ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 42

🧟‍♀️🧟‍♀️                        🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/gyynAt_MaW8

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-42-hausa.html


*^ Part 42  ^*


Abincin da Nana da Ikilma suke shiryawa a dinning ta shiga budewa, lafiyayyar shinkafa a gefe ga miya ga kuma naman kaji a dayar kula, ido ta kwalalo a zuciya ta ce, 'lalai bayin Allahn nan suna cin dadi da dukiyar Murja'. Batayi wata-wata ba ta dauki plate ta cika shi da shinkafa dayan plate din kuma ta debi miya da nama ta gyara zamanta hade da daukar cokali ta fara ci. Suna zaune suna binta da ido. Mama Dije ta ce, "Ashe yunwa take ji, wannan haukan ba'a banza ba". Nana ce ta kai wani katon kofi jug ta ajiye, Murja da ta cika baki da naman kaza ta ce, "Miye a cikin nan?". Nana ta ce, "Kunun aya ne da Hajiya ta ce muyi mata". Bata ce mata kalla ba ta dauki kofi daya ta cika da kunun aya ta shanye ta kara cika daya ta ajiye a gefe sanan ta cigaba da cin abincin. Jamcy ta ce, "Mama abincin da zamuci kuka bari wannan mahaukaciyar tana ci? To na rantse da Allah ba zanci abincin nan ba takeaway zansa Mubarak ya yo min order".  Hajiya Lami ta ce, "To ya muka iya da abinda ya fi karfin wuta? Kallo ne namu idan kuma zaki iya hanata ci ai gaki ga ta". Tashi tayi hade da yin tsaki ta bi hanyar waje ko gyale babu jikinta balle ayi maganar hijab, Hajiya Lami ta ce, "Idan kin tashi sayo abincin ki taho mana da shi don muma ba zamu ci abincin da wacce bamu sani ba ta ci wallahi".  


Murja na jinsu tayi banza da su, sai da ta cika cikinta fall, sannan ta kora da kunun ayar da aka zuba mai kankara yayi sanyi. Bayan ta mike tayi gyatsa hade da cewa, "Alhamdulillah yau dai yarinya ta ci abincin gidan ubanta". Ta kalli su Hajiya Lami da suma ita suke kallo, "Yanzu dai in na fahimta dai-dai, gaba dayanku ba zaku ci wannan abincin ba don na ci ko?".  Basu ce da ita kala ba, ta ce , "Abu yayi kyau, Nana! Nana! Zo nan". Nana ta fito daga kitchen, Murja ta ce, "Akwai sauran abincin nan a kitchen ne?".  Nana ta ce, "Aa duka ne na kwaso saura namu wanda zamu ci kawai ya rage a tukunya". Murja ta ce, "Su masu gadi fa kin basu nasu?".  "Aa ai su masu gadi ba daga cikin gida ake kai musu abinci ba, su suke dafa abincinsu ko kuma su saya". Murja ta ce, "Yayi kyau, maza sako hijab dinki ki daukko wannan kular da wannan, ni zan dauki wannan sai muje mu kai musu tunda yan gidan ba zasu ci ba". Kallon Hajiya Lami Nana tayi, taga harararta take, Murja da ta daukko kula biyu tayi gaba, ganin Nana ta tsaya tana kallon Hajiya Lami ta ce, "Ke malama ki daukko mu tafi wannan da kike ganinsu su suka ce sun koshi". Ba yadda ta iya haka ta daukko kulolin ta wuce ta gabansu saboda hararar da suke mata tamkar idanunsu zasu fado kasa. 


Bayan sun fita Mama Dije ta ce, "Oh! Yau ni na ga karfin hali bako ya fi dan gida".  Hajiya Lami ta ce, "Wallahi Mama akwai matsala ni na rasa ta inda zan bullowa lamarin nan ma, gaba daya kaina ya kulle". Mama Dije ta ce, "Ai kawai sojoji zaki daukko mata gobe, irin wadannan yaran daga ganinsu yan iskan kauye ne da ta ga bindiga zaki ga tana karkarwa".  Hajiya Lami ta ce, "To shinenan insha Allah gobe kuwa zan kirayo mata sojoji, akwai wani kanin kawata sojane kuma a nan yake aiki". A bangaren Murja kuwa suna zuwa wajen su Sunusi ta ajiye kular da kofin kunun aya hade da cewa, "Assalamu Alaikum, yauwa ga abinci su waye masu jin yunwa a cikinku?".  Kallo suka bita da shi, sannan suka fara zarewa juna ido, ganin suna ta kallonta sunki cewa komai ta ce, "Ko kuma ba zaku ci bane? Abinci ne lafiyayye yan gidan ne suka ce ba zasu ci ba, don na diba na ci, shine na ce bari na kawo muku". Da sauri Lurwan ya ce, "Ni dai na koshi dama yanzu na ci abinci". Kafin ya rufe baki Sunusi ma ya ce, "Wallahi nima ban dade da cin abinci ba".


Dayan zaiyi magana Murja ta dakatar da shi ta hanyar yin tsaki hade da cewa, "Yan rainin wayo tunda bakwa so ai shikenan". Ta dauki kulolin ta cewa Nana ta biyota. Kai tsaye gidan Saratu ta nufa dake gaban gidan nasu. A kokarin daukar kular da Nana zatayi murfin kular da Naman kaza yake ciki ya fadi kasa, ai kuwa su Sunusi sukayi ido hudu da soyayen naman kazan nan take suka kama hadiyar yawu gashi kuma sun riga sun ce ba zasu ci ba.  Suna yin gaba Lurwan ya ce, "Amma na rantse da Allah da na san cewa akwai naman can, ba wacce ban sani ba ko mayyace ita sai na ci naman nan".  Sunusi yayi tsaki hade da cewa, "To kura mayen nama". "Kaga malam kai kanka na san cewa yawunka ya tsinke, kawai dai ta ciki na ciki, yaushe rabon mu ci nama irin wancan". Hamza ya ce, "Kai ni fa abun nan ya fara daure mun kai, anya wannan yarinyar ba da gaske yar gidan bace?".  Sunusi ya ce, "Me ka gani ka ce haka? Bayan kasan mun fi shekara biyar muna aiki a gidan nan amma ko mai irin kama da ita bamu taba gani ba". "To ai na ga in ba da gaske yar gidan ba ce, ya za'ayi kawai ka fada gidan mutane ka rika musu abinda ka ga dama bayan baka sansu ba kuma babu abinda ka taka". Lurwan ya ce, "Wallahi maganarka abun dubawa ce, amma dai in tayi tsami maji". 


Sallama tayi taji an amsa kai tsaye ta kutsa kai cikin gidan, Nana  na biye da ita a baya. Gida ne mai daki biyu sai dan guntun kitchen dinsu na langa-langa da ta hango wata yar budurwa a ciki tana ta aikin hura wuta. A gefe kuma da bandaki ginin kasa sai gefenshi an daure awaki guda biyu. Daga can taji Saratu na fadin, "Ku iso-ku iso, kai Affan daukko musu musu kujera".  Dubanta ta kai garesu duk da dare ne amma tana iya ganin su cikin yar rumfar kwanon dake gaban dakunan nasu. Suna zaune a kan tabarma yaranta biyu maza na tayata tsintar wake bayan fitilar da suka makale a jikin bango ta haske gidan. Bayan ta zauna suka gaisa cikin fara'a, Murja ta ajiye kular ta ce, "Dama abinci ne ban sani ba ko yara zasu ci na kawo muku, Nana mika musu". Cikin farin ciki Saratu tace, "Aa ai ko mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ke Ummi maza nemo kwano ki zo a juye abincin nan a basu kwanon". Da sauri yarinyar da aka kira da Ummi ta bar aikin hura wuta da take ta daukko kwana ta zo ta fara aikin juye abincin. Sai dai ko shinkafar ba'a karashe juyewa ba kwanon ya cika, Murja ta lura da cewa babu kwanukan ne dan ta ga sai kame-kame ake wajen neman mazubi har za'a aika yara makwabta su aro. Don haka ta ce su barshi da safe a tura yara su kaiwa mai gadi ko kuma Nana zata dawo ta dauka. 


Har Murja ta tashi zasu tafi ta ji Saratu ta ce, "Yauwa ni kuwa dan Allah in ba zaki damu ba baiwar Allah ko zaki tuna min a ina kika sanni? Ina miki kallon sani amma na rasa a inda na sanki kuma tun dazu da naji kin kira sunana abun yake min yawo a zuciya". Da jin haka Safuratu tayi sauri ta fita daga jikin Murja, nan take kan Murja ya fara ciwo, bayan ta dan dawo hayyacinta ta fara kalle-kalle na inda ta tsinci kanta. Safuratu ta ce, "Yauwa Murja ki natsu gidan Saratu muka zo na kawo mata abinci, shine take tambayar a inda na santa, kuma ni ba komai na sani game da rayuwarki ba shiyasa na fita daga jikinki don kiyi mata bayani da kanki".  Gyada kai kawai Murja tayi bayan ta ji kan nata ya fara yi mata saukin ciwon da ya fara. Komawa tayi ta zauna tana murmushi hade da cewa, "Aunty Saratu ashe baki ganeni ba? Ni ce fa Murja Rabe".  Fuskarta dauke da alamun tambaya ta ce, "Wace Murja Rabe din". Murja ta ce, "Haba Aunty Saratu, ni ce dai Murjar diyar Alhaji Rabe Naira da kika sani, idan baki manta ba lokacin da ina yarinya ina shigowa ina sayan tabar malam da dan ta matsitsi, bana mantawa akwai ranar da babana ya bani dari biyar na kawo na ce a bani tabar malam ta duka, kika ce ai duka ko ta dari biyu bata kai ba".


Zabura Saratu tayi hade da dafe kirji ta dan ja baya daga zaunen da take, "Innalillahi wa'inna Illaihir raji'un, Murja dama kina raye baki mutu ba?". Murja tayi murmushi hade da cewa, "Ina raye gani kuwa a gabanki kina gani". Saratu ta ce, "Wallahi tun ganin farko da nayi miki ina wa fuskarki kallon sani amma na rasa a ina na sanki, dake mu tuni kowa ya sallama kin mutu, don mu Aunty Lami da ta hada zaman makokinki ce mana tayi mota ce ta bigeki kika mutu, wai ko namanki da kyar aka tattara aka hada waje daya aka binne shiyasa ba'a kawo gawarki ba". Shiru Murja tayi tana tunani, ashe da wannan salon Hajiya Lami tayi amfani wajen yada mutuwarta". Dan wai-waigawa Murja tayi hade da cewa, "Aunty Saratu ina Yaya Isihu mu gaisa?". Hawaye taga sun zubo daga fuskar Saratu sannan ta dora da cewa, "Allah sarki Baban Ummi ya rasu nan da shekara biyar da suka wuce, bayan yayi fama da jinya mai tsawo ta tsawon lokaci". Murja ta ce, "Ayya Allah sarki, ashe lokaci yayi, to Allah ubangiji ya jikanshi ya gafarta masa sannan ya bamu guzurin tarar da su na alkhairi". Saratu ta amsa da "Ameen". "Amma Aunty Saratu me yasa bakiyi aure ba, naga dai har yanzu baki wuce zaman aure ba". 


Saratu ta ce, "Allah sarki, ai nayi aure shekara biyu da ta wuce, amma abun ya ki yuyuwa, saboda marayun yarana uku, a zamanin nan kuwa samun mai rike su famane, to don dole muka rabu da mijin da na aura".  Murja ta ce, "Allah sarki, wannan sune yaran Yaya Isihu?".  "Sune ga babbar ta su nan, Ummi sai mai bi mata Affan ga kuma karaminsu Jibrin". Ummi da ke tsaye ta dan sunkuya hade da cewa, "Ina wuni?". "Lafiya kalau Ummi yan mata ya ayyuka?". Ta ce, "Alhamdulillah". Nan take sauran yaran suka gaishe da Murja ta amsa. Murja ta ce, "Amma aunty kasuwancin me kike ne? Don na sanki da kokarin neman kudi, balle ga nauyin yara ya sake hawa kanki, ko kuma yan uwan babansu na taimaka miki ne?".  Saratu ta ce, "Eh to kayan miya nake sayarwa, ita kuma Ummi da rana tana fita bakin tasha tallar shinkafa da wake, da haka muke samun na abinci, har ma da kudin makarantarsu, yanzu haka Ummi tana karatu na boko da na islamiyya don har ta kusa kammala secondary ma".  Murja ta ce, "Masha Allah ashe na sama malama, zan rika zuwa kuwa tana koya min karatu, don ni nan haka nake ba arabi ba boko".  Saratu tayi dariya don ta dauki zancen a matsayin barkwanci ne. Safuratu ta kalli Murja hade da cewa, "Ke malama hirar ta isa haka tashi mu koma gida".  Sallama tayiwa Saratu, suna ta yi mata godiyar abinci, domin dama yunwa suke ji, waken da suke tsincewa na abincin daren da suke kokarin dafawa ne. 


Zaune suka tarar da su Hajiya Lami a tsakar falo suna ta cin abincin takeaway da sauran kayan kwadayi da Jamsy ta sayo musu, ganin Murja ta fara labe-labe alamun tsoro, Safuratu ta ce, "Na rantse da Allah idan kika sake nuna tsoron wadannan mutanen irin na dazu sai na yi miki rashin mutunci. Miye na tsoro a tare da su, ko kina tunanin zan bari su cutar da ke ne?". Murja ta girgiza kai alamar aa, hade da neman waje ta zauna tana kallon tv. Zuwa can Safuratu ta ce, "Murja ta shi ki daukko min wancan chocolate din na kusa da Mama Dije, ki daukko guda biyu daya naki daya nawa". Zaro ido Murja tayi hade da kallon Safuratu, taga lalai da gaske take ba wasa a fuskarta, sannan ta kai dubanta ga chocolate din dake cikin kwali a gaban Mama Dije. A zahiri har a zuciyarta tsoron Mama Dije da Hajiya Lami take duk kuwa da Safuratu na gefenta.....................
Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments