ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 40


🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/qLO_AZQzBf0

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-40-hausa.html


*^ Part 40 ^*

Shiru yaji karen bai cijeshi ba, don haka ya bude idonsa, bisa mamaki sai gani yayi babu kowa a cikin ofishin nasa. Tashi yayi ya nufi kofar fita a hankali yake tafiya har ya kama kofar ya dan bude a tsorace. Yayi mamaki da bai ga Murja da karnukan ba a wajen, don haka ya fara kiran sunan yaranshi yan sanda amma shiru baiji motsin kowa ba, nan take ya fara leka ko wane ofishi da kuma bayan kanta inda suke ajiye masu laifi baki daya ba kowa. Kai tsaye ya fito tsakar harabar police din ta su, a tsakiyar wajen ya fara hango mutum a tsugunne kuma ya lulube da bak'in zani. Kai tsaye ya nufi wajen a tsorace yana tafe a hankali yana kiran sunan yaranshi yan sanda. Har ya karasa wajen baiji anyi magana ba, kai tsaye ya nufi gun a hankali ya kama zanin ya yaye shi, mace ya gani a durkushe ta rufe fuskarta da tafin hannuwanta, "Wacece? Baiwar Allah? Wacece ke?". Ya dan jima yana tambayarta tayi banza da shi, zuwa can kuma ta bude fuska hade da yage wangalelen bakinta tayi masa dariya, hakorata da basu wuce a kirga ba suka bayyana a cikin bakin wanda suka karawa fuskar tata muni da ban tsoro. Baya yaja hade da cewa, "Wayyo Allah na, Ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba". Ta bata rai hade da cewa, "Nura me kake nufi ba ka gane ni bane?". 


A tsorace ya ce, "Wallahi ban sanki ba ma balle in ganeki, don Allah mutum ce ke ko aljana? Me yasa na ga babu kowa a ofishin nan gaba daya kaina ya kulle na rasa gane me ke faruwa". "Haba Nura na, ni ce fa, Hajara tsohuwar budurwarka, karka ce baka ganeni ba, yaran ka kuma ni na koresu gaba daya saboda yau ina son musha soyayya mu baiwa juna kulawa da hirarraki irin na soyayya masu sosa zukata". Jin muryata yake ba dadi tamkar ana buga garwa, idan ya kalli fuskarta kuma sai yaji wani irin tsoro ya da bai-baiyeshi. "Wallahi ni bani da wata budurwa mai suna Hajara, matata daya Feenat kuma ita kadai na taba yin soyayya da ita". Tsawa yaji an daka masa, "Kaii! Nura karya kake, ni zaka yaudara? Sau nawa kana cewa ba zaka rayu a duniyar nan idan ba ni ba, amma shine ka yaudareni kayi aure?". Kuka ya ga ta fashe da shi, nan take ya fara mika hannu yana so yayi mata magana amma ya rasa abinda zai ce mata ma. Gani yayi ta mike tsaye, yayin da ya kalli kwala-kwalan idanunta sai ya ga maimakon hawaye wani bakin abu ne ke zubowa. Bata rai tayi sannan ta zaro wata wuka daga cikin zaninta ta daga wukar hade da cewa, "Ni banga amfanin rayuwata ba tunda ka yaudareni Nura, yanzu zan kashe kaina kuma kaima in kasheka tunda na rasaka to kowa ma ya rasa". 


Tana gama fadin hakan ya ga ta cakawa kanta wuka, nan take jini yayi feshi, ta kwala ihu, sannan ta zube a wajen cikin jini. Kan Dpo ne ya kwance nan take kwakwalwarsa ta dingi juyawa, gaba daya ya rasa gane me ke faruwa da shi, tsunkulin jikinsa yayi da hannu yaji zafin, abinda ya tabbatar mai ba mafarki yake yi ba kenan. Amma ya rasa gane dalilin da yasa abubuwa suke faruwa a gareshi tamkar a mafarki, to shi wannan matar ma a ina ya santa da har take ikirarin ita tsohuwar budurwarsa? Gashi dai ta cakawa kanta wuka da alamu kwakwalwarta ta tabu ne, in ba mahaukaci ba waye zai kashe kansa? Ko da yake shi dama yana kokonto a kan matar anya mutum ce. Tunanin da yake a zuciya ne ya katse bayan ya ga jini na ta malalowa daga cikin matar inda ta cakawa kanta wuka. Kai tsaye yaje kusa da ita yana karewa fuskarta kallo, bisa dukkan alamu ta mutu, domin babu alamar lumfashi a tare da ita. A hankali ya kara zare ido hade da kallon fuskarta da kyau, domin gani yayi fuskarta ta rikide ta koma fuskar Murja. Bai ankara ba ya ga ta bude ido ta kalleshi, ai kuwa a tsorace ya fadi kasa daga tsugunnen da yaki, nan take ta tashi zaune hade da kyalkyalewa da dariya. Zuwa lokacin shi kuwa tsoro ya gama cika zuciyarsa, ji yayi kawai tana cewa.


"Sun kwace min gidana, yanzu na koma cikin gidana, ina kokarin kwato gidana shine ka fito dani, kuma ka zo ka caka min wuka a ciki, so kake ka kasheni". Ta karasa maganar da karfi. Kallonta yake cikin tsoro yana jan jiki da baya-baya a zaunen da yake, gaba daya ya kasa gane me take nufi, in ya fahimta dai-dai kenan wancan matar ta bace kuma ta bar zancen ita tsohuwar budurwarsa ce yanzu ta juye ta zama Murja kuma tana masa maganar gidanta. Kamar zaiyi kuka ya farin fadin, "Na rantse da Allah bani na caka miki wuka ba, ke kika caka da kanki". Mikewa tayi tsaye, ta zare wukar dake cikinta nan take jini ya cigaba da zuba ta nufe shi a hankali hade da daka masa tsawa ta ce, "Karya zanyi maka?". Da sauri ya ce, "Aa ba karya kika mun ba". "To wa ya caka min wukar in ba kai ba". "Nine na caka miki". "Wato kun hada baki ne da Hajiya Lami kuna so ku kasheni ku cinye mun gida ko?". Cikin tsoro bakinsa har yana rawa ganin ta kusan karasowa gareshi ya ce, "Tsautsayi ne yasa na caka miki don Allah kiyi hakuri ki yafe mun". Dariya yaji ta kyalkyale da ita hade da cewa, "Ka zabi daya in rama da kaina ko kuma in baka wukar ka rama mun". Shiru yayi yana nazari bayan ya ma rasa abinda zai ce mata, wukar ya ga ta wullo masa a gabanshi sanna ta ce, "Dauka!". Da karfi tayi maganar don haka ya dauka da sauri hannunsa na karkarwa, "Maza ka caka a cikinka". Cikin tsoro ya fara fadin, "Don Allah don annabi kiyi hakuri, karki kasheni Ina da mata da 'ya'ya wallahi idan na mutu babu wanda zai kular min da su". Ji yayi ta ce, "Rufe min baki, Allah ne zai kula da su bayan ka mutu, karka bata min lokaci kayi gaggawar cakawa kanka ko kuma in karba da kaina in cakama".


