ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 46

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/AB4u7gJG9C0

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-46-hausa.html


*^ Part 46 ^*


Ihu ta kwala mai rikitarwa, nan take ta ruga da gudu ta kunna fitilar dakin, bisa mamakinta sai gani tayi ba komai a kan gadon, ta kashe fitilar har ta kwanta kuma ta ce, "Kai wallahi ba zan kwana a dakin nan ba". Tashi tayi da niyar fita daga dakin amma sai taji ta ci karo da mutum, a hankali tayi baya tana fadin, "Waye ne? Waye?". A haka har ta jingini da bango ta lalubo wayarta dake kan mirror ta haska torch sai gani tayi ba kowa, don haka tayi gaggawar fita daga dakin ta je ta fara kwankwasawa Mama Dije kofa. Cikin bacci ta ji ana kwankwasa mata kofa don haka tayi shiru, bayan tuna abinda ta gani jiya bayan an kwankwasa ta bude, "Mama, Mama ki bude". Jin shirin yayi yawa gashi kuma a matukar tsorace take ba shiri ta koma ta kwankwasa dakin Jamsy ta bude mata sannan ta samu ta kwanta a dakin. 


Da safe bayan sun karya kai tsaye suka hau mota suka biya suka dauki Sailuba a hanya, sannan suka wuce domin zuwa wajen Boka Kare Dangi. Zaune suke a gabanshi sai waige-waige suke kallo daya zakayi musu ka gane cewa dukkansu a tsorace suke, saboda wani irin sauti da suke ji shi ba kuka ba shi ba dariya ba, haka zalika ba magana ba. Sannan sun kasa bambance sautin da suke ji na mutum ne ko na dabba ko kuma dai na aljani. Boka Kare Dangi kuwa ya juya musu baya ya dage kai sama sai motsa baki yake amma basa iya jin abinda yake fada, ya dade a haka sannan ya juyo garesu hade da kyalkyalewa da mahaukaciyar dariya, su kansu sai da suka tsorata tamkar su tashi su zura da gudu ganin yadda ya bude bakinshi da ke cike da jajayen hakora da suka dafe saboda datti sai dariya yake, ya jima yana yi sannan lokaci guda kuma ya bata rai tamkar bai taba yin dariya ba, hade da cewa, "Nasan me ke tafe daku, tabbas ba zargi bane yarinyar da ta dawo gidanku Murja ce". Dafe kirji Hajiya Lami tayi hade da cewa, "Innalillahi Mama itace wallahi na shiga uku". Tsawa mai karfi Boka ya daka mata hade da cewa, "Na sha gargadinku da fada muku a nan ba'a kiran sunan Allah, mu da shedanun aljannu muke aiki, wannan shine gargadi na karshe da zan miki a yau, idan kika sake ambaton sunan Allah ko da wasa ne sai na bar aljannu sun kwakwada miki mari ko kuma su murgude miki baki". 


Shiru Hajiya Lami tayi tana bin Boka da ido, Mama Dije ta ce, "Boka ka taimakemu yanzu miye abun yi tunda ka tabbatar mana da cewa idan Murja ta warke wani mummunan abu na iya samun Lami". Dariya Boka ya sake kwashewa da ita ya dan jima yana yi, a zuciyar Hajiya Lami ta ce, "Banza kawai mahaukaci ana magana mai muhimmanci ta ceto rayuwata amma shi dariyarsa kawai yake yi". Zuwa can ya sake bata rai hade da cewa, "Ku kwantar da hankalinku, idan har zaku iya kawowa aljannu wadatattun kudi to zamu iya sake haukatar da yarinyar kamar yanda akayi da farko, kuma a wannan karon ina da yakinin ba zata sake warkewa ba, domin a wnacan karon ma wata hatsabibiyar aljanace ta taimaka mata wajen karya sihirin, a sanadiyarta har ta kashe mana aljanar da muka sa tayi mana aikin". Cikin sauri Hajiya Lami ta ce, "Boka bana son a haukatar da ita, so nake a kasheta". Dariya ya kyalkyale da ita sannan ya ce, "Kasheta shine abu mafi sauki ai a wajena, ku kawowa aljannu wadatattun kudi, sannan ku hado da hotonta, ni kuma zansa a kasheta cikin gaggawa". 


Da jin haka farin ciki ya lullube Hajiya Lami ta ce, "Boka kudi ba matsala bane, ko nawa kake so zan kawo, sannan hotoma ba zai zama matsala ba tunda a gidanmu take kwana ko tana bacci ne zan daukko hoton sai a wankoshi a kawo maka". "Ku tashi ku tafi". Tashi sukayi suka tafi cikin farin ciki.


Zaune suke suna hira bayan ta kwaso musu abincin gidan baki daya ta kawo, Ummi ce tayi sallama ta shigo gidan, Murja ta ce, "Waalaiki salam sannu da zuwa yan talla dama ke nake jira". Bayan ta ajiye kayan talla ta mikawa Saratu kudin hannunta tana murmushi ta ce, "Aunty Murja ina wuni". "Lafiya kalau, yauwa Ummi karatun nan na zo mu fara". "Karatu kuma Aunty Murja? Ni fa wallahi na zata wasa kike". Murja ta ce, "Babu wani wasa, kawai dai ina sha'awar cigaba da karatu ne ko akwai makarantar manya ne irina?" Ummi ta ce, "Sosai ma akwai makarantun manya a cikin garin nan, sai wacce kika zaba zaki shiga". "Amma nayi farin cikin jin haka, so samu ne ma a sama wacce ake koya baki daya boko da islamiyya". Ummi ta ce, "Zan bincika miki Aunty Murja.


Bayan la'asar Murja ta koma gida, tun kafin ta shiga falon ta fara jin masifar Hajiya, Safuratu na gefenta ta ce, "To fa wannan jarababbun sun dawo ashe". "Na ce ku fada min dan uwarku Murja ce ta dauke ku aiki ko ni na daukeku?". Kai suka sadda kasa Nana da Ikilima cikin hadin baki suka ce, "Kece". "Ok ni na dauke ku aiki, amma uban wa yace ku dauki abincin ku bawa Murja bayan kun san mun tafi unguwa kuma zamu iya dawowa mu bukaci abincin?". Cike da tsoro Lami ta ce, "Wallahi Hajiya itace ta ce mu juye abincin duka mu bata zata kai gidan su Saratu, ni kuma ganin kwana biyu idan ta taba abinci bakwa ci sai dai ta dauka ta kai gidan Saratu shiyasa kawai na bata". Cikin bacin rai Hajiya Lami tace, "Na baku mintuna goma sha biyar, idan baku dafo abinci kun kawo mana ba duk sai na koreku daga aikin gidan nan, banzaye marar amfani kawai ku bace mun da gani". Nan take suka tashi suka nufi kitchen cikin sauri. Dai-dai lokacin Hajiya Lami ta lura da Murja da ta shigo falon amma tayi tsaye a bakin kofa tana kallonsu, harara ta wulla mata hade da jan tsaki, ita kuwa Murja dan rissinawa tayi hade da cewa, "Sannunku da dawowa, ina wunin?". Sailuba ce ta amsa ciki-ciki yayin da su kuma su Mama Dije sai cin magani suke suna yiwa Murja mugun kallo. 


Safuratu dake gefe tayi tsaki hade da cewa, "Wawiya kawai, harda yi musu sannu da kin san inda sukaje ba zakiyi musu sannu ba". Juyawa tayi ta kalli Safuratu hade da cewa, "Ina suka je?". Kallo suka bita da shi baki daya, suna kallon saitin wajne da ta kalla tayi magana domin babu komai a wajen, a zukatansu suna tunanin ko haukan nata ne bai tafi ba. Safuratu kuwa cewa tayi, "Zan fada miki amma ba yanzu ba". "To". Ta ce ta sama waje ta zauna. Sun dade a wajen suna rarraba ido ganin Murja ta ki tashi yasa suka mike da niyar haurawa sama. Sai ji sukayi Murja ta ce, "Ke Lami ina da maganar da zan fada miki". Kallon juna suka shiga yi, Sailuba ta kama baki hade da cewa, "Lalai abun ya girmama, ba batun girmamawa ma Lami kai tsaye ko dan Hajiya babu?". Daga inda take ta tsaya hade da juyowa ta ce, "Ina jinki". Murja rai a bace ta ce, "So nake in fada miki, na baki kwana Goma ke da mijinki ku tattara duk dukiyata ku kawo min sannan ku kama gabanku ku bar min gidana, naji ance ya tafi kasar waje harkar kasuwanci ko". Kan Hajiya Lami ne ya dau zafi, lalai yarinyar ta raina mata wayo, ita bata ma karasa fahimtar me yarinyar take nufi ba don haka ta ce, "Wace dukiyar taki?". Murja ta ce, "Karkiyi kamar baki san komai ba, kinsan me nake nufi, domin duk dukiyar da kike takama da ita ke da Lawal Abokin babana kuma mijinki na yanzu, dukiyar babana ce, ban damu da cewa kunyi kasuwanci kun juya dukiyar ta kara yawa ba, ina iya yafe muku abinda kuka ci kuma kukayi amfani da shi ke da iyalanki a matsayin ladan juya kudin da kukayi, amma ko kwandalata ba zatayi ciwon kai ba sai kun bani abuna".


Hajiya Lami ta kyalkyale da dariya hade cewa, "Duk wannan dogon bayanin da kike sauraronki kawai nake, idan ma kece Murja ta gaskiya, wa zai yarda? A idon kowa da zuciyar kowa Murja ta dade da mutuwa, ke idan ma an yarda kece Murja me kike takama da shi, wa kike da shi wanda zai tsaya miki ya amsar tarin dukiya daga wajenmu ya damka miki? Nasan tuni kin ba wa kanki amsa babu shi, don haka ki daina mafarkin zaune". Bisa mamaki sai ji sukayi Murja ta kyalkyale da dariya ta dade tana yi, ta ce, "Kinyi kuskure Lami, zaki iya cewa bani da wanda ya tsaya min, amma ina da kowa, domin ina da Allah, shine kowa na, kuma shi zai kwatar min dukiyata daga hannunku. Na sha alwashi kafin nan da kwana goma da kanki zaki dawo min da duk wani abu mallakina hannuna". Duk da maganar ba Lami ba hatta su Mama Dije ta basu mamaki da tsoro, amma sai Lami ta bushe da dariya sannan ta ce, "Mu zuba mu gani, ni da ke". .............


☹️

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments