ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 44

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/x7Tz5SUWI2c

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-44-hausa.html


*^ Part 44 ^*Bisa mamaki sai ji tayi Murja ta dagata sama duk nauyita ta maka ta da kasa amma a kan gado, bata daddara ba ta sake kama Murja, ai kuwa ta sake dagata wannan karon ta yarda ita a kan tile, sannan ta bita da bulala. Ba shiri ta fara ihu nan take ta yi waje a guje tana sosa jiki. Daya bayan daya ta bi dakunsu ta tayar da su sallah da bulala. Mama Dije na kwance ta ji ana tsula mata bulala don haka ta tashi a firgice tana fadin, "Don Allah kuyi hakuri, innahu min sulaimana". Ganin Murja ce a tsaye ya sata yin shiru tana zare mata idanu, a yayin da take tunanin yadda akayi Murja ta shigo dakin nata bayan kuma daga ciki ta kulle. "Tsohuwar banza tashi kiyi sallah". Harara ta fara bin Murja da shi daga bisani ta ce, "Yanzu ke yarinyar nan ashe rashin kunyar taki har ya kai haka? Ba ki ga girman duk tsufan nan nawa ba ni kike tayarwa da bulala?". Murja tayi murmushi hade da cewa, "Wane girma gareki, ai ke tsohuwar banza ce, kuma ai aikin Allah ne, kamata yayi ma ki gode min na tayar dake kiyi ibada a kan lokaci. Don duk tsufanan naki idan kika mutu bakya sallah, mala'iku jifgarki zasuyi". Tana tsaki ta fara yunkurin saukkowa daga gadon, ganin laima a jikin bargon ya sa Murja ta tsuntsire da dariya, hade da cewa, "Tsufan naki har ya kai ki rika fitsari a kwance?". Da jin haka Mama Dije ta kai dubanta ga bargo ta ganshi a jike, sai a lokacin ta ankara kayan jikinta ma akwai lema a jiki.


Lalai jiya ta tsorata sosai domin bata ma san tayi fitsarin ba, "Ai sai kije kiyi wanka sannan ki zo kiyi sallah". Bata cewa Murja kala ba ta shega bandaki, ita kuma Murja ta fice a dakin bayan ta tabbatar ta tayar da kowa. Da safe duk wanda ka kalli fuskarsa, sai ka ga kamar fuskar shanu saboda bacin rai, suna zaune a dinning suna breakfast Jamsy ta kalli Hajiya Lami hade da cewa, "Mom ni fa gaskiya cin zarafin da akayi min a gidan nan yau in ba'a dauki mataki ba ni zan dauki mataki da kaina". Cikin rashin fahimta Hajiya Lami ta ce, "Wane kalan cin zarafi akayi miki?". Kuka ta fashe da shi hade da cewa, "Ina cikin baccina mai dadi fa wannan mahaukaciyar ta shigo dakina ta dingi zafga min bulala wai na tashi sallar asuba". Khalil ya ce, "Wallahi nima haka Mom, wai ita wannan din yar gidan uban waye, wallahi zan tattaka ta a cikin gidan nan". Karar mari kawai suka ji, nan take suka kai idanunsu bayan Khalil dake magana, basu san lokacin da ta taho ba kawai ganinta sukayi a bayan Khalil kuma ta falla masa mari ta baya. "Magulmata kawai, ku yanzu ko kunya baku ji ba harda ku uwayen ake gulamata?".


Zare ido suka shiga yi, su gaba daya lamarin yarinya tsoro yake basu, "Kai kuma me kunnuwana suka ji kana fada? Zaka tattaka ni ka ce?". Cikin fushi ya mike tamkar zaiyi wani abun kirki, "Tun da kika mareni na rantse da Allah sai na fasa miki baki yau din nan". Hannu ya dunkule ya saita kafafunta ya fuskanci Murja tamkar zasuyi dambe, abun har dariya ya bata, naushi ya kai mata da nufin ya zubar mata da hakora, bisa mamaki sai ji yayi ta damke hannu hade da sake wanka masa mari da dayan hannunta. Ba shiri ya gyara tsayuwarsa hade da dafe fuskarsa tabbas ya maru sosai, don har ji yayi kunnuwansa na fidda wani sauti na daban. "Koma inda kake ka zauna, marar kunya kawai". Ba musu ya juya ya zauna a kujera nan take itama Murja ta zauna hade da cewa, "Saboda tsabar bakin hali da rowa abincin karin ma so akayi a cinye ba mu ko". Da fadar haka ta dauki plate ta fara zuba indomie dake cikin kula sannan ta hada shayi mai kauri. 


Duk abinda take Hajiya Lami na kallonta, zuciyarta na ta mata zafi saboda kaf duniya babu mahalukin da ya taba ko kwatanta irin rainin wayon da Murja ta ke yi mata a cikin gida. Abubuwan da take yi mata yayi yawa, ai ko mutuwa hausawa sun ce tana kunyar idon mahaifi, amma wannan yarinyar a gabanta take dukar mata yara. Khalil ne ya tashi ya nufi sama, itama Jamsy ta bar cin abincin ta tashi, hade da cewa, "Nima wallahi ba zanci abinci da mahaukaciya ba". Gaba daya tashi sukayi har su Hajiya Lami wai ba zasu ci abinci da mahaukaci ba, ita kuwa Murja ta gyara zama ta take cikinta, sauran da sukayi kuma ta kira Nana ta rike mata suka kai gidan Saratu. Misalin karfe 12 na rana suna zazzaune a falo kowa na harkar gabansa, yayin da ita kuma Murja ta sa Tv gaba tana kallon wani malam dake jawabi da larabci. Sallama suka ji anyi, Hajiya Lami na ganin wanda sukayi sallamar fuskarta ta cika da farin ciki, ta amsa hade da mikewa tsaye. Sojojine guda biyar ko wanne rike da bindigarsa sun sha kaki kai da ganin fuskar nan ka san ba wasa. "Laminu sannunku da zuwa, ai tun dazun nake jiranku". Wanda ta kira da Laminu yayi murmushi hade da gaisheta sama-sama sannan ya ce, "Wallahi Aunty Jasmeen ce ta turoni ta ce wai akwai wani bata gari da ya addabeku a gida, mu kuma irinsu muke nema domin muyi maganinsu, shiyasa ma na kira abokaina gasu nan suka rakoni". 


Kallo daya Murja tayi musu kasa da sama sannan ta juya ta cigaba da kallonta. Hajiya Lami kuwa bata rai tayi hade da cewa, "Ai nayi farin cikin zuwanku wallahi wata yarinya ce wacce bamu san ko daga gidan ubanwa take ba jiya-jiya ta shigo gidan nan amma ta addabi kowa". Dai-dai lokacin Mama Dije ta gaishe da su, sannan ta dora da cewa, "Gata nan a zaune don Allah ku ci ubanta sosai, idan ma ta kama ku kakkaryata alhaki a kaina". Laminu da sauran abokansa suka kalli inda Mama Dije ta nuna musu da hannu cikin rashin fahimta, Laminu ya ce, "To ina take ku nuna min ita, idan na fahimta dai wacce kuke magana a kanta mahaukaciya ce, domin in ba mahaukaci ba ai babu wanda zai shigo gidan mutane ba tare da ya sansu ba kuma har ma ya rika musu abubuwan da ba dai-dai ba". Hajiya Lami ta ce, "Kai Laminu bari na fada ma mai kankat ma a nan gidan babu wanda yarinyar nan bata daka ba har ni kaina. Gata nan don Allah duk yadda zakuyi da ita kuyi". Ta karashe maganar tana nuna musu saitin inda Murja take zaune. Sake bin wajen da kallo sukayi gaba daya su basu ga komai ba a gun illa kujerun dake jere. Daya daga cikin sojojin ya ce, "Hajiya mu fa ba mu ga mutum a nan ba, bayan ku ukun nan amma sai nuna mana kujera kukeyi kuna cewa gata nan". Sake juyawa Hajiya Lami tayi, a dai-dai lokacin Murja har juyowa tayi tana kallonta. Ba irin nunawar da basuyiwa sojojin ba, amma su sun tabbatar basa ganin kowa a wajen. Daga karshe Mama Dije har zuwa tayi ta dafa Murja tana fadin "Gata nan fa a zaune".


Babu irin nunawar da basuyiwa sojojin ba, amma sun rantse basa ganin komai illa kujerar dake wajen. Mama Dije har zuwa tayi ta taba jikin Murja hade sa cewa, "Yanzu nan ba ku ga na taba mutum ba?". Zan sojojin ne ya fara baci, don haka suka fara tsaki suna tunanin kawai rainin wayo ne ya sa Hajiya Lami ta gayyato su, gashi sai nuna musu kujera take tana cewa wai akwai mutum a zaune. Haka dai tai-ta basu hakuri suka fita suna masifa. Kujerar dake fuskantar wacce Murja ke kai Mama Dije ta zauna, hade da tsare Murja da Ido ko kiftawa bata yi. Hajiya Lami ta je ta zauna kusa da ita, cikin rada magana kasa-kasa ta ce, "Mama ni fa na fara zargi anya wannan yarinyar ba aljana bace? Idan ba Aljana ba taya za'a ce muna ganinta amma su Laminu basa iya ganinta?". Mama Dije tayi kwafa cike da takaici, don ta fi kowa kaunar a fidda Murja daga gidan, hade da cewa, "Baki da hankali, in da aljana ce ai ko kashemu take son yi da yanzu ta kashemu wani ma bai ji ba, kawai dai na fi tunanin irin hatsabiban mutanan nan ne, kuma karki raba dayan biyu da rufa ido tayi amfani ta bacewa yaran nan shiyasa suka kasa ganinta". Hab'a Hajiya Lami ta kama cike da mamaki ta ce, "Ashe akwai rufa idon da zaka iya yi ka hana wasu su ganka?". "Sosai ma kuwa". 


Murja ce ta taso hade da cewa, "Aunty Lami kudi nake so, kamar dubu dari biyu haka, domin ina son zuwa nayi sayayyar kayan sawa da kayan kyalkyali dai irin namu na mata". Kallo suka rika binta da shi cike da mamaki. Jamsy dake latse-latse a waya jin furucin Murja ya sata tasowa hade da cewa, "Idan an baki ficika a cikin kudin nan shegiya nake, ke din banza, ke din wofi". Harara Murja ta warga mata, hade daka mata tsawo ta ce, "In kika sake saka min baki sai na zubar miki da hakora, ke kuma Aunty Lami yi sauri ki daukko min, in kuma katinki zaki bani na tafi da shi duk daya ne". Mama Dije ce mike tsaye hade da cire dan kwalin dake kanta na shadda ta daura a kugu sannan ta ce, "Ba za'a bayar da kudin ba, na ga uban da zaki turo ya kwatar miki, ke tsaya kiji sanda ina kauye iskanci babu irin wanda ba muyi ba, mu ne yan iskan kauye. Idan kuma wani sihiri kike takama da shi ki sani bokana ya take naki ya dame ya shanye". 


Dariya Murja ta kyalkyale da ita harda rike ciki, sannan ta sa hannu daya ta tura Mama Dije sai gata tayi baya ta baje a kan kujera. Da ganin haka ta sake kyalkyalewa da dariya. Ta jima tana yi sannan ta bata rai hade da cewa, "Ke Lami dake nake, kin tsaya kina kallon mutane ki tashi ki daukko min ko na je na bincike dakin naki na daukko da kaina". "Da kuwa yau kinga tashin hankali a cikin gidan nan, Mama ai ku kuka ma biyata ni maganganun da take duk a matsayin hauka na dauke su, kina jin kudin da take cewa in bata fa, kamar ubata ne ya bani ajiyarsu". "Ubana ba bayarwa yayi ba, kwata akayi bayan an kashe shi, ko in fada miki yadda mutuwar tashi ta kasance ne? Boka Kare Dangi....". Tun kafin ta rufe baki hankullan su Hajiya Lami suka dugunzuma, nan take wata irin zufa ta karyo musu lokaci guda. A zahiri sunyi tunanin babu wani mahaluki da zai san wannan sirri a duniya fa ce su da kuma Allah da ya san abinda yake fili da na boye.....................


Na gaji 😳

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments