Abban Sojoji Book 3 Takun Karshe Complete New Page By Boss Bature

💋Boss Bature💋*

Join this link to follow my tiktok acct👇


https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*


*Father of soldiers**🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Tunkafin ma yaji dalilin kiran Na Ammi har ya fara jin fargaba,duk da baya tunanin Sehrish zata bashi matsala,Ajiyar Zuciya ya ɗan sauke Still Eyes dinshi na akan fuskarta,


Yana kokarin sanar da ita kiran da Ammi ke yi masu,Mommy Azeema ta shigo cikin ɗakin da sallama abakinta,"Assalamu alaikum",


Har suna haɗa baki wurin Amsa mata sallamar"Wa'alaikum Salaam,"tunda ta shigo idanuwanta na akan Sgr daya tsare Sehrish da ido,


Gyaran murya ta ɗanyi"Rafayet Ya mai jikin"?

  Daƙyar ya iya amsa mata"jiki Alhamdulillah,fatan kun Tashi lafiya,"

  "Lafiya lou,"kafin ta mayar da idanuwanta kan Sehrish"Ya jikin naki Daughter"?

  Cikin sanyin murya tace"da sauƙi Mommy,"

  "Allah ya ƙaro sauƙi,"

"Ameen,"ta amsa mata,


Miƙewa Tsaye Sgr yayi a tsanake Ya soma magana"Ammi nason ganinmu yanzu,"

  Hajiya azeema tace"Eh dama Daga can nake,nazo ne don in taimaka mata mu tafi,Sai kuma na same ku atare,"

  "Okey,"ya ambaci hakan tare da kama hanyar fita daga ɗakin,


Daƙyar sehrish ta sauko daga saman gadon,Da taimakon Hajiya Azeema ta canza rigar jikinta zuwa jallabiya baƙa,Ta yafa mata gyale,Yadda kasan balarabiya saboda hasken da tayi,


Dafa Hajiya azeema tayi itama ta tallabota don ta samu damar yin tafiya,Fitowa suka yi daga ɗakin,kaitsaye suka Nufi bedroom ɗin Ammi,Lokacin da suka Shiga,sun tarar da Abba da Abusufyan Zaune gefen gadon Ammi,Mommy na zaune saman Sofa tare da Sgr duk ya kame kanshi,Yayin da Ammi ke zaune Saman Kujerar gaban Madubin ɗakin ta juyo da ita,Yadda zata samu damar ganin kowannansu,


Ganin sun shigo Yasa Mommy ta mike ta koma gefen Abba ta zauna,da hannu ta nuna ma Sehrish gefen Sgr,Ba don taso ba,ta zauna kusa dashi,ƙamshin turarenshi duk ya cika mata hancinta,a hannun Sofa ɗin Hajiya Azeema ta zauna ta 6angaren Sehrish,cike da girmamawa Sehrish ta soma gaishe dasu,Fuskar kowannansu asake suke Amsa mata gaisuwarta,haɗi da yi mata Ya jiki,daƙyar take amsa masu da sauƙi,daga haka Ta duƙar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta,sai da kowa ya natsuwa,tukunna Ammi ta soma magana atsanake,

  "Muyi ma Annabi salati" gaba daya suka amsa da Sallallahu alaihi wasallam,bayan sun gama Ammi taci gaba"Alhamdullilah,Naji daɗin ganin kowannanku,ko ban faɗi ba nasan kunsan dalilin kiran naku da nayi,dafarko dai kuskure ne anriga da an yishi,tun daga kan iyayenku da suka yanke shawarar yi maku aure batare da sunyi shawara dani ba...."dakatawa ta ɗanyi da yin maganar tana mayar da numfashi,kafin ta ɗaura da cewa"kamar yarda nace zanyi adalci atsakaninku,in har kun amince zaku cigaba da zama da junanku to falillahil Hamdu,ba wanda zai raba ku,In kuma ɗaya daga cikinku Ya nuna baya ra'ayin auren to za'a rabashi,'


Hankalin Sgr ba ƙaramin tashi yayi ba,don har saida ya ɗago ya kalli Ammi dake kora jawabi,hakanan ya dinga jin zuciyarshi na bugawa,


"Amma kafin In fara jin ra'ayoyinku,zan yi maku wata ƴar nasiha,"kowa ya kasa kunne yana sauraronta,sosai tayi masu nasiha akan Kuskuren da kowannansu Yayi,tun daga kan Abusufyan da Abba da suka haɗa auran har izuwa kan tursasa mashi akan Ya saketan da sukayi,Sgr ma tayi mashi faɗa sosai Akan abunda ya aikata,jikin kowannansu Yayi sanyi sosai,


Bayan ta kammala Yi masu nasihar Ta kalli Sgr tace"Inaso naji ra'ayinka game da yarinyar nan,Shin kana ra'ayin cigaba da zama da ita amatsayin matarka ko kuwa.... ?"


Jim ya ɗan yi kafin ya jinjina kanshi tare cewa"zan cigaba da zama da ita a matsayin matata,"Sehrish tayi mamakin amsar da ya bayar,kuma bilhakki dagaske yayi maganar,On a serious matter,

  Nunata Ammi tayi da sandar hannunta"Saura ke,Shin kin amince zaki cigaba da rayuwa dashi A matsayin mijinki......?"gaba ɗaya ido ya dawo kan Sehrish ana jiran jin amsarta,musamman Sgr duk da bai ɗago ya kalleta ba,Amma a ƙagare yake da yaji amsarta,haka hajiya azeema ma duk ta ƙosa taji amsar da Sehrish zata bayar,itama Mommy idonta na akan Sehrish,


Jin tayi shiru Yasa Abusufyan Ya tanka mata"Daughter amsarki muke son ji,"


A ruɗe tace"Ni banason shi,bazan cigaba da rayuwa dashi ba,Dan Allah a rabani dashi,"


A firgice Sgr ya ɗago yana kallon fuskarta,tashin hankali,Ko a mafarki bai ta6a tunanin Sehrish zata iya furta waɗannan kalaman ba,


Ita kanta Hajiya Azeema sai da gabanta Ya faɗi jin amsar da sehrish ta bayar,Babu wanda ya tsammaci hakan daga gareta,


Daƙyar Sgr ya iya daurewa Ya cije Ya soma magana cikin sanyin murya ta wanda ya karaya"Idan har akan laifin da nayi maki ne,inaso ki sani ba'a son raina nayi maki hakan ba,kuma ina baki hakuri akan hakan,'


Girgiza kai ta shiga tana fadin"Dan Allah Ammi a rabani dashi,Ya rafayet bai ta6a sona ba,yana so yaci gaba da zama dani ne saboda wata manufa tashi,ya fadi hakan ne saboda Yaci gaba da ƙasƙantar dani a matsayin ƴar aikinshi ba matarshi ba......'


Jikinshi har tsuma yake yi,ba don Allah yasa Manyanshi na akusa ba,da ba abunda zai hana ya ham6are bakinta,just speechless Yama rasa me zaice!!


Ƙasa ƙasa da murya Hajiya Azeema ta soma yi mata magana"Ki shiga natsuwarki,sannan ki gyara kalamanki,ban hanaki ki faɗi ra'ayinki ba,Amma ina guje maki kizo kiyi abunda zakiyi danasani,"


Mommy kuwa cewa tayi"har yanzu yarinyar nan bata dawo hayyacinta ba,tundaga kan yarda take magana babu natsuwa atare da ita,nasan ta faɗi hakan ne saboda Abunda Rafayet yayi mata,"


Shidai Abusufyan bai tanka masu ba,sam baiji dadin abunda Sehrish tace ba,Saboda yanzu kowa Shi zai zarga,za'ayi tunanin koshi ya tunzurata ne,Kamar kuwa ya sani tunda Sehrish ta fara surutannan idanuwan Abba na akanshi,Kallon tuhuma kawai yake yi mashi,


Duk wannan abun dake wakana Akan Kunnan Omar,wanda bai jima da shigowa ba,Yana atsaye Ya goya hannayenshi Asaman kirjinshi,Hankinshi ba ƙaramin tashi yayi ba jin abunda Sehrish take faɗi,dama sai da yakawo hakan aranshi,ta tsorata ne sosai,gani take kamar in taci gaba da rayuwa dashi zai kasheta ne wata rana,

>>>Also Click Here To Download Complete Book Document

"Sure i know initially nayi accepting aurenta don tayi mun aiki,ko wannan lokacin banyi don na ƙasƙantar da ita ba,kuma na amince da aurenta ne,don ina ra'ayin zama da ita,Ba amatsayin contract ba"tuni idanuwanshi sun cicciko tab da kwalla,duk ya muzanta a idanuwansu,tun da yake arayuwarshi bai ta6a tunanin wata ƴa' mace zata Iya rejecting dinshi ba,abun Ya girgiza shi fiye da tunanin me tunani don tuni zazza6i Ya rufar mashi,duk da Sanyin A.c ɗin dake shawagi a ɗakin,Hakan bai hanashi Yin zufa ba,fuskarshi sharkaf take tamkar an watsa mashi ruwa,kowa Ya lura da Yanayin da Sgr ya shiga,


