ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 18


🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/LgVOwZek43U


http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-17-hausa.html


*^ Part 18 ^*


πŸ™„ *Ba editing ayi hakuri da typing error*


"Yaya Fito kiji abinda take fada, yanzu ke Fatsuma ashe zargin da muke gaskiya ne maitarki ba a iya mu kadai ta tsaya ba harda awakinmu, to na rantse ahir dinki kurwar awakin nan tafi karfinki nan gani na bari". Kubura da ta fito tana tabe baki ta ce, "Ah to wallahi duk bakin cikinki haka zaki gansu ki barsu, yar akuyata ma da kika ci biya zakiyi ba yafewa zan ba. Kai ma dai Bukar tun a daki na ke so in fada ma ba sai ka sanar da ita ba yanzu miye amfanin sanar da ita? Kawai ka kama akuyar kaje ka sayar dare nayi kar kasuwa ta watse ma".


Da fadar haka Bukar kamar jira yake ya kama hanya ya kunce akuyar, babu irin rokon da Fatsuma ba tayi masa ba tana kuka amma yayi tsaki ya fuce da akuyar ya sayar. Wajejen Karfe biyar Fatsuma da ta dawo gida ta sama mahaifiyar tata na kuka nan itama ta hau kuka tana tambayarta me aka mata. A lokacin da ta ji abinda mahaifin nata yayi ita kanta sai da tayi nadama ta ji a zuciyarta dama bata dau fansar a kan yar tinkiyar Kubura ba. Duk da tana yarinyar ta san cewa babu komai a cikin abinda mahaifin nata ya aikata face hauka tsantsa, taya zaka kama akuyar mutane ka sayar. A zuciya taita sake-saken mafita daga karshe dai ta yanke shawarar tafiya gidan Inna Ma'u domjn ta sanar mata abinda mahaifin nata ya aikata. 


Bayan magariba ya dawo gida fuska cike da farin ciki, yayo tsarabar kasuwa su rogo ne, tsire, rake da yalo. "Ina kuke ku fito yau kasuwa tayi kyau na rantse da Allah". Da jin maganarsa Kubura da Laure suka fito suka taryesa suna lale maraba. Fatsuma na jinsu suna ta dariya musamman su Kubura wacce tayi kama da ta mugunta amma tayi banza da su ta cigaba da kai kukanta ga Allah. "Fatsuw! Fatsuma! Fito-fito yau ai dake za'a raba tsaraba". Tana daki ta ji yana kwala mata kira ta amsa amma tayi zamanta domin idan ta je wani bakin cikin ne ma zasu kara kunsa mata. Jin ya matsa mata da kira dole ta tashi ta je a gefe ta tsugunna, yayin da Kubura da Laure suka sa Bukar a tsakiya a kan tabarma sai tusa rogo a baki suke tun kafin a raba.


Hannu ya sa a aljihu ya fiddo da kudin "Ai akuyar nan tayi kudi, Ina Fatsuma kinga ga kudin akuya nan dubu talatin da biyar aka sayar da akuya kinga kuwa tayi kudi". Fatsuma ba ta ce masa kala ba ya cigaba da cewa "Yauwa yanzu ke Kubura nawa ne ainahin kudin yar tinkiyar taki". Tabe baki tayi hade da cewa "Wallahi yar tinkiyar nan na dora burika sosai a kanta, amma tunda yar gida ce kuma abunda ya faru ya riga ya faru kawai ta bada dubu goma sha biyar tunda akuya ce mai kyau, watakil da ta girma yan biyu zata rika haifa daga ganinta ai siffar manyan tumaki gareta". 


Zare ido Fatsuma tayi hade da cewa, "Duhu sha biyar kuma Yaya?". A yatsine ta kalleta hade da cewa "Eh kunnuwanki sunji dai-dai sha biyar na ce, ko kina so ki ce naman yar tinkiyar da kikayi maita kika cinye bai kai darajar dubu sha biyar ba?". Shiru Fatsuma tayi bata kuma cewa komai ba domin ta san cewa babu abinda zata iya canzawa a cikin lamarin nan. Ita tun dazun sake-saken zuwa ta sanarwa Ladi take da a yadda ta so ma shine ta je ta fadawa Ladi tun yana kasuwa su zo gidan su kasa su tsare Bukar na zuwa Ladi ta kwace kudin akuyarta. To amma tana ta tunanin yadda zata tunkari Ladi da wannan batu abun yayi nauyi sosai. Maganar Bukar ne ta tsinke mata tunanin da take, "Yanzu dai ke Kubura hakuri zakiyi ki karbi dubu goma, dubu ashirin din kuma gobe zan shiga birni in saro takalma domin in zo in kama sana'a, sauran dubu biyar a ciki ne nayi la'ada na kuma sayo wannan kayan tsarabar don haka dubu biyu ce ta rage gata sai a bawa Fatsuma dari biyar ke a baki dari biyar Laure ma a bata dari biyar, sauran dari biyar din kuma sai a rabawa yara kunsan ance la'ada tana sa dukiya albarka".


Da sauri Fatsuma ta ce "Ni dai bana so". Laure ta ce, "Af! Shikenan ai tunda bakya so sai mu rabe dama ni banji dadi da aka ce za'a baki ba". Bukar ya ce, "Rabu da ita ni zan dau na wajen nata dama wannan ashirin din a lissafe suke kudin jari ne". Shiru Kubura tayi wai ita tayi fushi jaririyar tinkiyarta ta fi dubu goma, da kyau Bukar ya sa ta karba. Daga karshe suka raba tsire da rogo da yalo Fatsuma ma an fidda mata kasonta ita da Mairo duk da bai kai na yan gidan yawa ba amma Fatsuma ta ce ta koshi su kara su cinye. Nan suka bita da bakaken magana wai mai bakin hali tana ji bata tanka musu ba, daga karshe ma da ta lura zamanta a wajen baya da amfani sai ta tashi ta koma daki domin yin sallar isha'a.


A bangaren Mairo kuwa tun da yamma take zaman jiran Inna Ma'u ance mata sun tafi wani kauye makwabtansu wajen gaisuwa. Shiyasa ma sai bayan isha'a ta dawo, Mairo tana kuka ta zayyana mata abinda Bukar yayi, ai kuwa Inna Ma'u kafin ta shiga gidan ma ta ce su je can gidan su Mairon su sama Bukar tun kafin ya kashe kudin. Haka kuwa akayi, tun a hanya Inna take balbala masifa har suka je gidan, Kubura na jinta tana yi a tsakar gida ai kuwa ta nanade kudinta ta boye a karkashin gado. Fatsuma na kuka ta fito ta zayyanawa Inna Ma'u duk abubuwan da suka faru, Inna Ma'u hannu kawai take tafawa tana salati jin irin wannan katobara. 


 "Ina Kuburar take ta fito ai nasan duk wani makirci ko mugunta da Bukar zai aikata tare da ita ake kullawa to fito ki kawo kudin nan tun muna shaida juna wallahi". Kubura na ji amma tayi shiru a daki, da abun ya ba Inna Ma'u haushi da kanta ta fada dakin. Bayan tayi-tayi Kubura ta fiddo dubu goman taki da kanta ta bincike dakin amma bata sama kudin ba. Daga karshe Inna Ma'u ta ce to ba zata bar gidan ba tana nan sai Bukar din ya dawo ya sameta a nan, ai kuwa ta nema waje ta zauna a tsakar gida ranar sunga masifa a wajen Inna Ma'u. Kubura da ta ga haka sai ta aika Wasila wajen Bukar ta fada mai duk abinda ke faruwa daga karshe ta ce, Wasila ta cewa Bukar din kar ya kuskura ya dawo gida domin Inna Ma'u na nan tana jiranshi.


Har wajen karfe sha biyu Inna Ma'u na jira Bukar bai dawo gida ba, don haka daga karshe dole ta tashi ta tafi gida tare da bar musu sakon cewa idan Bukar ya dawo ya tabbatar ya sameta a gidan kuma kar ya sake ya taba kudin nan. Washe gari Bukar tun da safe ya hau mota ya nufi birni da tunanin zuwa saro takalmi don ya san cewa idan Inna Ma'u ta ritsashi a gida duk bala'insa sai ya fiddo kudin shiyasa ya ke so yaje ya kaso su, ya san cewa idan ya kashe kudin dole ayi masa uzuri. Bayan ya sauka daga mota ne ya tsinci kanshi a wani sabon tashin hankali domin kuwa a lokacin ne ya ankara an yanke masa aljihu an sace kudin............


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

😍

Comments