Mahaukaci Ne Ko Aljani? Chapter 1 and 2 Hausa Novel By Aisha A. Yabo

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
    MAHAUKACI NE KO ALJANI? 🧟‍♂️


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
                     Mallakin
   Aisha Abdullahi Yabo


*PAID.*
BOOK.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*


Da sunan Allah mai Rahama Mai jinƙai. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga Fiyayyen Halittu Annabi Muhammadu RasululLah (S.A.W) da matayensa 'ya'yansa da kuma Sahabbansa da jikokinsa baki ɗaya.

  Allah ka ƙara haskaka ƙabari da kuma ruhin Mahaifiyata Hajiya Zhara'u M. Abdullahi Yabo. Tare da Malamina Yayana M. Abubakar Abi Allah ka jajjada Rahamarka a garesu tare da dukan Musulmi baki ɗaya Saboda Alfarmar Annabi (S.A.W) Ina baran addu'a a gare su ga duk wanda ya ga littafin nan.

  Haƙƙin mallaka (m) Aisha Abbdullahi Yabo.


 Banyi wannan littafin don wani ko wata ba, na yi shi ne don faɗakarwa da nishaɗantar da al'umma. Don haka duk wanda ya ga wani abun ya zo daidai da rayuwar shi ba da shi nake yi ba arashi ne.
 .Ina Alfahari da ku 'yan Kainuwa Writer Association.

*Gargaɗi*
A guji juya min littafi ta ko wacce siga ba tare da izini na ba, yin hakan kuskure ne, zan ɗauki mataki ga ko waye a kiyaye sai a zauna lafiya.


 Marubuciyar
AMAL
MUKULA 'YAN MATAN ZAMANI
MA'AURATA
KAR KA GUJE NI
ILLAR AUREN DOLE
NURADDIN
RAYUWAR MU
KUSKUREN WAYE?
ƘASATA
SU NE SILA

_~AMINTATTU GUDA UKU DAGA AMINAN JUNA UKU~_
*AISHA A YABO FULANI*
*RASHIDAT USMAN OUM NASMAH*
*ZAHRA'U ABDUL M AHLAN*
_PAID BOOKS CIKIN FARASHI MAI SAUKI_
_GUDA ƊAYA #200 GUDA BIYU #300 GUDA UKUN #500, AMMA PAYMENT TA KATI YA SHA BAMBAN DA TA ACCT, GUDA DAYA #300 BIYU #500 UKUN #600, BIYA KUDIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKI 0006064512 Rashida Usman JAIZ BANK ko kuma katin waya ta daya daga cikin waɗannan lambobin_
08147537180
08162576936
08165550116 
*Masu turo da evidence of payment wadanda suka yi transfer to acct ku turawa ɗaya daga cikin mu, don girman Allah banda vtu inde kika yiwa ɗayan mu vtu to kinyi sadaka Anty. Mu na godiya gareku masoya*


    
1&2

Wata irin sansanyar iska mai haɗi da sassanyan sanyi ne su ka tasu duk da jikin ta da akwai rigar sanyi mai jikin damisa hakan bai hana sanyin ratsa dukan sassan jikinta ba, rungumi hannayenta ta yi a ƙirjinta ta na karkarwar sanyi. Bin dajin ta yi da idanu shiru babu motsin kowa sai kukan tsintsaye ne ya karaɗi dajin Allah mai ɗauki da bishiyoyi iri-iri, tsoro ne ya shige ta ta nusa cikin dajin gudu ta ke babu ko waige, gajiya tasa ta durƙushe a gefen wani babban jijji da ta kasa hango ƙarshen sa ta na mayar da numfashi hawaye masu ɗumi ne su ka kwararo a kan fuskarta "Momy Dady ina kuka shiga ne ku ka barni a wannan dajin mai tsoratarwa, wayyo Allah!" Wata guguwa ta tasu mai ƙarfi wanda hakan yasa ta ɗagowa ya yin da zuciyarta ta shiga bugawa tamkar za ta faso ƙirjin ta ta fito tsabar firgici, idanunta su ka kai kan inuwar da ta ke kusanto wajan da ta ke, bugun zuciyarta ya tsaya cak sanƙamewa ta yi a wajan ahankali ta dinga ɗago kanta ta na kallon tun da ga ƙafafunsa da su ke sanye cikin takalmin fata ba a ganin komai na ƙafar hannunsa na riƙi da wani buhu da ba za ta iya cewa ga abin da ya ke ciki ba, gashin kan shi ya yi buzu-buzu ya rufe fuskarsa sam ba a ganin ainahin fuskar sa, tufafin da su ke jikin shi sun yi duƙun-duƙun da ga wajan gwauwar shi duk wandon ya yage, da ga saman wuyar rigarsa ma duk a yagi. Ɗaya hannunsa ya miƙo zai taɓata tasa ihu "Momy!!!!!" Zabura ta yi ta tashi zaune ta na mayar da numfashi tamkar wacce tai tseran gudu Momy ta hankaɗo ƙodar da sassarfa ta shigo "lafiya Mina me ya faru ki ke wannan ihun?" Ta yi ma ta tambayar ta na hahowa kan gadon shigewa ta yi jikin Momy jikinta na karkarwa sai gumi ta ke. "Mene ne, lafiya ki ke kuwa?"
   "Momy mafarki na yi... Ta ba ta labarin mafarkin, ajiyar zuciya Momy ta yi ta na faɗin "ba kya yin addu'a idan za ki kwanta shi ya sa ki ke mafarkai na tsoro. Ki din ga yin alwala da kuma addu'a kafin ki kwanta bacci kin ji ko?" Kanta kawai ta iya gyaɗa wa. "Tashi ki ɗauro alwala lokacin sallah asuba ya yi ni ma tashi na kenan na jiyo ihun ki" zamewa ta yi da ga jikin Momy ta na faɗin "ni tsoro na ke ji mu je ki raka ni banɗakin" zungurinta ta yi "shagwaɓaɓɓiya kawai mu je na raka ki, ko ba mafarki dama haka rigimar ki ta ke" murmushi ta yi tare da saukowa da ga kan gadon, riƙi kanta ta yi "mene ne kuma?" 
"Kaina ne ya ke ciwo"
"Sannu, bari ki yi sallah sai ki sha magani" kanta kawai ta gyaɗa ta shiga banɗaki taƙi rufe ƙofar Momy ta tsaya da ga bakin ƙofar ta na jiran ta.
 Wuraren sha ɗaya na safe Hindu da ke mata gyaran ɗaki ta shigo ta samu har yanzu bacci ta ke hakan yasa ta shiga banɗaki ta na wankewa motsin ta ne ya tashi Mina juye ta yi haɗi da tsaki idanunta ta a rufe ta ce. "Waye ne?"
 "Ranki ya daɗi ni ce ina wanki banɗaki ne"
  "Mtsw! Shi ne kuma ba za ki iya bari har sai na tashi ba za ki zo ki hanani bacci saboda rashin tunani!" Fitowa ta yi da sauri ta durƙusa gefen gadon "ki yi haƙuri ban ɗauka zan tashe ki da ga bacci ba ne shi ya sa" harararta ta yi ta na saukowa da ga kan gadon ta ce. "dalla can ba ni waje na wuce sakarya kawai!, Ke kullum sai kin san yadda ki ka yi ki ka ɓata wa mutum rai ban san me ya sa ma wallahi a ka ɗauke ki aikin nan ba wata ƙazama da ke!" Haƙuri ta shiga ba ta ko ta kanta ba ta sake bi ba ta faɗa banɗaki. Jiki a sanyaye ta gyara gadon zuciyarta babu daɗi a ranta ta na ji idan ba dan babu ta na babu da me zai sa ta aiki ka zo neman halak yarinya sa'ar ƙanwar ka ta uku ta zo ta na wulaƙanta ka. 

Kwance ta ke a jikin Momy idanunta a rufi ya yin da zuciyarta ta ke dawo mata da mafarkin da ta yi tiryan-tiryan tamkar a yanzu ne ta ke yinsa, shafa goshinta Momy ta yi ta na faɗin "lafiya ki ke wannan gumin kamar wacce ta yi tseran gudu?"
  "Uhm! Momy mafarkin da na yi ne ya ke ta dawo mini ina jin tsoro Momy" cikin kwantar da murya ta ce. "Dan kin sa abin a ranki ne shi ya sa tsoro ya ƙi bari zuciyar ki, ki yi ƙoƙarin yaƙinci mafarkin sai ki ga kin dawo daidai" ajiyar zuciya ta yi tare da gyara kwanciyarta ta tsurawa tv idanu a zahiri za ka ɗauka kallon ta ke sai dai sam ba hakan ba ne fuskarsa da buzu-buzun gashin da ya rufe masa fuska ta ke ga ni. Dare ya raba Momy na hamma ta kai dubanta ga Mina da tuni bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. "Oh wai har kin yi bacci, to tashi ki je ɗaki ki kwanta"
  "Uhmm ni a wajan ki zan kwanta tsoro na ke ji" ta yi maganar cikin muryar bacci da shagwaɓa, "to na ji tashi mu tafi rigimammiya" tashi ta yi ta na miƙa tabi bayan Momy zuwan ɗakinta.

Sannu a hankali ta karyo kan motar ta zuwa wata kwana ta na bin waƙar Ado gwanja wayarta da ta ke ajiye a kan kujerar mai zaman banza ta yi ringing ta ɗan kai duban ta gefen tsaki ta yi tare da ɗaga kiran 'yar rainin hankali sai yanzu ki ka ga damar kiran nawa"
   "Yi haƙuri babbar yarinya Allah ko da ki ka kira ban kusa da wayar ta na ɗaki na barta zuwa na kenan na ga kiran ki"
  "Na ji. Dama na kira ne na ji ko za ki je birthday ɗin TK anjima?"
"Abu dole kema kin san ai mu ne a sahun gaba, Nabila ce dai na ji ta ce da wahala ta zo Yayanta ya na gari kin kuma san halin shi ɗan takura ne"
  "Hum-um ta ji za ta iya ne wallahi ni ina zan yarda da wannan. Sai dai mun haɗu anjima yanzu ina hanya" tsinki kiran tayi ta na a jiye wayar ta ɗago kenan idanunta su ka kai kan wani dattijo da ya zo wuce wa ƙiris ya rage ta kaɗe shi da ƙyar ta samu ta ci burki duk da hakan sai da ta ɗan bugi shi ya yi gefe, kifi kanta ta yi jikin sitarin motar ta na mayar da numfashi ƙwanƙwasa ƙofa ta ji anyi hakan yasa ta ɗago samari biyu ne tsaye su na mazurai sauke gilas ɗin ta yi ta na masu kallon sama da ƙasa.

  "Wani irin sakarci ne wannan ki na tuƙi kamar wacce ta ke a bugi har ki kaɗe bawan Allah. Sai ki buɗe mota a sa shi ki kai shi asibiti" harararsa ta yi ta na faɗin "tun da ni nasa shi hawa kan hanyar kansa tsaye kamar ya na shiga ɗakin sa ba" ta kai duban ta ga wajan da dattijon ya ke ya tashi tsaye ya na karkaɗe jikinsa "ya godewa Allah ma da ban ragargaza ƙafafun nasa ba, gobe ma sai ya ƙara" ta yi wa motar ta key za ta ja ɗaya saurayin ya buga motar a fusace ya ce. "In kin tafi Allah tsinan! Tunda ba ki san mutunci ba kuma ba kya daraja tsufaffin gidan ku yau kuwa za ki gane shaye ruwa ne dan sai mun lallasa ki a wajan nan!"
  Dattijon ya ƙarasu ya na faɗin "yara ku ƙyaleta ku yi tafiyar ku ai AlhamdulilLah tun da ba sosai na ji ciwon ba"
  "Kar ma su ƙyale ni ɗin! Su yi abin da su ke ganin za su iya ɗin, ba kusan ni ɗin wace ce ba shi ya sa ku ke ƙoƙarin shigar mini hanci da ƙudunduni! Ɗauke mini ƙazamin hannun ka a kan mota ta!!" Fito da idanu dukan su su ka yi su na kallonta "lallaima yarinyar nan ki yi abu ba za ki bayar da haƙuri ba sannan kuma ki nemi ki faɗa mana magana! Ina ruwan mu da ku ke wace ce idan ma ƙaruna ne ya dawo ya haifi ki ba ruwan mu wallahi lallasa ki za mu yi a wajan nan banza kawai!!"
  Ƙwafa ta yi sai hawaye "ni ku ke zagi za kuwa ku sa ni wallahi sai kun san wace ce ni!" Ta tashi motar su ka dafi gaban motar su na rantsuwar ba za ta tafi ba. "Kun ga idan har za ku ji maganata don Allah don isar Annabi ku ƙyaleta ku tafi za ta haɗu da daidai ita ne in dai har wulaƙaci halinta ne" janye wa su ka yi da ga jikin motar su na harararta a yanda su ke ji ba dan ya hana su ba wallahi da yau sai ta ji a jikinta. Ko ta kansu ba ta sa ke bi ba ta ja motar a guje ta bar wajan ranta a ɓace.

Da ɗingishi ya kama hanya zai wuce ɗayan ya ce. "Mu je na kai ka kimis a duba ka"
   "Kar ka damu yaro na gode ai bugawa ce kawai ita ma ɗin ba sosai ba. Allah dai ya yi ma ku albarka" 
   "Amin. Allah ya ba ka lafiya ya kuma kiyaye gaba" su kai maganar a tare. 

Ta na shigar da motar ko parking ɗin kwarai ba ta yi ba ta fito ta na masifa "Wani irin dabbanci ne wannan za ka barni a waje ina ta danna hon!" Rufe ƙofar da bai ƙarasa yi ba kenan ya karasu wajan ta da sassarfa ya durƙusa a gabanta "ki yi haƙuri ranki ya daɗi wallahi ko da ki ka zo ina banɗaki yau ban tashi da lafiyar ciki ba shi ya sa na jima ban buɗe ma ki ba, ki mini aikin gafara" 
  "Mtsw! Banza ɗan ƙauye kawai da ga yanzu ka sake yi mini irin wannan sakarcin a bakin aikin ka wallahi!!"  
  "Don Allah ki mini gafara wallahi ba da gangan na yi ba" tsaki ta yi tabi ta gefen shi kamar za ta bangaje shi ta shi ge ciki. Ajiyar zuciya ya yi ya je ya rufe ƙofa a ransa ya na addu'ar Allah ya rufa masa asiri kar sanadin yarinyar nan ya rasa aikin shi da ya ke rufa wa kan shi asiri. 

Zaune ta samu Dady ya na waya ya miƙa ƙafafunsa Momy na zaune a ƙasa ta na daddana masa. Ta na zuwa ta kife jikin shi ta na kuka. "Alhaji Bashir za mu yi magana anjima" ya ajiye wayar hankali tashi "waye ya taɓa mini shalele ko ba ki da lafiya ne?" Shiru ta masa ta na ƙara sautin kukan ta. Momy ta girgiza kai "Mina na ga sanda za ki girma ki daina wannan taɓarar wallahi"
  "Ya mutum zai zo ya na kuka ki ce da ita taɓara a maimakon ki tambaye ta damuwar ta"
"Humm Alhaji na dai san ko ma mene ne bai kai ya kawo ba kawai ta zama ruwa-ruwa komai kuka"  
   Ɗago kanta ya yi ya na kallon fuskarta "kin ga Shalelena ƙyale Momyn ki faɗa mini me ke damun ki"
  "Dady ba wasu ne su ka tare ni a hanya ba su na ta zagina wai har da faɗin ko ƙaruna ne Babana su ba ruwan su dukana za su yi"
   "Duka! Su waye su da har za su nemi su dakar mini ke? Faɗa mini su ɗin su waye ne yanzu na kira DPO a ka ma su"
"Uhm-um Alhaji ina raba ka da biyewa Mina ka na ɗaukar ko wani irin hukunci kar a zo watarana a ji kunya da" kallonta ya yi ransa a ɓace ya ce. "Oh so ki ke na zuba idanu a dinga taka 'yata yadda a ka so kare da biri kowa ya yi mata abin da ya ga dama saboda ba ta da galihu ko?"
  "Ba hakan na ke nufi ba, ka dinga bincike kafin hukunci yanzu haka ita ɗin ce ba ta da gaskiya. Ke me ya haɗa ku?" Ta ma ta tambayar ta na mai zuba mata idanu cikin nuna ba wasa. Cikin turo baki ta ce. "To ba wani tsoho ba ne ya zo ta gabana ina waya ban san da shi ba na ɗan kaɗe shi, shi ne su kuma su ka zo dan na ƙi fitowa na duba shi su ka hau zagina" 

Gyaɗa kanta ta yi ta na faɗin "ka ji ko? Yanzu saboda Allah ki kaɗe mutum ba za ki duba shi ba ai ko dabba ki ka kade kya fito ki duba bare kuma ɗan adam. Mina ina raba ki da wannan halin na tozarta mutane ba kya ji ko. Yanzu ina mutumin ya ke?" 
 Tashi ta yi ta haura sama da gudu ta na na ihun kuka. "Shalelena tsaya ki ji" ko waige babu ta yi tafiyarta "hankalin ki ya kwanta ba, ta zo da kuka a maimakon ki kwantar mata da hankali shi ne za ki ƙara ma ta wani ɓacin ran a kan wanda ta ke ciki ko" 
"Ni fa ba hakan na ke nufi ba amma abin da yarinyar nan ta ke yi sam bai kamata ba Alhaji, kuma kai ne ka ke ɗaure ma ta ta ke yin abin da ta ga d... "Barin wajan ya yi a zuciye hakan ya sa ta bi shi da idanu ba tare da ta iya ƙara sa zancen ba. "Wato da ga shi har ita sun mayar da ni shashasha ai shi kenan Allah ya kyauta" tashi ta yi ta zauna a kan kujera idanunta a kan tv sai dai zuciyarta sam babu daɗi.

Kwance ya same ta ta yi rub da ciki ta na kuka, hannunsa ya kai ya tallafu ta tare da kwantar da ita a jikin shi ya na yi mata magana cikin sigar lalllashi "kin ga ki yi haƙuri ki kyale Momyn ki faɗa mini me ki ke so a yi wa mutane nan da zai sa zuciyar ki ta yi sanyi?"
  "To ai ni Dady ban san a ina su ke da zama ba, amma duk ranar da su ka yarda na sake sa ka su a idanuna sai sun gani kurin su"
  "Na ma ki wannan alƙawarin matuƙar ki ka gano su sai na sa an masu hukuncin da ba za su sake gigin shi ga sabgar da ba ta shafe su ba"
  "Ni ba na son motar tun da har su ka sa ƙazamin hannun su a kanta" shafa kanta ya yi ya na faɗin "in dai wannan ne an gama yau ɗin nan za a kawo ma ki sabowar mota irin wacce ki ke so" murmushin jin daɗi ta yi "yawwa Allah ya bar mini kai Dady na. Ina tsarabata tun jiya da ka dawo Momy ta hanani tambayar ka wai na bar ka ka huta" saukowa ya yi da ga kan gadon hannunsa na a cikin na ta ya ce. "Rabu da Momyn ki tashi mu tafi ɗakina na ba ki tsarabar ki, duk abin da ki ka ce na sayo ma ki ban manta ko ɗaya ba har da ƙari ma" rungume shi ta yi "I love You So much my Dady"
  "Love you too Sweet Shalelena" ɗakin shi su ka nufa tuni ta manta da abin da ya faru.

Guguwa ce ta tasu mai ƙarfe wanda hakan yasa sararin samaniyar ya lulluɓe da hazo sam ba ka hango abin da ya ke gaban ka zuciyarta ta shiga bugawa fat! Fat!! Fat!!!" Kashe motar ta yi ta ɗauki jakarta ta na lalubo wayarta wani irin iska mai ƙarfe ya sa ke tasuwa jakar kawai ta ga ta bi ta ƙofar motar ta fice kamar abin da a ka fizge, jikin ta ya shiga karkarwa yayin da bugun zuciyarta ya daɗa ƙaruwa fiye da ƙima kamar za ta faso ƙirjinta ta fito.
    Cikin ƙarfin hali ta buɗe motar ta fito wani irin sautin kuka mai firgitar wa ta din ga jiyo wa nesa da ita, a tsorace ta kai dubanta gabas da yamma kudu da arewa komai ba ta iya gani ko da ita kanta, sautin kukan sai daɗa ƙaruwa ya ke haka ta nusa wajan da ta ke jiyo kukan na fitowa ta na tafiya zuciyarta na dukan uku-uku. 
   'Ke! Mina yi ta kan ki ki samu hanyar da ki ka yi ki ka koma gida ki bar hanyar nan dare ya suma, kar garin ganin ƙwam ɗin ki ki je ki ganowa kan ki ajalin ki' zuciyarta ta ji ta na bata shawara ba tare da ta tsaya dogon nazari ba kawai ta juya karo ta yi da wani abun da ba ta iya ganganci ko meye ba. Zuciyarta ta dinga bugawa da ƙarfe, guguwar ta ragu duhu guguwan ya fara yaye wa a sararin samaniya wanda hakan ne ya bata damar ganin shi tsaye ƙyam a gabanta a cikin ɗan hasken farin watan da ya fara kunno kai gashin kansa buzu-buzu har ya fi na ranar farko da ta fara ganin shi a mafarki. Girgije kansa ya yi gashin da ya rufe kansa ya ɗan janye hakan ya bata damar hango danunsa da su ka yi jawor kamar jan gauta, saukar wasu ruwa masu ɗumi ta jiyo a kan tafukan hannunta wanda hakan ya ƙara sa tsoronta bayyana numfashin ta ya din ga yin sama kamar za ta shiƙe.


Fulani

Comments