ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 41

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/gyynAt_MaW8

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-41-hausa.html


*^ Part 41 ^*


Kallo yake binta da shi tamkar wanda ya ga fatalwa ko wani abun tsoron, "Malam lafiya keke bina da irin wannan kallo kamar baka sanni ba? Ka zo ka bude min gida dallah". Ba gardama yaje ya bude mata gida, ai kuwa ta kutsa kai ta shige. Banani ne ya karaso wajensa da sauri hade da cewa, "Kai Sunusi wacece na ga ka budewa gida yanzu". Tsaki yayi hade da cewa, "Wallahi wannan mahaukaciyar ce wacce yan sanda suka tafi da ita dazun". "Amma sai yau na tabbata baka da hankali Sunusi, taya zaka bude mata gida ta shiga bayan kasan da kyar aka samu aka fiddota daga cikin gidan". Sunusi ya ce, "To ya kake so nayi? Kasan halinta sarai, idan ban bude mata gidan nan ba na lahira ma sai ya fini jin dadi. Dubi fuskata har yanzu bata idasa sacewa ba saboda marin da tayi mun dazu". "Wallahi idan Hajiya ta tambaya cewa zanyi kai ka bude mata gida ba ruwana, ga su Mubarak ma suna shaida". Mubarak ya taso daga tabarmar da sukayi sallah hade da cewa, "Wai me ke faruwa ne? Hayaniyar me kuke?". Da sauri Banani ya ce, "Wai fa wannan mahaukaciyar da ta zanemu dazu ita ce ta dawo shine wannan dan mahaukaciyar ya bude mata kofa ta shiga ciki". Mubarak ya dafe kai hade da cewa, "Innalillahi! Ya akayi yarinyar nan ta kubuto daga wajen yan sanda?". Sunusi ya ce, "Oho! Ni dai gudun shan mari yasa na bude mata gida ta shiga". 


Zaune suke a falo kowa na harkar gabansa, sukaji sallamarta, Mama Dije, Hajiya Lami Da Jamsy suka mike tsaye cikin tsoro suna mai kare mata kallo, domin tabbatar da abinda idanunsu suke gani. "Ku zazzauna ni ce dai Murja Rabe mammalakiyar wannan gida, ba wata bakuwa ba, naga kun wani mimmike tsaye tamkar kun ga abin tsoro". Da alamun tsoro Hajiya Lami tana zaunawa ta ce, "Baiwar Allah ba dazun nan yan sanda suka kamaki ba, ya akayi kika dawo yanzu kuma?". Murmushi tayi hade da cewa, "Miye abun mamaki a ciki? Bayan sun kamani sun tabbatar da cewa ni ba mahaukaciya bace, kuma na basu hujojji gamsassu akan laifin da kuke tuhumata da shi, shiyasa suka ji sun gamsu suka sakeni. Kuma dama ai na fada muku zan dawo kafin in tafi, ko laifi ne idan mutum ya dawo gidansa?". Shiru sukayi suna rarraba idanu a tsakaninsu, Mama Dije ta ce, "Wannan bala'i dame yayi kama". Zumbur Hajiya Lami ta mike, har ta fara tafiya Murja ta ce, "Ina zaki". "Ina da wani uzurine zan hau sama". "Ok muje nima alwala nake so inyi zanyi sallar magariba". Da sauri ta nuna mata wani bangare hade da cewa, "Ki shiga can dakin akwai bandaki da ruwa har sallayarma akwai". Tana fadar haka ta haura sama da sauri-sauri gudu-gudu. 


Da zuwa ta fara latsa waya hannunta har karkarwa take ta kira Dpo Nura, yana dauka ta cewa, "Haba Dpo ya zakayi mun haka, ba haka mukayi da kai ba yanzun nan na ga yarinyar nan ta dawo gidan nan bayan ka shaida mana har gidan yari sai ka sa tayi". Daga can ta ji ya ce, "Hmm! Hajiya Lami kenan, ai bansan haka lamarin nan yake ba da tun farko ko kudinki ba zan karba ba, kai da na sani ko daga wayarki ba zanyi ba a karon farko ma. Yanzu ni rokona ma shine don Allah don Annabi karki kara sakoni cikin sabgar da ta shafi wannan yarinyar domin bana fatan wani abu ya sake hadamu". "Ban fahimci maganganunka ba Dpo ita yarinyar yar gidan uban wacece da har zata baka tsoro ka rika tunanin ba zaka iya daukar mataki a kanta ba?". Ji tayi ya ce, "Ba yar gidan kowa bace, amma ni naga abinda na gani a tattare da ita, kuma ga dukkan alamu nan kusa zaku fara gani kuma, amma shawarata a gareku idan kunga abin ya fi karfinku ku hakura da gidan ku bar mata shi kuje ku saya wani". Tsaki ta ja hade da kashe wayar tana fadin, "Mu bata gida? Zancen banza zancen wofi". Dai-dai lokacin Mama Dije ta shiga dakin hade da cewa, "Lami kin kira Dpo din kuwa? Ya kukayi ne, wane dalili ne yasa ya sakota". Kallonta tayi ranta a bace hade da cewa, "Wallahi Mama wasu maganganun banza yake fada mun, wai ya ga abinda ya gani, minene-minene wai kar a sake sakoshi cikin safgar da ta shafi yarinyar, kuma muma zamu ga abinda ya gani, maganganu dai mararsa kan gado daga karshe har cewa yake wai idan mun ga abu ya fi karfinmu mu bata gidan". 


Mama Dije ta ce, "Ke rabu da shi, bisa ga dukkan alamu yana shaye-shaye, ni dama duk ganin da nake masa idanunsa jawur nake ganinsu, karki raba dayan biyu har giya yana sha. Kawai mu fita batunsa a nemo wani, ai ba su kadai bane yan sanda a garin nan, kai idan ma ta gagara har sojoji ana iya nemowa". Tsaki Hajiya Lami tayi hade da cewa, "Wai a kan wannan yar yarinyar nake batawa kaina lokaci, Mama barni da ita nasan yanda zanyi da ita". Tana fadar haka ta tashi ta fita fuuu!. Murja ce zaune a kan sallaya bayan ta gama sallah, kanta ta rike da ke ciwo kadan-kadan hade da cewa, "Wai me ke faruwa ne? Kaina gaba daya ya juye tunda muka zo bakin kofar gidanmu muna magana da masu gadi daga nan bansan me ke faruwa ba sai yanzu da naji kin tayar dani muyi sallah". Safuratu ta kyalkyale da dariya hade da cewa, "Dama ina zaki san abunda ya faru? ke da kika shigo gidanku tunda rana kike ta sharar bacci da alamu kinyi kewar katifar gidanku sosai"


Murja ta daga kai tana karewa dakin kallo, akwai komai na bukata a cikinsa, sannan ta ce, "Lalai Hajiya Lami ta kudance, dubi kayan kyale-kyaleto da ta sa a dakinta". Safuratu ta ce, "Waye ya fada miki dakinta ne? Dakinta yana sama watakil nan dakin bak'i ne". Murja ta ce, "Amma dan Allah ya akayi na tsinci kaina a nan bansan duk abubuwan da suka faru ba". Nan take Safuratu ta kwashe labarin duk abubuwan da suka faru ta fadi mata tana dariya. Murja ma tayi dariya ba kadan ba sannan ta ce, "Wai don Allah yanzu duk ni na aikata abubuwan nan amma bansan nayi ko daya ba?". Safuratu ta ce, "Bake kikayi ba, ni dai nayi a matsayinke, yanzu tashi muyi sallar isha'i sannan mu fita mu ga wace wainar ake toyawa". Tashi sukayi suka yi sallah sanna suka fito, sai da suka zagaya dakunan suna lallekawa ganin ko wane daki a share a goge tsaf kuma da komai a ciki, sannan suka nufi falon Safuratu a gaba Murja na biye da ita, amma ba mai ganin Safuratu ko jin maganarta sai Murja. Tun daga nesa ta fara hango Mama Dije da Jamsy zaune, tabbas ta gane Mama Dije sarai duk da tsufa ya fara kamata, amma jikinta baiyi komai ba balle ya nuna alama, bisa ga dukkan alamu tana hutawa sosai a gidan. Nan take ta fara tuno irin wahalar da ta sha a wajen Mama Dije da Hajiya Lami, tsoro ne ya ziyarci zuciyarta sai take ganin kamar yanzu ma zasu iya cigaba da gasa mata aya a hannu kamar yanda suka saba.


Don haka taje gaban Mama Dije hade da durkusawa ta ce, "Mama ina wuni?". A dan tsorace ta dago ta kalleta domin kara tabbatarwa ko da gaske take gaisuwar, ganin lallai da gaske take gaisuwar ya sa ta ce, "Lafiya kalau". ta amsa ciki-ciki. Ta ga sauye-sauye da dama a tare da Murjar ba kamar yadda take dazu ba, Safuratu tayi tsaki hade da cewa, "Murja miye haka? Dallah ta shi ki zauna a kan kujera ko so kike su sake rainaki ne?". Mama Dije dake kalllonta cike da mamaki gani tayi ta juya gefen da ba kowa hade da cewa, "To". Sai kuma ta ga Murja ta mike ta zauna a kan kujera ta tsurawa Tv Ido. Bangaren Hajiya Lami kuwa bayan ta gaji da zama a falo tana tsaki ita daya, ta tashi ta nufi bangaren masu gadi yayin da ta sa Sunusi ya tattara ma'aikatan dukansu ta fara musu jawabi kamar haka, "Wai wane irin ragwagen maza Alhaji ya tara mun a cikin gida ne? Kuna so ku ce a banza muke biyanku kudin aiki kenan? A matsayinku na garada masu jini a jika yarinya karama ta gagareku fitarwa daga gidan nan, kenan idan wani abun cutarwa ya shigo gidan a gabanku zai cutar damu ba zaku iya daukar mataki ba". Mubakar driver ya sosa kai hade da cewa, "Hajiya ayi hakuri, amma na ga yarinyar nan kamar ba ita daya bace, don dazu nayi mamakin yadda ta rika tsallake kujeru tana tsala mana bulala anya babu aljannu a tare da ita?". "Rufe mun baki raggon maza kawai, a yadda kuke kattin nan ko aljanace ita zaku iya maganinta, amma kun kasa fitar da yarinya daga gida gashi ta zo ta addabe mu". Murya kasa-kasa Sunusi ya ce, "Tabb, wallahi ba zamu iya fada da aljana ba". Da sauri Hajiya Lami ta ce, "Me kace". Ya ce, "Aa ni banyi magana ba".


"To bari ku ji in fada muku, idan baku fitar min da yarinyar nan daga gida ba, kuka yarda ta kwana a gidan nan duk sai na koreku daga aiki". Tana fadar haka ta juya ta fuce a fusace, su kuma suka rike baki suna mamakin furcinta, zuwa can Sunusi ya ce, "Kai wallahi ba zani ba, haba rabon da wani mahaluki ya sa bulala ya dakeni an fi shekara goma amma yau haka yarinyar nan ta rika zura min belt na kasa tabuka komai, yanzu haka ji nake kamar ta fasa min jiki da kan belt, kuma saboda nine dan Saratu sai in koma ko? Ai sai dai in korata za'ayi ayi". Mubarak ya ce, "Wallahi nima ban zuwa, a gabanmu fa yan sanda suka zo suka kamata, kuna kallo da idanunku da hannu ta karya wani dan sanda. Bisa ga dukkan alamu suma yan sandan ta gagaresu ne shiyasa kuka ga Hajiya ta sake dawowa ta kanmu".


Hajiya Lami na shiga falon gabon Murja ya yanke ya fadi bayan ta ganta, hakan yasa tayi saurin zubewa kasa daga kan kujera hade da cewa, "Aunty Lami Ina wuni?". Tsaye Hajiya Lami tayi tana kallon Murja dake durkushe tana gaisheta, abubuwa da yawa ne ke yawo a kwakwalwarta, "Aunty Lami?" Sunan ta sake nanatawa a zuciyarta, domin shine sunan da Murja ta asali da ta sani take kiranta da shi. Ita kuma Murja kallon tsoro take wa Hajiya Lami ganin ta kara kiba da kyau ta zama babbar mace amma har lokacin bak'inta na gado yana nan bai barta ba. Safuratu sai magana take mata amma taki tashi, domin a zahiri ba karamin tsoron Aunty Lami take ba, tsawa ta ji Hajiya Lami ta daka mata, sai da ta zabura sannan ta ce, "Ni ba auntynki bace kuma kiyi gaggawar tashi ki bar gidan nan kafin na yanke danyen hukunci a kanki". Da jin haka Murja ta tashi jikinta yana rawa ta nufi hanyar da ta tabbata ita ce hanyar fita, sakin baki Safuratu tayi tana kallonta, a zuciya tana tunanin ko gidan ubanwa zataje in ta fita?.


Ji tayi ance, "Ke Murja dawo nan ki zauna". Jin irin tsawar da akayi mata gaba daya sai da hantar cikinta ta kada, tana juyawa ta ga Safuratu ce fuskarta babu annuri. Ba gardama ta nufi inda Safuratu ta nuna mata domin ta zauna, Hajiya Lami da Mama Dije da har sun fara jin farin ciki a zukatansu ganin Murja ta nufi hanyar waje, ganin ta dawo Hajiya ta sake cewa, "Me kike dawo yi fitar mana daga gida malama kuma kar in sake ganinki a gidan nan". "To". ta ce hade da juyawa zata fita, tsulum! Ta ga Safuratu a gabanta ta daka mata tsawa, ta ce, "Idan kika kara tako daya daga nan inda kike sai na kwakwule miki idanu na mayar dake makauniya". Da jin haka ta yi tsaye cik a wajen hade da fashewa da kuka don ta rasa maganar wa zata bi, kowa a cikinsu tsoronsa take. Yayin da su kuma gaba daya suke binta da kallo cikin rashin gane ainahin abinda yake faruwa da ita. Hatta Jamsy dake gefe tana chat a wayarta sai da ta tsaya tana kallon Murja. Ita kuma Murja cikin lokaci kankani ta sake jin wani masifaffen ciwon kai, daga nan kuma bata sake sanin me ke faruwa da ita ba.


Balbaleta da masifa Hajiya Lami tayi tana ta korarta amma tayi shiru haka kuma ta ki motsawa, zuwa can kuma suka ga ta share hawayenta, nan take ta fara dube-dube a falon tamkar tana neman wani abu, kuma sai su ka ga ta nufi dinning ta ja kujera ta zauna. Mama Dije da ta saki baki tana kallonta ta ce, "Lami wallahi wannan yarinyar bata da lafiya ba dai-dai take ba, mu bita a hankali har mu san yanda za'ayi mu rabu da ita lafiya". Hajiya Lami ta ce, "Nima yanzu na ganta kamar wata daban ba ita ba, hallau kinga ta fashe da kuka ta kuma ki yin magana, kai da gaske wannan mahaukaciya ce". Jamsy ta ce, "Wallahi ba wani hauka hankalinta garas, iskanci ne kawai". Harara ta ga Murja ta watso mata, hakan yasa tayi saurin gimtse baki hade da cigaba da danna wayarta.................


Yan Aljanar Fatima Fans WhatsApp ne suka dauki nauyi kawo muku wannan Page din 😅 ni kuma na gaji

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments