ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 43

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/x7Tz5SUWI2c

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-43-hausa.html


*^ Part 43 ^*


Ba yadda ta iya haka ta mike ta fara tafiya tana waigen baya, tamkar kazar da kwai ya fashe mata a ciki, Gaba daya ido suke binta da shi yadda ta tunkarosu tana tafe tamkar bata so kuma tana waigen baya, duk sai suka daina abinda suke suna jira ta karaso. Tana zuwa ta durkusa hade da cewa, "Mama Dije Don Allah zan dauki chocolate din nan kwara biyu". Safuratu na daga can baya tayi tsaki hade da cewa, "Shegen tsoro, malama ce miki nayi kawai ki daukko". Mama Dije kuwa bata rai tayi hade da cewa, "Da kudin ubanki aka sayo da zaki ce zaki dauka? Ku ji min yarinya dan Allah". Da saurayi Safuratu ta ce, "Ki ce eh kudin ubanki ne". Murja kuwa shiru tayi hade da girgiza kai alamun "A'a", Mama Dije ta ce, "To bace mun da gani, mahaukaciya kawai". Tashi tayi sume-sume ta juya ta fara tafiya, rike kanta tayi jin ya fara mata ciwo daga nan kuma bata san a duniyar da take ba. Gani sukayi Murja ta juyo kai tsaye taje ta dauki gaba daya kwalin chocolate din. Ai kuwa da ganin haka Mama Dije ta rike mata hannu hade da cewa, "Ajiye shi don ubanki". Murja ta ce, "Idon baki sakar min hannu ba sai na karya ki yanzun nan". 


Mama Dije tuno yadda aka karya hannun Dan Sanda tayi, don haka tayi gaggawar sakin hannun, Murja ta zari daya daga cikin chocolate din ta bare hade da kaiwa baki tana fadin, "Kaji matsiyata, kuna cin arzikina amma kuma kuna min rowa da nuna bakin hali". Tsaye Jamsy ta mike hade da cewa, "Ke malama shiru-shiru ba tsoro bane ba fa. Na ga abun naki ya fara yin yawa, kudin nan ba na uban kowa bane nawa ne kuma babana ya bani, ya zaki zo ki rika cewa kudinki ne. Wa ya sanki? Ke wacece? Da zaki zo gidan mutane ki addabesu". Kallo Murja ta karewa Jamsy sama da kasa, yarinya ce karama ba zata wuce shekara 14 zuwa 15 ba, amma saboda gata da take samu ta zama zafgegiya, haka zalika an sangartata a yadda ta fahimci yarinyar bata ganin girman kowa ciki kuwa harda iyayenta balle kuma ta ga giraman bare. Lafiyayyen mari ta ji an wanketa da shi, wanda ya sa ta fashewa da kuka ta koma ta zauna a cinyar mamanta. 


Murja ta ce, "Yi mun shiru marar kunyar yarinya, me kika sani da har kike tsoma mana baki a cikin maganar nan, kudin da ubanki da uwar taki suke takama da shi ki tambayesu asali daga ina suka samesu. Ga uwar taki nan a zaune ko kin san cewa asalinta yar aiki ce a gidan nan". Gaban Hajiya Lami da Mama Dije ne yayi mummunan faduwa, nan take kuma zukatansu suka kara tsorata da lamarin Murja. A zahiri sunyi tunanin a duniyar nan babu wanda zai iya bankado wannan tsohon sirrin, kasancewar yanzu ko giyar wake mutum ya sha, yayi kadan ya kalli Hajiya Lami ya ce asalinta yar kauye ce kuma yar aiki, domin naira ta zauna a kugunta. Sai dai sun manta tarihi baya boyuwa. Cikin kuka ta ce, "Wallahi karya kike Mamana ba yar aiki bace, kije ki nemo yar aikinku a can wani waje". "To ai ga uwar taki nan a kusa dake sai ki tambayeta a gabana muji ko zata musa, ko kuma ki tambayi kakarki ai gata nan zaune". Jamsy ta daga baki zatayi magana, da sauri Hajiya Lami ta rufe mata baki hade da cewa, "Jamsy yi shiru mana, bana son cacar bakin nan da mutumin da ko saninsa bakiyi ba".  


Komawa Murja tayi kan kujera ta zauna tana dariya hade da cewa, "Idan an isa a musa mana". Shiru falon yayi sai tv da ke ta hayaniyarta, Murja kuma bayan Safuratu ta fita a jikinta, ta cigaba da shan chocolate Safuratu na ta balbaleta da masifa saboda tsoron su Mama Dije da take ji. Bayan dare ya fara yi sosai, Murja ta mike tsaye hade da cewa, "Ni fa bacci nake ji ina dakina yake?" Hajiya Lami da Mama Dije dake zaune shiru sukayi suna kallonta, Safuratu ta ce, "Malama ki zabi dakin da duk ya miki a cikin gidan nan ki shiga ki kwanta, ai gidan ubanki ne ba na wani ba". Murmushi Murja tayi hade da cewa, "Yanzu wancan dakin da muka fito dazu ba na kowa bane? Idan ba mai shi to ni ya zama dakina". "Idan shi kike so ai shikenan sai mu dauke shi din". Murja ta ce, "To muje". Bayan Murja ta tafi ganin ba kowa a falon, Hajiya Lami ta ce, "Wallahi Mama gabana faduwa yake a duk sadda na kalli yarinyar nan, da gaske fa tayi kama da Murja, kuma kina jin abinda take fada wai tasan asali ni yar aiki ce abinda ba kowa ya sani ba sai mutane na kusa da ni ko yan asalin kauyenmu". 


Kwafa Mama Dije tayi hade da cewa, "Kwantar da hankalinki, wannan ai ba wani abu bane don ta san ke asalin yar aiki ce a nan gidan, domin wani wanda ya sani ma yana iya bata labari, kinsan zance a wajen mutanenmu baya boyuwa musamman talakawa". Hajiya Lami ta ce, "Kuma fa haka ne, amma gobe dole yarinyar nan ta bar gidan nan, dama dazu nayi waya da kawata, wacce nake fada miki kaninta soja ne, ta tabbatar min gobe zata turo su harda ma karin abokansa, in suka zo na tabbata zasuyi min maganin wannan yar iskar yarinyar". Ajiyar zuciya Mama Dije tayi, sannan ta ce, "Wallahi har hankalina ya fara kwanciya, idan suka zo sai na kara tabbatar masu su yi mata dukan kawo wuka, yadda ko marmarin sake shigowa gidan nan ba zatayi ba. Safuratu dake gefensu a kan kujera tana jin duk abinda suke fada tayi murmushin mugunta, tana jinsu suka gama hirarsu suka tashi suka nufi saman bene domin kwantawa, Hajiya Lami na ta korafin yadda Khalil ke cika dare a waje.


Kwance take tana bacci cikin kwanciyar hankali, wanda baccin baifi awa daya da dauketa ba. Cikin bacci ta ji ana kwankwasa kofar dakin da karfi ana fadin, "Mama Dije?-Mama Dije". Zaune ta tashi tana murtsike ido, sam bata dau murya ba, don haka ta ce, "Waye yake tashin mutane haka tsakar dare?". Daga waje ta ji ance, "Gobara ta kama gidan gaba daya ta babbake kasa, kiyi gaggawar fitowa kafin wutar ta hauro sama". Neman baccin da ke idonta tayi ta rasa, wani irin karfi ta ji ya zo mata a hanzarce ta diro daga kan gado, hade da kokarin rugawa da gudu, ai kuwa bata san kafarta ta nannado bargo ba, sai ji kake rigijif ta zube a kan tiles. Ihu ta kwada hade da cewa "Wayyo Allah Gobara jama'a". Ba ta wani tsayawa dubawa ta ji ciwo ko bata ji ba, tayi waje a guje bayan ta murza kofar ta bude. Sai dai tana fitowa waje bata ga kowa ba, amma bata damu ba haka ta gangaro a guje ta yo kasan bene. Bisa mamaki tana gangarowa ta ga komai dai-dai, tv na tayi ita daya. Huci ta fara da sauri hakan ya sa ta nemi waje ta zauna tana zage-zage ita kadai a falo. Sai da ta huta sannan ta koma sama bayan ta lalleka dakunan su Jamsy ta tabbatar bacci suke yi. Ta kwanta kenan bacci na shirin sake kwasheta ta ji an sake kwankwasa kofar. Wannan karon zaune ta tashi ta fara soka ashar da zagi kala-kala. "In ma shegun yan aikin nan ne kuke min wannan iskancin wallahi ku kyayeni, na dau murya gobe zan sa a kori mutum, kuma in baka yarda ba ka cigaba". 


Tana gama fadin haka, ta koma ta kwanta, sai dai ko minti daya ba'a yi da kwanciyarta ba, ta ji an sake kwankwasa kofar, bayan kuma lokacin da tana zage-zage ba'a cigaba da bubbugawa ba, "Mama Dije idan baki fito ba zaki mutu a cikin dakin nan ke kadai". Abinda ta ji an fada kenan, ashar din ta sake jefowa hade da cewa, "Wai wane shege ne wannan? Ko kai wanene ka tsaya har in fito". Ji tayi ance, "Gani nan a kofa ina jiranki". Cikin sauri ta tashi ta nufi kofa a fusace, bude kofar da zatayi, ta ga gangar jikin mutum, a jingine a bango yana fuskantar kofar dakinta, amma babu kai a saman wuyansa amma ta lura wuyan yana motsi. Ihu ta kwada mai karfi, hade da banka kofar ta rufe, cikin ganggawa ta sa jam lock, ba tare da duban jikin tsufanta ba tun kafin ta karasa wajen gadon nata tayi tsalle ta haye hade da jan bargo ta kudundune ta rufa tayi shiru, ko lumfashin kirki bata son yi balle motsi. 


Suna cikin bacci suka ji ihunta hade da karan rufe kofa, don haka suka fito baki daya, Hajiya Lami ta ce, "Ihun waye na ji haka?". Khalil na murza idanu ya ce, "Wallahi nima ihun ne ya tasheni". "Ni na ji kamar ihun Mama Dije". Hajiya Lami ta ce, "Nima dai naji kamar ita, tare da karar rufe kofa amma ina fitowa na ga ba kowa". "Bari mu buga dakinta muji ko lafiya, ta tayar da mutane suna baccinsu". Jamsy ta fada hade da nufar dakin Mama Dije ta murza ta ji a kulle daga ciki, don haka ta fara kwankwasawa. Tana ji ana bubbugawa hade da kiranta amma tsoronta sai kara karuwa yake, don ji take ma kamar mutum ne a kusa da ita a kwance, ita kanta bata san tana da tsoro haka ba, ko da yake abinda ta gani ya fi karfin tunaninta.


Haka su Hajiya Lami suka gaji da kwankwasa kofa Mama Dije ta ki motsawa balle ta tashi ta bude, dole ta sa suka koma daki suka kwanta suna fatan Allah yasa lafiya. Da asuba Safuratu ta tayar da Murja sukayi sallah, bayan sun gama sallah Safuratu ta cewa Murja, "Kiyi addu'a sosai kafin ki koma bacci ni zan haura sama na ji ko motsin mutanen nan banji sun tashi sallah ba". "To". Kawai Murja ta ce. Safuratu na fitowa daga dakin ta koma suffar Murja komai-da-komai. A falo ta dauki wata wayar socket ta linkata biyu, sannan ta jijinata ta bugawa daya daga cikin kujerun falon, ta jijiga kai hade da cewa, "Yauwa wannan zatayi". Kai tsaye ta haura sama dakin Hajiya Lami ta fara murdawa cikin sa'a ta ga ta bude ashe basa murza key auto jamlock ne kawai yake shiga. Kwance take tana sharar baccinta hankali kwance ko tunanin tashi batayi, kamar a mafarki ta ji saukar bulala, bata gaskata abinda ta ji ba don haka ta kara gyara kwanciyarta, sake jin wata saukar bulalar tayi, kafin ta ankara ta sake jin wata. Ai kuwa cikin lokaci kankani baccin ya wartsake saboda yadda bulalar ta ratsata, kasancewar kayan baccine kawai a jikinta. Ido ta fara bin Murja dake tsaye gabanta da shi tana sosa bayanta in da bulalar ta daka. "Katuwar banza asuba tayi kina kwance, kina baccin asara, ke da zaki tashi har ma ki tayar da yaranki suyi sallah amma kina nan kina bacci ko? Anya kuna yin sallar ma kuwa? To na rantse da Allah maza ki tashi kiyi sallah". Ta kaici da bakin ciki ne ya turnuke Hajiya Lami, nan take taji zuciyarta na tafarfasa tabbas ba zata iya jure wannan rashin mutuncin ba. 


Rabon da bulala ta taba jikinta tun tana yarinya, amma yau a matsayinta na babba kuma Hajiya guda, wata yarinya kanwar-kanwarta ta daketa. Kukan kura tayi ta rukunkumi Murja da kokkowa..................



Ni kuma na gaji 🤔


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments