ALJANAR FATIMA BOOK 1 Part 57

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/7qDMR8puSwE

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-57-hausa.html


*^ Part57 ^*



Cikin fushi Safuratu ta ce, "Kinyi babban kuskure da kika karbo aikin kashe wannan yarinyar, kuma kuskure ne wanda babu yafiya, domin ko don ciwon da kika ji mata a fuska ya isa ace na karya miki kafafu ta dalilinsa. Amma yanzu bani da lokacin batawa a kanki, don haka yanzu zan kashe ki kuma na batar da gawarki, nasan Bokan da ya aikoki zai biyo didigi to ina jiransu". Zilzilla da ke jin masifa saboda yadda Safuratu ta danne mata kai a kasa, ta daga baki zatayi magana kenan, ta ga Safuratu ta kama kanta da hannaye biyu ta fizge kan. Nan take kan ya fita bakin jini ya fara kwarara a tsakar falon, da ganin haka Safuratu ta rufe ido cikin dan lokaci kankani ta fiddo wata kwalba yayin da jinin da gawar Zilzilla suka shige ciki. Washe gari da safe da farkawarta daga bacci ko brush batayi ba tayi saurin daukar safaya key na dakinsu Murja, kai tsaye taje ta kwankwasa dakin Mama Dije itama tashinta kenan ta bude. Cikin farin ciki Mama Dije ta ce, "Sun mutu ne?". Hajiya Lami tayi murmushi hade da cewa, "Banje ba tukun, yanzu zanje shine na biyo in tayar dake mu je tare, na tabbata yanzu sun mutu". Mama Dije ta kyalkyale da dariya hade da cewa, "Shegu munyi maganinsu, yanzu ya zamuyi da gawarwakinsu?". Hajiya Lami tayi gaba tana fadin, "Yanzu dai muje dakin nasu, gawarwakinsu ai abu ne mai sauki muna iya cewa guba suka ci suka mutu bamu sani ba, kinga sai a musu sutura ba damuwarmu bace". 


Kai tsaye dakin suka nufa cike da farin ciki, domin boka ya tabbatar musu da mutuwar Murjojin guda biyu, kuma sun tabbatar ba zai musu karya ba, a shekarun baya ma kamar haka yayi musu albishir da mutuwar baban Murja kuma da safe sai gawarsa aka samu. Tana zuwa ba tare da wani fargaba ba ta sa key din ta murza kai tsaye suka kutsa kai suka fada dakin suna murmushi irin na farin ciki da zummar zasu tarar da gawarwakin Murjojin guda biyu. Suman tsaye sukayi a waje daya, ba don komai ba sai don ganin Murja a zaune kan gado ta dan rufe kafafunta da bargo bayanta kuma ta jingina da filo. Suka kai kallonsu ga dayar Murja wacce ke kwance a gefenta da alama bacci take yi, amma in da haka suka tarar da dayar Murjarma da suna iya cewa mutuwa tayi ba bacci suke ba. Bayan kallon juna da sukayi na dan lokaci, Safuratu dake a suffar Murja ta ce, "Hajiya Lami lafiya kuwa, kun fado daki haka tun da sassafe?". Murmushi ta saki hade da cewa, "Lafiya kalau wallahi, zuwa mukayi mu ga lafiyarku, kinsan yanzu cuta da mutuwa sun zama ruwan dare, in kuna tare da mutum ko makwabci ba sai gida daya ba, ya dace ka rika lekawa a ko wace safiya domin ganin lafiyarsa". Mama Dije ta ce, "Kwarai kuwa, kwanaki wasu mata da miji suka mutu a cikin gida amma ko makwabtansu basu sani ba sai bayan kwanaki, kinga irin haka ai ko kadan bai dace ba". Ita dai Safuratu kallonsu kawai take, domin tasan ko miye a zukatansu, sunsan makircin da suka kulla da boka zuwansu dakin sun zo ne domin su tarar da gawarwaki.


Hajiya Lami ce ta karasa gefen da dayar Murjar take ta kare mata kallo sosai, taga tana lumfashi hakan ya tabbatar mata da cewa lalai bacci take ba mutuwa tayi ba. Nan take wani irin bakin ciki ya ziyarci zuciyarta, wato aikin da boka yayi a kan kashe su baiyi ba kenan, lalai dole su koma wajen boka domin jin abinda ya faru. A zahiri kuma murmushi tayi hade da cewa, "Mama itama dayar Murjar lafiyarta kalau ba abinda ya sameta". "Madallah ai haka ake so, zo mu tafi mu basu waje ai gwara suyi bacci su huta". Mama Dije ta fada, kai tsaye suka fita daga dakin har lokacin Safuratu na binsu da ido tana kara jinjina makirci irin nasu a zuciyarta. Suna fita bayan sun haura sama Hajiya Lami ta dunkule hannu ta kaiwa bango duka cikin takaici da kunar rai, da sauri Mama Dije ta riketa tana fadin, "Haba miye na wani tada hankalinki don basu mutu yau ba ai ba lalai su tsallake gobe ba. Ni da ke gaba daya munsan aikin boka tamkar yankan wuka ne, watakil yanzu ma an samu wani akasin ne". Hajiya Lami ta ce, "Wallahi na tsani yarinyar nan kamar yadda na tsani mutuwata, gani nake kamar da gaske kamar yanda ta fada zata amshe duk dukiyarta da ke hannunmu, duk da bansan dame take takama ba amma ni duk sanda na tuna maganganunta sai inji gabana yana faduwa, na fadawa Lawal bai dauki maganar da muhimmanci ba yace ba zai dawo ba sai ya ga komai ya daidaita a harkar kasuwancin da ya tafi UK". Mama Dije ta ce, "Bake kadai ba hatta ni din nan idan na ganta ji nake tamkar na shaketa in kasheta har lahira". 


Zaune suke sun saka tv gaba amma da alamu hankullansu ba a kan tv take ba, Murja tayi sallama da farko basu ji ba sai a ta biyun suka karba. Waje ta samu ta zaune hade da cewa, "Aunty Saratu Ina wuni? Wai duk tv din ce ta dauke muku hankali haka ina sallama bakuji ba?". Saratu tayi murmushi hade da cewa, "Lafiya kalau Murja, wallahi hankalinmu ba a kan tv din ba ma take, Ummi ce ta zo tana fada min wai masu shagunan kasuwa inda take kai tallar abinci suna yi mata korafin dalilin da yasa ta daina kaiwa, shine nima nake ce mata ya kamata mu cigaba da yin abincin nan domin mu samu mu tara kudi muyi gaggawar gyara gidanmu, don ba ma zo mu tare a gidan mutane ba, mafakar da aka bamu ma ta isa Allah ya saka da alkhairi, amma sai dai kuma ina tunanin yadda lamarin zai wakana kasancewar yanzu rayuwarmu ta dawo nan gidan gaba daya kinga ba mutuncinku bane a ga yarinya na fita da kayan tallar daga nan gidan". Bayan jin dogon jawabinta Murja tayi murmushi hade da cewa, "Haba Aunty Saratu, ai ba sai kun cigaba da yin abincin sayarwa ba, maganar gida kuma insha Allah ni da kaina zan gyara muku shi". Da sauri Saratu ta ce, "Aa Murja wallahi karki dorawa kanki wannan nauyi, duk da nasan cewa a yanayin dukiyar gidanku gyaran gidanmu ba wani abu bane, amma dan zaman da mukayi a gidan nan na fahimci ke kanki ba zaman dadi kuke da Hajiya Lami ba, to dan haka karki takurawa kanki hakan ma mun gode". Murja ta sake sakin murmushi a karo na barkatai hade da cewa, "Ai ni na ce zan gyara muku dan haka ba maganar daukar nauyi a nan, Hajiya Lami kuma karki damu da ita".


Saratu tace, "Yauwa Murja, wai ni kuwa ina wannan dayar Murjar? Wacece ita kuma ya kuka kare da ita, naga kwana biyu kin cigaba da harkokinki ba tare da wani damuwa ba". Murja ta ce, "Tana nan, yanzu haka tana cikin gida, kuma a daki daya muke kwana, duk da bansanta ba ban kuma san yaya akayi ta zama kamar ni ba, amma ta tabbatar min da cewa ba cutata zatayi ba". Saratu ta jijina kai cikin mamaki ta ce, "Lalai Murja a gaisheki, a daki daya fa kika ce kuna kwana? Ai wallahi ba zan iya ba, ni yanzu da zan ga mai kama dani komai da komai, in na fara gudu ai bansan inda zan tsaya ba". Dariya Murja ta kyalkyale da ita, Ummi da tunda ta gaida Murja bata sake cewa komai ba ta ce, "To Mama ai yanzu ma bamu san da wacce Murjar muke magana ba, tunda komai nasu iri daya hatta kaya fa nasu iri daya ne yanzu". Murja ta ce, "Ai kuwa ba nice ta gaskiyar ba". Da sauri su Ummi suka ja baya, ita kuwa ta bushe da dariya hade da cewa, "Wasa fa nake muku ni ce dai Murja". A lokacin suka lura da ciwon dake fuskarta suka tambayata tace karfen kofa ne ya ji mata ciwo da daddare. Washe gari ma tun da sassafe su Hajiya Lami suka shiga dakin su Murja amma bisa mamaki sai suka tarar da su gaba daya suna bacci, nan ma ba karamin mamaki abun ya basu ba, domin sun zata gawarwakinsu zasu tarar. Don haka rana tana fara yi suka kira Sailuba tayi musu jagora zuwa wajen Boka Kare Dangi.


Bayan sun kora mai bayani ya daga kai yana wasu surutai wanda basa fahimtar komai a cikinsa, cikin dan kankanin lokaci fuskarsa ta sauya da alamun bacin rai, ya kalli su Hajiya Lami ya ce yana mai basu hakuri, wai aljanar da ya sa aikin kashe Murja tun da ta tafi bata dawo ba. Kuma yasa wasu aljannu su nemota amma sunje duk inda take zuwa basu samota ba. Shi kanshi ya nuna musu matukar mamakin da yadda akayi Murja ta kasance a raye har zuwa ranar, domin shi a tunaninsa tuni aljana Zilzilla ta kashesu kuma ta kada wani wajen saboda ya santa da shegen yawo. Nan dai ya bukaci sai sun sake kawo hoton Murja din, sannan zai sake tura wani aljani ya kasheta. Hajiya Lami ta duba wayarta amma bisa mamaki sai ta rasa hoton Murja wanda suka dauka, don haka ba yadda suka iya haka suka koma gida. A hanya daidai wajen bada hannu Mama Dije ta ga wani mai sayar da maganin bera da fiya-fiya ai kuwa ta saya ta sa a jaka, Hajiya Lami na tambayarta abinda zatayi da shi ta ce zata fada mata in sunje gida. Bayan sunje gida suna zaune a daki Hajiya Lami ta tuno da maganin bera da taga Mama Dije ta saya, don haka ta sake tambayar Mama Dije a kansu. Mama Dije ta ce su Murja zata zubawa a cikin abinci su ci su mutu, ita ta matsu ta ga gawarsu.


Dariya Hajiya Lami ta kyalkyale da ita hade da cewa, "Mama gaskiya kinyi tunani mai kyau, ni tun farko ma na manta da wannan shawara, amma fiya-fiya da maganin bera za'a iya gane su a cikin abinci, don haka bari na kira doctor na tambayeshi guba mai karfi marar kamshi da wari kuma wacce zata iya kashe mutum farar daya". Da jin haka Mama Dije ta ce, "Kwarai kuwa ni na sha'afa ma wannan shegen fiya-fiya din dan banzan wari gareshi, ko mahaukaci aka zubawa a cikin abinci ba zai yarda ya ci abincin ba". Hajiya Lami ta dauki waya ta kira likitansu nan take ta zayyana masa irin gubar da take bukata, har ya tambatayeta abinda zatayi da ita amma ta ce ba ruwansa, ita dai in akwai zata aiko direba ya karba. Haka kuwa akayi direba ya je ya karbo shi kanshi baisan ko miye ba yar kwalba ce karama da farin ruwa a ciki, ya kawowa Hajiya Lami ta karba cikin farin ciki. Tun daga lokacin suke kitsa yadda zasuyi su zuba gubar a cikin abinci su ba Murjojin biyu domin su ci su mutu. Bayan kwana daya da rana Hajiya Lami ta tura direba da su Nana suka je suka hado cefane na musamman domin ranar Hajiya Lami da Mama Dije sunce su zasuyi girki da kansu wai saboda sun dade ba suyi ba yau suna so kowa ya ci abincin da suka girka da hannayensu. Haka kuwa akayi bayan an kawo cefanan suka shiga kitchen da kansu suka girka abinci lafiyayye. Bayan an zuba abincin kowa ya ci ya watse Hajiya Lami ta zuba abinci kwano biyu, kasancewar su biyu ne a wajen ba tare da fargaba ba ta fiddo gubar ta zuba a ciki. Nan take ta sa Nana ta kira mata Murjojin guda biyu, wai ta ce su zo su ci abincin da ta girka da hannunta. Da Nana ta je dakin Murja daya ta samu tana bacci don haka ta kirata dayar Murjar kuma tana bangaren su Saratu, da Nana ta je kiranta ma ta ce abinci ne Hajiya ta ce ta zo ta ci, Murjar tace ita ta koshi domin sunci abinci da su Saratu.


Ita kuwa dayar Murjar fitowa tayi tana murza ido alamun bacci, ta zo ta zauna yayin da suka mika mata plate din abinci. Lafiyayyar shinkafa ce dafa duka ta sha mai, duk inda ka kalla a ciki nama ne yankakke, kamshi kawai yake tashi, Murja ta kai idonta ga plate din hade da jawo shi gabanta tana hadiyar yawo. Su kuwa baki daya suka tsura mata ido jira kawai suke su ga ta fara cin abinci domin ta garzaya lahira su rage mugun iri. Sau uku suna aikawa a kira dayar Murjar amma ta ce ita ta koshi, ba haka suka so ba amma tunda sun samu dayar adduar da suke Allah sa itace Murjar ta gaskiya ta ci gubar ta mutu kowa ma ya huta. Cokali ta cika zata kai baki, ganin yadda suka tsurawa bakin nata ido yasa ta kalle su hade da cewa, "Lafiya kuwa?". Da sauri suka kauda kansu suna dan murmushi, ta sake yunkurin kai abincin baki yayin da su kuma suka sake bin cokalin da kallo burinsu daya ta kai abincin baki. Ganin suna kallonta ta ajiye cokalin cikin abinci hade da cewa, "Wai ni kam me ya faru ne naga kuna ta kallona, ko dai abincin bashi da kyau ne?". Mama Dije ta ce, "Wa? Ni dai ba ke nake kallo ba, Lami kece mai kallon nata ko? Ki daina kallonta mana, babu kyau mutum yana cin abinci ana kallonsa. Kuma abincin nan lafiyarsa lau da zafinsa kinga yanzu aka zuba miki shi daga kula muma yanzu muka ci namu". Hajiya Lami ta ce, "Wallahi gani nayi Murjar ta wani kara kyau shiyasa nake kallonta ba wani abu ba, amma ni yanzu ma zan tashi cikina ne ya danyi nauyi abun abincin da na ci". Kallonsu tayi daya bayan daya cike da shakku, duk sun yi mata wani iri ba yadda ta sansu ba. Kasancewar tana jin yunwa ga kamshin abincin na ta kai mata karo, ba tare da tunanin wani abu ba ta dauki abinci ta kai baki. Suna ganin haka kamar hadin baki suka sauke ajiyar zuciya, Murja bata kula ba ta cigaba da cin abincin hankali kwance domin abincin ba karya yayi dadi. 


Cikinta taji ya fara murdawa a hankali, cikin lokaci kankani kuma ta fara jin wani azababben ciwon ciki, ba shiri ta sa hannu ta dafe cikin tana rarraba idanu. "Lafiya Murja? Me ya faru". Hajiya Lami ta fada tana kallon Murja cikin tsamanin wani abu. "Cikina naji yana ciwo"..... "Ga ruwa". Mama Dije ta fada hade da mika mata ruwan wanda shima sun zuba gubar a ciki, ai kuwa Murja ta karbi kofin ta shanye ruwan, ji tayi kamar an kara mata wani ciwon don haka ta fadi daga kan kujerar da take kai hannunta rike da ciki tana yarfa dayan hannun tana fadin, "Cikina-cikina zan mutu". Da kyar take maganar......................


🏃‍♂️ Bari na kira motar asibiti karta mutu, idan na dawo sai mu cigaba


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments