ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 59

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/ToPPCpqTGlM

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-59-hausa.html


*^ Part59 ^*


Sunusi ya ce, "Hajiya tsakani da Allah ba zubar da su muka yi ba, cinye su mukayi baki daya". Hannu Hajiya Lami ta fara tafawa tana fadin, "Innalillahi wainna illahir raji'un, yanzu mushen agwagin kuka ci Sunusi?". Sunusi ya dan shafa keya hade da cewa, "Gani nayi kamar basu mutu, ba shiyasa naje na sa wuka na karasa yanka su". Cikin masifa Hajiya Lami ta ce, "Ai yayi muku kyau, gobe dan Allah idan kun ga irin haka ku kara yanka ku cinye, na tabbata wataran zaku ciyo abunda zai kasheku". Mubarak yana daga kwance ya yunkura ya tashi zaune hade da gallawa Sunusi harara yace, "Yanzu tsakani da Allah Sunusi dama agwagin nan mushe ne amma ka sa muka ci?". Sunusi ya mayar masa da martanin harara hade da cewa, "Kaga malama tun da farko sai da na fada maka kuma na fita hakkinka". Hamza ya ce, "Wallahi ko ni da nasan mushe ne da ba zanci ba". Sunusi ya ce, "Daga baya kenan, wai anyi sadaka da karuwa". Hajiya Lami cikin takaici ta kalli Mubarak hade da cewa, "Mubarak wai yanzu ba zaka iya lallabawa mu fita ba?". Dafe ciki yayi hade da cewa, "Wallahi Hajiya cikin nan nawa a bace yake baki daya, in kin lura daga dare zuwa yanzu har na rame. Ba zan iya ba wallahi". Ba yadda ta iya haka ta sa doctor ya sa musu ruwa hade da allurai da magunguna. Gaba daya ranta a bace yake, ita dai ba iya motar tayi ba kuma ba zata je ta hau motar haya ba, sannan ba zata yarda Jamsy ko Khalil ya kaita wajen boka ba. Dole ta dage tafiyar zuwa washe gari. 


Haka akayi washe gari tun da safe ta budewa Mubarak wuta, jikinsa bai idasa warwarewa ba amma saboda jarabar Hajiya Lami haka ya daure ya ja motar suka tafi. Zaune suka a gaban Boka bayan sun mika masa hoton, ya karba hade da kyalkyalewa da dariya. Sannan ya shaida musu lalai-lalai gobe su shirya jana'izar Murjojin guda biyu, domin zai tura ifiritun aljani wanda zai je ya kashe su kafin kiftawar ido. Sunyi farin ciki sosai, don haka Hajiya Lami ta ajiye masa kudi masu yawa sannan suka koma gida. Zaune suke a falo sun sa tire a gaba na tsire da Hajiya ta sayo musu mai yawa a hanya, sai ci suke suna hira cikin farin ciki da jin dadi gobe zasu rabu da annoba. Murja ce ta fito daga daki, tana zuwa ta dauke tire dake gabansu. Kallo kawai suka bita da shi cike da mamaki, Sailuba ta ce, "Aa Hajiya Dije me nake gani haka? Tsaurin idon yarinyar nan dama har ya kai haka, ace kuna cin abu ta zo ta dauke kwanon?". Cikin takaici Mama Dije ta ce, "Ai nake fada miki yarinyar nan ba kanta daya ba, domin irin abubuwan da take mana a cikin gidan nan mai hankali ba zai iya ba. Ke yanzu fa kullum da asuba da bulala take tashinmu, haka kuma ta tsaremu sai munyi sallar asuba sannan muke da damar komawa baccin safe". Sailuba ta saki baki cike da mamaki, "Innalillahi, lalai abun ba na wasa bane, amma Hajiya haka kuma kuke tsayawa kuna kallonta ba tare da kun dau wani mataki ba?".


Murja ce ta dauki hanta a cikin tsiran, ta lakuma baki hade da cewa, "An girma ba'a san an girma ba sai munafurci da tsegumi. Amma zanyi maganinku, ina gaf da kwace duk dukiyata dake hannunku domin lokacin da na baki ya kusan cika, idan lokacin yayi ba sai na ce ku tashi daga gidan nan ba da kanku zaku tashi. Kuma tsiran nan kunci rabonku wannna sauran su Saratu zan kaiwa". Tana gama fadin haka bata tsaya sauraronsu ba tayi gaba. A fusace Sailuba ta mike ta kamo hannun Murja tana fadin, "Ke yarinya wannan iskanci da rainin wayo ba'a gabana ba, kawo tiran tsiran nan ko in gaggaura miki mari". Wani irin fusga Safuratu dake a sufar Murja tayiwa hannunta, nan take kuwa karfin fusgar ya sa Sailuba ta fadi can gefe, Allah ya taimaketa a kan kujera ta fada. Safuratu bata kulata ba tayi gaba. Sailuba ta mike tsaye ta rike baki hade da cewa, "Iyeee! Lalai abun babba ne". Har ga Allah tsiran bai isheta ba, ta bi hanya zata bi bayan Safuratu, Mama Dije ta ce, "Sailuba dawo, dawo rabu da ita, wannan yarinyar da kike gani haka muke fama da ita, duk gidan nan babu mai iya ja da ita a fagen karfi, shiyasa sau da dama nake tunanin karfin nan ba nata bane ita kadai, da aljannu a jikinta". Sailuba ta koma ta zauna tana lashe hannu, Hajiya Lami ta ce, "Ai ni yarinyar nan tun ranar da na ga ta daga ni sama duk girman nan nawa, ta nuna ga sararin samaniya ta yaddoni kasa na sallama mata. Shiyasa yanzu duk abinda zatayi sai dai na bita da ido, in kuma ya kama na masifa ne in mata masifa daga baya-baya, amma na daina gangancin tararta da fada". 


Sailuba ta kada kai hade da cewa, "Ah! Lalai kuna zaune da masifa a cikin gida, gaske na ga hankalinku ya tashi matuka a kan kawar da ita". Mama Dije tayi murmushi sannan ta ce, "Yanzu dai na tabbata komai ya zo karshe, domin gobe war haka tuni an kaisu makabarta, muma mu sarara". Dariya sukayi gaba daya cikin farin ciki. Su Murja suna zaune a bangaren su Saratu suka ga shigowar Safuratu rike da farantin tsire. Kai tsaye ta ajiye shi a tsakiyar falon hade da cewa, "Ku saukko abun dadi ya samu". Kallon juna suka farayi, domin su Saratu har lokacin tsoron Murjar suke, ita kuwa Murja ta asali kai tsaye ta sauka kasa ta fara dibar tsiran tana kaiwa baki, "Aa Murja a ina kika sama tsire haka?". Safuratu ta ce, "Su Hajiya Lami suka sayo nasan daga unguwar da suka dawo ne suka yo tsarabarsa, na ga suna ci basu fidda mana namu ba, ni kuwa na daukko kwanon gaba daya na ce ai muma muna da hakki a ciki". Dariya Murja tayi, a lokacin ta kalli Saratu da Ummi da suke binsu da ido, sai hadiyar yawu suke amma saboda tsoro sun kasu sauka domin cin tsiran. "Ummi, Aunty Saratu kun koshi ne? Kai Affan kuma ku sa hannunku ku ci mana". Da fadar haka su Affan din kamar jira suke, suka fara dauka suna kaiwa baki, Ummi da Saratu ma ganin zasuyiwa kansu yasa suka sakko suka fara aikashi lahira, dama an dan dade ba'a hadu ba.


Dare mahutar bawa, kowa dake gidan yayi bacci, hatta su Hajiya Lami da suka dade ba suyi bacci ba saboda zumudin abinda suka so ya faru na kashe su Murja gobe, tuni sun gaji har bacci ya kwashesu. A hankali wani irin bakin hayaki mai cike da gunji da wata irin hayaniya ya fara kutsawa cikin falon. Kai tsaye hayakin ya nufi dakin su Murja, ko da ya je bakin gadonsu Murja, nan take hayakin ya fara dunkulewa waje guda. Ba'a dade ba hayakin nan ya zama aljani Duduge, cikin halittarsu irin ta shaidanun aljannu, domin ya kasance baki mummuna mai wata iriyar halitta mai matukar ban tsoro. Ko da ya bayyana a cikin dakin Safuratu dake kwance tana bacci ta tashi zumbur, yayin da ta fara binshi da kallo sama da kasa, tabbas a kallon farko ta gane shi. Shi kuwa a lokacin da ta tashi zaune tana kallonsa, sai ya tsura mata jajjayen idanunsa ko kiftawa bayayi, sai da ya kusan dakika ashirin a haka sannan ya daga kai sama ya kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya, mai fidda sauti uku-uku. Ko kadan dariyar bata da dadin saurare, domin idan mutum ya ji sautin dariyar tsoro na iya kamashi har ya saki fitsari a wando. Bayan yayi dariyar mai isarsa kuma sai ya kalli Safuratu hade da daka mata tsawa ya ce, "Ke karamar alhaki wacece ke? Na ga kin canza suffa ta yadda ba'a iya ganin suffarki ta asali irin ta aljannu duk da kasancewar na san ke aljana ce?". Ko da jin haka sai Safuratu ta kyalkyale da dariya itama, kana ta murtuke fuska ta ce, "Sanin suffata ba damuwarka bace, sannan kuma na san abinda ya kawo ka gidan nan, sai dai ina shawartarka da kayi gaggawar komawa inda ka fito domin abinda ka zo da nufin aikatawa ko kusa ba zai yuyu ba, Zilzilla ma ta gwada bata ci nasara ba". 


Ran aljani Duduge ne yayi matukar baci, inda nan take ya kara dakawa Aljana Safuratu tsawa wacce ta fi ta farko karfi, domin a wannan karon hatta kasar wajen gaba daya sai da ta amsa. "Ke yarinya, ki sani ba wasa na zo yi ko bata lokaci ba a gidan nan. Aiki na zo aiwartawa tunda kin san abinda na zo aiwatarwa nima a cikin irin tawa alfarmar ina shawartarki da ki ceci ranki ki kama gabanki, in kuma ba haka ba zan hadaku gaba daya dake da wannan bil adamar na kasheku". Ko da jin haka sai aljana Safuratu ta murza yatsun hannunta hade da cewa, "Karyarka ta sha karya". Da faruwar haka sai ga suffarta ta asali ta bayyana. Tana bayyana Duduge ya ganta sai da ya ja baya da sauri cikin tsoro, domin ya ganeta kuma yasan ko ita wacece. Amma kuma sai yayi ta maza ya dake hade da gyara tsayuwarsa sannan ya tuntsire da mahaukaciyar dariya ya ce, "Ashe kece kike ba wannan bil adaman kariya? Gaske Aljana Zilzilla ta kasa cika umarnin Boka a kanta saboda kin fita karfi, amma sa'arki ta yanke tunda a wannan karon ni boka ya umarta da kammala wannan aikin, na kuwa tabbata baki isa ki dakatar da ni ba". Da jin haka sai Safuratu ta ce, "Da alamu ka manta ko ni wacece ko? Bari na tuna maka, a karonmu na farko ku uku kukayi mun tarayya ni kadai, amma daga karshe baku iya samun cikakkiyar nasara a kaina ba. Yanzu kuma kai kadai ne baka da mataimaka kana iya gwada sa'arka a kaina idan zaka iya".


Da jin haka aljani Duduge ya bata rai, nan take ya ware dogayen yatsunsa masu cike da wasu zankala-zankalan farata, nan take doguwar bulalarsa mai kauri ta bayyana a hannun nasa hayaki na fita daga jikinta. Sannan ya ce, "Na baki dama amma kinyi fatali da ita, don haka karki zargeni bisa duk abinda ya faru dake". Ko da jin haka sai Safuratu ta mike tsaye, yayin da itama ta ware hannunta, nan take bulalarta mai cike da wukake ta bayyana. Cikin kaushin murya ta ce, "Tabbas yau ba zaka iya kashe Murja ba muddun ina raye, idan ka ga ka kasheta to ni ka fara kashewa". Tana gama fadar haka tayi tsalle sai gata ta bayyana a sama cikin sararin iska, yayin da shima aljani Duduge ya bita sama cikin iska. Sun dade suna kallon juna kowa na tunanin kalar shigar da zaiyiwa makiyinsa, Safuratu ta san cewa ba lalai Aljani Duduge yayi nasara a kanta ba, duk da kuwa ya fita karfi amma a wancan karon da suka fafata ta gano cewa tsereyar karfi dake a tsakaninsu ba ta da yawa. Shi kuwa a bangaren aljani Duduge gabanshi sai faduwa yake amma ya rasa dalili, ya san dai cewa yarinyar bata fishi karfi ba, amma baya da tabbacin zai iya yin nasara a kanta. Ana cikin haka kamar hadin baki suka ruga da gudu suna masu kaiwa juna duka da bulalin hannunsu, nan take ko wanne ya goce dukan ya daki iska yayin da suka cigaba da kai wa junansu duka ta ko ina a cikin iska.


Sun kai tsawon mintuna ashirin suna azabben fada a tsakaninsu amma dayansu ya kasa samun damar cutar da daya, domin a lokacin aljani Duduge gani yayi kamar karfinsu ya zo daya da na aljana Safuratu. Al'amarin da ya bashi mamaki kenan kuma ya kara fusata shi, nan take ya kara dagewa hade da kara sauri wurin kaiwa Safuratu duka da bulalar tashi cikin sauri da zafin nama. Yayin da itama ta rika karewa cikin zafin nama irin nasu na aljannu yan baiwa, kuma itama tana kai masa martanin duka. Ganin Safuratu na bata masa lokaci hakan yasa aljani Duduge ya tsaya a waje guda, nan take ya ware hannayensa ya fara karanto wasu surutai, wanda ba'a fahimtar komai a cikinsa. Da faruwar hakan sai ga bulalar hannunsa ta koma ja jawur tamkar garwashi, kuma a duk lokacin da ya dan jijigata sai dai ka ga tartsatsin wuta yana fita daga jikinta. Yana ganin haka sai ya kyalkyale da dariya, sannan ya dubi Safuratu cikin bacin rai ya ce, "Hakika zarrar ki ta burgeni, kuma kinyi matukar bani mamaki da har kika iya kaiwa tsawan wannan lokaci muna fafata fada amma na kasa samun galaba a kanki balle na kasheki. Bansan ko dame kike takama ba, amma a yau ko dame kike takama ko tunkaho sai na ga bayanki kuma sai na kashe bil adaman da kike karewa". Ko da ganin abinda ya faru, sai Safuratu ta fara karanto duk adduar da ta fado mata a zuciya, sannan ta kara tsarkake zuciyarta cikin kyakyawar niyar da take shirin aikatawa na hana barna da kauda zalinci. A yau ta tabbatarwa kanta ko da mutuwa tayi tasan cewa haka Allah ya kaddara, sannan kuma ba yana nufin Allah yana goyan bayyan azzalumai bane, amma Allah yana ba azzalumi dama da karfi domin yayi zaluncinsa son ranshi, kafin Allah ya kamashi a lokaci daya. 


Ji tayi wani sabon karfi ya shigeta, yayin da taji ko kadan bata tsoron aljani Duduge, don haka ta mayar masa da martanin dariya hade da cewa, "Ai kafi kowa sanin wanda nake takama da shi, kuma kafin kowa sanin mai taimakona wato Allah kenan, shine mahaliccin kowa da komai, kuma shi kadai ya cancanta a bautawa da gaskiya. Sabanin kai da ka rike hanya marar bullewa ka rike shaidani a matsayin mataimaki kuma abun bauta. Ka sani a yau ko da ka yi nasarar kasheni to Allah ba zai barka ba, da kai da duk azzalumai na cikinmu aljanu dama mutane baki daya. Ko wane azzalamu akwai ranar da Allah zai kama shi". Ko da ta kai karshe a zancenta sai ta ga kan aljani Duduge yayi ja tamkar garwashi, kahon dake kanshi yana fitar da wani irin turiri na bakin hayaki, alamun ranshi yayi matukar baci. A cikin haka bata ankara ba ya falfalo da masifaffen gudu irin nasu na aljannu hade da kwada mata wannan bulala mai kama da garwashi. Cikin sauri ta sa tata bulalar ta kare, amma duk da haka bai hana karfin dukan samunta ba, har sai da tayi baya kamar zata fado kasa, kuma sai ta turje a cikin iska. Yayin da itama ta kai mai wani mugun duka, nan take ya kare da tashi bulalar. A cikin lokaci kankani Safuratu ta fahimci karfin aljani Duduge ya karo matuka, domin tuni ya fara galabaitar da ita, har ta fara kasa tare dukan da yake mata. Ana cikin haka ne bata kula ba ya zafga mata wannan katurar bulala tashi a baya, nan take karfin dukan ya wullata can nesa. Ta durkushe cikin iska tana aman jini cikin matukar galabaita. Ko da ganin haka sai aljani Duduge ya bayyana a gabanta yana gaggaba wata irin dariya irin ta mugayen aljannu, sannan ya ce, "Nan ne iyakarki, don haka yanzu zan kasheki kuma na kashe waccan bil adama da kike karewa". Da fadar haka ya daga bulalarshi sama, yayin da bulalar ta furzar da wata kalar wuta mai tartsatsi..................... 
 

😩 Ni dai ba zan juri ganin an kashe Safuratu ba, don haka a sama wasu suje su tayata fadan ko ma samu mu cigaba da rubutun cikin dadin rai

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments