ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 10

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/i_1jj2TTNzY


*^ Part 10 ^*


Bayan magariba tun daga kofar gida yake kwalla kira "Mairo-Mairo zo nan dan uwaki". Gaba daya yan gidan har na daki sai da suka fito ciki kuwa harda Fatsuma da gama sallarta kenan taji kiran da Bukar din ya shigo yana yi. Kubura tace "Haba Bukar lafiya irin wannan kira duk ka tsoratamu me kuma Mairon ta sake yi dama tun rana nake jira ka zo in fada ma laifin da ta yi domin kayi mata hukunci". Cikin fushi ya nufi dakin Fatsuma yana fadin "Barni da ita wai har ni Mairo zata kai kara wajen Inna Ma'u wai kin kashe musu akuya da ganga amma na kasa daukar mataki tana ina dan malfar ubanta". 


Fadima a tsorace tace, "Ta fita wasa". Hannu yasa ya mangareta hade da cewa "Ai duk ke kike koya mata rashin kunyar nan to wallahi ba zan rabu dake ba ke kanki". Nan take ya fara dube-dube a tsakar gida. Kubura tace, "Innalillahi Wa'inna Illaihir Raji'un yanzu wannan yarinyar Mairo har ta iya sharri haka? Kowa a gidan nan ya san cewa kwanan yar akuyar nan ne ya kare da sanadi ta zo gindin turmi ni kuwa tabarya ta subuce mun ta fada kanta ta mutu, sanin kowa ne kuma in ajali yayi kira sai anje". Bukar dake kokarin karyo bulalar bedi yace "Haka na fadawa Inna kamar yadda kika fada min amma ta fi yarda da maganar Mairo bansan wacce karyar ta kitsa mata ba Inna Ma'u harda sa hannu tayi ta dakeni don haka dole in fanshe a kansu shegu".  


Jikin Fatsuma ya dauki rawa tun daga nesa take bashi hakuri amma ina dan banzan duka ya lakada mata su Kubura na kara zuga shi da cewa tunda Mairo tayi sanadiyar da yasa Inna ta daki Bukar to ya ci uban Fatsuma kawai itama da daurin gindinta watakil ma ita ta tura Mairo. Cikin rashin sa'a bai gama dukan Fatsuma ba sai ga Mairo ta shigo ai kuwa ya hada da ita ya zanesu baki daya sai da bulalar ta kakkarye sannan ya rabu da su ya fita daga gidan yana masifa. 


Fatsuma ta rungume Mairo suna kuka Kubura dake dariyar mugunta ta karaso wajen hade da cewa "Maganinku kenan dangin mayu kadan ma kika gani wallahi, akuya dai ce Allah ya dauki abinsa in ma da gangan na kasheta ai Allah ne ya rubuta zata mutu a hannuna balle ma kowa ya shaida wannan abu tsautsayine". Laure tace "Fada mata dai Yaya yanzu ai gashi ta sha dukan banza, gobe ma ta kara kai karar Bukar wajen Inna Ma'u". Bata ce musu Uffan ba taja hannun Mairo suka shiga cikin daki tana lalashinta.



A kwana a tashi ba wuya karamar sallah ta zo, tun kafin azumi ya raba Bukar ya tattara yaran gaba daya ya kaisu wajen Idi tela ya aunasu baki daya amma banda Mairo da mahaifiyarta Fatsuma domin su kansu sunsan cewa basa daga cikin wanda ake wa dinki a sallah. Abun ba karamin kona ran Fatsuma yake ba, a ganinta ko da ita baya mata dinki ai bai kamata ya daina yiwa Mairo dinki ba a matsayinta na yarsa ta jini. Ita babba ce zata iya jurewa amma Mairo yarinya ce kusan ko wacce sallah haka take wuni a gida ba walwala kasancewar tana ganin duk kawayenta da sabbin kaya amma ita bata da shi. 


Bayan magariba Fatsuma na jin shigowar Bukar ta fito da sauri ya nufi dakin Kubura ta kira sunanshi "Baban Zubairu". Ya juyo "Miye kuma zaki wani kwalawa mutum kira da tsakar daren nan". Kokari tayi ta yafice tsoron da ya mamaye zuciyarta a zahiri wannan karon tayi nufin kwatawa yarta hakkinta ko da kuwa Bukar zai doketa kamar yadda ya saba, don haka ta fara da cewa 


"Dama so nake dan Allah kayi hakuri ayiwa Mairo dinki kamar yanda akayiwa sauran yaran, ko wane sallah cikin kunci take yinta saboda rashin sabbin kaya". Tsaki yaja mtswww! "Dama a kan wannan banzar maganar kika tsayar dani? To ba za'ayi mata ba na karfine ki kwata kiyi mata". Har yayi gaba zai shige tace "Haba Baban Zubairu kaji tsoron Allah, ka sani fa duk abinda kake na zaluntarmu ni da Mairo Allah yana gani kuma zai saka mana domin Allah baya barin zalunci". Tsaye yayi ya zuba mata ido, wanda zuwa lokacin cikin kuka take maganar, a dai-dai lokacin kuma Kubura da Laure suka fito daga dakunansu 


"Yau kuma sabuwar mai wa'azi muka samu a gidan?". Kubura ce tayi maganar Laure ta ce "Allahu Akbar! Kin dai ji yaya nima ina daga daki na jiyo nace ba'ayi bani ba dole in fito in saurara ko na kara ilimi". Fatsuma bata kula su ba ta cigaba da cewa "Baban Zubairu bansan laifin da nayi maka ba a rayuwa ka tsaneni tun sadda ka aureni ban taba samun farin ciki daga gareka ba, yanzu kiyayyar da take mun ta gangaro har kan yarka ta cikinka wannan wace irin rayuwa ce, kaji tsoron Allah ka sani dukkan hakokinmu da ake takewa a cikin gidan nan da yardarka akwai ranar da zaka tsaya a gaban Allah kayi masa jawabi...". Saukar lafiyayyan mari taji, wanda ya talisata mata katse maganar, daga bisani kuma ta ji saukar duka.......


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 
https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

Comments