ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 39

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/qLO_AZQzBf0

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-38-hausa.html


*^ Part 39 ^*


Su ukun baki daya suka tsaya suna kallon ikon Allah, yayin da Bala ya durkushe yana ta fadin ta karyani. Sun dan jima a haka daga bisani dan sanda daya ya ce, "Kai-kai-kai... Lalai wannan mahaukaciya ce, ofisan kika lankwasawa hannu?". Kai tsaye ya nufeta da nufin jawota, wata tsawa ta daka masa wacce ta sa ya tsawa wajen ya kasa kara ko da tako daya ne. "Idan ka kuskura ka taba ni sai na balla ma hannu". Tsaye sukayi suna mazurai, su Hajiya Lami kuwa tuni sun haye sama suna lekowa ta kasan matakala. Daya ne ya ji wayarsa ta kama ringing, ya fiddo hade da karawa a kunne, yana fadin "Hello sir, eh mun zo sir, aa wallahi bamu kamata ba amma tabbas mahaukaciyar ce, ina ga sai ka zo da kanka yanzu haka ta karyawa Bala hannu wai don ya kama mata hannu, to sai ka zo sir". Yana fadin haka ya kashe wayarsa hade da cewa, "Sir ne ya kira waya yace gashi nan zuwa". Bayan mintuna sha biyar sai gasu sun iso kai tsaye suka fado falon, Dpo ne da wasu yan sandan guda biyar. Hajiya Lami na jin shigowarsu ta saukko daga benen ta na fadin, "Yauwa Allah ya kawoka, don Allah ayi kokari a fitar mana da wannan mahaukaciyar. 


Kai tsaye hannun Bala yaje ya kama yana dubawa sannan ya daga kai ya kalleta, hankalinta kwance tana kallo a tv ko kallonsu batayi ba balle ta nuna alamun ta ji shigowarsu, "Keeeee!". Ya daka mata tsawa, shiru tayi ba tare da ta dubeshi ba balle ta amsa. "Ke magana nake, ke yar gidan uban waye da har zaki kama hannun dan sanda ki karya? Kinsan kuskuren da kika aikata kuwa". Shiru tayi nan ma bata tanka ba, a fusace ya nufeta da nufin ya fara ball da ita, juyowa tayi ta kallesa idanunta dauke da wata irin harara da sai da ta sa Dpo da kansa yaji faduwar gaba, domin idanun tamkar zasu fado kasa. "Yallabai karka soma taba ni in ba so kake abinda ya faru da shi ya faru da kai ba". Turus ya ja ya tsaya yana nazari a kwakwalwarsa, shi sai yanzu ma yake kara karewa yarinyar kallo, taya ma akayi ta iya karya Bala, gaba daya batayi zubin masu karfi ba. Yaranshi ya kalla hade da cewa, "Kai kun tabbata itace ta karya Bala?". "Kwarai da gaske sir wallahi itace, kuma da hannu ta karyashi ba da wani mabugi ba". Ya kalli wasu daga ciki hade da cewa, "Ku dauki Bala a mota ku kaishi asibiti". Ya juya ga Murja hade da cewa, "Ke kuma ba hauka ba, ko sama kike cizo yau zan nuna miki karshen hauka idan har baki tashi kika biyomu office ba". 


"Me zanyi maka a office din?". "Idan munje zaki gani". Murja ta mike tsaye hade da cewa, "Muje office din, ina fatan ba zakayi ladamar tayar dani daga gidana ka kaini ofishinku ba". Hajiya Lami ta ce, "Yauwa Dpo Nura ai nasanka ba wasa, wallahi wannan mahaukaciyar ba karamin ci mutunci tayi mana a nan gidan ba, haka kawai ta fado bamu san daga inda take ba, don haka don Allah ku tabbatar kunyi mata irin horon da ko kalar gidan nan idan ta gani zata canza hanya ba ma tayi yunkurin shiga gidan ba". Dpo yayi gyaran murya hade da cewa, "Karki damu Hajiya ai yanzu laifuka biyu ne a kanta, kinsan hukuncin dukan dan sanda kuwa a hukumance, balle ma ace karyawa, dan sanda fa ta karya". Wasu yan sanda guda biyu ya kalla hade da cewa, "Me kuke jira ne? Oya ku sakata gaba kuje mota gani nan zuwa". Gaba Murja tayi, har ta fara tafiya ta juyo hade da cewa, "Idan anyi abincin dare kar a manta da nawa, don komai dare yau a gidana zan kwana, idan kuma aka cinye abinci ba'a ajiye mun ba na rantse da Allah kowa sai yaji a jikinsa a cikin gidan nan". Hajiya Lami ta daga murya hade da cewa, "Ba zaki dawo gidan nan ba insha Allah, mahaukaciyar banza". Haka dai su Murja sukayi waje, masu gadi ma har bakin kofa suka bi yan sandan suna cewa, don Allah su tabbatar Murja bata dawo gidan ba. 


Bayan su Murja sun fita, Hajiya Lami ta ce wa Dpo ya zauna tana zuwa, nan ta haura sama ta barshi da Mama Dije zaune tana ta kora masa bayani. Ba jimawa ta fito da kudi cikin takarda ta mikawa Dpo hade da cewa, "Yallabai wanna tukwicinka ne, don Allah ayi duk mai yuyuwa a hana yarinyar nan dawowa gidan nan, mahaukaciya ce ziryan, wai har cewa take wannan gidan nata ne, wai itace Murja diyar mai gidan, zantuka dai marar kan gado". DPO Nura yace, "Karki damu Hajiya, ki kwantar da hankalinki insha Allah daga yau ko nuna mata gidan nan akayi akace ta shigo sai tayi tunani sau uku kafin ta shigo, domin kamar yanda na fada miki laifinta ma ya karu tunda ta karya mana officer ina mai tabbatar miki sai tayi gidan yari"? Mama Dije ta ce, "Yauwa dan nan don Allah idan so samu ne ayi mata daurin rai da rai". Zare ido yayi hade da cewa, "Mama ai sai wanda yayi kisan kai ko wani mummunan aiki makamancin haka sannan ake yankewa hukuncin daurin rai da rai". Mama Dije ta ce, "Yo wannan idan har tana irin haka ai har kisan kan ma sai tayi". Nan dai Dpo yayi musu sallama ya tashi ya tafi.



Zaune take a kan binci sai zare ido take tana kallon mutane masu shige da fice, da kuma masu zuwa kan kanta ana rubuce-rubuce. Ita dai a cewarsu sai Dpo ya zo zaiji da lamarinta don ya ce ta jirasa. Tana nan zaune ta ga wucewar Dpo din amma an kusan awa daya bata ji an kirata ba, kai tsaye Murja ta nufi kan kanta hade da cewa dan siririn dan sandan da ta samu yana rubuce-rubuce, "Bawan Allah na ce ko zakayi wa Dpo magana ne, ya barni ina ta jira ai gwara ya sallameni in koma gida". Tsawa ya daka mata hade da cewa, "Ke baki da hankali ne? Ko dan kinji mutane suna cewa ke mahaukaciya ce, bari kiji kallon farko da nai miki na gane cewa ke ba mahaukaciya bace, don haka Dpo ba yaronki bane balle ki umarce shi da ya kulaki a lokacin da kika so. Ke bude idonki da kyau ki karewa inda kike kallo, nan fa ba gidan ubanki bane, maza koma ki zauna". Murmushi kawai Murja ta kalleshi tayi irin murmushin dake bayyana cewa, "Rashin sani ya fi dare dubu". Ba tare da gardama ba ta koma ta zauna tana cigaba da kalle-kallen mutane. Sai da aka shafe wani rabin awa sannan aka aiko Dpo na kiranta. Kai tsaye ta fada ofishin tana zuwa tayi mai tsaye kerere hade da cewa, "Gani". Kallonta yayi cikin takaici tamkar ya tashi ya kwada mata mari, amma sai ya daka mata tsawa hade da cewa, "Idan baki zauna a kasa ba sai na sa an babbalaki a cikin ofishin nan". Bisa mamaki sai gani yayi Murja ta zauna a daya daga cikin kujerar da aka tanada domin bakin Dpo. Girgiza kai yayi da ya tuno cewa, Hajiya Lami ma tace mahaukaciya ce. 


"Ya sunanki? Kuma me ya kaiki gidan mutanen da basu sanki ba har kika iya daga hannu ki dake su?". "Sunana Murja Rabe, kuma ba gidan mutane bane, gida na ne sune ma ya kamata a tuhumesu dalilin da yasa suke zama a gidana ba tare a izinina ba". Kallonta yayi ido cikin ido hade da zare mata ido ya ce, "Ke kina da hankali kuwa". Ta ce, "Taya kake so na tabbatar maka ina da shi ko bani da shi". Kudi ya fiddo naira dubu da dari biyar daga aljihunsa, ya daga sama yana nuna mata hade da cewa, "Nawa ne wannan?". "Dubu daya da dari biyar ne". Ya ce, "Idan aka kara dari uku a kai fa?". "Ya zama dubu da dari takwas". Ya jijiga kai hade da cewa, "Eh lalai da ragowar hankalinki, ko dake kudi shegune sai ka samu mahaukaci ma ya san kudi". Ya sake kallota hade da cewa, "Amma fada min taya akayi gidan ya zama naki". Murja ta gyara zama hade sa cewa, "Tun ina yarinya na sama lalura a kwakwalwa na bar gidan, yanzu kuma na sama lafiya gani na dawo, ina tunanin ba laifi bane don na karbi gidana da duk dukiyata ko?". Dariya ya kyalkyale da ita hade da cewa, "Tabbas akwai yar Alhaji Rabe mai suna Murja da ta bace, don lokacin ma Hajiya Lami ta kawo report, suna miki kallon mahaukaciya ashe ke cikakkiyar yan damfara ce, bana son bata lokaci yi gaggawa ki fada mun abokan aikinki wanda kika hada baki da su kuke son damfarar Hajiya Lami". 


Murja tayi murmushi hade da cewa, "Ina fada maka wannan maganar ne don kawai ka tambaya, amma ba don ina bukatar wani taimako daga gareka ba, domin ni zan karbi gidana da dukiyata da hannuna". Dpo ya dubeta da kyau ya ga lalai da gaske take maganarta, lamarin da ya kara bashi dariya kenan, "Yanzu misali idan ma kotu zaki je, minene shaidar cewa kece Murja yar Alhaji Rabe?". Murja ta ce, "Ai nice shaidar kaina". Dariya ya kara kyalkyalewa da ita, daga bisani kuma ya bata rai hade da cewa, "Ba wannan ba kinsan hukuncin laifin da kika aikata na karya hannun dan sanda kuwa?". Murja ta ce, "Ban sani ba amma na san hukuncin taba jikin matar da ba taka ba, kuma shi nayiwa dan sandan". Tsawa ya daka mata hade da kara murtuke fuska ya ce, "Kee! Nan ba wajen wasa bane, bari na fara tabbatar miki da cewa kin aikata babban laifi". Juyawa baya yayi, ya daukko wani katon bak'in kulkinsu na yan sanda kai tsaye ya nufi Murja da nufin fara dukanta.



Kanshi yaji yayi wani irin nauyi, nan take yaji ya fara jin jiri tamkar zai fadi, haka ya koma kan kujera ya zauna saboda jin da yake duniyar baki daya tana juyawa. Da karfi ya rike kanshi hade da runtse idanu saboda yadda kan nashi yayi wani irin juyawa. Bayan yaji kan ya sassauta a hankali ya bude ido, zare ido yayi bayan ganinshi shi kadai a tsaye a cikin office din. Ba wannan ya bashi mamaki ba sai ganin babu komai a ciki hatta kujerar da yake kai kuma babu Murja. A hankali yake jin sautin kukan mutum a ta kofar fita daga ofishin nashi, mutum din ma mace, don haka ya nufi kofa bai kawo komai a ranshi ba ya bude office din. Kara ya saki hade da yin baya kadan tamkar zai zura a guje. Murja ya gani kwance a gefen kantar yan sanda, karnuka na cin naman jikinta, jini ya bata ko ina a office din ita kuma sai kuka take a hankali tana ture kan bakaken karnukan yayin da su kuma suke kara kai mata farmaki hade da yagar naman jikinta. "Ka taimaka min zasu kasheni". Abinda ya ji ta fada kenan, ai kuwa da yin maganarta ya ga karnukan sun juyo gaba daya sun kalleshi, sai da gabanshi yayi mummunan faduwa bayan ganin idanunsu da bakunansu saboda muni da rashin kyan gani. Kafin yayi wani yunkuri tuni karnukan suka nufeshi da masifaffen gudu. Ihu ya kwada hade da jan kofar da karfi ya rufeta ya makala kubobi hade da komawa daga jikin bango yana haki.


Yana jinsu suna dukan kofar da kawunansu tamkar zasu karya kofar, yayin da tsoronsa ya kara tsananta. Zuwa yayi ya danne kofar da dukkanin karfinsa, nan take ya fara kwalawa yaranshi yan sanda kira, amma yaji shiru, tamkar yayi kuka haka yake danna kofar don ganin kofar dake jikin kofar tana gaf da karyewa, kafin yayi wani yunkuri sai ji yayi sun banko da karfi nan take kofar ta karye, shima saboda yana jikin kofar can yaji an watsar da shi. Da ganin lamarin yasan aikin aljannu ne don haka tun daga kwancen da yake ya fara kwada ihu hade da tashi ya nufi bandaki dake cikin ofishin nashi. Cikin rashin sa'a kafin ya karasa kare daya ya cafki kafarsa da baki nan take ya jashi kasa, sai gashi ya fadi kwance. Dayan karen ne yayi tsalle hade da wangame baki ya cafki wuyan Dpo shi kuwa ya fasa wani uban ihu da bai taba yjn kalarsa ba tunda yake a duniya...................



☹️ Yau makara nayi,


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments