ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 38

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/bUybxojRV7g

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-38-hausa.html


*^ Part 38 ^*

A hankali suke kare mata kallo, tabbas duk wanda ya san Murja lokacin da tana yarinya, idan ya ganta yanzu ma zai ganeta duk da kasancewar ta dan rame. Dariya Lami tayi hade da cewa, "Ke yarinya karki dauki mutane mahaukata mana, wace Murja kike magana? Murjar da ta dade da mutuwa, ko kina so ki ce ke din fatalwarta ce?". Mama Dije ta ce, "Ke kika tsaya kina sauraron maganarta, ina masu gadin nan ku shigo ku ma yarinyar nan dan banzan duka sannnan ku fiddata waje, kaji shirmen banza ba Murja ba Murjalo". 


Murja ta ce, "Ok ashe ku a tunaninku tuni na mutu, shiyasa kuka zo kuka bararraje kuke cin dukiyata yadda kuka ga dama, to gani ban mutu ba, hauka ai ba mutuwa bane ana warkewa kamar yadda nima na warke a halin yanzu". Gaban Hajiya Lami da Mama Dije ne yayi mummunar faduwa, lokacin da maganar Boka Kare Dangi ta dawo musu kwakwalwa tamkar yanzu yake musu maganar, inda yake cewa, "Hakika zan yi muku aiki mai matukar kyau tunda kuka sauke mun manyan kudade haka, aikina kamar yankan wuka ne sha yanzu magani yanzu, yarinyar nan a yau zata haukace. Amma aikin da zanyi muku yana da sharadi, tabbas idan sihirin nan ya karye wacce akayiwa zata sama lafiya ku kuma ko bayan lokacin da shekara ne wani mummunar lamari zai faru da ku, watakil a kan dukiyarku ko a lafiyar jikinku, ko kuma ma yayi sanadin rayuwarku, don haka wannan ne sharadin idan har kun aminta, duk da kasancewar karyewar asirin abu ne kusan marar yuyuwa".


A hankali Hajiya Lami ta taka kusa da mahaifiyar tata, cikin rada ta ce, "Mama ni fa naji gabana ya tsananta da faduwa, Kamar yanda na fada miki gabana na yawan faduwa a cikin yan kwanakin nan, kuma a duk sanda na kalli wannan yarinyar sai naji gabana ya fadi". Mama Dije itama cikin rada ta ce, "Ke gabanki ya daina faduwa ba ita bace, Murja ta dade da mutuwa, babu mahalukin da zai iya rayuwa cikin tsananin hauka har na tsawon shekara 18. Ina mai tabbatar miki kawai irin mutanen nan yan yaudara ne zasu je su samo mai kama da Murja domin su damfaremu kudade, amma ba wasa zamu tsaya yi mata ba maza a fitar da ita waje". Dai-dai lokacin su Sunusi suka shigo falon, garada da su har su hudu, da ganinsu Hajiya Lami ta nuna Murja da ke zaune tana kallon sunnah tv da ta kamo hankali kwnace, "Ku lakadawa wannan yarinyar duka sannan ku dauketa ku fitar da ita daga gidan nan, duk wanda yayi muku magana ku ce ni ce na sa ku". 


Kai tsaye suka nufeta yayin da suka isa gabanta sukayi tsaye suna mata muzurai, d'aga kai tayi tana kare musu kallo, tubarkalla kattai ne na gaske wanda ita kanta tasan cewa su dageta sama su fitar da ita waje bayan sun bata dan banzan kashi ba wani abu mai wahala bane a wajensu. Tsawa Mubarak ya daka mata hade da cewa, "Ke tashi ki fita daga gidan nan". Banza tayi da shi hade da kauda kanta ta cigaba da kallon TV, sun dan jima suna mata magana amma tayi ko in kula da su. Hajiya Dije ta ce, "Wai me kuke jira ne da ita? Aka ce ku zaneta yadda gobe ko ance ta shigo gidan mutane kafin ta shiga sai tayi tunani sau biyu". Da gama fadin haka Sunusi ya zare belt din kugunsa hade da nufarta yana hura hanci dama haushinta yake ji. Bayan ya nanade karshen belt din a hannunsa yadda kan belt din na karfe shine ke reto a kasa, ya daga da niyar zafgawa Murja, caraf yaji an rike belt din hade da ja da karfi dole ta sa ya saki belt din don ganin yana neman faduwa. Murja a fusace ta ce, "Wato duk marin da nayi muka a baya bai isheka a matsayin gargadi ba, to bari nayi muku gargadi da irin yaren da zaku fi ganewa. Da fadar haka ta nannde belt din a hannunta, Sunusi na tsaye yana kallonta ya ji ta lafta masa kan belt din a kai. Nan take ya rike wajen yana fadin, "Kai-kai! kai-kai! Ni kika....". 


Saukar wani dukan da yaji ne ya hanashi karasa fadin abinda zai fada. Zai kara wata maganar ya sake jin wani dukan a baya, wanda hakan ya tilasta masa zurwa a guje yayi waje. Murja kuwa sai ta cigaba da dukan sauran tamkar ta sama 'ya'yanta. Mubarak da aka zura masa belt a wuya saboda tsabar zafin dukan ya rikice, ai kuwa da gudu ya nufi bayan Mama Dije maimakon ya fita daga falon, Murja kuwa ta bishi, a kokarin ta zafgawa Mubarak bulala ta samu Mama Dije a baya ta zafga mata, ai kuwa Mama Dije ta saka ihu hade da rugawa ta nufi saman bene. Mubarak kuwa da Murja haka suka cigaba da zagaye falon tana dukansa a cikin hakan kuwa duk wanda ta tarar sai ta zura masa belt babu wanda bata zugawa belt ba ciki kuwa harda Hajiya Lami, cikin lokaci kankani falon ya hargitse Hajiya Lami, Khalil, da Jamsy suka rika rige-rigen haurawa saman bene suna sosa baya. Mubarak kuwa yayi waje sai a lokacin Murja ta rabu da shi, ta dawo falo ta zauna ta cigaba da kallonta hade da cewa, "Ashe ma ku yan iskan karya ne".


Mama Dije dake cikin daki tana leke daga kofa, ganin Khalil ya rugo da gudu yasa ta fada cikin dakin ba tare da ta tsaya ko rufe kofar dakin ba, kai tsaye ta fada cikin bandaki ta rufe kofar. Suna shiga dakin su ka mayar da kofa suka rufe, Hajiya Lami ta cewa Khalil, "Ina Mama take?". Ya dubeta yana lumfashi daya-daya ya ce, "Na dai ganta tana leko kofa, amma da na shigo ban ganta ba". Ji sukayi ance, "Gani nan". Suka juya gaba daya suka ga Mama Dije ta fito daga toilet tana sosa baya. "Ina! Ina! Na rantse da Allah ba zata sabu ba bindiga a ruwa. Wannan yarinyar duk inda ta fito mahaukaciya ce, yanzu na karasa tabbatarwa, in ba mahaukaciya ba ya za'ayi ki shigo gidan mutanen da basu sanki ba baki sansu ba, ki ci kisha kuma ki dinga dukan yan gidan kamar kin sama jakai. Dubi fa dan Allah duk tsufana haka yarinyar nan ta ware karfi ta zafga min belt rabon da ayi min irin wannan bulalar tun ina yar karama". 


Hajiya Lami ta ce, "Ai ni wallahi tunda na ji ta ce wai itace Murja kuma gidan nan nata ne, na tabbatar da cewa mahaukaciya ce". "Ba wannan ba yanzu duk yadda za'ayi ayi a fitar da yarinyar nan daga gidan nan, wannan ai sai ta kashe mutum idan ba'ayi gaggawar daukar mata ki ba, to maza wallahi tunda Lawal din baya nan ke kiyi iya kokarinki tunda kinsan mutane, sojoji zaki kira ko yan sanda koma wata tsiyace ke kika sani amma ki tabbatar yarinyar nan bata kara minti goma a gidan nan ba". Hajiya Lami ta ce, "Yanzu kuwa, zan sa ayi maganinta". Ta fiddo waya tana bincikar lambar da zata kira, Khalil ya ce, "Mom ashe mahaukaciya ce har nake mata magana dazu, kinga yadda ta rika dukan mutane kuma wallahi shegen gudu gareta don ina kallo ta tsallake kujera". Jamsy ta ce, "Ni ban taba ganin mahaukaciya mai kama da masu hankali ba sai yau". 


Dai-dai lokacin aka daga wayar da Hajiya Lami ta kira, cikin kaguwa ta ce, "Yallabai, yauwa sannu da aiki, don Allah ina bukatar ma'aikatanka kamar mota guda haka, eh, don Allah su taho da shirin ko ta kwana, saboda wata mahaukaciya ce ta shigo mana gida gata nan tana ta dukan mutane don Allah su zo su fiddata, in ma da kanka zaka zo ka zo don Allah". Tana gama yin wayar ba jimawa mai gadi yaji ana buga kofa, yana zuwa ya bude ya ga yan sanda su hudu, bayan sun ce Hajiya ce ta sa aka kira su zasu fitar da mahaukaciya, nan take yayi musu iso zuwa falon. A zaune take hankalinta kwance ta mayar da hankalinta baki daya ga TV su Hajiya Lami daga saman bene suke lekenta suna son fitowa amma suna tsoronta. Jin mai gadi yayi sallama hade da cewa ga yan sandan sun iso, ya sa Hajiya Lami ta yi saurin saukkowa kasa tana fadin, "Yauwa ku shigo gata nan su shigo su fitar da ita". Yan sandan ne suka kutsa kai cikin falon bayan sun gaishe da Hajiya suka duba ko ina basu ga alamar mahaukaciyar da aka kira su fitar ba, domin idanunsu duk mutane masu hankali suka gane musu. Daya ya dubeta hade da cewa, "Hajiya Dpo ne ya turo mu, yace muyi sauri mu zo zamu fitar miki da mahaukaciya mai dukan mutane, shiyasa ma in kika lura gaba daya mun sako rigar bullet, a nuna mana mahaukaciyar sai mu fitar da ita". 


Hajiya Lami ta nuna Murja da hannu hade da cewa, "Ga ta nan a zaune". Suka kalleta gaba daya amma sam batayi musu kama da mahaukaciya ba, amma haka suka karasa gabanta hade da cewa, "Ke mahaukaciya tashi mu wuce office". Banza tayi musu tamkar bata ji, a dai-dai lokacin aka sako karatu a sunna Tv da take kallo, nan take ta fara bin surar da ake karantawa tana kwaikwayon kira'a. Yan sandan suka kalli juna, daya yace, "Dama mahaukata na karatu ne?". Dayan ma ya ce, "Nima dai abinda zan tambaya kenan". Hajiya Lami ta ce, "Wai me kuke jira ne, don Allah ku dauketa ku tafi da ita, mahaukaciya ce tuburan, ku duba falon nan da kyau, zaku ga yayi kaca-kaca to wallahi ita tayi masa haka, a gidan nan babu wanda bata zana da belt ba har ni kaina kuwa". Dan sandan na uku ya rike baki hade da cewa, "Ah! lalai mahaukaciya ce, har ta daga hannu ta daki Hajiya". Na farkon ya ce, "Ke baiwar Allah magana muke, nasan ke ba kurma bace tunda gashi kina bin karatu, amma muna magana kinyi shiru, ki tashi ki fitarwa mutane daga gidansu tun kafin mu ci mutuncinki".


Murja ta dube shi hade da cewa, "Wai dani kake dama? Ai naji kana cewa mahaukaciya ni kuma ba mahaukaciya bace, to na zata ba dani kake ba. Gida kuma ni ce mai gidan don haka ba inda zani sai dai in su ne zasu fita su bar gidan tunda ba gidan ubansu bane na ubana ne". Da jin haka dayan dan sandan ya ce, "Eh lalai wannan bata da lafiya". Hajiya Lami a kagauce ta ce, "Wai me kuke jira ne da ita, ko janta a kasa ne kuyi don Allah ku fitar min da ita daga gidan nan na gaji da ganinta". Dan sanda na uku wanda aka rubuta Bala Ahmed a gaban rigarsa ne ya nufi Murja nan take ya kama hannunta da nufin ya ja ta waje, wani irin ihu ya kwada, wanda ya sa Hajiya Lami, Mama Dije da su Khalil dake bakin bene suka sake haurawa sama da gudu har suna neman faduwa. Su kansu sauran yan sandan sai da suka ja baya suna karewa halin da ake ciki kallo. Murja ce ta kama hannun dan sandan wanda ya riketa da shi, da dayan hannunta ta murda hannun, shine dalilin da ya sa ya kwada ihu hade da zubewa a wajen yana fadin, "Ta karyani- Ta Karyani". Cikin fushi Murja ta ce, "Gobe ma ka sake kama hannun macen da ba muharramarka ba".....................................


🤔 Kamar fa na gaji

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments