ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 58

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/DwvT9mXB7zw

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-57-hausa.html


*^ Part58 ^*


Bayan ta fadi daga kan kujerar nan take ta fara juye-juye tana rike ciki harda kwanciya a kasa, ganin yadda take ya tabbatar musu da cewa lalai gubar da suka zuba a cikin abincin ne ta fara tsitsinka mata yan hanji. "Murja! Murja me ya faru? Yi mun magana me cikin naki yayi". Hajiya Lami ke fadar haka yayin da ta taso ta durkusa a gaban Murjar, ko da ganin haka itama Mama Dije ta taso tana kallon Murjar cikin tashin hankali irin na karya. "Nana! Nana zo nan kira su Saratu su zo su gani Murja ba lafiya kar ta mutu". Mama Dije ce ke fadar haka da karfi. Hakan yasa Nana Da Karima suka fito daga kitchen a guje. Su kansu ganin halin da Murja take ciki sun tausaya mata, Mama Dije ta ce, "Me kuka tsaya kallo, kuje ku kira su Saratun mana". Da gudu Nana ta ruga ta kira su, su kansu a kidime suka karasa wajen Murja suna tambaya me ya sameta. Dayar Murja taje ta tallafi kan Murja da har wani farin abu ya fara zubo mata daga cikin baki, "Murja-Murja me ya same ki? Don Allah karki mutu, Innalillahi Hajiya a kira likita a kaita asibiti zata mutu". Murjar ce ke magana a kidime. "Hajiya me ya sameta ne haka?". Saratu ta tambaya, Hajiya Lami tayi kwafa hade da cewa, "Haka kawai tana cin abinci ta rike ciki ta fara fadin cikinta na ciwo shine fa muka ga ta fadi tana rike ciki". Murja kuka take ba ji ba gani, ganin Murjar na kokarin mutuwa, "Aunty Saratu don Allah taimaka mu kaimata mu je a nemo mota mu tafi asibiti". Murja ta fada a lokacin da ta tashi tana kokarin daga dayar Murjar, da sauri Saratu ta je ta fara kokarin kama Murjar, gani tayi kan Murjar ya langabe wani farin ruwa na zuba a bakinta idanunta sun kafe. Gaban Saratu ne ya fadi, a dan tsorace ta fara kokarin kai hannunta a hancin Murja domin kara tabbatar da abinda take zargi. "Innalillahi wa'inna Illahir raji'un". Abinda Saratu taita maimaitawa kenan, yayin da ta sa hannu ta shafa fuskar Murja ta rufe mata idanu. 


Ita kuwa dayar Murja da sai kokarin cicibar Murjar take a kokarinta na a kaita asibiti, jin Saratu na ta maimaita innalillahi yasa tayi tsaye tana kallonta, don bata fuskanci abinda take nufi ba. "Aunty Saratu don Allah ki tayani mu dauketa mu kaita asibiti karta mutu". Hajiya Lami ce tayi farar ta ce, "Ta mutu ko?". Ta fada tana kallon Saratu. Mama Dije farin ciki fall a zuciyarta ta karasa wajen Murja din ta sa hannunta a gefen hancinta, jin babu lumfashi yasa wani irin farin ciki ya kumeta, yayin da a zahiri kuwa ta ce, "Innalillahi Murja ta mutu, sai dai kuma wata ba ita ba". Kuka dayar Murjar ta fashe da shi yayin da ta rungume Murjar da ake cewa ta mutu tana fadin, "Don Allah karki mutu Murja, ki tashi dan Allah". Su Hajiya Lami suka ja gefe cike da farin ciki, duk yadda suka yi kokarin boye farin cikin amma sai da ya bayyana a fuskokinsu. Saratu da Ummi kuwa suna durkushe a wajen suna bin Murjoji biyu da kallo cikin jimana. Mama Dije ce ta ce, "Baiwar Allah kiyi hakuri mana ki daina kukan nan haka, wanda ya mutu fa ya riga ya mutu kukanki ko magiyarki ba zai dawo da shi ba. Yanzu zan sa su Sunusi su nemo mutane a zo ayi mata sutura a kaita gidan gaskiya. Ni yanzu damuwata daya bansan ko wace Murjar bace a ciki, shin ta asalin ce ko kuma wacce muka ga ta bayyana ne lokaci guda?". Murja dai tana jin duk maganganun da Mama Dije take amma bata ce mata kala ba. Hajiya Lami ta ce, "Allah sarki ran dan Adam ba a bakin komai yake ba, yanzun nan fa yarinyar nan take cin abinci cikin farin ciki, amma wai gashi yanzu har rai yayi halinsa ta mutu sai dai gawarta". Murja tana kuka ta kalli saitin kwanon abincin da Murjar ta ci. A zuciyarta take tunani anya ba guba suka saka a cikin abincin ba? Ta san halin makircinsu sarai, kashe ran mutum ba wani abu mai wahala bane a garesu, don sun kashe a baya kara kashewa ba zai musu wahala ba. 



Wani bangare na zuciyarta kuma yana tunanin ko aljannu ma suna mutuwa ne idan suka ci guba. Don gashi dai tana kallo Safuratu ta daina lumfashi wanda ya daina lumfashi kuma ya mutu. Idan Safuratu ta mutu ta tabbata itama ba zasu barta a raye ba kasheta zasuyi, to ita dama me take takama da shi Safuratun ce dai. Ta wutsiyar idonta ta ga hannun Safuratu din ya dan motsa, don haka ta tsurawa yatsun hannun ido. Gani tayi ta kara motsawa, wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta. Nan take ta fara share hawayenta tana dariya ta ce, "Wallahi na ga ta motsa hannu bata mutu ba, watakil suma ne tayi". Dom! Gaban Hajiya Lami da Mama Dije ya fadi, suka ji tamkar an duka musu guduma a kirji, nan take farin cikinsu ya fara juyewa zuwa bakin ciki. Saratu ce ta yi saurin rike hannun Murjar hade da sa yatsarta a hancin Murja ta ji tana lumfashi kadan-kadan. "Tana lumfashi wallahi, bata mutu ba". Cikin farin ciki Murja ta ce, "Alhmadulillah Allah na gode maka". Ba'a jima ba Safuratu ta bude idanunta, ai kuwa ta fara bulbula amai a falon, da sauri Mama Dije da Hajiya Lami suka bar falon suna fadin aman da take zai saka su amai. Bayan ta gama Aman Murja da farin ciki ne fal a zuciyarta taje ta daukko abin kwashe shara da bokiti da ruwa ta kwashe aman ta share wajen ta wanke tass. Bayan ta gama ta rike Safuratu sukayi daki, su ma su Saratu suka koma bangarensu cike da mamaki yadda Murja ta damu da dayar Murjar gaba daya abin ya basu mamaki. 


Bayan sun shiga daki Safuratu dake cikin suffar Murja ta saki ajiyar zuciya bayan Murja ta saketa, sannan ta kalli Murja ta ce, "Yau Allah ya taimake mu ba ke kika ci abincin can ba, da yanzu sai dai wani labarin". Murja ta kalli Safuratu cikin zare ido hade da cewa, "Kar dai zargin da nake gaskiya ne, guba suka zuba a cikin abincin da suka baki". Safuratu ta ce, "Kwarai kuwa guba ce mai karfin gaske ma, amma ni bata min illar komai ba, duk abinda ya faru ina sane kuma ni na tsara hakan dan suyi tunanin lalai na ci gubar". Murja ta fashe da kuka, nan take tunanin abubuwa da yawa suka fado mata kwakwalwa. Wato yanzu su Hajiya Lami neman rayuwarta suke ido rufe, so suke su rabata da duniya, tabbas ba don Safuratu da ta matsa mata a kan ta dawo gidan ba, babu abinda zai sa ta dawo, da rayuwa a gidan ji take gwara rayuwa a kauye ko gidan kurkuku, domin can ko da ya kasance babu kayan more rayuwa amma dai ba za'a samu masu bibiyar rayuwarka suna neman daukarta a duk saada suka sama dama ba.



A bangaren su Hajiya Lami kuwa, zarya kawai take a cikin daki ta dunkule hannu sai sake-sake take a zuciya tana cije lebe. Mama Dije ma zaune take a gefen gado, kallo daya zakayi mata ka gane cewa hankalinta ba a tare da ita yake ba, domin ta fi kama da mutumin da yayi zurfi a tunani. Hajiya Lami ta latsa wayarta hade da karawa a kunne, ringing farko wanda ta kira a wayar ya dauka cikin masifa ta fara magana, "Haba doctor guba fa na ce maka ina bukata, wannan abun da ka aiko min ba guba bane domin mun gwada baiyi aiki ba". Daga can ya ce a kan me suka gwada amma ta ki fada masa ta kama yan kauce-kauce. Jin haka ta sa ya kara musu bayani a kan gubar, ya tabbatar musu idan mutum ya sha wannan gubar ba zai kara mintuna biyar a raye ba, domin ciccira hanji da sauran kayan ciki take, wanda nan take mutum zai mutu. Kashe wayar tayi tana tsaki, "Aikin banza, wallahi na fi tunanin cutarmu kawai yayi ya amshi kudi ya bamu wani ruwan banza a matsayin guba". Mama Dije ta ce, "Ni fa wani bangare na kwakwalwata yana zargin wannan yarinyar, domin lokacin da na tabata tabbas babu lumfashi ko kadan a jikinta, anya kuwa ba aljana bace". Hajiya Lami ta ce, "Babu wani Aljana Mama kawai gubar ce bata aiki". Mama Dije ta tashi hade da cewa, "Nasan yadda za'ayi mu gane na gaskiya ne ko na karya biyo ni ki gani". Tana fadar haka tayi waje, Hajiya Lami ba gardama ta bita baya. Kai tsaye sauran abincin da Murja bata karasa cinyewa ba Mama Dije ta dauka, Hajiya Lami na tambayar me zatayi da shi tace ta dai biyota zata gani. 



Kai tsaye wajen da suke kiwon kaji da kwakwa da dawisu ta nufa, wasu agwagi guda biyu ta ba abincin, ai kuwa suna fara ci ba'a dade ba suka fara mimmikewa nan take suka fadi suka mutu. Idanu Hajiya Lami ta kwalalo tabbas ta yarda gubar tana aiki yanzu. Mama Dije ta ce, "To kin gani alamun lalai gubar gaske ce". "Na gani Mama amma abun ya daure min kai ya akayi wannan yarinyar ta tsira da ranta? Amma bari mu koma mu shiga dakin bamu sani ba ko tana can ta idasa mutuwa". Mama Dije ta ce, "Allah yasa ma ta mutum". Sun nufi hanyar komawa falon ta ga Sunusi wajen bakin kofa don haka ta kira shi ta ce ya je ya dauke agwagin da suka mutu ya zubar da su. Kai tsaye suka nufi dakin su Murja, bayan sun kwankwasa Murja ta ce su shigo, bakin ciki ne ya sake turnuke zukatansu ganin Murjojin biyu a zaune a kan gado, daya tana ba daya madara, da alama marar lafiyar ce ake ba madarar. "Murja ya jikin?". Mama Dije ta tambaya yayin da take kallon Safuratu fuska da alamar tausayi, "Da sauki". Safuratu ta ce sannan itama Hajiya Lami tayi mata ya jiki. Ita dai Murja kallonsu kawai take cikin tsoro, domin a kullum sha'anin su Aunty Lami kara bata tsoro yake, tunda take a duniya bata taba ganin azzaluman mutane ba kamar Hajiya Lami da uwarta Mama Dije. Bayan sun fita Safuratu ta ce, "Kingansu nan ba zuwan Allah da annabi sukayi ba, da alamu akwai abinda ya kawo su". Murja ta ce, "Ba zan musa ba wallahi". Suna fita daga dakin Hajiya Lami ta wangale baki cikin farin ciki. Mama Dije ta ce, "Me kuma ya faru, bayan mun tarar da su lafiya kalau ai kamata yayi ace kinyi bakin ciki ba farin ciki ba". Hajiya Lami ta nunawa Mama Dije wayarta hade da cewa, "Mama Kalli nan".


Hoton Murja Mama Dije ta gani, nan take itama fuskarta ta cika da farin ciki, ta ce, "Lami yaushe kika dauki hoton nan?". Hajiya Lami cikin murmushi ta ce, "Wallahi kuna gaisuwar nan na kara wayata na dauka, su kansu na tabbata ba su san na dauki hoton ba". Mama Dije ta ce, "Amma wallahi na ji dadi, gobe kawai sai mu koma a kaiwa Boka kare dangi". Sunusi ne dauke da jifga-jifgan agwagin sai sauri yake, zuciyarsa na ta saka masa abubuwa, daga karshe dai ya tsayar da matsayarsa na cinye agwagin maimakon zubar da su. Da sauri ya karasa dan dakinsu na mai gadi ya daukko wuka, fitowarsa tayi dai-dai da shigowar Hamza. "Aa Sunusi ina ka sama agwagi kuma". Sunusi bai bashi amsa ba ya ce, "Dalla malam kama a yanka kafin su karasa mutuwa". Ba musu Hamza ya kama wuyan agwagin Sunusi ya yanka su. Bayan an yanke jini yaki zuwa, Hamza ya ce, "Sunusi jini fa yaki zuwa anya agwagin nan basu mutu ba, domin ni naga ko da na kama banji suna motsi ba, haka zalika da ka yanka ma banji suna motsin fitar rai ba". Sunusi ya kyalkyale da dariya hade da cewa, "Duk wannna ana yi ne idan da lafiya, agwagin da basu da lafiya rai hannun Allah ya za'ayi suyi motsin kirki. Kaga malam da so nayi in maka muguwar tare in cinye agwagin nan ni kadai, amma tunda Allah ya kawo ka kuma ka gani, yanzu boyesu zamuyi a daki sai dare yayi idan wadannan mayun su Mubarak sun tafi makwancinsu mu fiddo mu gyara su mu ci dadi". Cikin washe baki Hamza ya ce, "Wallahi wannan shawarar tayi dama na dade banyi wa nama cin Allah tsine uwar mai karya ba". 


Da dare har wajen karfe sha biyu Mubarak bai je wajensu ba, sai Lurwan da yaje ya zauna, yana ta kawo musu hira kala-kala su kuma suna katse hirar wani lokacin ma su yi shiru, shi dai ya lura basa son hirar don haka ya shiga cikin gida. Suna ganin ya tashi kuma Mubarak bai je wajensu ba don haka sukayi tunanin ba zai zo ba sai da safe. Kai tsaye suka je suka hau gyaran agwagi, suna cikin yayanka wa domin wankewa su zuba a tukunya kamar daga sama suka ji muryar Mubarak, "Aa maza ta samu ashe shine ba gayyata?". Murtuke fuska suka yi baki daya suna dariyar yake, har ga Allah su biyu suka so su cinye agwagin kowa ya ci daya, amma ga wannan mayen ya bayyana, ya dan dade yana musu magana su kuwa suna binshi da "Uhmm" ko "Uhm uhmm". Da ya lura da abinda suke nufi ya ja tsaki hade da cewa, "Haba Sunusi miye duniyar? Dan an sama abun duniya kuma sai a juyawa mutane baya, abun duniya ai samammene kuma kararre, goben nan zaku cinye mu dawo mu zama daya". Da fadar haka har zai juya sai ji yayi Sunusi yayi murmushi ya ce, "Aa kaga dawo Mubarak, wallahi abunda yasa kaga tun farko bamu gayyato ka ba, agwagin ne muke tunanin kamar mushe ne ga Hamza nan lokacin da aka yanka su jini bai zubo ba, kuma basuyi motsin fitar rai ba ko". Hamza ya jijiga kai, shi kuwa Mubarak sai yayi tunanin ko duk rowar ce ta sa suka fadi haka, don haka yayi dariya hade da cewa, "Ai ba mushe ba ko miye in dai zaku ci nima wallahi zan ci" . ba yadda suka iya haka suka barshi ya shigo cikin gyaran agwagin. 


Romo suka yi mai dadi suka ci suka sha, kowa a cikinsu yayi gyatsa, hira kadan sukayi Mubarak ya tashi ya koma cikin gida makwancinsa, domin su Sunusi dama kusan zaune suke kwana a kofa suna gadi. Cikin dare ko wanne yaji cikinsa ya fara ciwo, ba shiri suka fara zarya bandaki. Mubarak ma haka cikinsa ya dingi ciwo amai da gudawa ba shiri ya fara zarya bandaki, ba komai ya fado masa a rai ba sai agwagin da suka ci, don haka ya je wajen su Sunusi masu gadi da niyar yi musu masifa amma sai ya tarar da suma lalurar da ke damunsa tana damunsu. Sun sha matukar wuya duk daren basuyi bacci ba, sai da asuba ta taho sannan cikin ya dan lafa. Da safe Mama Dije tuni ta yiwa Sailuba waya domin tafiya wajen Boka. Hajiya Lami ta kira Mubarak a waya amma yaki daukar waya, don haka ta aiki Nana domin taje ta fada masa zasu fita yanzu. Da Nana taje da kyar Mubarak ya iya ta shi ya bude kofar yana rike ciki, nan yake fada mata baya da lafiya ba zai iya fita ba. Da Nana ta koma ta fadawa Hajiya Lami ba karamin fusata tayi ba, don ya bata musu shiri. Daga karshe dai ta kira mishi doctor a lokacin ne ma Nana take fada mata ai har su Sunusi ma basu da lafiya kamar yanda Mubarak ya fada ma. Bayan doctor ya duba su ya tabbatarwa Hajiya Lami guba suka ci, amma Allah ya taimaka ba da yawa bane shiyasa ma abun ya tsaya a iya amai da gudawa. Tunani take me ya hada su Mubarak da guba, agwagi ne suka fado mata a rai, don haka ta shiga dakin da suke ta tambaya ina suka zubar agwagin da Mama Dije ta ce Sunusi ya zubar. Da jin haka suka shiga cicira idanu....................

 
🤭 Yo ko ni na samu agwagin nan fa ba bari zanyi ba,

Comments