ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 22

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*AljanaR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/Cwm4wecksEE

http://www.bonitomi.com/2023/05/Aljanar-fatima-book-2-part-21-hausa.html*^ Part 22 ^*


A cikin saurinsu irin na aljannu Aljana Safuratu ta cafke Aljana Marakisiyya nan take suka bace su ukun tare da Murja, can suka bayyana a kan wani katon dutse nan take Aljana Safuratu tayi nuni da hannunta zuwa kan Aljana Marakisiyya nan take wasu irin sarkoki suka bayyana suka daure Marakisiyya tayi iya kokarinta domin ta kubuce da duk karfinta na aljannu amma abun ya gagara domin ita kanta ta san cewa Aljana Safuratu ta fita karfi. Zaunawa tayi ta zubawa Marakisiyya da kuma Murja ido na dan lokaci, nan take abubuwa da dama da suka faru suka dawo mata sabo a kwakwalwarta. 


Shekara sha takwas da suka wuce bayan ta tabbatar da cewa komai ya dai-daita a gidan su Fatima a lokacin su Mama Asiya sun koma salahai na karfi da yaji, domin irin ladabtarwa da Safuratu ta rika yi musu, sai da ya kasance idan Fatima na waje ko magana basa son yi don kar su batawa Fatima rai Aljana Safuratu ta hukunta su, don haka a lokacin zaman gidan yayi dadi ba kadan ba domin duk mugunta irin ta Mama Asiya da rashin ji irin na su Nasmat da Asmart sai da suka natsu suka zubda makamansu. Wataran Safuratu ta fita yawo kamar yanda ta saba tana zaga gare ta hangi Murja lokacin Murja yarinya ce karama a ciki hali irin na sabon hauka, don haka tayi yunkurin taimaka mata tun kafin haukan yayi nisa. 


A kokarinta na shiga jikin Murja ne ta samu Marakisiyya a cikin jikin na Murja, abun yayi matukar bata mamaki don haka a matsayinta na musulmar Aljana wacce tayi niyar taimakon Murja tambaya ta farko da tayi wa Marakisiyya shine, "Ke Musulma ce ko kafura?". "Ni musulma ce amma ina shawartarki da kiyi gaggawar fita daga wannan safgar domin kuwa lamarin nan ya wuce duk inda kike tunani idan kuma kika dage a kan cewa sai kin karya sihirin jikin Murja kuma kin koreni to tabbas zakiyi nadama". Murmushi kawai Safuratu tayi domin tun a lokacin ta san cewa ta fi karfin Aljana Marakisiyya nesa ba kusan ba amma gashi har barazana take yi mata don haka sai ta fara da nasiha tana mai cewa. 


 "Yake yar uwata Sunana Safuratu ni musulmar Aljana ce, na kasance ba kamar sauran yan uwanmu wasu aljannu ba domin bana yin zalunci bana kuma bari ayi zalunci a gabana, haka zalika bana bautar shedan ko boka ko kuma wani malami kamar yanda shedanun cikinmu suke yi. Ina miki nasiha da kiji tsoron Allah tunda kin ce ke musulma ce ki sani akwai hisabi tsakanin mutum da aljan kamar yadda kike tunanin kinfi karfin wannan baiwar Allah a duniya har kike kokarin gusar mata da hankali to fa ki sani hakkinta ba zai barki ba zai iya hallaka ki ya sakaki wuta. Don haka ina umartarki da ki warware duk wani sihiri da kuka shiryawa wannan baiwar Allah domin gusar mata da hankali, tunda nasan mafi yawanci mu aljannu masu haukata mutane muna bin umarnin wani Boka ne ko kuma Malami wanda ya biya mana wata bukata don haka kiyi hakuri ki bar wannan baiwar Allah".


Wata iriyar dariya mai rikitarwa Aljana Marakisiyya tayi daga bisani kuma ta murtuke fuska ta ce, "Ni in bar Murja? wannan tatsuniya ce ma, ki sani ko kasa da sama zata hade ba zan saurara ba sai na haukata Murja sai kuma na dai-daita rayuwarta". Murmushi Aljana Safuratu tayi a zuciyarta tana mamaki ko da yake ta san halin taurin kai irin na jinsun su na aljannu don haka ta ce, "Ke kuwa ya sunanki? Kuma me Murja tayi miki da har kike ikirarin sai kin Ι—ai-Ι—aita rayuwarta, ko dai wani mugun bokan ne ya saki wannan aiki?" Wata dariyar Marakisiyya ta sake yi yayin da ta ce, "Kinyi kadan da ki sa in fada miki komai". Babu irin lalashi da lallabo da Aljana Safuratu ba tayiwa Marakisiyya ba amma taki yarda ta bayana mata komai dangane da Murja ko kuma dalilin da yasa take so ta haukatata.


Sai da aka kwashe tsawon kwana takwas Aljana Safuratu tana bibiyar Marakisiyya da Murja tana lallabon Aljanar Marakisiyya ta hanyar lalama amma ta ki yarda ta karya shirin haukata Murja da take, yau ma kamar kullum a tsakiyar titi Murja ta cire dan kwali sai ihu take tana surutai irin na mararsa hankali, mutane sai kallonta suke cike da tausayawa kasancewarta kyakykyawar yarinya duk da kasancewarta ba fara ba, amma ba zaka sakata a cikin jerin bakaken mutane ba ta kasance wankan tarwada Murja bata wuce shekara 11 ba a lokacin duk da kasancewar tana da jikin girma, kayan da ke sanye a jikinta na iya tabbatarwa mutum cewa daga gidan alfarma ta fito.


Shiyasa Aljanata Safuratu take ta mamakin yadda yarinya kamar wannan ta bace amma babu sanarwar cigiya a gidajen jaridu ko na tv. Dai-dai lokacin ne Safuratu ta lura da abinda Marakisiyya take niyar sa Murja aikatawa, ruwan kwata take kokarin saka baki ta sha, a lokacin ne fa ran Safuratu ya ba ci nan take ta sa hannu ta shake wuyan Marakisiyya hade da cewa, "Yi gaggawar dakatar da ita daga abinda take shirin yi ko kuma in aikaki lahira yanzu domin nasan cewa ke kike juya ruhinta". Jin shakar da akayi mata ba na wasa bane kuma tayi kokarin kwacewa amma ta kasa domin karfnsu ba daya ba, babu shiri ta dakatar da Murja daga abinda ke shirin yi. Sakin Marakisiyya Aljana Safuratu tayi hade da cewa, "Ke wacece kuma wannan yarinyar da kike kokarin cutarwa wacece ki min bayanin komai kuma karki kuskura kiyi min karya domin na tsani makaryaci a cikin jinsinmu na aljannu ko kuma na yan adam".  


Marakisiyya da ba karamin jin jiki tayi ba domin sai fitar da lumfashi daya bayan daya take ba, ta dau lokaci a wannan halin ba tare da ta cewa Safuratu komai ba, nan take sai kawai ta daga kai yayin da ta bushe da dariya hade da cewa,


 "Safuratu kike ko wa? A zahiri nasan kin fini karfi kuma nasan kina da baiwa da yawa ko a cikin jinsinmu na aljannu ma daya-daya ne ke da baiwa irin naki domin nasan kina da fuka-fukai kina iya tashi kuma kina iya bacewa ki bayyana a duk inda kika ga dama kuma kina iya canza suffa wanda a cikin wadannan abubuwan da na lissafo ni kadan ne nake da su. To amma ki sani wannan yarinyar babu makawa sai na haukatata kuma ko irinku guda dubu zasu taru basu isa su dakatar dani ba". 


Tana gama fadar haka ta faki idon Aljanata Safuratu nan take ta bude bakinta hade da tsartawa Aljana Safuratu wani bakin ruwa wanda ya fito daga cikin harshenta. Cikin zafin nama Aljana Safuratu ta goce abin ya wuce ta gefenta, kafin ta waiwayo tuni Aljana Marakisiyya ta sake watso mata wannan dafi na cikin bakinta sai dai da faruwar haka Aljana Safuratu ta bace sai gata ta bayyana a bayan Aljana Marakisiyya da bayyanarta ta ware karfinta ta dirkawa Aljanata Marakisiyya kulli a baya wanda ya sa ta sakin wani kara na wahala yayin da jini ya furzo daga bakinta.


Aljana Safuratu ta durkusa a gabanta tana kallonta yayin da ita kuma ke fitar da lumfashi a wahalce ta ce, "Hakika kin jahilci kanki yar uwa da kike tunanin zaki iya yin amfani da gubar sankarau ki cutar dani, tun farko na san cewa kina dauke da wannan guba kuma zaki iya amfani da ita kiyi kokarin cutar da ni, domin nasan Gubar Sankarau ita ce idan ta taba jikin aljani har ta ratsa cikin jikinsa to duk jijiyoyin jiki suke tsayawa cik mutum ya kasa motsa ko da dan yatsa ne. Na tabbata haka kikayi niyar aikawa a gareni daga nan kuma ki hallaka ni amma Allah bai baki iko ba, ki sani ni bana nufin cutar dake shiyasa nake binki ta cikin laluma tsawon kwanaki amma zuwa yanzu kin fara fusata ni, amma idan kika yadda naje bango zan miki azaba irin wacce bakiyi tsammani ba". 


 
Duk da tana cikin galabaita haka ta sake tuntsirewa da dariya hade da cewa, "Kin tsallake tarkona na farko amma ba lalai ki iya tsallake na biyun ba". Safuratu ta ce, "Saboda ina tunanin ke musulma ce shiyasa nake tauyasa miki amma idan kika kara kokarin cutar dani zan nuna miki bambancina da naki duk da muna jinsi daya". Kafin ta gama rufe baki tuni Aljana Marakisiyya ta wullo mata wasu irin wukake masu kama da kibiya saboda tsini, cikin zafin nama Aljana Safuratu ta goce bisa tsautsayi wuka daya ta caketa a kafa, nan take ta kwala ihu saboda irin radadin zafi da ta ji. Kasancewar duk abinda yake faruwa suna yi ne a cikin duniyar ruhi ta su ta aljannu amma a zahiri har a lokacin suna jikin Murja


Ran Safuratu ba karamin baci yayi ba don haka cikin lokaci kankani jikinta ya fara tafarfasa, idanunta sukayi jawur yayin da gashin kanta ya mimike tsaye. Ita kanta Marakisiyya sai da ta firgita ta tsorata matuka amma a zahiri dariya take kyalkyalawa marar dadin saurare. Hannu kawai Safuratu ta daga sama nan take suka bace tare da Marakisiyya, sai gasu sun bayyana a cikin wani bakin daji mai dogayen itatuwa, lafiyayyen mari Safuratu ta wankawa Marakisiyya sannan ta ce, "Yanzu zan nuna miki asalin kala, kuma zan ga karshen taurin kanki". Da fadar haka a cikin wani irin sauri wanda ko su aljannun sai wanda yake da baiwa yake da shi Safuratu ta rika duka da naushin Marakisiyya ta ko wane bangare, saboda tsananin gudu irin nata tamkar walkiya ita kanta Marakisiyya kasa tare dukan tayi domin bata ganin Safuratu sai dai ta ji duka. 


Cikin lokaci kankani Safuratu ta hadawa Marakisiyya jini da majina, amma saboda taurin kai irin na Marakisiyya sai ta rika dariya abinda ya kara fusata Safuratu kenan, nan take ta kamata ta daure mata hannaye da kafafuwa ta ratayeta a jikin bishiya kanta a kasa kafafuwa a sama, bata barta haka ba ta debo wasu irin kwari na su na aljannu masu cizo ta zuba a jikin Marakisiyya, ai kuwa tun tana daurewa tana dariya sai da ta fara ihu tare da rokon afuwa a wajen Safuratu ita kuwa tayi banza da ita tamkar bata san da zamanta a wajen ba daga karshe ma ta bace sai bayan kwana biyu ta koma. A lokacin ba karamin ladabtuwa Marakisiyya tayi ba, domin jikinta ko ina saida yayi kullutu na cizon kwari duk kammaninta suka sauya. A lokacin tana ganin Safuratu tun kafin Safuratu tayi mata magana ta fara da cewa, "Don Allah don Annabi ki kunceni za fada miki komai, Sunana Marakisiyya kuma ni musulma ce don Allah ki kunce ni zan fada miki komai kuma zan karya sihirin da nayi wa Murja".............


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

😍

Comments