Sharri Kare Ne Part 1 Littafin Dare Dubu Da Daya

 SHARRI KARE NE 1


HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI


(Daga Littafin Dare Dubu Da Ɗaya)



Waziri Aku 


Abuƙir da Abusir maƙwabtan juna ne a cikin kasuwar birnin Iskandariya, shagunansu na kallon juna. Abuƙir marini ne, yayin da Abusir ya kasance wanzami.


Kamar yadda sana'o'insu suka banbanta haka ma halayensu suka sha bamban tamkar wuta da saɓi. Abuƙir dai duk inda mutumin banza ya kai to ya wuce nan. Mutum ne maƙaryaci, mai saɓa alkawari, mara amana, mayaudari, ga kwaɗayi kamar kura, rowa kamar na goye. Rashin kunya a wurinsa kuwa ko ɗan bashirwa na shafa masa lafiya.


Duk sa'adda wani ya kawo masa tufafi domin ya rina masa, Abuƙir zai fara neman kuɗi a wurin mutumin, wai zai sayi kayan aiki. Idan aka ba shi kuɗin sai kuma ya ɗauki tufafin ya sayar, ya shiga kasuwa ya samu tozon raƙumi da shinkafa ya saya, ya kai gida a yi masa dabge, sauran canji kuma ya sayi goro da sigari yana busawa abinsa.


Idan mai kaya ya dawo karɓar kayansa, sai ya kalallame shi da baki, ya ba shi haƙuri, sa'anna ya ce, "ka dawo gobe war haka, insha Allahu za ka samu kayanka."


Idan mai kaya ya sake dawowa, sai kuma ya kawo masa wani uzurin yana cewa, "ka sani jiya fa har na ɗauko kayanka zan fara aiki, sai aka aiko mini na yi baƙi a gida. Na rufe shago na tafi, to ban sake buɗe shagon ba sai yanzun nan. Ka yi haƙuri ka dawo gobe war haka, za ka samu kayanka." 


Haka mutumin zai haƙura ya tafi. Washe gari idan ya dawo sai Abuƙir kuma ya ce, "Wallahi jiya har na haɗa kayan aiki sai aka aiko mini matata ba ta da lafiya, tilas na rufe shagon na nufi gida, ban kuwa sake buɗe shagon ba sai yau. Ka yi haƙuri, ba makawa gobe ka samu kayanka."


Idan mai kaya ya sake dawowa sai kuma ya samu wata ƙaryar ya gwabza masa. Haka zai yi ta yi wa mutum je-ka-ka-dawo har ya gaji ya daina zuwa. Idan kuma mutumin ya yi gajin haƙuri ya ce a ɗauko masa kayansa haka nan, sai Abuƙir ya langaɓe kai, kamar tsuntsun da ruwa ya yi wa duka, ya iya kissa kamar tsohuwar karuwa, sai ya ce wa mutumin, "bawan Allah, bari dai na faɗa maka gaskiya, ka san an ce ranar wanka ba a ɓoyon cibi. Tun ranar da ka kawo mini kayanka na rine su tsaf, rini kuwa ɗan ubansu, na shanya su a gaban shagona domin su bushe, na shiga kasuwa in sayo wasu kayan aiki, ko da na dawo sai na tarar da wani mara imani ya sace kayan. Ina jin kunyar in faɗa maka wannan batu, shi ya sa nake ta yi maka 'yan kusurwoyi."


Idan mutumin mai tausayi ne sai ya ce, "ayya! Ai ba komai, ƙaddara ce. Allah ya tsare gaba." Sai ya juya ya tafi. Da zarar Abuƙir ya ga ya ba da baya, sai ya riƙa yi masa gwalo. Idan kuwa mutumin mai zafin rai ne, sai ya zazzage shi, ya ce sakacinsa ne ya jawo. Idan ya ga wani abu mai amfani a cikin shagon, sai ya ɗauke ya tafi da shi, wai ko ya rage asara. Saboda haka shagon nasa ya koma fanko, ban da ruɓaɓɓun tukwanen ƙasa babu wani abin kirki a ciki.


Sannu a hankali duk mutane suka gane halin Abuƙir, aka daina kawo masa rini. Idan ya buɗe shagonsa tun da safe, sai rana ta koma ga Ubangiji babu wanda ya leƙa shagon, balle a kai masa aiki. Idan ka ga mutum a ƙofar shagonsa to baƙo ne ko irin ƙauyawan da kan shigo birni waɗanda ba su san halinsa ba.


To kullum idan ya buɗe shagonsa sai ya tafi shagon Abusir ya zauna tare da shi suna hira, yana kuma hangen shagonsa. Da ya hango wani ya tsaya a bakin shagon da kaya a hannu, sai ya zabura ya tafi wurinsa, idan na rini ne sai ya karɓa, ya kuma karɓe kuɗin aikin, ya ce masa ya dawo gobe. Da mutumin ya tafi, shi kuma sai ya shiga kasuwa ya sayar da kayan, ya sayi nama da kayan abinci ya kai gida. Su sha shagalinsu shi da matarsa.


Amma idan ya hangi wanda ya ba shi aiki ne tsaye a bakin shagon, sai ya ƙi fitowa daga shagon Abusir, har sai mutumin ya gaji da tsayuwa ya tafi. Ran nan dai ya karɓi kayan wani mai zuciya kusa, da mutumin ya gaji da zirga-zirga, ya kuma leƙa shagon bai ga kayansa ba, bai kuma ga wani abin amfani da zai ɗauka ba, sai ya kai ƙara wurin Alƙali. Alƙali ya aiko da masinja domin a tafi da Abuƙir. Da aka zo ba a same shi ba, sai masinjan ya samu kwaɗo ya datse shagon, ya ce wa mutane a gaya wa Abuƙir, idan ya dawo, ya je wajen Alƙali ya karɓo mabuɗi. Ya juya ya tafi.


Ashe duk abin nan, Abuƙir na cikin shagon Abusir yana hange. Da Abusir ya ga an rufe shagon Marini sai ya ce masa, "kai kuwa me yasa kake wasa da sana'arka haka? Duk sadda aka kawo maka rini ba a kwashewa lafiya. Ka je ka kai wa mutumin nan kayansa ka karɓo makullin shagonka."


Abuƙir ya ce, "wallahi an sace su."


Abusir ya ce, "haba, sai ka ce kai kaɗai ɓarayi suka raina a kasuwar nan. Duk wanda ya kawo maka rini sai ka ce an sace kayansa. Kai dai faɗa mini gaskiya."


Marini ya duƙar da kai, kamar wani mummuni, yana susar ƙeya ya ce, "abokina bari dai in faɗa maka gaskiya, sayar da kayan nake yi, ni kuwa sai na ce musu an sace."


Wanzami ya ce, "amma dai ba ka kyauta ba, wannan babban zunubi ne kake aikawata, Allah kuwa na fushi da masu saɓo."


Marini ya ce, "ban aikata haka ba sai don lalura. Kasuwancina ya durƙushe ba na samun aiki yanzu, balle na samu abin ɓatarwa. Talauci ya yi mini katutu, na rasa yadda zan yi da raina."


Wanzami ya ce, "ba kai kaɗai ba, ni kaina kullum da kyar nake samun na cefane a shagon nan. Ga shi dai na iya aski amma sai mutane su tsallake shagona su tafi wani shagon, wai don nawa shagon babu kayan alatu a ciki, sai ka ce kayan alatun ke yi musu aski. Ni da nake talaka, ina na ga kuɗin da zan ƙawata shago kamar na 'yan birni?"


Marini ya ce, "abin da na ga ya fi, idan ka yarda, mu bar garin nan, mu shiga duniya mu ga abin da Allah zai ba mu ta hanyar sana'o'in nan namu. Duniyar nan ta Assamadu dai da faɗi da yalwa, bai kamata mu tsaya wurin da za mu takura ba, motsi ai ya fi laɓewa." Marini ya yi ta jan hankalin Wanzami har ya ciwo kansa, ya yarda za su shiga duniya su nemi arziki daga falalar Ubangiji.


Za mu ci gaba.


Bukar Mada

02/10/2022

Comments