"Ni shaida ne Ammi,wlh Rafayet Yana sonta sosai,da ace baisonta ko aurenta bazai kar6a ba,kuma abunda ya faru atsakaninsu tsautsayine,ba don son ranshi yayi mata hakan ba"Marshal Omar ne yayi maganar,duk ya shiga damuwa,Sehrish naso ta 6allo masu aiki,


"Ki fadamun me nayi Maki da har kike guduna?Na ta6a cutar dake ne hakanan,bayan wannan abunda ya faru"?yayi maganar muryarshi tamkar zai fashe da kuka,yayin da idanuwanshi ke akan fuskarta,kwata kwata babu annuri akan fuskar Sehrish,ta canza tamkar ba ita ba,


"Idan har akwai abunda nake yi maki,wanda bakyaso ki fadamun zan daina,"cikin lalama yake lallashinta,


Ammi dai ta kasa kunne tana sauraron kowannansu,tana jira su gama,Ta zartar da hukuncin daya dace,


Fashewa Sehrish tayi da matsanancin kuka,tamkar ranta zai fita,cikin shessheƙar kuka take cewa"Don Allah A sanya ya sake ni,shi dakanshi yace duk hukuncin dana yanke mashi zai kar6a hannu bibbiyu don haka inaso Ya bani takardar Sakina,kuma bayan aurenmu saida ya bani damar cewar Zan iya kula duk wanda nakeso koda Namiji ne shi bai damu ba,don haka Ni Ina da wanda nakeso Yanzu haka ......... ."

  Gaban Sgr ne Ya faɗi rasss!lokaci guda yabi ya susuce ya dabarbarce,jikinshi sai kerma yakeyi,Zuciyarshi sai faman tafarfasa take yi,Ya harzuƙa sosai but he's trying to control his anger,don ta fara wuce gona da iri,


Kowa na wurin sai da yayi mamakin kalaman sehrish basu ta6a tsammanin zata iya furta su ba,gaba ɗaya ammi ta karancesu tsaf,


Gyaran Murya ta ɗanyi,hankalinsu ya dawo kanta,yayin da idanuwanta ke akan Sehrish dake ta faman matsar kwalla,

  "Share hawayenki,kukan ya isa haka!Ae dama nace zanyi maku adalci atsakaninku,To ki kwantar da hankalinki,"jin wannan maganar yasa Sehrish taji hankalinta ya kwanta,


  "Amma inaso ki natsu kiyi tunani kafin ki yanke hukunci,don na lura kina acikin fushi sosai,kada kiyi irin kuskuren da iyayenku suka yi na tursasa mashi akan Ya sake ki,wanda silar hakan ne yasa shi rafayet din Ya huce akanki,daga baya akazo ana danasani,to banaso kiyi danasani daga baya jikata,Tabbas Rafayet bai kyauta maki ba,amma inaso ki sani saboda son da yake yi maki ne duk yajawo hakan,saboda bayaso a rabashi dake,yayi tunanin hakan shi zaisa abarmashi ke sai dai kash Yayi abu cikin fushi,kuma daga baya yazo yana danasani,sannan kuma karki manta da kanshi ya gyara 6arnar da yayi maki,wanda da ace da mugunta yayi maki zai tafi ya barki ne,Kiyi rai ko ki mutu,Amma saboda yasan bai kyauta ba,Ya tsaya har sai daya ga kin samu Lafiya,Ina faɗa maki wannan ne ba don ina goyan bayanshi ba,Sai don ina guje maki yin danasani,musamman idan ya kasance kinason Shi tun fil,azal,"Ajiyar zuciya ammi ta ɗan sauke bayan takai ƙarshen maganarta,ɗaya bayan ɗaya take kallon fuskokinsu,ɗakin yayi tsit baka jin komai sai shessheƙar kukan Sehrish,


Cigaba da magana tayi a tsanake"zan tambayeki a karo na ƙarshe,Amma inaso Ki fara yin tunani kafin ki bani Amsa,kinaji ko"?


Cikin shessheƙar kuka tace"Eh ammi,"

Ita kanta ammin bason rabasu takeyi ba,don ta fahimci akwai soyayya mai ƙarfi atsakaninsu,daƙyar ta iya buɗe baki tace"Har yanzu kina akan bakanki na son rabuwa dashi"?cike da fargaba ammi tayi maganar,ba ita ba hatta su Mommy,kowa hankalinshi ya tashi,Sgr kuwa tuni Ya karaya,ya rufe fuskarshi da tafin hannunshi,


Cike da kwarin guiwa tace"Eh,Nidai arabani dashi,"yadda kasan Ya shako wuyanta haka yake ji,takaishi ƙarshe,tuni ciwon kai ya farmasa,


Duk yadda Abusufyan yaso ta ɗago su hada ido don ya dakatar da ita,Amma yarinyar nan ta kafe,taki kallon kowa daga cikinsu,


Jinjina kai ammi tayi"Shikenan,rafayet ina fata kaji abunda tace!tana buƙatar ka sake ta,"Yadda kasan tayi magana da bango haka Sgr yayi masu shiru,baice uffan ba,domin kuwa baya acikin hayyacinsa,Sama sama yake jinsu,

>>>Also Click Here To Download Complete Book Document

"Amma kuma wani hanzari ba gudu ba,"ammi ce tayi maganar tana kallon Sehrish,

  "Har yanzu da sauran jikinki kuma shine likitan dake dubaki,ni aganina,me zai hana ki bari kiji sauƙi sosai sai ya sake ki?Ni nayi maki alƙawarin da zarar kinji sauƙi zansa ya sake ki,"

Tunda Ammi taso ma magana,Abba ya fara sakin murmushin gefen fuska,don ya gane wayau ammi takeso tayi mata,don tasan kafin lokacin zaiyi wuya in bata sauko daga fushin da take yi dashi ba,

  "Ki amince Sehrish,kinga baki da lafiya kuma shi kaɗaine zai iya dubaki acikin gidan nan,shi yasan kan abun,kuma kinga da igiyar auran nan kawai zai iya yin hakan,"Hajiya Azeema ce ke yi mata raɗa acikin kunnanta,shiru sehrish tayi da alama tana yanke shawara da zuciyarta ne,ita aganinta za'a iya ɗauko wani likitan yaci gaba da dubata ba dole sai shi ba,tana kokarin bude baki tayi magana Hajiya azeema tayi saurin cewa"Ta amince,"

  Ammi tace"Nafiso naji ta bakinta,"

  Nauyin Hajiya azeema da take ji ne yasa tace"Na amince,"saboda bata son ta ƙaryatata," dama da biyu Hajiya Azeema tayi mata hakan,don tasan Sehrish bazata Iya musawa ba,in har tasa baki,"


  Ajiyar Zuciya kowannansu ya sauke,har Lokacin Sgr bai ɗago ya kallesu ba,


"Shikenan magana ta ƙare,Zamu zuba ido har Allah ya baki Lafiya,daga nan ni kuma zan Kar6ar maki takardar sakinki,"tana kai ƙarshen maganar,Tace ma azeema"Ki taimaka mata,ta koma ɗaki,"

  "To ammi,"ta amsa tare da ruko sehrish ta miƙe daƙyar,suka fuce daga dakin,


Bayan fitarsu ammi taci gaba da magana"kar kuga laifinta,tana cikin wani hali ne wanda dama karshe hakance zata faru,anma ci sa'a da ta dawo hayyacinta don mafi akasarin wadanda irin hakan ya faru dasu sukan fita hayyacinsu tsawon lokaci wasu ma ta6in hankaline ke samunsu,yayin da wasu kuma daga haka sai su fara tsoron maza....." dan dakatawa tayi sakamakon shigowa da Hajiya Azeema tayi,ta koma kan hannun kujeran data tashi ta zauna,


Ammin ta dasa"kamar ita dae,na tabbatar bata rasa son shi kawae abunda yayi mata ne yasa take tsoron cigaba da zama dashi",

   "Tabbas Ammi tana son shi wllh don ni shaida ce baki na da nata munyi maganar lokacin da aka daura masu Auren,wanda hakanne ma yasa lokacin da ta gano dalilin da yasa ya auretan ba don yana sonta bane don tayi masa aikine yasa ta shiga wani hali har ta kulle kanta acikin Toilet"Hajiya Azeema ce tayi maganar,gaba daya suka shiga jinjina kai,

Kallon Sgr Ammi tayi wanda har lokacin tafin hannunshi na rufe da fuskarshi,sai dae duk abunda suke fada yana jinsu,


"Rafayet",Ammi ta kira sunanshi,a hankali ya zame tafin hannunshi ya kalleta, blue eyes dinshi sun canja launi don ba karamin sarawa kanshi ke mashi ba,

"Matarka tana son ka tunda ga tabbaci nan daga Azeema,muma kuma ba son rabuwarku muke ba,don haka inason kayi amfani da wannan damar dana samar maka wurin ganin ka shawo kanta daga dokin zuciyar da ta hau,kaima kuma inason na kara jan hankalinka,ba komae ne karfi ke samarwa Mutun ba,wani abun in kace zaka sa mashi karfi to kuwa zaka rasa shine gaba daya kamar dae aurenka yanzu,inason kabi komae a hankali in sha Allah komae zai zama daidai,sannan wannan bakar zuciyar dole sai ka rinka yin yaki da ita,ka rinka neman tsari daga wurin Allah akan ya rabaka da sharrinta don in dae zaka rinka yanke hukunci cikin fushi to wllh ka dinga yin dana sani kenan,A duk lokacin da wani abu ya 6ata ma rae kayi kokarin ganin ka daidaita natsuwarka kafin ka yanke hukunci,Yadda kake yin nasara Akan aikinka haka nikeson ka rinka yin nasara akan zuciyarka aduk lokacin da ta taso maka kaji?" dan jinjina mata kae yayi,

Cike da zolaya ta juya ta kalli su Abba tace"Yakamata a siyo mashi buta ya rinka yin alwala da ita,yana rage sauran ruwan yana sha ya daina yi a famfo ko Allah ya sanyaya mashi ita"gaba daya sukae Murmushi,shi dai still yayi bai tanka ba,


"Ko akwae mai magana?" gaba daya suka ce a'a,kallon Marshal Omar tayi"sai ka rufe mana da Addu'a"gaba daya suka daga hannu harda Mommy,Omar ya shiga jero Addu'oi daga bisani suka shafa.


Daga haka Ammi ta basu Iznin Tafiya,


ƙoƙarin miƙewa Sgr yayi wani irin Jiri ne ya soma ƙoƙarin kwasarshi,da sauri Omar ya ruƙe shi,ya taimaka mashi har suka fita daga ɗakin,


A bedroom ɗinshi Omar ya shigar dashi,Kaitsaye ya faɗa yaraaaf saman gadon,jiki babu kwari,yadda kasan baya numfashi,hawa saman gadon Omar yayi,Yasa hannu ya cire mashi rigar jikinshi,ganin yadda zufa ke tsastsafowa daga jikinshi,


"Bro,Are u not feeling well"?yayi tambayar yana kallonshi,ya runtse idanuwanshi sai faman Cizon pink lip ɗinsa yake yi,daƙyar ya iyacewa"Omar,zuciyata babu daɗi,yarinyar can ta 6ata mun rai,wai har ni zatace bataso?bata ra'ayin zama dani?wacece ita?mata nawa suke neman wannan damar a wurina"?......daƙyar sautin muryarshi 

 ke fita,da wani irin hucin zafin zazza6in jikinshi,


murmushin gefen fuska Omar ya saki,wato har yanzu rafayet bai gane cewa Ya afka tarkon so ba,babban takaicinshi Yadda Sehrish ta furta bata ra'ayinshi agaban kowa,ba ƙaramin ƙona mashi rai tayi ba,


"Am sorry bro,just forget about her,idan ka shareta zata dawo maka ne"

  A hasale yace"tafita daga cikin zuciyata mana,"

  Ƙiris ya rage Omar ya fashe da dariya,Aranshi yace"Kaine ka sanyata acikin zuciyarka malam,"

   Miƙewa yayi daga kwancen da yake,Ya sauko ƙafafunshi ƙasa,sumar kanshi duk ta rufe mashi gefe da gefen fuskarshi,

    "Zan shiga toilet,pls before na fito,ina bukatar magani ciwon kai,"yana kai ƙarshen maganar,ya sauko daga saman gadon Ya nufi toilet ya shige,kafin ya fito Omar ya ajiye mashi medicine ɗin asaman side drawer tare robar ruwa,


Sehrish kuwa,bayan mommy azeema takaita ɗakinsu,Saman gadon ta haye fuskarta sharkaf da hawaye,taso ace Sgr ya sake ta,don yanzu batason duk wani abu da zai alaƙantata dashi,ta wani 6angaren kuma taji daɗin hukuncin da Ammi ta yanke,koba komai tayi mata alƙawarin zata amsar mata takardar sakinta,

>>>Also Click Here To Download Complete Book Document

Tana cikin yin wannan zancen zucin nata,Hajiya azeema ta turo ƙopar ɗakin fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa,xama tayi daga gefen gadon cikin sanyin murya ta soma magana"Why sehrish?Don me zaki nemi ya baki takardar sakinki!Ba kina sonshi ba"?

  cikin shessheƙar tace"Yanzu bana sonshi aunty azeema,bana iya rayuwa dashi,Nidai kawai nafison arabani dashi,"

  "Indan kan abunda yayi maki ne yasa kika yanke shawarar rabuwa dashi,to kuwa zaki tabka kuskure,Domin kuwa Kina sonshi,Kuma shima ba ason ranshi yayi maki haka ba,Kuma ga dukkan alamu ba ƙaramin so yake yi maki ba,wanda silar hakan yasa shi yi maki haka duk don kada araba shi dake....."dakatawa ta ɗanyi da yin maganar 

  "Aunty azeema,wlh baya sona,bani yakeso ba,kema kinsani yana yin amfani dani ne kawai don biyan buƙatarshi,Sannan don naci gaba dayi mashi aiki,ba amatasayin matarshi ba,tunda nake dashi bai ta6a furta mun kalmarso ba,"tana magana hawaye na wanke fuskarta,

  Shiru azeema tayi tana kallonta,Lamarin Ya fara bata tsoro,don dagaske sehrish take yin maganarta 

Cikin sigar lallashi tace"Haba sehrish,duk irin wahalar dana sha wurin ganin na gyara tsakaninki da Sgr saboda in taimaka maki ki samu soyayyarshi,amma shine kike ƙoƙarin lalata mana shirinmu why pls"?cike da takaici tayi maganar,

"Am sorry aunty azeema kada ranki ya 6aci,Wlh yanzu bana sonshi,Ko son kallon fuskarshi ma banayi,"

  Jinjina kai Hajiya azeema tayi"Shikenan,tunda kin nuna baki sonshi,bazan tursasa maki ba,"shiru suka ɗanyi na wani lokacin kafin tace"inaso zanyi wanka,jikina duk yayi mun tsami,"

    "Okey,Yakamata ki dage da yin sit bath,ko kin dawo daidai,naga tafiya ma daƙyar kike yinta,kuma bazan fasa gyaraki ba,kamar yadda nayi niyya,zan ɗaura daga inda na tsaya ne,sannan cikin kayan dana kawo maki akwai wasu sabulai na nan,zasu taimaka maki sosai,idan har kika dage da yin amfani dasu"


"Shikenan,nagode sosai,"saukowa tayi daga saman gadon,a hankali take tafiya,Azeema na binta da kallo harta shige cikin toilet,Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta miƙe ta fuce daga ɗakin,


After some minutes,sehrish ta fito jikinta ɗaure da towel fari,gaban mirror ta zauna,ta jima tana kallon kanta,ta cikin mirror batare data motsa ba,ita kanta ta lura da sauyawar da tayi,kodan saboda jinyar da tayi ne yasa tayi haske sosai,Amma tafi tunanin Jinin Sgr ne da aka ƙara mata, yasa tayi haske,Anata shirmen,hannu tasa tana shafa ƙashin wuyanta daya fito,Ba ƙaramin kyau yayi mata ba,almost 15 mins,Tana zaune,kafin daga bisani ta mike,Ta koma gaban wadrobe ta budeta,doguwar riga ta ɗauko mara nauyi red colour ta zurata ajikinta,Lalla6awa tayi ta koma saman gadon,idanuwanta cike tab da ƙwalla tarasa meke yi mata daɗi,


Yinin ranar daga ita harshi babu wanda yaci abinci,saboda yanayin da suka tsinci kansu,ita tana kukan arabata dashi,Yayin dashi kuma yake neman mafita kafin lokaci ya qure mashi,Saboda tsabar farga duk in agogo ta buga sai gabanshi ya faɗi,saboda lokacine ke tafiya......'acikin bargonshi ya yini kiran sallane kawai ke fito dashi,kamar yadda itama Take ƙumshe acikin bargonta,Kiran sallah ne kawai ke tayar da ita,


*Boss Bature*


Wuraren ƙarfe 8:30 na dare sehrish na ƙumshe cikin bargo,ita kaɗai ta rage acikin ɗakin,Su jahad da oummansu sun fita wurinsu Mommy dake zaune suna fira a babban palourn gidan,tare da gwaggon katsina dasu hafsat,duk sun hallara a palourn,Hada wasu daga cikin matasan gidan,Gwanin ban sha'awa,


Turo ƙopar ɗakin akayi,Duk a tunaninta Sgr ne yazo dubata,tuni ranta ya 6aci,jin muryar hajiya azeema ne yasa ta leƙo daga cikin bargon,

  "Ya jikin naki"?

"Da sauƙi,"ta amsa mata a yayin da take kokarin mikewa daga zaune,ta sauko ƙafafunta kasa,

"Me zai hana ki koma ɗakin azmee da yin jinyar?nan kamar zaki takura ne,"

  Girgiza kai sehrish tayi"A'a,nafi jin daɗin zama anan,"

  "Gaskiya ni ban goyi bayan ki zauna anan ba,can sai kin fi sakewa,Yanzu haka ma daga can ɗakin nake,Na gyara maki shi,ki taso in taimaka maki ki koma can,kinga nan yayi maki kaɗan,kuma dama can kike kwana ae "

  Ba don taso ba,tace"toh,"

Miƙewa tayi hajiya azeema ta taimaka mata,suka fito daga ɗakin takaita ɗakin azmee,Lokacin da suka shiga cikin ɗakin,An gyara ko'ina tsaf sai ƙamshi ke tashi acikinshi,ita kanta ba ƙaramin kyau ɗakin yayi mata ba,"


Kaitsaye saman gadon ta hau ta kwanta,tana faman sauke ajiyar zuciya,

  'Bari na kawo maki dinner ɗinki nasan kina jin yunwa,"

  "Aunty kona ci,Amayar dashi nake yi,bakomai ke zama cikin cikina ba,bana jin daɗin abincin ma,"ta ƙarasa maganar,tare da jan bargo ta lullu6e rabin jikinta,

  "Kada ki damu,ba wani abu mai nauyi zan haɗo maki ba,in sha Allah,ba zaki amayar ba,".  

  "Toh,"iya amsar data bata kenan,

Bayan Aunty azeema ta fita daga ɗakin abakin ƙopar ɗakin ta tsaya,Hannu tasa cikin aljihun rigar jikinta ta ciro wayarta,


Call log ta shiga,ta danna ma layin Marshal Kira,Tana fara ringing ya ɗaga awayar,

  "Omar,ina rafayet din?Yakamata yazo ya dubata,yanzu haka na dawo da ita ɗakin azmeen,inaga kamar zasu fi sakewa anan,"

  On the other hand Omar yace"Yanzu zanyi mashi magana,nagode ssai,"

Daga haka su kayi sallama,Ta nufi kitchen,


After some minutes harta fara jin bacci,hajiya azema ta turo kopar ɗakin hannunta ɗauke da tray,Wanda ta shirya mata dinner ɗinta,a saman table ta ajiye mata shi,tare da janyoshi izuwa gaban gadon,

  "Ki daure ki ci,Zaki ji sauƙin jikinki,"

  Yunƙuwa sehrish tayi daƙyar ta miƙe zaune,ta sauko da ƙafafunta ƙasa,

   Wayar hajiya azeema ce ta soma ringing,Da sauri tace"ina zuwa,ki fara ci kafin in dawo,"tana kai karshen maganar tayi saurin fucewa daga ɗakin,

>>>Also Click Here To Download Complete Book Document

Ajiyar zuciya sehrish ta sauke,a hankali ta kai hannu ta ɗauki kofin tea mai zafi,takai bakinta tana kur6arshi a hankali,ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,tana cikin Shan tea ɗinnan,Taji an turo ƙopar ɗakin,Afirgice ta ɗago don taga wanene koda sukayi arba da Sgr,Nan take ta saki kofin hannunta,Ya faɗi ƙasa,ruwan tea ɗin data rage ya zube,


Abakin ƙopar ya tsaya yana kallonta,yayin da ya goya hannunshi asaman ƙirjinshi,wani irin daddaɗan ƙamshine ke fitowa daga jikinshi,Yana sanye cikin Sleeping dress dinshi,blue colour, hasken shi ya fito ssai,ya ɗaure sumar kanshi ta baya,Kyau Iya kyau,


Duk da taji tsoranshi,amma bata bari ya gane hakan ba,tuni ta ɗaure fuska,tare da kawar da idanuwanta gefe guda,


Slowly ya ƙarasa cikin ɗakin tare da samun wuri gefen gadon ya zauna a kusa da ita,gaba ɗaya ƙamshin turarenshi ya cika mata hancinta,sam bata so zuwanshi ba,yayi tunanin zata gaishe shi amma ko kallo wannan bai isheta ba,

  "Ya jikin naki,"?

daƙyar ta iya amsa mashi"da sauki,"

  Shiru su ka ɗanyi wani lokaci,bakomai yake tunawa ba,face maganar dasuka tattauna da Omar,

    "Laifin me na aikata maki da har kike son na sake ki"!

    Wannan tambayar da yayi mata ba ƙaramin 6ata mata rai yayi ba,wato baima son laifin da yayi mata ba,Saboda shi bai ɗauki abun serious ba,

  "Ko don saboda abunda ya shiga tsakanina dake ne"?

  Girgiza mashi kai tayi Alamar a'a,


Ya kuma cewa"I won't hurt you anymore,i promised u"

 Ko uffan bata ƙara ce mashi ba,ranshi ya 6aci sosai,hakanan ya daure yaci gaba da magana,

   "Its Okey,just calm down ur mind,da zarar kinji sauƙi,zanyi maki yadda kikeso,Hakan yayi maki"?.

  ɗaga mashi kai tayi alamar eh,

Hannu yakai tare da ɗaukar cup din data jefar,Ya haɗa mata wani tea din Ya miƙa mata,

  Hannu tasa ta kar6a,har lokacin bata ɗaura idanuwanta akanshi ba,

  Sosai tashiga shan tea din,don ba ƙaramar yunwa take ji ba,

  Abunda zai baka mamaki da kanshi,Ya shiga yin serving ɗinta,bayan ta kammala shan tea ɗin,Ya zuba mata farfesu acikin plate mai zafin gaske,yaso ya bata abaki amma sai ta nuna cewa zata Iyaci da kanta,natsuwa yayi yana kallonta,Daƙyar take ɗaukar Naman tana turawa acikin bakinta,Jurewa kawai yake yi,amma shi kaɗai yasan yadda yake ji acikin zuciyarshi,baisan ya zaiyi ya shawo kanta ba,gashi Omar ya gargaɗeshi akan ya guji 6acin ranta,kuma aduk lokacin da yake tare da ita,ya manta da matsayinshi na Suregon general,


Ganin ya sanya hannunshi acikin plate ɗinne,yasa ta dakata da shan farfesun,batare data ɗago ta kalleshi ba,sai ma cire hannunta da tayi,Har ya harzuƙa zai daka mata tsawa,Sai ya tuna sharuɗɗan da Omar ya bashi,a hankali ya furta Ya salaam,

  Sai da ya cire hannunshi daga cikin plate ɗin tukunna ta mayar da nata hannun taci gaba ci,'abun ya ɗaure mashi kai,Kuma ya kasa yi mata komai,,

   Turo ƙopar ɗakin hajiya azeema tayi fuskarta ɗauke da murmushi,hannunta na ruƙe da ledar magungunan sehrish,Asaman bedside drawer ta ajiye mashi ledar,"kafin ta juya ta nufi ƙopar fita daga ɗakin,A lokacin Amrish na ƙoƙarin shigowa ɗakin,su kayi kici6us da Aunty azeema,da sauri Amrish ta gaishe da ita,

  Fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa mata,

  "Lafiyalou,amrish har an gama firar"?

  "A'a,bacci nake jine,"

  Ruƙo hannunta hajiya azeema tayi,"mu tafi ɗakina ki kwanta,"batare da tayi mata musu ba,tabita suka nufi ɗakinta 


Bayan sehrish ta kammala cin abincin,ya bata magungunanta,kafin ta gyara kwanciyarta saman gadon,Sai faman hura hanci takeyi,ita duk atakure take jinta,saboda kallon Da sgr keyi mata,ta kosa ya tafi yabar mata ɗakin,a ƙarshe data lura daɗin kallonta yake ji,Sai ta janyo bargo ta lullu6e jikinta duka hada fuskarta,


Kusan minti 5 ta soma tunanin koya tafi ko yana nan oho,Hannu tasa a hankali ta ɗan zame bargon ta leƙo don taga idan ya tafi,Abun mamaki saita same shi zaune yana cin sauran abincin data rage,ta6e baki tayi kafin ta koma cikin bargon,tayi mamaki sosai,Ko meyasa yake cin kingin abincinta Ohom masa,


Bawan Allah,Duk yinin ranar baici abinci ba,saboda damuwar daya shiga,Shiyasa yake cin sauran abincin data rage,ko zai samu sauƙi acikin zuciyarshi,don ba ƙaramin ƙona mashi rai tayi ba,Bayan ya kammala cin abincin,Ya kora da ruwa mai sanyi,ita duk a tunaninta zai tafi ne idan ya kammala cin abincin,amma har wurin ƙarfe goma sha biyu na dare,Yana zaune gefen gadon,Ya kasa motsawa,ya saba da ita koda yaushe a irin wannan lokacin suna manne da junansu,ko yaje ɗakinshi bazai iya runtsawa ba,Kwarama ya zauna yana kallonta nannaɗe cikin bargo,zaifi samun natsuwa,


>>>Also Click Here To Download Complete Book Document

Boss Bature✍️_Ina rokon Allah Ya bani Ikon Kammala Littafin Nan cikin sati mai zuwa I need ur prayers,ga duk mai buƙatar karanta Littafin abban Sojoji from book one two 3 ya tuntu6i ne,Amma ta whatsapp za'ayi mun magana 08103884440_ Click Here To Download This BookLatsa Nan Domin Sauke Wannan Littafin A Wayarka

Comments