ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 60 Hausa Novel 2023

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/9ms4eDdKgOY

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-60-hausa.html


*Busy* 🥱


*^ Part 60 ^*


Ya wulwula bulalar sama, sannnan ya kaiwa Safuratu wani mugun duka da nufin ya cire mata wuya baki daya. Sai da bulalar ta kusan kaiwa gareta, ba zato ba tsammani sai ji yayi Aljana Safuratu ta kwarara wani kara hade da cewa, "Ya Allah!", shi kanshi sai da ya dan razana saboda karan da tayi, yayin da lokaci daya yaga wata wuka ta bayyana a hannunta na hagu sai walkiya take. cikin gaggawa da zafin nama ta saki fuka-fukanta nan take ta sa wuka ta tare dukan da ya kawo mata. Yayin da ta mayar masa da martanin sara da takobi. Karfin sarar da ta yi masa ba don ya sa bulalarsa ya tare ba, shi kanshi yasan da takobin ta sameshi ba shakka yana iya tsagewa gida biyu. A hakan ma sai da karfin sarar ya sa shi ya yi baya cikin tangal-tangal tamkar zai fadi a kasa, sai kuma ya turje ya tsaya cikin iska yana kallon Safuratu yana huci cike da mamaki yadda yaji karfinta ya karu matuka. Ba tare da ya ankara ba ya ga Safuratu ta bayyana a gabanshi hade da kai masa sara da suka ta ko wane bangare da takobin hannunta. Nan fa hankalinsa ya tashi ya kasance ko saran nata da kyar yake iya karewa. Ana cikin haka Safuratu ta kai masa wani mugun sara, yayi yunkurin karewa da bulalar hannunsa amma sai ta juya takobinta ta kai masa wani saran a hannu. Da faruwar haka sai ga hannun nasa dake rike da bulala ya cire ya fado kasa. Ko da ganin haka sai aljani Duduge ya daga kai sama ya kwarara wani uban ihu. Ya dade yana yi tukun ya durkushe a kan iska cikin galabaita. Aljana Safuratu ta kalleshi cikin fushi hade da cewa, "Ba zan kashe ka yanzu ba, saboda ina so ka mika wannan sakon wajen wanda ya aiko ka. Ka gaya wa makasankancin shugaban naku Boka Kare Dangi cewa, muddun ina raye a doron kasa ba zan bari ya taba Murja ba, zalincin da yayi mata a baya ma da sannu zan bi mata hakkinta. Sannan ka fada masa ni na kashe Aljana Zilzilla bayan ya turota domin kashe Murja. Sannan in ya ga dama a kullum ya cigaba da aiko wasu aljannun ni kuwa bayan kai da zan bari yanzu, nan gaba duk wanda ya zo kashe Murja ba zan barshi da ranshi ba".


Aljani Duduge ya zabura cikin matukar jin radadi da kuna ya mike tsaye, hannunsa na ta zubar da wani irin bakin jini. Cikin dauriya magana na fita da kyar ya ce, "Tunda kikayi kuskuren yankar wani sashe a jikina, nasha alwashin ni zan zama ajalinki, ki rubuta ki ajiye". Aljana Safuratu ta kyalkyale da dariya, kana ta ce, "To me zai hana yanzu ka karaso gareni ka zama ajalin nawa?". Da jin haka sai ran Duduge ya kara baci, nan take yayi wani irin ihu mai karfin gaske, sannan ya zama hayaki ya bi iska yayi sama. Safuratu tana kallonsa hatta guntun hannunsa da ta yanke, da bulalar da take rike a hannun suka zama hayaki suka bi iska. Su Boka Kare Dangi suna zaune shida sauran shedanun aljannusa suna aikin kulla sihiri. Ba zato ba tsammani sai gani sukayi aljani Duduge ya fado kasa a bakin kofar kogon. Nan take su Aljani Huhuge suka karasa gareshi, suna zuwa suka ga dan uwansu ne Aljani Duduge a sume cikin galabaita. Nan take suka dauke shi suka karasa da shi gaban Boka Kare Dangi. Boka ya kare masa kallo ganin dungun hannun Duduge yana zubar da jini, ya sa ya dakawa su Huhuge tsawa hade da cewa, "Kuyi gaggawar sa mashi magani magan, ko so kuke jininsa ya kare ne ya mutu?". Aljannun suka zube kasa a gaban Boka hade da cewa, "Ya Boka Kare Dangi ai hannun Duduge babu wani magani da za'a saka mishi jinin nan ya tsaya face a sa hannun cikin tafasasshen ruwan mai a toya hannun yadda wajen zai zama dungu". Ko da jin haka sai Boka Kare Dangi ya ce, "Kuna nufin yanzu shikenan ya rasa hannu guda, hannun ba zai dawo ba?". Aljannun suka ce, "Kwarai kuwa ai shima kamar dai hannunku ne na yan adam ko kafa idan an sare, sai dai ayi gaggawar kone wajen ya zama dungu domin jini ya daina zuba, amma wani ba zai sake tohowa ba a wajen". Boka Kare Dangi ya daga kai sama ya kwarara uban ihu irin na takaici, hade da zuwa ya tallabi kan Duduge dake kwance a sume ya ce, "Banza malalacin aljani, kayi gaggawar farkawa ka fadamin mahalukin da ya sare maka hannu, Na lashi takobin ko waye ba zan raga mishi ba". Ya kalli su Jujuge hade da cewa, "Ku kuma kuyi gaggawar yi masa duk wani abun da kuka san zai tseratar da rayuwarsa?". Da jin haka su Huhuge suka tashi Jujuge ya rike Duduge gam a jikinsa, yayin da Huhuge ya daukko wani da mai a ciki yayi jawur a cikin wuta, ya kawo ya nanawa hannun Duduge inda aka sare. Da faruwar haka Duduge ya kwalla wani uban ihu, wanda yasa sai da gaba daya kogon dutsen yayi jijiga tamkar zai rushe, sannan ya sake sumewa a karo na biyu. 


Ko da gama haka sai Huhuge ya daukko wasu kwalabe guda biyu, daya ya shafawa dugun hannun Duduge abinda yake ciki, dayan kuma suka daga bakin Duduge suka dura masa abinda yake ciki, ashe ruwan magani ne. Da faruwar haka suke ajiye Duduge yayin da daga su har Boka Kare Dangi suka daina abinda suke suka sakashi gaba suna jiran ya farka domin ya basu labarin abinda ya faru da shi har ya rasa hannun nashi. Duduge bai farka ba sai da safe har rana ta fara fitowa. A hankali ya daga idanunsa, nan take ya fara karewa inda yake kallo, ganin a cikin kogon Boka Kare Dangi yake, hakan yasa ya kalli gabansa sai gani yayi su Boka Kare Dangi a Zagaye da shi, suna ganin ya bude ido suka nufeshi cikin kulawa suna yi masa sannu-sannu. Cikin lokaci kalilan ya fara tuna abinda ya faru da shi jiya da daddare, lamarin da ko kadan baiyi tsammani ba. Yana iya tuna Boka Kare Dangi ya bashi hoton Murja da wasu kulle-kulle na sihiri kamar yanda aka saba hatimin da ke jikin hoton shi ke bada umarnin kashe mutumin da ke jikin hoton. Haka ya karbi aikin da nufin yaje ya kashe yarinyar cikin abinda bai fi yan sekonni ba. Amma a lokacin da yaje sai ya tarar da Aljana Safuratu wacce itama ta rikede zuwa suffar yarinyar da yaje domin kashewa. Yana iya tuna masayar yawun da sukayi da ita kafin daga bisani suka tashi cikin iska suka fara gwabza mummunar fada a tsakaninsu, inda da farko ya fara yin nasara a kanta, bayan yayi amfani da sihirin kara karfi da kuzari wanda Boka ke basu. Yasan cewa saura kadan ya hallaka Safuratu, amma sai yaga tayi wani irin ihu hade da mimike hannuwanta inda nan take ya ga wata wuka mai walkiya ta bayyana a hannunta. Yana iya tuna lokacin da ta sare masa hannu da kuma sakon da ta bashi domin ya kawowa Boka Kare Dangi wanda ba don sakon ba da shima kasheshi zatayi kamar yanda ta ce ita ta kashe Zilzilla. Yasan cewa ba don ya kasance jarumin aljani kuma ifiritu mai matukar karfi ba, to da babu yadda za'ayi ya iya kawo kanshi fadar Boka Kare Dangi.


Boka Kare Dangi ne ya katse masa tunanin da yake ta hanyar cewa, "Kai Duduge ka tsaya sai raba mana idanu kake kana kallonmu, tunda ka farka kayi gaggawar fada mana mahalukin da ya sare maka hannu, yanzu ni kuma na aika masa Huhuge da Jujuge da karin rundunar wasu aljannun domin su je suyi fata-fata da namanshi". Ko da jin abinda Boka ya fada sai Duduge ya daga hannunsa, wanda nan take ya ga sai dungu da aka toye wajen aka daure. Da ganin haka sai ya daga kai sama ya fara kwalla uban ihu na jin haushi da takaici, sai da yayi ihu mai isarsa sannan ya sunkuyar da kai, na take wasu irin hawaye irin na bakin ciki suka zuba daga cikin idanunsa ya ce, "Ina mai matukar baka hakuri Ya kai Boka Kare Dangi, sanin kanka ne babu wani aiki da ka taba bani wanda ya gagare ni. Amma jiya a karon farko ka bani aikin da na kasa aiwatarwa". Boka ya tsura masa ido yana kallonshi cike da mamaki, domin shi dai yasan cewa aikin da ya ba Duduge na kashe Murja, ba wani aiki mai wahala bane a wajen Duduge, don haka ya ce, "Kana so ka ce, aikin kashe wannan yarinyar da ka karba jiya shine ya gagareka?". Aljani Duduge ya ce, "Kwarai na kasa aiwatar da wannan aiki, saboda lokacin da naje kashe yarinyar nan, sai na tarar da aljana Safuratu a tare da ita, ashe ita take gadin yarinyar".


Da jin haka sai Aljani Huhuge ya ce, "Safuratu? Kana so kace wannan yar budurwar aljanar da muka taba fafata fada a tsakaninmu da ita?". Duduge ya ce, "Kwarai kuwa, yarinyar tayi matukar bani mamaki bayan mun fafata kazamin yaki da ita, har na kusan cin nasara a kanta, na kusa hallakata nan take sai naji ta furta wata kalma irin ta larabci cikin ihu mai kara, da faruwar haka sai karfinta ya karu kuma naga wata wuka wacce ban taba ganin kalarta ba ta bayyana a hannunta, da wannan wuka tayi amfani ta sare mun hannun nan nawa, domin karfinta sai da ya linka nawa duk da nayi amfani da sihirin kara karfi. Kai daga karshe ma sako ta bani in kawo ma wanda tace sakon shine dalilin da yasa ba zata kasheni ba a wannan lokacin". Ko da jin haka sai jikin Boka Kare Dangi ya fara tsuma, nan take wani irin barin rai ya mamaye zuciyarsa ya ce, "Wane irin sako ne ta baka ta ce ka kawo min?". Aljani Duduge cikin kunar rai ya ce, "Ta ce ka ma daina tunanin kashe wannan bil adamar domin ba zata bari kayi nasara ba, haka zalika haukatar da itama da kasa akayi sai ta bi mata hakkinta, sannan ta ce itace ta kashe wannan yar budurwar aljanar Zilzilla da ka tura domin kashe yarinyar. Daga yanzu ta ce duk wanda ka sake turawa domin kashe wannan yarinyar to ita zata kasheshi da hannunta daga kaina ba zata sake barin wani wanda yaje kashe yarinyar a raye ba". Ko da jin haka sai Boka, Jujuge, da Huhuge suka fara kurma wani uban ihu irin na bacin rai. Aljani Huhuge ya mike yana huci, nan take jikinsa ya kama da wuta ya ce, "Ya kai Boka Kare Dangi, ina so ka bani izinin zuwa in kashe wannan yarinyar cikin yan dakiku kalilan". Da jin haka kafin Boka ya ce wani abu, Aljani Duduge yayi saurin cewa, "Aa! Aa! Wannan kuskure ne mai girma, sanin kanka ne a cikinku babu wanda ya fini karfi, amma ku dubi yadda yarinyar nan ta kusan hallaka ni, saboda haka ina tunanin zuwa ka tunkari yarinyar nan da niyar kasheta tamkar kisan kanka ne zakayi".  


Boka yayi shiru yana tunani, amma tabbas ya san cewa maganar Duduge gaskiya ce, don haka ya mike tsaye ya fara kwala ihu yana kiran sunan Safuratu hade da cewa, "Yanzu kin kashe min aljannu masu yi min hidima guda biyu, kuma kin illata min babban ifirituna. Tabbas haduwarmu ba zatayi kyau ba, sai na miki kisa mafi munin kisa ki jira ki gani". A bangaren su Hajiya Lami baccinsu suke cikin kwanciyar hankali, kamar yadda aka saba ba zato ba tsammani sai jin bulala tayi. A firgice ta farka daga bacci, tana tashi zaune a kan gado sai ta ga Murja ce tsaye rike da bulala. Murjar ta ce ta tashi lokacin sallah yayi sannan ta fice daga dakin. Mamaki ne ya cika ta wai anya kuwa wannan Murja ce? Ita fa a tunaninta ba zata kara ganin Murja ba sai a lahira, tunda jiya da farin cikin boka zai kashe su Murja suka kwanta. Hannu ta sa a kai tana yatsine gashinta tana ta wuwwula hannuwa sama kamar mahaukaciya tana fadin, "No! No! Wallahi ba zai yuyu ba, Murja ta mutu, na tabbata Boka ya kashe Murja". Tana cikin haka sai ga Mama Dije ta shigo dakin nata, itama a rikece take, tana zuwa ta ririke Hajiya Lami jin abinda take fada.


Lalashinta ta shiga yi tana fadin, "Kwantar da hankalinki yi alwala mu fita ai har yanzu bamu tabbatar ko dayar ce a raya daya ta mutu ba". Da kyar ta samu ta lalaba Hajiya Lami tayi alwala suka fito falo, kamar kullum domin a nan suke sallar asuba, Murja daya suke gani tana nafila don haka tuni farin ciki ya cika ran Hajiya Lami, bata san lokacin da ta karasa wajen Murja da take nafila ba. Ba tare da la'akari da tana sallah ba ta ce, "Allah sarki Murja ashe dayar Murjar ta mutu, Allah ya jikanta Allah ya kara hakuri, bari mu gama sallah in sa su Sunusi su hado mutane ayi mata jana'iza". Ba zato ba tsammani sai ji tayi ance, "Wace Murjar ce ta mutu?". Tana juyawa baya ta ga dayar Murjar ce ta fito rike da sallaya a hannu. Bakin ciki ne ya cika zuciyarta, yanzu dai ta tabbatar duka Murjojin babu abinda ya samesu, wato Boka ya musu karya kenan, ji tayi har ta matsu gari ya waye domin su dauki hanyar zuwa wajen Boka domin ta ji dalilin da ya hana ya kashe Murjojin biyu. Ji tayi Murja ta ce, "Me yasa kike tunanin na mutu? Ko ce miki akayi yau ne ranar mutuwata?". Dan murmushi Hajiya Lami tayi hade da cewa, "Ke kuwa yar nan ai mutuwar nan ba sallama take yi ba, yanzu mutum ba cuta ba ciwon kai haka kurum sai a wayi gari a ga ya mutu, shiyasa nayi tunanin ko taki ta zo ne". Murja bata ce mata kala ba tayi murmushi hade da shimfida sallaya da ke hannunta ta tayar da sallah.


Wajen karfe uku suka dawo gida, duk wacce ka kalla a cikinsu ranta a bace tamkar macen da akawa kishiyoyi uku reras a rana guda. A falo suka wuce Murja tana kallon Sunna tv kamar yadda ta saba, a gefe guda kuma Jamsy ce take ta faman duba littafi tana biya karato domin yanzu har ta saba da karatun dole da aljana ta sakata take yi. Bayan sun zauna a daki Mama Dije ce tayi tsaki hade da cewa, "Banza kawai sakaran Boka, Allah na tuba kashe wannan yan yaran ne zai gagareshi?" Sailuba ta kama baki hade da cewa, "Ke Hajiya Dije raba kanki da zagin Boka Kare Dangi, na rantse miki yanzu kina iya jin saukar mari ya turo aljana ta mareki". Hajiya Lami tayi tsaki hade da cewa, "Inna Sailuba wallahi abun da haushi, kina jin abinda yake fada wai ba zai iya kashe Murja ba, saboda dayar Murjar aljana ce, wai jiya ma ta cirewa ifiritunsa hannu, kiji karya inda aljanar ce da gaske ai da tuni ta kashemu yanda take jin haushinmu". Mama Dije ta ce, "Ni sai yanzu ma nake ganin kamar ba bokan gaske ba, anya lokacin da muka sa ya kashe Alhaji ba katari ne akayi ba dama kwanan Alhaji ya kare?". "Nima dai abinda nake tunani kenan". Sailuba ta ce, "Kunga yanzu dai miye mafita, tunda Boka Kare Dangi ya ce ba zai iya kashe Murja ba me kuke ganin za'ayi?". Mama Dije ta ce, "Mafita daya yanzu bincikawa zakiyi ki nemo mana wani bokan ko kuma malamin zaure wanda ya fi Boka Kare Dangi zafi. Wanda zai kashe mana su farat daya". Sailuba ta jinjina kai hade da cewa, "Samun shu'umi kuma hatsabibin Boka kamar Boka Kare Dangi sai an tona fa, amma ba damuwa zan bincika a cikin mutanena". Hajiya Lami ta ce, "Ni duk abun duniya ya sha min kai ma wallahi, yara kanana suna neman fin karfina". 



Dare yayi kowa yayi bacci, su Sunusi na zaune a waje, gefensu da sanduna da addunansu harda bindiga irin ta maharba a ajiye, sai hira suke cikin nishadi kamar kullum. Bakar mota doguwa suka ga ta faka kiii! Cikin gaggawa suka ga katti suna dirowa daga cikin motar ko wanne rike da bindiga ya rufe fuskarsa da bakar hula. Sunusi ya tashi da yunkurin daukar adda, sai ji yayi wani ya harba bindiga a gefen kafarsa, hade da cewa, "Kana kara daga kafarka sai na harbeka, ka mutu yanzun nan". A wajen ya tsaya kamar gunki yana karkarwa, cikin lokaci kankani ya jika wandonsa da fitsari, don bai taba ganin mutuwa ido da ido ba kamar yau, wai shi aka nunawa bindiga ana shirin harbewa.............................


😌 Ayi mun uzuri, aljani Duduge ne yayi wani irin shaka shiyasa na kasa typing kwana biyu, 🤪 ku dai busy ne, ai na fishi karfi, har Safuratu ma tsorona take


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments