*ALJANAR FATIMA BOOK 2*
🧟♀️🧟♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟♀️🧟♀️
By *Kingboy Isah*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/s1yyCcIIF6Y
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-37-hausa.html
*^ Part 37 ^*
Dafe kumatu yayi hade da cewa, "Ni kika mara? To na rantse da Allah sai na gwada miki karshen hauka yau". Da fadar haka yayi saurin fadawa cikin gidan ya nufi dakinsu na masu gadi hade da daukko wata katuwar adda, ita kuwa Murja ta nufi gidan zata shiga dayan ya ta so da gudu zai tare mata gaba ta sa hannu biyu ta ture shi can ya fadi kasa, ya tashi ya kakkabe jiki hade da rufa mata baya cikin gidan. Sai da Murja ta shiga ta kara tabbatar da girman gidan da kalar tsaruwarsa, parts uku ne a gidan na tsakiya shine babba da alamu sauran masaukan baki ne, gefe ga wajen ijiye motoci, ta hangi motaci a kalla sun kai biyar. Irin shukokin dake tsakar gidan da gani kasan gidan masu hannu da shuni ne domin kula da ayyukan gidan kadai na iya lakume manyan kudade a duk wata. A hankali Murja take tafe cikin kwanciyar hankali tana karewa gidan kallo, yayin da ta nufi babban falon mai bene hawa daya, "Ke marar kunya na rantse da Allah ki yi gaggawar fita daga gidan nan ko na sassara miki addar nan". Daga baya ta jiyo mai gadin na fadar haka yayin da ta juyo ta ganshi rike da adda yana barazanar sara mata.
Tsaki ta ja hade da cewa, "Idan ka yarda addar nan ta taba ko da rigar jikina ce sai na sa an kulle duk danginka" hayaniya ce ta yawaita daga dayan bangaren da Murja ke tunanin part din bak'i ne ta ga garada biyu sun fito suna tambayar ya akayi.
Dayan mai gadin ne ya kora musu bayani, yayin da dayan saurayin yayi tsaki hade da cewa, "Kai dai wallahi Sunusi kaji kunya, ace a matsayinka na mai gadi ka kasa tare yan maula a bakin gate, sau da dama Hajiya na yi ma fada akan idan kana barin irin yan maulan nan suna shigowa gidan nan zakayi ta aikinka". Wanda aka kira da Sanusin ya ce, "Ka ga Mubarak karka fada min maganar banza wankin mota da tuka mota ne aikinka a cikin gidan nan, to ka ji da naka ta nan bangaren kuma ka barmu muyi aikinmu, ke yar maula kiyi gaggawar ficewa daga gidan nan kafin raina ya baci". Dayan saurayin ya ce, "Rabu da shi Mubarak da alamu sai mun fara taya su aikin hana mutane shigowa gidan nan, dube su gardawa har biyu amma sun kasa tare mace a bakin gate wannan idan barawo ne ya zo da bindiga ai tserewa kawai zasuyi". Da gama fadar haka suka fashe da dariya shi da Mubarak din, abun ba karamin fusata su Sunusi yayi ba, don haka rai a bace ya karasa gaban Murja dake kallonsu daya bayan daya ya ce, "Na rantse da Allah idan baki fita daga gidan nan ba kama ki zamuyi mu fitar dake da karfin tsiya, bar ganin kina mace". Hannu Murja ta daga ta sake wanka masa mari a karo na biyu, da ganin hakan shima dayan mai gadin yayo gaba da nufin dukan Murja dan ta kaisu bango, zazzafan marin da yaji ne yasa yayi baya hade da dafe kumatunsa.
A fusace Sunusi ya daga adda zai sarawa Murja, daga can nesa yaji ana fadin, "Kai! Kai! Kai baka da hankali ne". Nan take suka juya gaba daya suna kallon mai magana ciki kuwa harda Murja, da sauri wacce tayi maganar ta karaso wajen tana fadin, "Haba Sunusi so kake kayi kisa a cikin gidan nan, yanzu da banyi maka magana ba sai ka sari yar mutane da adda?". Ya kalli matar wacce ta dan kwana biyu hade da cewa, "Haba Nana marina fa tayi, bayan ta shigo gida ba tare da izini ba". "Kayi hakuri mana ka san sha'anin mutane, dama gidan nan ya saba da jama'a ai". Ta kalli Murja hade da cewa, "Baiwar Allah lafiya kuwa wa kike nema na ga ban wayi fuskarki ba a cikin kawayen Jamsy ko yan uwan Hajiya da suke zuwa gidan nan, ban sani ba ko kina daga cikin masu zuwa neman taimako ne". Murja ta ce, "Nima ban wayi fuskarki ba, kuma ni yar gidan ce ko da ke na dade bana gidan bansan adadin bakin mutanen da aka tara ba, don ga wasu ma na gani har suna neman wulakanta ni amma zasu girbi abinda suka shuka nan kusa bayan sun san ko ni wacece".
Matar ta danyi dariya hade da cewa, "Ikon Allah, yau kuma da sabon salon da aka shigo gidan kenan, to bari kiji yar uwa kowa yasan Hajiya da Alhaji Lawal 'Ya'ya biyu kadai garesu a duniya, kinga idan neman taimako kike, zan iya yi miki hanya ki fada min matsalolinki in je in fadawa Hajiya, in kin taki sa'a a taimaka miki. Nima ba kowa bace ni yar aiki ce a gidan nan sunana Nana Fiddausi amma an fi kirana da Nana kawai, kowa yasan irin halin da jama'a suke ciki na talauci a wannan kasar to don haka neman taimako a irin gidajen nan na masu kudi ba laifi bane, amma shigowa gidan mutane haka kai tsaye ba dai-dai bane". Murmushi Murja tayi hade da cewa, "Dukanku bakin zuwa ne babu abinda kuka sani, shiyasa tun farko na bukaci ku kira mun Lami din da kanta, amma tunda hakan ya gagara bari na shiga da kaina ai gidan ubanane yanzu kuma mallakina ne ba na kowa ba". Tana fadar haka tayi gaba su Nana suka bita baya suna tsayar da ita amma ta ki tsayawa, duk wanda ya shiga gabanta kuwa ko kuma yayi kokarin kamata domin ya jata baya sai dai yaji ta gaura masa mari, a haka har ta karasa cikin falon ta barsu tsai-tsaye suna fargabar abinda zai je ya zo bayan sun bar wata ta shiga har falon musamman ma su Sunusi masu gadi gabansu har dukan tara-tara yake.
Da salama ta shiga makeken falon, da katuwar tv suka fara yin ido hudu, sannan ta fara bin farfajiyar falon da kallo, iya haduwa ya hadu kujeru ne ruwan pinky zagaye da falon, a hankali ta kai dubanta ga mutane hudu dake kan kujerun wanda suma ita suke kallo. Murmushi tayi domin ta gane Aunty Lami da Mahaifiyarta Dije. Sauran yan matasa kuma mace da namjji ta tabbata sune 'ya'yan Lami biyu da ake fada, macan na rike da waya tana latsawa cikin yanga shi kuma dan saurayin ya sa faskekiyar waya a gaba yana game ga remote din tv a gefanshi. Ita kuwa Lami ta kara waya kirar iphone a kunne da alamu magana take, bangaren Mama Dije kuma dan tebur ne karami na glass a gabanta, samansa da gasasshiyar kaza a kan faranta dayan farantun kuma da kayan marmari hade da madara mai sanyi a gefe. Kai tsaye Murja ta nufi wajen Mama Dije ta zauna a kujerar dake gefenta hade da jan tebur din dake gabanta, nan take ta fara yagar kaza tana kaiwa a baki, da ido kawai suke binta har suwa wannan lokacin, tukun Mama Dije cikin bala'i ta fara fadin, "Yau na ga rashi kunya da fitsara, ke Lami kina kallo fa, yaushe kika fara ba masu gadi izinin barin mahauka su shigo mana gida? In ba mahaukaciya ba wa zatayi haka?".
Dai-dai lokacin Hajiya Lami ta katse wayar da take ta kalli Nana hade da cewa, "Ke Nana wane dan kutt..uba ne ya ba wannan marar kunyar yarinyar izinin shigowa gidan?". Nana a dan tsorace ta durkusa hade da cewa, "Wallahi Hajiya gaba daya ma'aikatan gidan nan sunyi iya yinsu domin dakatar da ita amma ta ki tsayawa, daga karshe mari ta rika binsu da shi, harda su Sunusi mai gadi. yanzu haka suna kofar falon nan ba yadda suka iya ne suka barta ta shigo". Mama Dije ta kalli Murja da ke cin kaza tana korawa da madara hankali kwance hade da cewa, "Ke marar kunyar yarinya ke yar gidan uban waye da zaki shigo wa mutane gida haka kamar gidan ubanki harda neman wajen zama?". "Ai gidan uban nawa ne" Cewar Murja da ta cika baki da naman kaza. "Mom kinga irinta ko? Shiyasa na ke ce miki ki bar sakarwa yan maulan nan fuska yanzu ga irin abinda ake gudu dubi wata kazama ta zo ta zaunawa mutane a kan kujera, ni da ga yau ba zan kara zama a kan kujerar can ba ma" Khalil ne ya fada haka yana yatsine fuska hade da nuna kujerar da Murja take kai da hannu.
Murja ta dube shi hade da cewa, "Ka ga yara marar kunya, kuna kallon mutane ba zaku gaishesu ba saboda ba'a baku tarbiya ta kwarai ba, ko da yake iyayen naku ma ba tarbiyar ce ta wadace su ba". Ta karashe maganar tana kallon Lami da gefen ido hade da cizgar cinyar kaza. Gaba daya mamaki ya dabai-baye zuciyar Hajiya Lami da Mama Dije, tunda suke basu taba ganin rainin wayo kalar wannan ba. "Kai miko mun remote din tvn nan ko kuma ka canza tasha, marar kunyan yara a gaban iyayenku kun zo kun kamo tashar arna sai rawa suke kusan tsirara ku kuma ko kunya bakwa ji kuna kallo". Tsaki ya ja hade da yi mata banza kamar baiji ba, "Idan na kirga biyar baka kawo min ba sai na ta so na falla maka mari a wajen nan, marar kunyan banza". Murja ta fada har a lokacin dai bai yi alamun zai tashi ba, don haka ta fara kirgawa, tana zuwa biyar kuwa ta mike hade da nufarshi da zuwa ta dalla masa mari da hannunta mai maikon kaza, sannan ta dauki remote din ta ta canza kujera ta koma ta zauna tana latsa Tvn.
Kuka ya saka hade da dafe gefen da Murja ta mare sa, Hajiya Lami ciki masifa ta ce, "Dan lelen nawa kika mara? ke Nana maza fita waje ki tattaro duk yan aikin gidan nan, ki ce na musu izini su shigo har falon nan su ci uban yarinyar nan sannan su dauketa su jefar da ita a waje". Da jin haka Nana ta tashi ta fita da sauri. "Mom wai ita wannan din yar gidan uban waye da zata shigo har falo tana abubuwan da ta ga dama". Jamsy ce ta fadi haka, ita da sai a lokacin ta sa baki. Wata irin harara Murja ta aikawa Jamsy da ta sa sai da tayi gaggawar sunkuyar da kanta kasa. "Kaji yara marar tarbiyya, to me gidan ce, kuma yar mai gidan dan uwarki. Ko uwar taki bata tafa fadi muku cewa gidan nan ba nata bane na Murja ne yar mai gidan". Da jin haka Mama Dije da Hajiya Lami suka zabura tamkar wanda aka tsirawa allura. Mama Dije harda mikewa tsaye tana kara karewa Murja kallo................
Ku ma na gaji
Muje zuwa
Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group
Wa.me/+2348096831009
😍