SHARRI KARE NE 6
HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI
Waziri Aku
Wanzami ya matsa har ya zo kusa da ƙofar shagon, ya ja ya tsaya. Ya tabbata idan Marini ya gan shi, zai taso ya rungume shi cikin farin ciki, ya ja hannunsa ya zaunar da shi kusa gare shi, ya girmama shi, ya yi masa hidima.
Sa'adda idanu biyu suka afku cikin idanu biyu, Abuƙir ya yi ido huɗu da Abusir, sai ya game girar sama da ta ƙasa kamar wanda aka aiko wa da saƙon mutuwa. Da yake an ce mai kaza aljihu ba ya jimirin as, haka kuma mai mugun hali, gani yake kamar kowa ma haka halinsa yake, sai Marini ya yi tsammani Abusir ya zo ne domin ya kware masa baya cikin mutane, ya tambayi kuɗinsa da ya ɗauke masa, saboda haka ya daka masa tsawa, "kai lalatacce! Ka biyo ni nan ne domin ka tozarta ni? Sau nawa na yi maka kashedi da zuwa nan? Ɓarawon banza mai kunnen ƙashi!" Ya dubi bayi ya ce, "ku kama shi."
Masu fushi da fushin wani suka zabura suka yi cacukwi da Abusir. Abuƙir ya miƙe daga inda yake zaune, ya ɗauki tsumagiya ya ce wa bayi su kwantar da Wanzami. Ya yi ta tsala masa tsabga ga baya, sai da ya yi masa tsumagiya ɗari. Ya kuma ce a birkice shi. Ya yi masa wasu tsabgogi ɗari ga ciki, sa'annan ya ce a sake shi.
Abuƙir ya dubi Abusir ya ce, "idan na sake ganin ka kusa ga shagona, zan kai ka gun Sarki ya sa hauni ya sare maka wuya kowa ya huta da zambarka, ɓarawon banza, lalatacce! Tafi ka ba mu wuri, Allah ya tsine maka albarka!" Abusir ya juya ya tafi yana kukan zuci bisa ga tozarta shi da abokinsa ya yi. Da mutane suka tambayi Abuƙir, "me wannan mutum ya yi maka?"
Sai ya amsa musu da cewa, "ɓarawo ne mai sace kayan mutane. Yakan lallaɓo nan ya faki idona, idan ya ga hankalina ya ɗauku ya yi mini sata. Ya jawo mini asara mai yawa wajen biyan mutane kuɗin kayan da ya sace mini. Duk sadda na kama shi, sai na ji tausayinsa in ƙyale shi, nakan ce a raina wataƙila talauci ne ke damunsa, nakan ja masa kunne in sake shi. Amma tunda na ga kunnen ƙashi gare shi, lallai idan na sake kama shi in kai shi ga Sarki ya sa a kashe shi kowa ya huta." Da mutane suka ji haka sai suka yi ta tsine wa Wanzami, suna la'antar shi. Kun ji kaɗan daga halayen Abuƙir.
Shi kuwa Abusir sai ya koma gidan baƙi, ya shige ɗakinsa ya zauna yana jinjina wulaƙancin da Marini ya yi masa, ga kuma jikinsa na yi masa raɗaɗi saboda bulala. Can zuwa wani lokaci bayan ya ɗan sarara, sai ya sake ɗaukar zabirarsa ya nufi cikin gari wajen sana'arsa. Da ya ji jikinsa dai ya dame shi da zogi, sai ya yanke shawarar zuwa gidan wanka, ya samu ruwan ɗumi ya watsa ko ya ji 'yar dama-dama. Yana cikin tafiya sai ya haɗu da wani mutum, ya tambaye shi hanyar gidan wanka. Mutumin ya ce, "menene gidan wanka kuma?"
Abusir ya ce, "wurin da aka keɓe domin mutane su je su cire dauɗar da ke jikinsu, fatarsu ta yi wasai su ji daɗin rayuwarsu."
Mutumin ya ce, "af, ka ce hanyar rafi kake nema. Ai mu duka nan garin rafi muke zuwa mu gurje dauɗar jikinmu. Hatta Sarki idan ya yi nufin watsa ruwa can yakan je. Mu ba mu san wani abu gidan wanka ba."
Wanzami ya yi ta yawo har Allah ya gajishe shi, amma bai samu gidan wanka ba, bai kuma samu wanda ya san abin da ake kira da haka ba. Ya yi mamaki matuƙar mamaki. Ya ce a ransa gari kamar wannan bai kamata a ce babu gidan wanka ba. Ya tuna an taɓa gaya masa Sarkin garin wayayye ne mai son abubuwan ci gaba a garinsa. Don haka sai ya shura takalmansa ya nufi gidan Sarki.
