*ALJANAR FATIMA BOOK 2*
🧟♀️🧟♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟♀️🧟♀️
By *Kingboy Isah*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/bUybxojRV7g
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-36-hausa.html
*^ Part 36 ^*
Nima No Editing 😆
Cikin sauri irin nasu ta gocewa bullet din, yayin da zai kara harbawa tayi saurin rike kan bindigar hade da dagata sama, yana harbawa bullet din yayi sama, nan take ta kwace bindigar hade da juyawa ta bayanshi ta dungura masa bindiga a keya sannan ta ce, "Ashe so kake ka riga su mutuwa, to zan cika ma muradinka kuwa, kai zan fara kashewa". Hawayen takaici ne suka zubo daga idanun Goje, ba koma yake wa takaici ba illa kuskuren da yayi na kasa kashe Safuratu, in da ya kasheta da hatta sauran uwayen daban su Dodo sai sun rika girmamashi. Don haka yanzu yasan kwanansa sun kare ba lalai ya tsira ba, "Me kike jira ki kashe ni din, ai kowa ma mutuwa zaiyi, ke ma idan kin kasheni ba tsayawa gadin duniyar zakiyi ba, wataran dole zaki mutu".
Dariya Safuratu ta tuntsire da ita hade da cewa, "Yau ga Dan Ta'addan daji yana wa'azi a kan mutuwa". Wani wawan mari ta gabza masa ta baya, sannan rai a bace ta fara da cewa, "Ashe kasan duk wannan amma kuke kashe mutane ba tare da hakkinsu ba? Kawai saboda burinku na duniya na ku tara kudi, iyayen nawa kuka raba da 'ya'yansu? 'Ya'ya nawa kuka raba da iyayensu, sannan kannai nawa kuka raba da danginsu? Duk na tabbata baku manta ba kuna tune da duk irin ta'addancin da kukayi, naji labari wai yan sanda da sojoji ma kansu tsoron shigowa dajin nan suke saboda kun gagara duk wanda ya shigo hallaka shi kuke ko kuma kuyi garkuwa da shi, to alhamdulillah yau dai kwananku ya kare". Ta dora hannu a kan maballin bindigar zata harba kenan ta ji daga nesa ana cewa, "Karki harba - karki kashe shi, kotu zamu kaisu".
Kai ta daga ta ga shugaban sojojin ne tafe a kan mashin, tsaki tayi hade da matsa bindigar, nan take bullet din ya ratsa kan Goje ya fadi kasa matacce, daga ganin haka su Dodo suka firgice suka shiga hada hannuwa biyu suna bata hakuri karta kashesu, daga can nesa ma shugaban sojojin na mata gargadin karta kashe su amma tayi kamar bata ji ba, ta sa bindiga ta harbesu baki daya. Yana karasowa ya faka mashin din hade da cewa, "Wayyo Allah na, me yasa kika kashesu, yanzu wannan kinsan irin neman da gwamanti take musu kuwa? Idan da mun mika wannan yan ta'adda hannun gwamnati da ba makawa sai mun sama karin girma amma yanzu gashi kin kashesu, yanzu sai yaransu kadai muka sama damar kama wasu daga ciki". Safuratu tayi masa murmushi hade da cewa,
"Ai yanzu ma ba zaka rasa karin girma ba, duk mutanen da na kashe ka hada kace jami'anka ne suka kashesu, sannan akwai jama'a da na kubutar suma ka ce kune kuka kubutar da su, kuma akwai iyalan yan ta'adda mata da yara da kuma shanunsu da mashinansu duk na bar muku ku san yanda zakuyi da su, batun mutanen da akayi garkuwa da su ma na tabbata zaku mika kowa ga danginsu tunda suna hannunku, amma sauran yan ta'addan da kuka kama ma ba zan barsu ba, domin kashesu rage mugun iri ne sun kashe mutane da yawa sun cancanci hukuncin kisa. Na tabbata a hannunku ba za'a zartar da hukuncin kisa a garesu ba sai dai a dauresu zuwa wani lokaci a sakesu". Shiru yayi ya tsaya yana kallonta, tabbas duk zantukanta babu karya a cikinsu, amma ko ba komai dai zai sama karin girma tunda ta ce ta bar masa duk ayyukan da tayi a matsayin rundunarsu ce tayi, "Baiwar Allah ke mutm ce ko aljana?". "Babu wani boye-boye ni aljana ce ba mutum ba". Da fadar haka Safuratu ta bace bat! Ta barshi tsaye ya saki baki yana mamaki.
Bata bayyana a ko ina ba sai wajenda aka daure ragowar masu garkuwa da mutanen da aka kama, basu fi sha biyar ba ta dauki bindiga ta sakar musu wuta, sojojin dake gefe basa ganin mai harbi sai harbin kawai suka rika ji yayin da yan ta'addan suka rika zubewa kasa matattu. Safuratu na gamawa da su ta ce, "To masha Allah yanzu hankalina zai kwanta tunda na gama zartar da hukunci dai-dai da fadar Allah". Zaune suke a harabar ofishin yan sanda, ana ta faman rarraba musu ruwa da abinci, zuwa lokacin hankalinsu ya fara dawowa jikinsu ganin sun kubuta daga sharrin masu garkuwa da mutane, Safuratu ta shiga wajen, yan sanda masu gadi nayi mata magana amma tayi banza da su, Murja na ganinta ta taso ta tare, Safuratu ta ce, "Ashe kina nan kina jin dadinki, maza muje mu hau mota mu tafi gidan naku". Gaban Murja ya fadi, ita har ga Allah idan ta tuno Lami da irin azabar da ta sha a gidan ko kallon hanyar gidan bata son yi balle ta koma rayuwa a gidan, nan take ta fashe da kuka hade da cewa, "Dan Allah Safuratu ki nemo min wani waje inda zan rayu ko da aiki zan rika yi domin in ciyar da kaina zan iya, amma bana sha'awar komawa gidan nan ko kadan don na tabbata idan na koma kasheni zasuyi".
Safuratu tayi murmushi hade da cewa, "Share hawayenki Murja, in dai Lami ce sai ta dawo tana jin tsoronki zan koya mata darasin da zata barki ki zauna lafiya a gidanku". Murja ta ce, "Wallahi baki san halin ta bane, ni dai gaskiya ba zan koma gidan nan in rayu ba sai dai in tare da ke zamu koma". Safuratu ta ce, "To ba matsala nayi miki alkawarin kasancewa tare dake har zuwa lokacin da komai zai dai-daita". Cikin farin ciki Murja ta ce, "To na gode sosai, ai na gane ofishin yan sandan nan, daga nan ma ai gidan namu babu nisa, a kafa ma zamu iya zuwa". Hannuta Safuratu ta kama hade da cewa, "Muje". Daga nesa suka ji ance, "Kai ku koma ku zauna ba'a sallameku ba tukun".
Safuratu ta ce, "Yi hakuri ofisa sauri muke zamu gida muna da dan wani uzuri ne". Tsawa ya daka mata hade da cewa, "Uzurin banza gareku uzurin wofi? Da can lokacin da kuke hannun masu garkuwa da mutanen kun manta da uzurin naku ne kenan da sai yanzu jami'anmu sun sayar da rayukansu sun shiga daji sun cetoku wato yanzu kun sama yanci zaku nuna mana sauri kuke yi ko? Ku gaku shanshani uwayen sauri". Wata mata daga cikin mutanen da aka kubutar daga hannun masu garkuwa da mutane ta ce, "Yallabai da kayi hakuri ka barsu sun tafi, wannan bayin Allah su biyu da kake gani sune suka ceto mu daga sansanin masu garkuwa da mutane". Harara ya watsa mata hade da cewa, "Ke karki fada min maganar banza mana, kina so ki ce jami'anmu da suka hana idanunsu bacci suka sadaukar da rayuwarsu ba su ne suka cetoku ba kenan? Shiyasa hausawa suke cewa Dan Adam butulu, du du du yaushe kika bar hannun yan ta'addan amma gashi har kin fara manta alkhairi da aka miki". Ya kalli su Safuratu hade da cewa, "Ku kuma ku dawo ku zaune, sai mun gama kirgaku yan jarida sun gama daukar hotuna da yin hira daku sannan za'a sallameku".
Hannun Murja kawai Safuratu ta ja hade da cewa, "Ke zo mu tafi na matsu in ga wannan azzalumar Aunty Lami din". A guje dan sandan ya nufi Safuratu da nufin falla mata mari domin ta ma raina shi, yana zuwa ya daga hannu kafin ya kai mari yaji kamar an hangiza shi baya da karfi ai ko yayi tangal-tangal ya kife a kasa, da faruwar hakan yayi saurin mikewa hade da ba yan sanda na kasa da shi umarnin sunyi gaggawar tare su Safuratu da suka nufi hanyar fita, ai ko duk dan sandan da ya tunkaresu kafin ya karasa sai yaji kamar an rike masa kafafu ya kasa tafiya. Masu gadi ma suna kallo su Safuratu suka fice amma suka kasa tare su. Tafiya mai dan nisa sukayi tukun suka karaso kofar gidan, Murja ta tsaya gaban wani tankamemen farin gida wanda in ka ganshi ka ce gidan wani babban ma'aikacin gwamnati ne a cikin masu fada a ji na kasa. Sai dube-dube take hakika in dai ba kwakwalwarta ce ta birkice ba nan ne gidan nasu, domin ta gane komai na unguwar duk da anyi sauye-sauye da yawa hatta gidan an canza komai nashi kuma an kara mashi tsawo. Can ta hango wata mata yar dattijuwa ta fito daga gida tana ba awaki ruwa, da sauri ta karasa wajen hade da cewa, "Aunty Saratu".
Matar ta daga kai tana karewa Murja kallo, hade da cewa, "Na'am amma ban wayi fuskarki ba". Murmushi Murja tayi a zuciya ta ce, "Dama ya za'ayi ki ganeni shekarun ai da yawa gashi yanzu na girma sosai ke ma dan dai nayi miki farin sani shiyasa na gane ki". A zahiri kuwa ta ce, "Dan Allah dama tambaya nake, gidan Alhaji Rabe muke nema". Shiru tayi tana tunani zuwa can kuma ta dago ta dube Murja hade da cewa, "Alhaji Rabe kuma a wannan layin? Gaskiya bamu da Alhaji Rabe watakil ba wannan layin bane". Murja ta ce, "Alhaji Rabe wanda ya rasu shekarun baya fa, yana da wata mata mai suna Lami sannan yana da yarinya kwara daya mai suna Murja". Matar da Murja ta kira da suna Aunty Saratu ta ce, "Allah sarki Alhaji Rabe Naira zaki ce, Allah ya jikansa mutumin kirki maza masu kyauta an kwanta dama. Yanzu ai in ba gidan Hajiya Lami naira kika ce ba, to ba wanda zai iya gane gidan da kike nema a yankin nan, ga gidan nan". Ta nunawa su Murja tamfatsetsen gidan mai farin fenti. Sakin baki Murja tayi tana mai karewa gidan kallo tare da sake maimaita sunan a zuciyarta, "Hajiya Lami Naira". Wato ta kashe mata uba, ta kwace dukiyarta, ta koreta, haka zalika sunanshi ma na naira yanzu ta karbe shi.
Murja ta kalli Lami har zatayi mata magana kuma sai dai ta fasa ta nufi kofar gidan Safuratu na biye da ita amma babu mai ganinta sai Murja ita kadai. "Assalamu Alaikum". Da kyar masu gadin suka juyo hade da amsa sallamar tamkar an musu dole saboda wulakanci, "Am dan Allah nan ne gidan Hajiya Lami Naira?". Murja ta fada tana kare musu kallo, daya ya kalleta hade da cewa, "Eh nan ne, kuma bata nan idan ma maular kudi kika zo Allah ya bada sa'a yau dai bata nan". Murja ta ce, "Ba maula na zo ba, na zo ne da abu mai muhimmanci kuma nima asalin yar nan gidan ce". Kallonta sukayi kasa da sama a wulakance daga bisani suka bushe da dariya, daya ya bata rai hade da cewa, "Ke bace mana daga gani ko na tashi na faffala miki mari, wato ku iri yan maular nan dan kunga ana sakar muku fuska sai ku rika zuwa kuna rainawa mutane wayo, to wallahi bani da mutunci da kuke ganina nan in karya mutum ba wani abu bane a wajena". Murja ta dade tana rokon masu gadi suyi ma Hajiya Lami sallama amma sun nace lalai-lalai yar maulace sai korarta suke yayin da suke kamar zasu ta so su daketa.
Lamarin da ya fusata Safuratu, ba tare da bata lokaci ba ta shiga jikin Murja, ita dai Murja tana tsaye taji kanta yayi nauyi nan take kuma ta sunkuyar da kai, a kalla ta kai minti biyar a haka sannan ta dago kai hade da nufar kofar gidan gadan-gadan da niyar shiga. Dogon mai gadin ne ya taso da niyar tare mata gaba, ai kuwa ta daga hannu hade da wanka masa mari sanna ta ce, "Ko kai kurma ne? Na fada maka nan gidan ubanane"..............
🤣 Na san kun gaji da jira wannan karon dai kam kuna kuka gaji ba ni ba
Muje zuwa
Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group
Wa.me/+2348096831009
😍