Hannunsa na karkarwa ya daga wukar ya kalleta, sai walkiya take saboda kaifi, ya sake kai dubansa ga Murja da ta zazzare masa ido alamun babu wasa. Ido ya rufe ya daga wukar sannan ya saita cikinsa ya caka wuka, dai-dai lokacin ya kwala wani uban ihu!. Yan sanda ne zagaye da shi, suna ta kira "Sir! sir Lafiya kuwa?". Yayin da shi kuma Dpo sai mimikewa yake yana zunduma uban ihu!. Wani daga cikin yan sandan ya dubi Murja hade da cewa, "Ke me ya faru da Sir? Me kikayi masa ne". Banza tayi masa tamkar ba da ita yake ba, ya kara cewa, "Ke magana nake miki fa, idan wani abu ya sama Sir na rantse da Allah sai kin yabawa aya zakinta". Nan ma shiru tayi bata ce kala ba, a dai-dai lokacin sukaji Dpo ya kwalla uban ibu hade da rike gefen cikinsa. Kanshi yaji ya fara bala'in ciwo kamar zai tsage, ya rike kan ba'afi mintuna biyu ba kuma sai yaji komai ya fara dawowa. A hankali ya daga idonsa, ya ganshi kwance kan tiles ga yan sanda a kanshi suna mishi sannu. Da sauri ya fara laluba cikinsa ganin ba komai ya sauke ajiyar zuciya, idanunsa ne suka suaka a kan Murja dake zaune a kan kujera tana kallon wani gefe, zabura yayi hade da cewa, "Don Allah dan Annabi kiyi hakuri, wallahi na tuba ba zan kara ba, bansan haka lamarin yake ba". 


Ko kallonshi batayi ba balle ta tanka mishi, daya daga cikin yaranshi Yan Sanda ya ce, "Sir. wai lafiya? Idan baka jin dadi ne mu tafi asibiti tun dazu kake ihi hankalinmu gaba daya ya tashi". Mikewa yayi tsaye duk zufa ta jika kayan jikinsa hade da cewa, "Lafiya kalau maza ku fita daga office din nan ina so zamuyi magana da ita". Har zasu musa ya daka musu tsawa, hade da cewa, "Get out nace". Dole ta sa suka fita ba don sun so ba, domin sun lura ogan nasu kamar ba a hayyacinsa yake ba. Suna fita ya nufi wajen Murja hade da cewa, "Nasan duk abubuwan da suka faru dani suna da alaka dake, to don Allah kiyi hakuri wallahi na fasa tsare ki, mun sallameki zaki iya tafiya yanzu". Ta juyo fuskarta da alamar rashin fahimta hade da cewa, "Yallabai bangane me kake nufi ba fa, a tunanina ni mai laifi ce to banga anyi min wani hukunci ba naji kuma kana cewa ka sallameni". Wata yar dariya yayi mai kama da yake, daga ka ganshi kasan cewa a tsorace yake, "Eh wallahi ai mun yafe miki ne, yaron da kika karya ma ni zan dauki nauyin komai mun yafe". 


Shiru tayi bata ce komai ba, yayin da shi kuma ya cigaba da bata hakuri, ita kuma ta ce bata yi masa laifin komai ba, ji yake tamkar a kan wuta yake don ya matsu ya bar office din ko kuma ita ta hakura ta bar office din, "Fitsari nake ji zan dan zagaya bandaki, daga nan kuma zansa a sallameki dama ba'a rubuta miki file ba kuma zansa su daukeki su mayar dake gida". Har ya nufi kofa ya fara tafiya ta ce, "Ina ce wannan bandaki ne na cikin office". Ta nuna wajen da hannu, da sauri ya juya ya ce, "Eh dake babu ruwa a ciki kuma lokacin sallah yayi ina son in gaggauta kar in makara". Bata ce masa kala ba ya fita da sauri, yana zuwa ya umarci yaransa dake bakin kanta a kan su sallami Murja kuma su dau mota su mayar da ita gida, ya gargadesu karsu kuskura su aikata mata ba dai-dai ba. Su kansu sunyi mamaki jin furucin nasa amma ba yadda suka iya dole su bi umarninsa, haka suka dauki Murja suka mayar da ita har kofar gida.
Suna zaune a kofar gida bayan sun gama sallah suka ji ana bubbuga gida, bayan ya juya ya ga Murja ce a kofa gabanshi ne ya fadi..........


πŸ™„ Mutane sun zo wajena ina typing, ana surutu ba zan iya ba mu hadu gobe

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments