ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 48

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/kGY_i0VKnqg 

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-48-hausa.html


*^ Part 48 ^*


Safuratu ta ke tsaye tana kallon duk abinda suke aikatawa, ganin sun fita ya sa tayi murmushi hade da cewa, "Au ta nan kuma aka bullo? To ayi mu gani idan tusa zata hura wuta". Su Hajiya Lami cikin farin ciki suka haura sama ko wacce ta shiga dakinta ta kwanta. Misalin karfe biyu da rabi duk sunyi bacci, Safuratu ta bayyana a dakin Hajiya Lami, kai tsaye ta dauke wayar Hajiya Lami hade da duba hotunan da ta dauka bayan tayi amfani da fingerprint na yatsar Hajiya Lami ta bude wayar. Kai tsaye ta goge hotunan baki daya. Kwance take tana bacci taji ana fadin, "Jamsyyy! Jamsyyy!". Ido ta bude baccin bai gama sakinta ba amma har zuwa lokacin tana jin sautin muryar dake kiranta, ga daki duhu rudum domin ta kashe kwayayyen dakin kafin ta kwanta. Ba zato ba tsamani sai ji mutum tayi a kusa da ita kan gado a zaune, a tsorace ta kwada ihu, hade da sauka daga kan gadon da gudu, tana fadin, "Wanene? Wanene?". Amma shiru, don haka tayi niyar karasawa wajen makunna domin ta kunna haska a dakin don ganin ko waye ya shigo mata daki tsakar dare duk da kuwa ta rufe kofarta. 


Ji tayi wani hannu ya rike mata kafa, bata san ko hannun minene ba amma tana jin kaushi a jikin hannun da ya riketa. Kokarin kwacewa ta shiga yi tana kurma uban ihu tana kiran Ummanta da Abbanta. Ji tayi an kyalkyale da dariya mai fidda sauti uku-uku. Daga bisani kuma ta ji an daka mata tsawa, "Yi mun shiru marar kunyar yarinya". Kame bakinta tayi tayi shiru tana karkarwa hade da kalle-kalle a cikin dakin duk da bata ganin kowa. A gefenta saitin kunne taji an kyalkyale da dariya. Don haka ta sake kurma uban ihu, wanda bata san lokacin da ta fincike kafarta ba ta ruga da masifaffen gudu jikin bango ta kunna kwan dakin hade da juyawa da sauri tana karewa dakin kallo. Tsit ta ji dakin yayi babu hayaniya da karar dariyar da take ji amma ta hangi mutum zaune cikin farin zani mai kama da likafani. A hankali ta fara fadin, "Waye? Waye ne a kan Gadona?". Mutumin ya juya baya amma a haka ya saukko daga kan gado ya nufi inda Jamsy take tsaye a jikin bango yana wata kalar dariya marar dadin saurare, ga kafafunsa a daure suke tsalle yake ba tafiya ba. 


Kara rikicewa tayi don haka ta nufi kofar dakinta da gudu domin ta bude ta fita, amma ta cire kubobi ta murza keys da jamlock ta ji kofar a rufe tamkar an saka kwado daga waje. Juyawa tayi ta ga mutumin yana daf da karasowa wajenta, don haka ta fara kwalla ihu da duk karfinta. Ta dade tana ihu a tunaninta Momynta ko su Khalil zasu ji amma ta ji shiru ga mutumin ya karaso gaf da, ita ba zato ba tsamani sai gani tayi mutumin ya juyo, wani ihun ta sake kwallawa mai karfi sannan ta bangajeta ta haura can saman gado, fuskar mace ta gani a jikin mutumin, budurwa ce mai matsakaicin shekaru, fuskar fara sal tamkar ta shafa hoda ko gari, hancinta a rufe yake da aduga sannan idanunta kwala-kwala abun tsoro. Bata taba gani a zahiri ba amma ta sha gani a film sak haka yan film suke hasko fatalwa musamman a film din tsoro. Tana daga kuryar kan gado a tsaye tana karkarwa ta fara fadin, "Don Allah don annabi kiyi hakuri karki kasheni fatalwa, me na miki?". Gani tayi matar ta dage kai ta kyalkyale da mahaukaciyar dariya sannan ta ce, "Ai yau sai na koya miki hankali, ba dai ni kika yiwa rashin kunya da zu ba? Gobe ba zaki kara yiwa wani ba". 


Da gama fadar haka ta ga idanun matar da ta kira fatalwa yayi wani irin baki, da faruwar hakan ta ji ta a saman iska. Nan take ta cigaba da kurma ihu tana hantsile-hantsile da hannu da kafafu. Ganin ihu da kiran sunan iyayenta da take ya ki mata amfani ya sa ta fara fadin, "Don Allah kiyi hakuri mama fatalwa, Mama Fatalwa ki yiwa Allah da Annabi karki kasheni wallahi bana son in mutu yanzu". Tsawa ta ji an daka mata wanda ya sa tayi shiru ba tare da tayi niya ba, "Idan kika sake yi mun ihu sai na karkatar miki da fuska, kuma ni aljana ce ba fatalwa ba". Kama baki tayi da hannaye biyu duk da tana matukar tsorace hade da cewa, "To Aljana wallahi Allah na daina". "Ai ba zaki daina rashin kunya da rashin tarbiya ba dole sai na taba lafiyar jikinki". Zatayi magana kenan taji an bugata da kasa, ai kuwa goshita ya bugu a tile nan take wajen ya kumbura.


Kuka ta fashe da shi tana shafa goshinta tana dubawa ko ya fashe amma sai bata ga jini ba. Zaunawa tayi a gefen gado ta kwalalawa Jamsy manyan idanunta hade da cewa, "Yi mun shiru ko na karya miki hanci yanzun nan". Ba tare da gardama ba tayi gaggawar gimtse bakinta, domin ta san cewa yau Allah ne kawai zai ceceta, duk da abin ganinshi take tamkar almara wai aljanace a gabanta kuma suke magana. Ta matsawa kwakwalwarta domin ta tuno inda tayiwa aljana rashin kunya amma ta kasa ganowa, ji tayi an fara magana da sautin da ya sa dakin yake amsa amo, "Yau na kara tabbatar da rashin tarbiyyar ki da alamu ko islamiyya baki yi ba, tunda ga shi kin ga abun tsoro amma maimakon ki kira sunan Allah sai kika rika ihu kina kiran sunan iyayenki, gashi dai har yanzu banga wani daga cikinsu ya kawo miki dauki ba, saboda haka yi wa kanki mari biyu lafiyayyu bisa wannan laifin". Hawaye na kwarara daga idanunta take jin maganar sama-sama. Kara kaimin kukan tayi ta fara fadin, "Don Allah don annabi kiyi hakuri". "Ki mari kanki ko na mareki da kaina". Maganar da ta ji anyi mata kenan cikin tsawa don haka cikin tsoro tana a durkushe gaban aljanar ta daga hannunta ta mari fuskarta ji kake fak! Aljanar ta ce, "Da karfi zaki mari kanki". "To". Ta fada yayin da ta daddage ta faskawa kanta mari. Aljanar tayi gyaran murya hade da cewa, "Dazu kin ce sai kin kori mutanen da Murja ta kawo gidan nan ko?". Cikin kuka ta fara girgiza kai, "Wallahi na fasa na rantse miki da Allah ba zan koresu ba ko dakina suke so ma su zo zan basu". 


Ji tayi an sake daka mata tsawa, wacce saboda karfinta sai da dakin yayi girgiza, "Ba rantsuwa nake so ba, maza ki murda kunnenki da karfi, idan kuma kika murda a hankali da kaina zan murde miki kuma ni idan zan murda sai na cire miki kunna". Da jin haka a tsorace ta kama kunnenta da kanta kamar ba a jikinta yake ba ta murda da karfi har sai da tayi kara, wani kukan ta sake saki. Aljanar ta ce, "Abu na uku karanta min sura uku a cikin alqurani". Da kyar ta karanta fatiha da suratul Iklas shima Aljanar na yi mata gyara a wurare da yawa. "Kin taba yin islamiyya?". Tana kuka ta ce, "Eh mun taba shiga amma bamu dade ba aka ciremu saboda malamin yana dukanmu". Tsaki ta ja hade da cewa, "Hegiya Lami saboda ita batayi karatun ba shiyasa bata damu yaranta suyi ba. To daga yau ki rika zuwa wajen Ummi wannan yarinyar da suka dawo gidanku kina koyan karatun alqurani kinji ko?". Da sauri ta girgiza kai tana fadin, "Eh na ji". "Karkiyi tunanin kin zuwa saboda ina cikin gidan nan ba barin gidan zanyi ba, karbi wannan ki dauki hotunan kanki da kanki". 


Hannu Jamsy ta mika ta amshi wayar da aljanar ta miko mata, bisa mamaki sai ta ga wayar mahaifiyarta ce, kai tsyae ta dauki hotuna guda uku ta mika wa aljanar, tana ta tunanin wannan wace irin aljana ce, aljannu da suke tsoron karatu amma ita wannan itace ma take cewa ayi. Dif ta ga fitilar dakin ta dauke, yayin da ta ji wata mahaukaciyar dariya ta karade dakin, rufe kanta da hannuwa tayi sannan ta runtse ido tana tunanin abinda zai biyo baya, bisa mamaki kuma sai ta ji dif dakin yayi shiru, ai kuwa tana bude ido ta ga haske ya dawo kuma aljanar ta bace, don haka ta tashe ta yi hanyar waje a guje, cikin sa'a tana murza key kofar ta bude, ai kuwa ta je ta fara kwankwasa kofofi, na mamarta da ta Khalil da ta Mama Dije, A rikice tana ihun su bude, Mama Dije ta farka a lokacin tana ana buga kofa amma tayi shiru kamar matatta, Khalil na bude kofar cikin magagin bacci ta bangajeshi ta wuce ta haye kuryar gado. "Ke lafiya? Wane kalan hauka ne wannan zaki wani buge mutum ki haye gado kuma, dallah fadi me ya kawoki ki tashi ki koma dakinki". "Aljana! Aljana! Wallahi aljana ce a dakina yanzu". Bayan Khalil ya tambayeta ta bashi labarin abun da ya faru yayi tsaki hade da cewa tsoro ne kawai irin nasu na mata, don haka ta jira yaje ya dubo dakin, tana dakatar da shi amma ya fuce ya nufi dakin nata....................😒 Ku dai yi hakuri mutanena, a yan kwanakin nan kuma sai ta Allah, domin rashin caji, wutar mu ta baci dama cikin satin nan da cajin power bank na dogara yanzu kuma shima ya isa limite dinsa. Don haka in na sama caji zan rika typing in ban samu ba kuma sai hakuri, domin wutarmu gyara ake wai.

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments