da kewar juna. Domin kuwa muna san junan mu sosai. Dan ko irin fadan nan na yarinta Yaya da kani mu Bamuyi ba. Sai bayan isha'i nayi musu sallama. Na koma gida._




_Bayan sallar juma'a ina kwance a daki  muna chat da Hajiya Safara'au nake gaya mata ni fa gabana sai faduwa yake a kan gobe asabar gani nake kamar in naje sato jariri za a kamani. Nan take gaya min akwai wani turaren tsafi da suke amfani da shi mai sa barci zai taimaka min sosai. Cikin zumudi nace mata ina so. Tace amma tsada gare shi. Ni kuwa nace ko nawa ne zan biya. Tace bama wasu uwayen kudi bane dubu dari biyar ne. Nace ba matsala ta sayo ta kawo zan bata kudi. Tace ai kuwa bari ta tashi taje wajen bokanta dan a can take sayo shi.  Nan take na tura mata address din gidana nace ina jiranta. Nasha jira sosai har na gaji bata zo ba._




 _Dan har cire rai nayi da zuwan ta. Gashi na bincika about dinta ba number a Facebook balle na kira.  Da magariba ina ina alwala naji sallama, wacce bana ko tantama nasan itace. Na amsa sallamar ina mai cewa ta shigo. Ina alwala muna gaisawa sai da na gama tukun naja ta zuwa daki. Nan ma nace dan Allah ta zauna a bakin gado ta jira nayi sallah kar lokaci ya fita. Dan magariba gajeren lokaci ne. Batayi gardama ba ta zauna har na idasa sallar  nayi addu'a na shafa. Tukun na kalle ta ina mai bata hakuri. Na lura da kallon wulakanci da take wa dakin nawa hakan yasa nayi saurin cewa. "Kinga yar bukkar tamu ba ko mirror balle gado Royal ko"._





_Dariya tayi tukun tace, "Nusaiba da abun dariya. Gado royal ai sai masarauta ko kuma manyan attajirai". Nayi kwafa nace, "Ina fatan dai kin taho da shi?". Dan tabe baki tayi ta daukko wata yar kolbar turare karamace amma irin wanda ake fesawa ne. Kasancewar kwalbar fara kana hango wani ruwa da ke ciki baki kirin da shi.  Ta rike shi a hannun ta na mika hannu zan karba tayi saurin jaye wa tana fadar "Tsaya mana. Ai ciniki ya tashi sai anyi sabon ciniki"._





_Kallon ta na tsaya yi nace, "Ba dubu dari biyar ba kika ce? Me kuma ya faru?". "Kwarai dari biyar ne. Amma wancan dan iskan bokan sai da yayi lalata dani tukun ya sayar min. Shiyasa ma na bata lokaci. Dan haka sai kin karan kudi. Million daya zaki bayar. Domin ya gajiyar dani. Ya ban wuya sosai".  Tsaki nayi cike da jin haushi nace. "To nayi ni in dai zai min amfani baki da matsala. Wai ke ina kike kai kudin da kike samu a kungiyar ne? Naga ni daga shiga ko wata banyi ba na sama millions"._





_Yar dariya tayi tace, "Ai mu da ku ba daya ba. Kin manta nace miki ni girki ne aiki na a can? Albashin mu 3 million ne duk wata". Nayi kwafa nace. "To ai shikenan bari na baki kudin. Ni dai gurina yayi aiki". Na zagaya baya karkashin gado na jawo jaka ina debo kudin. Ina jinta tane cewa. "In kika mallaki wannan turaren baki da matsala. Domin in kina da shi ko yaran duk asibitin kike so ki kwashe zaki kwasa ba tare da fargabar komai ba in dai kin fesa"._




 _Kudin na kawo mata ta daga jakar ta ta tura su gaba daya har da kyar jakar ta zagu. Tukun ta miko min turaren tace, Daga naje asibitin inda nake so in dauka jaririn ina fesa turaren gaba daya mutanen wajen  4 seconds yayi yawa barci zai kwashe su. Tace amma na tabbatar nasa noise mark kuma na dauke nufashina har sai na fito daga gun. Na karba ina tantama dan gani nake kamar damfara ta tayi. Amma da na tuna cewa na santa._




_Sai kawai na yarda. Bayan tayi min sallama ta tafi, haka kurum naji ina so na gwada turaren tsafin. Gidan Maryam na shiga. Da sallama, A daki na iske ta tana niyar shimfidar da Iliya. Tsayar da nunfashina nayi  na fesa turaren. Da fesawa naga Maryam ta sulale ta fadi tsakar daki. Da gudu nayi kanta. HR lokcin ban yarda na shaki iska ba.  Sai da na tabbatar tana nunfashi tukun nayi saurin fita daga dakin. Cike da jin dadi  na koma gida yanzu na tabbatar da maganar ta._




Ai kuwa har kaguwa nayi gari ya waye domin dai in haka ne satar kudi ma sai tafi min wuya a kan satar jariri. Gari na wayewa bayan nayi wanka na karya nasa wata rantsatsiyar atamfa wacce ta amsa sunan ta. Na zauna na kama chat abuna. Ina shige-shige a Internet. Karfe biyu dai-dai na saka sabon Niqap dina na rufe fuska ta. Karo na farko da nasa niqaf kenan a rayuwata. bana bukatar kayan nurse tunda na sama turaren nan. na dauki katuwar handbag dina, wacce katuwa ce sosai. Ban ko wa Maryam sallama ba na kulle gidana. Ina zuwa bakin titi na tsyar da napepk direct General hospital ya kai ni. Ina shiga kai tsaye MATERNITy Maternity na dosa. Cike na iske wani katan daki da mutane.Dake lokacin da naje an bada damar ashiga wajen dan duba masu haihuwa wanda aka fiddo daga labour room. Mata ne iri-iri ko wacce kwance gefen ta ga dan karamin gado wanda aka ke dauke da jariri. Zakaya su na farayi ina duba jariran daya-bayan-daya. Sai da na duba mumuna a cikin su wanda nake tunanin ko uwar shi ba sosai take sonshi ba. Nazo saitinsu na tsaya. Ba tare da bata lokaci ba na dauke nunfashi na. fiddo turaren a hankali na zuro hannu ta cikin hijab na fesa. abun har tsoro ya bani. Yanda naga mutanen gun sai zubewa suke. Wai barci, lalai tsafi gaskiyar mai shi. Cikin sauri na dauki jaririn na zaka a jaka. Sannan na fito da sauri. Na shaki wani dogon nunfashi tukun nayi saurin barin wajen.  Tafe nake ina waige. Nayi-nayi zuciyata ta natsu nayi tafiya ta masu gaskiya amma na kasa. Kasancewar ban saba ba. Nazo bakin gate kenan naga masu gadin biyu sun taso da sauri. "ke dakata-dakata daga ganin ki baki da gaskiya". Daya daga cikin su ya fadi haka. Cik! Na tsaya gabana yayi mugun faduwa. "To ni yanzu ya zanyi in aka kamani?"...............................................



😂😆 Nusaiba baki da mutunci Yaseen. Wai saida kika ga mumuna wanda ko uwar shi ba sosai take sanshi ba 🤣🤣🤣🤣🤣 Kutt!


Autan Writers, Autan Zamanawa. ✍





*DEDICATED TO ALL OF U FANS*  ❤😊

🙍🏻‍♂🎤 Na gode al'uma na gode. Zan fada muku nai godewa na kara muku godiya matan ku da mazan ku 👯 King boy Isah gani inai muku baitin gode wa.
 
👯 Ban raina abunda kuke ta yi mini ba.

🙍🏻🎤 Mun gode yan uwa.

🙍🏻‍♂🎤  Kun soni da riba wacce babu riba.


🙍🏻🎤 Mun gode yan uwa.

🙍🏻‍♂🎤 Gorin ku a ko yaushe ku ganni gaba.

🙍🏻🎤 Mun gode yan uwa.


🙍🏻‍♂🎤 Jirgin sama dan Allah ka kaini gari.


🙍🏻🎤 Mun gode yan uwa.

🙍🏻‍♂🎤 Naje naga Readers wanda ke sona.

🙍🏻🎤 Mun gode yan uwa.
☹🤸🏻‍♀ Kai Yaseen na kakare a nan 😍😘 Ina ji daku Readers din *'Yan mafiya*  I love you wujiga-wujiga 👨🏻‍💻


🙊 *Readers ku daiyi hakuri da Mistake din da ake samu wannan Book din. Wani yana faruwa ne sanadin... 🤔 Busy da nake ciki.And bana samun tym din duba typing error. To saidai kuyi hakuri da duk abunda kuka gani* 🤸🏻‍♀🏃🏻🙊





•           *KARSHEN PAGEN BAYA*     •
*~"ke dakata-dakata daga ganin ki baki da gaskiya". Daya daga cikin su ya fadi haka. Cik! Na tsaya gabana yayi mugun faduwa. "To ni yanzu ya zanyi in aka kamani?".~*

_*S*uka ta so su biyun da sauri suka shiga gabana suna ta surfa masifa wai ai dole sai na daga fuskana basu yarda dani ba ni namiji ne.  A fusace na wangame bakin kyalen niqap din daga fuskana na fara zuba masifa kamar na manta ni mai laifi ce. "Malam wannan wane irin iskan ci ne da cin fuska da zaku tare ni kuce wai ni namiji ne? Wannan ai iskan ci ne kuna so ku tozarta ni ne kawai. Ya zakuga matar mutane ku tare ta kuce sai ta bude fuskarta". Hakuri suka shiga bani duk jikin su yayi sanyi, masifar da nake tasa mutane suka fara taruwa domin cikin kwa-kwazo nake magana. Ina ganin haka nayi saurin rufe fuskata hade da murza musu yatsa nace, "Kunyi a karo na farko Wallahi karku kuma, dan in mai gidana ya san da wannan zancen to ina mai tabbatar muku da cewa cin abincin ku ya kare a gurin nan"._





_Ina fadar haka nayi tsaki nayi gaba. Ina jinsu sai faman bada hakuri suke har dama wasu daga can gefe ke taya su bani hakuri.  Dariya nayi nace, "Yan iska nayi maganin su". Na tari napep bai ajiye ni ko ina ba sai kofar gidan 'yan mafiyan, ina biyansa kudin shi kuwa nayi karatun tsafin su sai gani a falon. A zaune na iske Eng. Mansur tsakar falon a gindin katon gunkin wanda dama nan  ne wajen zaman sa. Yau ba mutane da yawa a gun duk basu wace su biyar ba. Yana gani na bullo ya saki murmushi ya taso ya tarye ni yayin da ni kuma na balla masa harara. Bayan na na fito masa da jaririn na mika masa ya karba yana fadar, "Kai Nusaiba gaskiya kina da kokari shiyasa ma dodon mu yake matukar ji dake, dan yana sane kin dawo yin sallah amma bai miki komai ba. Wanda da ace wani ne kuwa da ko bai mutu ba sai ya kamu da mugun ciwo, domin ko ni nan bana sallah.Nusaiba da kin saki jiki damu anyi harkar nan zakiyi alfahari da ita sosai, domin in dai batun dukiya ne ko government sai haka"._






 _Shiru nayi ina binshi da wani mugun kallo ban tanka mishi ba. Hanyar dakin ranar etayau ya nufa yace in zo mu tafi. Nace bazan shiga ba. Yace to in jira shi yana fitowa. Ba a dau lokaci ba ya fito da wata yar madai-daiciyar ghana masgo yazo da ita ya ajiye a gabana. Na dube shi a yatsine nace, "Miye wannan?". "Kudin ki ne na hado miki million biyar ne". Tsaki nayi na juya na fice ina mai cewa "ka rike bana bukata". Gida na koma naci abinci tukun na shiga gidan Maryam muka sha hira, ina taba chat kadan-kadan. Washe gari tun safe naji kiran Hajiya Safara'au na dauka muka gaisa. Nan take gayan wai jiya anyi taron kungiya kuma a kaina aka tattauna. Take lissafo min wai ance ni shegen taurin kai ne da ni. Ga wulakanci ga bana girmama manyan kungiya. Wai har wani daga cikin shugabannin kungiya yace me yasa baza a kashe ni ba oga Mansur yace ba yanzu ba. Bayan mun gama wayar nayi tsaki a zuciya nace, to su kashe ni mana. In kuwa basu kashe ni ba ni sai na kashe su._





_Bayan kwana uku gari duk ya kaurade anyi satar jariri a general hospital. Gidan jaridu da gidajen radio har dama gidajen TV. A kwana a tashi ba wuya yau ta kasance asabar. Yau munsha chat sosai da Jiddah da kuma sauran friends wanda wasu sukayi add nawa.  Shakuwa ce mai karfi ta shiga tsakanina da Jidda domin yanzu har waya muke da ita.    Ban ankara ba har uku tayi. Ai kuwa da sauri na tashi na saka kaya kasancewar dama tuni nayi wanka na. Wata sabuwar atamfa ruwan ganye mai ratsin fari na saka. Na shafa 'yar hoda sai kwalli da dan man lebe._







   _Tuni na tsara yanda abun zai kasance yau dan kuwa ba irin shigar wancan satin nayi ba. Zannuwa na tusa a bayana na daure sai ka rantse da  Allah yaro ne. Da nasa hijab sai abun ya kara yin dai-dai domin kuwa hijab din dogo ne. Jakata na dauka na fita na kulle gidan, anguwar sai kallona ake an ganni da d'a sai dai wasu tunanin su dan Maryam ne na goyo. Ina zuwa bakin layi na tsaida adai-daita ya kai ni wannan karon har cikin asbitin ya shiga dani. Na biya shi kudin sa a hankali na sako ina taku dai-dai abuna na nufi Maternity,  ina shiga naga kowa harkar gabanshi yake, tun daga bakin kofan na hangi wata bakar mata mumuna wacce ke kwace a kan gado da alama dai itama haihuwa tayi.  Tun daga bakin kofar na dauke lumfashina a hankali na zuro hannu na fara fesa turaren, ba tare da wani ya kula dani ba, dan kowa hankalin sa na kan mai haihuwar sa._





Ai kuwa duk inda na wuce sai dai kaga mutane na zubewa barci. Da sauri naje na dauki jaririn na kwance tsummunan dake bayana na zubar nan. Lokacin da na dubi dan sai naga wata kyakywar yarinya ce, duk da farin jarintaka amma fara ce. Sai naji kamar na dubo wata amma kuma nunfashi nake so na shaka. In kuwa nayi kuskure na shaka a nan aiki ya baci. Dan haka nayi saurin goyata na fito abuna. Mutane sai zurga-zurga suke a filin asibitin na fito na saje da su. Duk wanda ya shiga Maternity a lokacin kuwa kafin ya ankara barci zai debe shi. A wannan karon ban sama matsala wajen fita ba, ina fita na tsayar da adai-daita na kai wa yan mafiya jaririyar. Mataimakin ogane a wajen ba Mansur ne ba ina tausayin ta na mika mishi kawai na juya na koma gida._




_Sai da naje na kira Safara'au nake tambayar ta ya naga wani ne a karagar gidan mafiyan ba Mansur ba. Yace min "Ai mansur tun shekaran jiya ya dau hutu wai cikin matar sa ya tsufa zai koma gida yayi jinyar ta". Kash! banji dadi ba wannan ya batan bajuk! Na fada a zuciya.  Da dare muna chat da Jidda ina sane dan in tsokalo maganar nake tambayar ta ya akayi kwana biyu take sauka daga on da wuri. Nan take gayan wai ai maigidan ta ne ya dawo rainon ciki. Nayi Dariya nace, "Kai a gaskiya mijin nan naki naji dake". Tace, "Uhmm ba dai so ba yana son yaran shi dai ba ni ba". Nace "Saboda me kika ce yaron yake so ba ke ba?". Tace in da ita yake so tun can farko me yasa bai dawo gida ya tare ba. Muna cikin chat wayata tayi kara. Da sauri na dauka ganin mai kira._





_Muryar kani na Adamu ce cikin rudu da rudewa yake gaya min cewa wai yanzu aka kira shi yana gare ji ake gaya mai anzo gida an sace su Umman mu  har da Baba ma. A razane na mike cikin kaduwa nace "What! An sace su Umma kuma? Anyi kidnapped nasu kenan?".  Nan da nan kuwa na isa gidan. Jama'a yan anguwa tuni sun cika gidan namu mata da maza. Ban tabbatar da abunda ya gaya ba sai yanzu. Ai kuwa na fashe da kuka ina sambatu. Nan wasu sukayo kaina suna lalashi na. Nan ake fada min wai matasa ne guda hudu suka zo gabannin isha'i ko wanne hannun sa da bindiga fuskokin su a rurufe  suka zo suka kama su Umma. Wani dattijo ne ya gansu lokacin da suke kokarin tura su a mota kafin ya sheda wa jama'a tuni sun gudu.  Koka naci gaba da yi. Wani makwabcin mu yace ba kuka ne ya kamace ni ba. Abunda zamuyi shine muje police mu kai report. Haka kuwa akayi._





Ni da adamu muka runkuta muka kai report. Har gida aka hado mu da wasu polices din suka zo aka bayyana musu duk abunda ya faru sukace mu kasance a ankare wai masu garkuwa da mutane ne. Dan haka mu ringa barin wayoyin mu a kunne zasu kira. Da zarar sun kira mu sanar da su. Nan kowa ya watse aka barmu mu biyu a tsakar gida kuka nake ina fadar. "Haba wannan wane irin zamani ne? Wace irin masifa ce wannan? Mutum na abinci ma na  neman ya gagar shi haka kurin sai kuma a bullo musu da wata bala'in? To yanzu idan masu garkuwa da mutane ne ina zamu sama kudin da zamu basu?". Adamu kam lalashina yake yana bani baki har dai nayi shiru a raina na san  ko nawa ne kuwa zan biya kudin fansa. A nan gidan naci gaba da kwana. Su Umman bala duk sunzo mana jaje da sauran yan uwa ma._





_Kwana daya biyu shiru ba text massage balle a kira. A rana ta uku da mukaji shiru muka koma gun police muka bayana musu halin da ake ciki. Bamu samu wani kwakwaran  bayani ba muka koma gida. A ranar kuwa nima na koma gidan aure na. Ina zaune ina zaune a tsakar gida Umman bala ta shigo. Bayan na bata waje ta zauna mun gama gaisawa tayi gyaran murya tukun ta fara da cewa. "Yauwa Nusaiba ya batun iyayen ki fa har yanzu shiru ne?". Nan take kwalla ta kwaranyo min mace "Wallahi har yanzu shiru ba a ga su Maman mu ba". Tace, "Ayya yi hakur Allah ya bayyana su". Nace "Amin". Ina goge hawaye da zani. "Nusaiba dama zuwa nayi ki kirayo min Bala dan akwai wata muhimmiyar magana da nake son yi da shi yanzun nan". A firgice na dago kai ina kallon ta gabana yayi wani mumunar faduwa..................................................._

Tabb Nusaiba chakwakiya. Ni dai ina gefe


Autan Writers, Autan Zamanawa. ✍










👨🏻‍💻👩🏻‍💻 ​*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​


        *'YAN MAFIYA*​
            ☠☠☠☠☠☠
     ​Gajeren labari​

 ​*Part 80-85*

© 🤴🏻 ​*KINGBOY ISAH* ✍🏼


.                👨🏻‍💻👩🏻‍💻        .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


👨🏻‍💻 *Readers kuyi hakuri please. Wallahi abubuwan ne suke yawa, shiyasa bakwa jina kullum. Jiya ma anyi wa sister na sauka ne. Naso yau in kawo muku karshen labarin amma sai dai ko gobe in sha Allah.*


👨🏻‍💻 Masha Allah jiya a nan *Daura* dalibai *449* suka yi saukar alqura'ani. Ciki kuwa harda sister na *NAJA'ATU NASIR* 🤸🏻‍♀ 'yan Tahfeez manya wanda sukayi harda *23* . Da kuma yara wanda sukayi harda su *41.* Duk karkashin makarantar *MADINATUL AHBAB*  🤸🏻‍♀ Ina taya yan uwa da abokan arziki murna. Kuma Allah yasa kunyi karatun da zai amfane ku ya amfani jama'a duniya da lahira amin.


•        *KARSHEN PAGEN BAYA*      •
*~"Nusaiba dama zuwa nayi ki kirayo min Bala dan akwai wata muhimmiyar magana da nake son yi da shi yanzun nan". A firgice na dago kai ina kallon ta gabana yayi wani mumunar faduwa.~„*


_Da sauri kuma sai na kirkiro murmushi nace, "Umma kinsan fa baya da waya, dama nima a wayar Saifullahi abokin sa muke waya, bari nasa hijab naje naga ko yana gida". Daki na shiga na sako hijab na fito waje. Yayin da ita kuma Umma ta nema waje ta zauna.  Fita nayi na shiga dayan gidan muka dan gagaisa. Domin karya nayi ba wani Saifullahi. Na koma gida na sanar wa da Umma cewa baya nan. Ranta ya baci sosai kuma ta nuna damuwa a kai domin tace muhimmiyar magana ce take so suyi da shi. Haka dai mukayi sallama da ita ta tafi ba dadi. Washe gari tun da safe Salima ta yo mun sallama. Wai Umma ta aiko ta akan maganar su ta jiya in Saifullahi na nan ta koma ta gaya mata._



_Ni duk a zatona maganar ta kudi ce, hakan tasa na shiga daki na daukko mata kudin da na tanada. Dubu ashirin ne, na mika mata nace, jiya bayan ta tafi da yamma na koma gidan su Saifullahi  shine ya hada ni da Bala. Da na fada mai Umma na san magana da shi shine yace yasan matsalar bata wuce ta kudi, yace bala ya bani dubu ashirin din nan in bata".  Salima ta karfa bata ce komai ba ta juya ta tafi._



_Dadi ya kamani ina tunanin na wuce wannan matsalar. Fita nayi bani nan baya na dawo Maryam take gaya min "Umma ta zo da zun har take masifa wai wato kinga mijin ki baya nan shine kike fita yawo inda kike so. Kuma tace da daddare zata dawo"._


_Hankali na ya tashi matuka domin na lura abun na Umma ba na kudi bane Kawai, dole akwai dai abunda ya faruwa.  Da dare muna chat da Jidda take gaya min wai tun safe take fama da nakuda. Hankalina yayi matukar tashi nan take na fara bata shawarar taje asbiti, tace da mai gidan ta yace suje taki amma yanzu taji abun ya fara tsanan ta zasu tafi. Naji dadi a raina nan na fara bata shawarar taje General hospital dan yafi ma'aikata. Shiru naji gata a online amma ba  replay.  Da naga hakan baiyi ba na kira nan ma shiru. Hankalina ya tashi dan a tunanina Na kudar ce ta taso suka tafi asbiti gashi yanzu bansan ko wannen asibiti bane balle ma inje._



_Waka na kwana ina sake-sake cike da damuwa. Nayi kira har na gaji amma ba a dau wayar ba. Daren haka na kwana ido na biyu ban rintsa ba dan matsaloli sun mun caa! Ga tunanin zuwan Umma da safe dan bata zo da daren ba. Kuma bansan ko da wacce zata zo ba._




_Washe gari da safe wajen karfe bakwai na kira wayar cikin sa'a kuwa naji ta shiga. Mansur ne ya dauka bayan mun gaisa nake tambayar sa Jidda. Shine yake gaya min tana Asbiti ta haihu tun jiya da dare, yanzu ma kayan abinci ya zo dauka kuma ya sanar a gidan su.  Na nuna farin ciki sosai nan na sheda mai ni Aminiyar tace na tambaye shi asbitin da aka kai ta. Yace General._



_Naji  dadi sosai dan dama haka nake so. Amma sai nace, me yasa ka kaita General? Bayan kasan yanda ake satar jarirai a gurin". Yace, "Jiya lokacin da Haihuwar ta zo dare yayi nabi duk asbitocin kudi sun tashi dan dole muka je can general din domin a lokacin tana bukatar taimakon gaggawa. Sannan kuma an zuba matakan tsaro ai a general din"._ 



 _"Nace to Allah taimaka anjima zan zo ganin jariri ko jaririyar".  Yace "Jariri ne ma". Mukayi sallama na kashe wayar._


.
_Tashi nayi ko dama lokacin tuni nayi wanke tun safe. Ban ko tsaya na karya ba na kara goya tsuma kamar dai na wancan satin, na shirya tsaf! Na sa doguwar hijab dina na fita. Ban zame a ko'ina ba sai bakin asbiti. Bayan na sallami mai napep naga gate din asbitin kanshi sojoji uku ne ke gadi. Gabana ya dingi faduwa. Da nayi tunanin ko in naje za a dakatar dani ko a gano ni._



_Amma sai naga an kyale ni na wuce ba tare sa an tsayar da ni ba. Cikin asbitin duk ma'aikata ne aka raraba sojoji da yan sanda. Abun ya bani matukar mamaki, haka aka zuba matakan tsaro._




_Rasa inda zan nufa nayi dan ina tunanin ko ba a fito da Jidda daga labour room din ba. Gudun kar ma'akatan wajen su zarge ni yasa na nufi Maternity kai tsaye domin na duba naga ko tana nan._



_Da shiga kuwa na hangi Jidda kan gado  tana barci, gefen ta ga gadon jariri. Duk motanen gun hankalin su baya kai na. Hakan yasa nayi saurin fito da turaren na fara fesawa. Cikin sakwan ni kuwa duk suka bingire suka kama barci._



_Da sauri na nufi jidda nayi saurin kunce tsumman na goyi jaririn ciki  hanzari na bar dakin.  Da sauri na fito ina addu'a har na fita daga asbitin ba wata matsala. Napep na tsayar bai ajiye ni a ko ina ba sai kofar gidan 'yan mafiyan.  Sosai nake farin ciki dan wannan jaririn shine fansa ta. Dan kuwa kamar yanda na kudarta dama shima sai na kashe jinin sa kamar yanda ya kashe mijina._



_Ina shiga gidan gabana ya dingi faduwa ba dan komai ba sai dan ganin Ogan mu Mansur a tsaye sai bangala dariya yake. Cikin dakiya na isa wajen nasan fada musu haihuwar ne yake ni kuwa sai nayi fuska kamar bansan anyi masa haihuwa ba ma._



_Fuskar sa dauke da murmushi ya tarye ni yana mun sannu da zuwa hade da fada min matar shi ta haihu. Na taya shi murna kafin na kunto goyan har zan mikawa mataimakin sa jaririn hannuna sai yayi sauri ya tarye ni yana fadar._




_"Su Nusaiba manya ashe har an samo kawo ni zan bawa gunkin shi domin yau ina cikin farin ciki". Dum! Naji gaba na ya fadi dan ina tsoran bashi yaron kar aje ko ya gane yaron. Kuma sai na tuna cewa ba lalai ya sanshi ba domin haihuwar dare ce. Kuma da safe ya taho gida._





_Da na mika masa kallo naga ya tsare yaron da shi yayin da ni kuwa gaba na ya shiga faduwa yana dukan uku-uku amma sai na basar. Bayan kallon dan lokaci da yawa jaririn sai ya dago ya kalle ni yace, "Nusaiba wannan sabuwar haihuwar fa a ina aka samo shi"._




_Da har zance masa ina ruwan shi. Kuma sai na tuna kar ya zargi wani abu dan na gane cewa bai tabbatar da dan nashi bane.  Hakan tasa nayi murmushi nace,  "Kai dai bari oga yaron makwabciyar mu ne jiya da safe aka haife shi ni kuwa nayi yan dabaruna da dare na sace shi a wajena ma ya kwana"._



_Kallo na yake yana nazartar fuskata domin kuwa wannan kallon rashin yarda ne. Anma da jin  abunda na fada kuma na saki raina ina dariya sai yayi tunanin ba wani abu. Murmushi yayi yace, "Nusaiba iyayen sa'a. Bari naje na kaiwa Kudunbur dan jirana ake Asbiti"._ 



_Au kuwa nace zan bishi dan in tabbatar da ya yanka shi din hankali na dai ya kwanta. Har ciki na bishi zuciya ta cike da farin ciki kasancewar oga ne da kansa zai yanka Dansa hakan ba karamin dadi ya mun ba._ 




_A gabana ya dirka wa yaron sa wuka ya zuzuba jinin a inda yake so. Maimakon naji tausayin sa sai ma dadi da naji.  Haka ya fito yana sauri zai koma asbiti ni kuwa na fito na nufi gida ina jin dadin lalai na dauki fansa._




_Ina zuwa kuwa na shiga daki ina dariyar mugunta. Ana haka naji sallamar Umma abunda ya katse mun farin ciki jin dadi da walwala kenan. Nan take damuwa ta kori farin ciki daga kan fuskata._




_Na fito ina mata sannu da zuwa. Tsawa ta daka mun, "Ke Nusaiba ba gaisuwa ce ta kawo ni ba. Na gaji da wannan raini  wayon naki. Shin wai  Bala ba dana bane? Da kike hanani yin magana da shi. To Wallahi bazan bar gidan nan ba ko kwana zamuyi sai kin hada ni munyi magana da Bala"._




  _Shiru nayi ina tunanin ya zanyi ni kam. Sallamar da akayi ne ta dakatar da mu. Yan sanda da sojoji ne suka fara durowa cikin gidan. Cikin firgici nake tambaya meke faruwa. Wata macen police ce ta zo daf! Dani ta maka min kulkin hannun ta a kafa._





 _Tana fadin, "Shegiya macuciya azzaluma munafukar boye 'yar mafiya kawai. Asirin ki ya tonu...,............................................._



😢 *Wayyo Nusaiba sai slow.   Kamar yanda nima sai slow abubuwa ne suka taru suka jefa ni Busy 🙇🏻👨🏻‍💻 Fans shiyasa kuke jina shiru. But da yardar Allah next page zan kawo muku karshen labarin* ☺



Autan Writers, Autan Zamanawa. ✍






👨🏻‍💻👩🏻‍💻 ​*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​


        *'YAN MAFIYA*​
            ☠☠☠☠☠☠
     ​Gajeren labari​

 ​*Part 85-END*

© 🤴🏻 ​*KINGBOY ISAH* ✍🏼


.                👨🏻‍💻👩🏻‍💻        .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com


________________________________________
🌹🌹🌹🌹🥀
*DEDICATED TO YOU*  _*°MUHIEVERT INDIA°*_
🌹🌹🌹🌹🥀
________________________________________

Wannan page kyauta na baki. Naki ne ki yi yanda ma kike so da shi. Pagen naki ne in kinga dama ki bawa BIEBOH ko words uku ma.  Ke din dai da aka sani___ ♡ Muhievert india​♡
​♡Er india​♡
​♡ Er love​♡
​♡ Er Mumcy​♡
​♡ Er dad​♡​
♡ Muhien Mumcy'nta​♡
♡Er gayu ♡
♡ Er kwalisa ♡
♡Er makaranta ♡

Er ♡Er ♡Er ♡Er ♡Er ♡Er ♡Er ♡ ...........🤗 Barasu kare ba sai nata yi har karshen book in.


•       *KARSHEN PAGEN BAYA*    •
~Wata macen police ce ta zo daf! Dani ta maka min kulkin hannun ta a kafa.Tana fadin, "Shegiya macuciya azzaluma munafukar boye 'yar mafiya kawai. Asirin ki ya tonu.~

_*S*osai na shiga cikin rudu. Yar sandar kuwa dukan kafana da take yasa na zube kasa kan gwiwoyina ina bada hakuri. Umma ta rikice tambaya kawai take "Me yake faruwa-me ke faruwa".  "Wannan da kike gani yar mafiya ce, duk jariran da ake sacewa ita ke satar su. Kinga wannan mai gadin asibitin ne shi ya tona mata asiri". Ta nuna mutumin da ya fara shigowa gidan.  Umma ta shiga gardama tana rantse-rantse ni ba yar mafiya bace, amma ina suka ki sauraren ta. Wasu daga ciki suka fada dakina. Ina ji kwaramniya alamun bincike suke a dakin. Ba a jima ba suka fito da jakar kudin nan. Umma na gani ta kame baki tana mamaki._




_Keyata aka tasa gaba har mota Umma na biye damu, jama'ar anguwa tuni an taru wiwiwi! Aka tayar da motar ba a tsaya ko ina ba sai asbiti. Nayi mamakin ganin wajen cike makil. Ma'akata kuwa kala-kala a gun._



_Ta tsakiyar mutane aka ratsa dani kai na a sunkuye, wasu sai jifana suke. Yar sandan nan kuwa sai turani take gaba da karfi. A haka muka karasa wajen, D.P.O ne tsaye gaban shi Mansur sai zazaga masifa yake. Gefan su kuwa ga wani soja da nake kyautata zatan shima babba ne._



_Mansur na gani naga yayi tsuru yana kallona. Fuskar shi tashin hankali ya bayyana karara. Ni kuwa harare nake banshi da shi kawai.   Da zuwan mu D.P.O din nan ya kashe ni da mari  nan take na fadi kasa ina kuka. Dan marin ya gigita ni._




_Cikin tsawa ya fara magana. "Ke 'yar iskan banza azzaluma ina kika kai jaririn mutane? Ashe dama ke ce barauniyar gaki kamar mutuniyar kirki amma zuciyar ki baka ce kirin ashe. Maza ki fada mana ina kika kai jaririn da kika sata jiya dama wanda kika sata". Kai na daga cikin hawaye na kalli Mansur da tuni jikinsa ya fara rawa yana hararata._




_Na nuna shi da hannu nace "Shi na kaiwa jaririn kuma ya kashe shi".  Shiru naji mutanen gun sunyi suna kallona suna kuma kallon Mansur. Ganin haka yayo kai na yayi ball dani cikin masifa yake cewa. "Ke dan ubanki a ina kika sanni da zaki ce kin bani jariri? Taya ma zakice ni kika bawa dana kuma na kashe shi. Shin kinsan yanda nake sonshi kuwa?"._




_A fusace ya juya ya fuskanci D.P.O yake cewa. "yallabai kana ji fa yarinyar nan zata mayar damu mahaukata". D.P.O yace "barni da ita". Ya karaso waje na ya kara dauke ni da wani marin yana kara tugumata in fito da jariri. Ni kuwa na kekashe kasa nace yana Mansur na bawa._




_Kuma nace duk satar da nake yi shi yake saka ni. Kuma dan dole ya sakani domin ya kashe mun miji kuma ya kama iyaye na yayi garkuwa da su".   Mansur idanunsa ne suka furfuto jin abunda na fada.  Umma dake gefe da sauri tayo kaina tana cewa "Me kika ce?"._




_Cikin kuka nace, "Kwarai Umma wannan da kike gani mugu ne azzalumi shugaban yan mafiya ne. Shi ya kama Bala yace in banbi umarnin sa ba sai ya kashe shi. Yasa na ringa sato masa mutane, daga karshe bansa ko ya akayi ba ya kashe bala. Da yaga ya mutu shine fa ya kama su Mamana ya boye yace sai na ringa sato masa jarirai ko ya kashe su. Ni kuma naga ba yanda zanyi shiyasa nabi umarnin sa"._



_A fusace Mansur yayo kai na da nufin duka na. Da sauri D.P.O ya dakatar da shi da kyar yasa wasu yan sanda suka rike shi domin sai fusge-fusge yake yana zage-zagen wai karya nake sharri zan yi masa. Ganin abun da yake da yanda ya tashi hankalin shi ne yasa  D.P.O ya gane a kwai kamshin gaskiya a magana ta._




_D.P.O ya zo gabana ya tsuguna cikin sanyayyar murya yace, "Taya zamu gaskata duk abunda kike fada?".  Cikin kuka nace, "Yallabai ai nasan wajen da aka boye iyayyen nawa. Muje tare da shi wajen". D.P.O yace, "In fa Mukaje muka iske karya kike to kashin ki ya bushe". Nace "Na yarda"._




_Mansur naga rantse-rantsen karya nake ba a kula shi ba. Aka tura shi muta muka runkuta. Ina nuna musu hanya har muka karasa can cikin jeji ne wani gida da ba alamun mutane a ciki na kai su gurin.  Yan sandan suka bubuga gidan aka ki bude wa. Dan ansa sakata ne daga ciki. Dole sai wasu suka haura suka bude mana muka shiga gaba daya. Ana leke-leke kuwa aka gano dakin da Su maman mu suke. Dakin an rufe shi da kwado. Da sauri aka bige kwadon aka fiddo su._

.
_Muka rungumi juna ni da Mamana  muna kuka. Mansur kuwa tuni yan sanda sun fara dukan shi. Sai ihu yake yana cewa sharri akayi masa.  D.P.O Ya tambaye ni me yasa ban kai kara gun yan sanda ba bayan kuma nasan gidan.  Nan take na fada mai cewa ai bazan iya kawo kai na gidan ba. Domin tsafaffen gida ne. Yanzu ma dan tare da shi muka taho shiyasa muka gane gidan. Nan take na tuna masu lokacin da na taba kai kara wajen su nace muje na kai su gidan yan mafiya._



_Ba a bata lokaci kuwa wasu daga cikin su suka tuno nan suka tuna masa. Nu ce wace na dauke su muka ta zagaye gari na kasa gane gidan. Har suka mamare ni da muka dawo  D.P.O  ya sallame ni.  Sai da aka zo nan ya tuna yace kwarai kuwa anyi haka._




_Nan muka runkota muka dawo asbiti tun a mota ake dukan Mansur ya fadi inda matsafar su take amma yaki. Da muka dawo Asbitin jama'a sunyi mamaki sosai ganin an dawo da Ummana kuma wannan  karon mansur ake duka ba ni ba._



_Umman Bala hankalin ta a tashe tayo kai na tana kara tambayar Ina danta. Ai kuwa na fashe da kuka na sake nuna Mansur nace shi ya kashe shi. Sumammiya ta fadi a wajen wai Bala danta daya namiji wanda take ji da shi ya mutu. Aka kwashe ta aka nufi ciki da ita dan bata taimakon gaggawa._




_Duk dukan da ake wa Mansur kin fada yayi. Sai daga na zagaya na shawarci D.P.O nace ayi masa barazana za a kashe matar sa zai nuna. Ai kuwa D.P.O  ya umarta aka fito da Jidda aka dora mata bakin bindiga a gaban sa. Ana kokarin harbawa da yaga ba wasa ake ba yace a dakata zai fada. Duk yayi jina-jina aka saka mu a mota ya kai mu har gidan. Sojoji da yan sanda suka balla kofor gidan. Suka ringa duruwa ciki suna kamo mutane. Nayi mamaki dan sai da aka kama mutane maza da mata wajen su ashirin. D.P.O  ya umarci a bankawa gidan wuta. Ai kuwa da sauri nace a kwai gidan kasa inda dodon yake a fara toya shi sanann._




_Haka kuwa akayi dake ban mance hanya ba na kai su har gidan kasan. Aka kwanto tsafaffun gawarwakin yaran shi. Dan  musu sutura sannan aka watsa fetur aka cinnawa dakin wuta.  Wani ihu muka ringa ji na fitowa daga dagin mai tsoratar wa da sauri muka fito aka rufe dakin._




_Gaba daya kayan gidan sai da aka fitar aka toya su. Har da kudi daki guda cike. Cikin fridges kuma sasan jikin mutane ne akai ta fiddowa ana zuwa dan yi musu sutura.  Bayan an kone kayan ciki. Gidan ma aka kunna mai wuta._




_Farin cikina a wannan hali baya musaltuwa. Jidda kuwa kuka kamar ranta zai fita. Har suma tayi lokacin da taga gawar babban danta. Ashe dai Mansur tsafa shi yayi ba bata yayi ba._





_Washe gari kotu cike fal da jama'a kowa cewa yake a kashe Mansur. Haka kuwa akayi alkali yasa a kashe shi ta hanyar rataya a gaban jama'a. Sauran yan mafiyan kuwa daurin rai-da-rai akayi musu. Ni kuwa hukuncin shekara biyu a gidan yari. Wai saboda laifin da na aikata wanda Mansur ya saka ni yi._



_Mutane na ganin ba a kyauta min ba. Kamata yayi a sake ni. Ni kuwa kukan farin ciki kawai nake. Dan ko kadan ba wanda yasan kulla-kullar da nayi. Domin har su momy nice na biya kudi aka sace su. Me gadi ina sane na bari ya gane ni. Dan duk abubuwan da na tsara dai-dai suka gudana.  A duniya dai na wanke laifina a idon jama'a. Sai dai kuma wajen Allah bansan ya nake ba.  Hakan tasa shekara biyun nan da aka ce nayi na kudurci niyar zan nemi yafiya a gun Allah._

 *TAMMAT BIHAMDULILLAH.*

A ANAN NAKE KAWO KARSHEN WANNAN GAJERAN LABARIN. 



*****
*NA SADAUKAR DA GAJERAN LABARIN NAN GA*

 *PEN WRITERS ASS.*

AND

 *ELOQUENCE WRITERS ASS.*

🤓 ^^ANA MUGUN JONE DA ZAMANAWA.^^
*JINJINA DA FATAN ALKHAIRI*

Na jinjina muku readers din wannan littafi a duk inda kuke. Ina godiya da bani lokacin ku da kuka yi. Hade da juriyar bibiyata da kukayi. Na gode sosai Allah yasa mu amfana da shi gaba dayan mu. 😍 Ina son ku ina kaunar ku har kullum kuma ni naku ne. 🤸🏻‍♀


MU HADU A

SABON LITTAFI NA

MAI SUNA


*UWA KO KISHIYA?*


KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN BA KARAMAR CHAKWAKIYA CE A LITTAFIN BA.

LITTAFI NE DA YA KUNSHI


YAUDARA

CIN AMANA..

MUNAFURCI

SON ZUCIYA

MUGUN KISHI

SON KUDI

SHARI'A

Bari dai kar na cika ku da surutu. Sai kunji ni. In sha Allah nan ba da dade wa ba zaku jini 🤸🏻‍♀

SANNAN INA BADA HAKURIN KAN LITTAFIN JIRGIN SO DA BAKU JINI BA. HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON WASU DALILAI NAWA.


Autan Writers, Autan Zamanawa. ✍ (WHATSAPP 08096831009)










Comments