Da zuwa ya faɗi ya ɗauki ƙasa gaban Sarki, ya gayar da shi cikin ladabi da girmamawa, sannan ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ni baƙo ne, sana'ata wanzanci da kuma aikin gidan wanka. Na zagaya duka garin nan kaf ban samu gidan wanka ko ɗaya ba. Abin da na tabbata kuwa shi ne, duk garin da babu gidan wanka a cikinsa to tamkar abinci ne da babu gishiri."
Sarki ya dube shi ya ce, "menene muhimmancin gidan wankan nan da kake faɗi?"
Abusir ya nutsu ya yi ta bayyana wa Sarki alfanun gidan wanka, har sai da ya ga Sarki ya gamsu da bayaninsa sarai. Daga ƙarshe ya ce, "birni duka ba ya cika birni sai in akwai gidan wanka a cikinsa, ya Sarki."
Sarki ya yi farin ciki da zuwan Abusir, ya ce, "maraba da kai baƙo. Wallahi irin ku muke so, masu kawo mana ci gaba a gari, baƙo da gashi ai ya fi ɗan gida figagge." Ya kawo tufafi na alfarma ya ba shi. Ya ba shi ingarman doki da dukiya mai yawa. Ya kuma ba shi ƙayataccen gida cike da kayan alatu. Aka ba shi bayi biyu baƙaƙe da kuyangi huɗu da fararen bayi masu yawa. Sarki dai ya karrama shi fiye da yadda ya karrama Marini.
Washegari Sarki ya kira magina ya haɗa su da Abusir ya ce su zagaya da shi cikin gari, ya gwada musu duk inda yake so, su gina masa gidan wanka. Kada kuwa su kuskura su saɓa wa umurninsa. Haka kuwa aka yi, Abusir ya nuna wa magina wurin da yake so a yi gidan wankan. Masu gini suka duƙufa ga aiki, Abusir na gwada musu yadda yake son ginin ya kasance. Cikin 'yan kwanaki kaɗan aka gama ginin gidan wanka wanda babu kamarsa. Aka shafe bangayen da launuka masu ɗaukar ido.
Bayan an gama komai na gini, Abusir ya je gun Sarki ya durƙusa gabansa ya ce, "Allah ya taimake ka an gama gini, yanzu kayan aiki kurum suka rage a sanya."
Sarki ya kawo dinari dubu goma ya ba shi ya ce ya sayi duk abin da ake bukata. Abusir ya tafi kasuwa ya sayi komai da komai, ya zo ya shirya su a gidan wankan. Ya rarrataye mayafai na goge jiki a kan igiya, ga sabulu iri-iri, wasu na magani wasu masu sa ƙamahin jiki, an jejjera ko'ina. Mutanen da ke wucewa ta kan hanyar sai suka tsaya suka saki baki suna kallon irin kwalliya da tsarin da aka yi wa gidan wanda ba su taɓa gani ba, suka riƙa tambayar Abusir, "menene wannan?" Abusir ya amsa musu, "gidan wanka ne." Suka yi mamaki, mamaki mai yawa.
Daga nan Abusir ya fara aiki. Ya kunna turaren wuta, ƙamshi ya gauraye ciki da wajen gidan. Ya dafa ruwan zafi, ya kuma shirya ruwan yana ɓuɓɓuga ta cikin wata babbar kwatarniya wadda mutum zai iya shiga ciki ya kwanta. Duk wanda ya ga yadda ruwan nan ke fitowa daga cikin kwatarniyar, kamar dai yadda ruwa ke keto jikin dutse ya fito, sai abin ya ba shi sha'awa ya tsaya kurum yana kallon ikon Allah. Mutane suka riƙa tafa hannuwa cikin mamaki, suna faɗin aikin wani sai kallo.
Abusir ya tafi ga Sarki ya samo 'yan yara ƙanana guda goma, daga cikin fararen bayi, yaran nan kuwa sai ka ce watanni don kyau. Ya koya musu yadda za su yi wa mutane hidima, da yadda za su taje musu gashin kai idan sun fito daga wanka. Daga nan ya aika mai shela cikin gari yana cewa, "ya ku bayin Allah, ku zo maza ku yi wanka a wurin da aka keɓe, wanda ake kira Gidan Wankan Sarki."
Mutane suka yi ta tururuwa suna zuwa don yin wanka. Yaran nan suka himmatu wajen hidimta musu. Duk wanda ya yi wanka sai su taje masa kansa kamar yadda Abusir ya koya musu. Mutane suka yi ta zuwa suna yin wanka, tsawon kwana uku ba a karɓi dirhami ko ɗaya daga hannun kowa ba.
Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, insha Allah.
Bukar Mada
19/10/2022