ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 33


🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/nxoBNjP_ynY

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-33-hausa.html


*^ Part 33 ^*


Zaune suke sunyi jigum-jigum a cikinsu ba mai magana kowa na tunanin rayuwa da irin juyin duniya, dan adam dai idan yana raye bai gama ganin kaddara irin ta ubangiji a kanshi ba, wai yau sune a hannun masu garkuwa da mutane wasu sun fi wata guda a wajen, sunga abubuwa kala-kala sun sha kwana da yunwa tunda suka zo wajen babu wanda ya samu damar yin wanka balle wanki ko canza kaya. Sallah kuwa sai dai kayi nufi a zuciyarka don su kansu masu garkuwa da mutanen ba sallah suke ba balle su kunce ka kayi sallah idan lokaci yayi. "Ke ta so muje". Abinda ta ji ance kenan yayin da ta dago idonta ta kai duba ga wanda yayi maganar, wani katoton mutum ne baki kirin da shi sai kaurin wiwi yake. Murja ta sake kai dubanta gareshi ta ga da gaske ita yake kallo a zuciyarta take tunani ko sakinta za'ayi ne. Tsawa ya daka mata hade da cewa, "Ba zaki ta so ba sai na faffala miki mari?". Murja tayi shiru hade da kallon kafarta dake daure da kaca gashi yana mata barazanar duka don haka ta mike tsaye amma tafiya ta gagara, shi sai a lokacin ma ya lura da sarkar da ke kafarta saboda tsabar jarabar dake kwakwalarsa idanunsa har rufewa suke, yayi saurin zuwa ya karbo makulli ya zo yana kokarin kunce Murja.


Budurwar da ke gefen Murja ne ta fashe da kuka hade da cewa, "Idi don Allah don annabi na rokeka karka lalatawa wannan yarinyar rayuwa kamar yanda ka lalata mana, wallahi da ka lalata mata rayuwa gwara ka dauki daya a cikinmu kaje kayi lalata da ita kamar yanda ka saba, tunda mu tuni kun dade da bata mana rayuwa, amma wannan baiwar Allah ko auren fari bata yi ba ka tallafi rayuwarta". Tsaki yaja hade da cewa, "Zan zubar miki da hakora idan bakiyi mun shiru ba, shegiya me zanyi dake ga sabon zuwa ai ku na gama daku sai dai wasu kuma". Ita dai Murja sauraronsu kawai take sai daga baya ta gane me wannan budurwar take nufi da lalata rayuwa, don haka nan take itama ta kama kuka tana rokon Idi mugu domin ya rufa mata asiri karya lalata mata rayuwa, amma ina ko sauraronta baiyi ba ya jata yayi daji da ita. Sauran yan ta'addan suna yi masa dariya hade da cewa, "Shege Idi Mugu ya sha shegiyar tayi masa yawa, yau yarinyar nan sai ta gane shayi ruwa ne".


Tafiya sukayi mai nisa yana janta tana nokewa har suka karasa wani lungu a jejin, nan take Idi ya fara cire riga hade da dogon wandonsa, da ganin hakan Murja ta tsugunna hade da rufe idanunta, kamata yayi yana kokarin cire doguwar rigar dake jikinta yayin da ita kuma ta kankame jikinta nan suka shiga kunce domin taki bari ya cire mata rigar. Daga gefe yaji ance, "Kai Idi Mugu irin wannan kaya haka sun samu shine zaka ware kai kadai ko ka manta duk wanda ya ci shi daya, to shi daya zai mutu?". Da sauri ya kai dubansa wajen da yaji maganar ta fito, bisa mamaki idanunsa suka ga Gwaska jingine a jikin wata bishiya yana kallonsu. Ya dai san lokacin da suka zo wajen sai da ya karewa ko ina kallo amma baiga kowa ba shiyasa yake mamakin lokacin da Gwaska ya zo. "Kai Gwaska me ya kawo ka nan? Sanin kanka ne alakar dake tsakaninmu ta dade da yankewa, amma ban sani ba ko uwarka ta shirya haifar wani shine dalilin da ya sa ka shigo yankinmu".


Gwaska yayi dariya hade da cewa, "Kaga a kauda maganar gaba a gefe, ni fa ba fada na zo ba, kawai yarinyar da ke hannunka nake so ka bani muji dadin tare". Idi yace, "Kai din banza kai din wofi, na rantse da mai duka idan bakayi gaggawar barin wajen nan ba, sai na sa bindiga na raba kanka gida biyu". Ji yayi Gwaska ya fashe da dariya nan take kuma ya kara gyara tsayuwarsa yana kallonsu daga inda yake. Abinda yayi matukar fusata Idi Mugu kenan, nan take ya fara dube-dube da alama wani abun yake nema, Gwaska yayi murmushi hade da cewa, "Idan bindigarka kake nema ga ta nan a hannuna tun lokacin da ka zo ka jefar da ita saboda tsabar jaraba". Cikin tsawa ya ce, "Bani bindiga". Gwaska ya ce, "Idan naki fa?". A fusace Idi ya saki Murja ya nufi Gwaska yana zuwa ya daga hannu da niyar kashe Gwaska da mari, ji yayi hannunsa ya daki iska ya wuce, Gwaska ya bace bat. Zuciyar Idi kasa gaskata abinda idanunsa suka gani tayi, a tunaninsa wiwi hade da maganin karfin maza da ya banka ne sukayi masa yawa shiyasa yake ganin banza-banza don haka ya juya hade da nufar Murja don ya aiwatar da abinda ke ransa. 


Ita kanta Murja dake wajen a tsaye tana kallonsu ba karamin kidemewa tayi ba ganin Gwaska ya bace, a iya tunaninta dai yanzun nan ta ganshi a jikin bishiya a tsaye amma kuma yayin da Idi ya kai masa duka sai ta ga ya bace bat al'amarin da ya girgiza kwakwalwarta kenan, ganin Idi ya sake nufota a fusace ne ya dawo da ita hayyacinta, don haka zuciyarta bata yaudareta ba ta juya cikin daji hade da shekawa da gudu, duk da kasancewar bata san inda take tunkara ba. Ai kuwa Idi ya bita baya a guje, tana cikin gudu tun daga nesa ta fara hango mutum a gabanta, don haka ta nufi wajen tana fadin a taimaketa. Amma da ta kara matsawa sai ta ga macece sanye da doguwar riga a tsaye. Tana zuwa kusa da ita sai ta ga ashe Safuratu ce, abun ba karamin mamaki ya bata ba ganin Safuratu a dokar dajin nan, amma kuma sai tayi tunanin ko Safuratu batan kai tayi a cikin dajin ta kasa gane hanyar gari bayan ta tsere a daren da aka kamosu. Murja na zuwa wajen da Safuratu take sai taga a tsaye take tana mata murmushi tana zuwa ta kama hannun Safuratu hade da janta tana cewa, "Zo mu gudu gashi nan yana bina karya kamamu". Bisa mamaki sai Murja ta ji Safuratu ta tsaya kyam hade da kama hannunta ta tsaida ta, "Da alamu kin gaji zauna ki huta shi kuma dama shi nake jira". 


A rikice Murja tana kuka ta ce, "Dan Allah karki tsaya wallahi idan ya kama mu yana iya lalata mana rayuwa ko kuma ya kashemu ki zo mu gudu dan Allah". Duk abinda suke kafin Idi ya karaso wajen ne, Murja sai jan hannun Safuratu take, ba zato ba tsammani sai ji tayi Safuratu ta daka mata wata irin tsawa mai rikitarwa, idanunta sunyi ja muryata a kausashe ta ce mata, "Na ce miki kiyi mun shiru ki nema waje ki zauna". Ba shiri Murja ta hau karkarwa tare da zaunawa a tsorace tana kallon Safuratu, hakika idan idanunta da kunnuwanta ba gezo suke mata ba, idanun Safuratu ne ta ga sun koma ja kuma wannan muryar Safuratu ce taji mai kara da amo kamar muryar wani basamude. Idi Mugu shi kanshi da ya kusan karasawa garesu sai da yaja birki ya tsaya a dan nesa kadan da su jin irin tsawar da Safuratu tayi, nan take ya daka mata tsawa yana mai cewa, "Ke! yi mata ki miko mun wannan yarinyar da ta boye a bayanki idan kina son rayuwarki". Sassauta murya Safuratu tayi ga Murja hade da cewa, "Yi hakuri Murja na tsorata ki amma ina son daga yanzu duk abinda zaki gani a tare dani ya daina baki tsoro domin ni ba mutum bace, ni aljana ce". 


Gaban Murja ne yayi mummunar faduwa nan take ta fara ja da baya cikin tsoro, kwakwalwarta ta fara saka mata abubuwa da yawa, tabbas biri yayi kama da mutum, a zuciyarta take tunanin idan ba aljani ba dama me zai kai mace kyakykyawa kamar Safuratu cikin wannan dajin da ta farka ta tsinci kanta a ciki. Maganar Safuratu ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula, "Ki kwantar da hankalinki Murja kuma ki cire tsoron dake ranki, hakika ni musulmar aljana ce kuma mai taimako, babu nufin cutar dake a zuciyata ko dai-dai da kwayar zarra illah iyaka na shiga rayuwarki ne domin taimaka miki kamar yadda na saba taimakon wanda Allah ya nufa na taimaka....". "Ke magana nake miki kinyi banza dani, kiyi gaggawar miko wannan yarinyar tun kafin na fusata na hada dake nayi muku abinda nayi niyar yi mata tare dake". Maganar Idi Mugu ce ta katsewa Safuratu magana da takewa Murja, don haka ta dago hade da kallon Idi Mugu ranta a bace tamkar bata taba yin dariya ba tace, "Lokacin wasa ya kare yi gaggawar fadin irin mutuwar da kake so kayi, domin banga dalilin da zai sa in barka a raye ba, amma ina da dalilai da yawa da zan bayar ko a gaban Allah ne idan na kasheka". 


Lokacin da Safuratu ta juyo hankalin Idi ba karamin kara tashi yayi ba, domin ji yayi a lokacin gaba daya sha'awarshi ta tashi daga kan Murja ta koma kan Safuratu, amma bayan jin abinda ta fada sai ya bushe da dariya hade da cewa, "Na dade banga mace mai kyawan sura kamarki ba, don haka na baki zabi biyu, ki zama karuwata ko kuma ki zama matata, ko wanne daga ciki idan kika zama nayi miki alkawarin zan mayar dake yar gata, duk abinda kike bukata a duniya zan baki, kama daga kan kudi da gwalagwalai duk ba damuwa bace a wajena". Safuratu ta bata rai hade da juyawa ga Murja ta ce, "Ke Murja yi maza kiyi tunani a kwakwalwarki wannan mutumi ya dade yana lalata rayuwar yan mata da matan aure da suke garkuwa da su, sannan ki dauka cewa kema yanzu ya lalata miki rayuwa a matsayinki na budurwa wane irin hukunci ne ya dace da shi?". Tunanin da nazarin Murja ya sa ta gaskata cewa Safuratu aljana ce kuma ta tabbatar ba tayi niyar cutar da ita ba tun a sahun farko, don haka a lokacin da taji Safuratu ta watso mata wannan tambaya sai ta bata rai hade da cewa, "Wallahi wannan ba mutum bane dabba ne, ya cancanci mutuwa mafi muni, da ina da karfi da ni da kaina zan rataye shi a jikin bishiya kuma nayi masa tsirara watakil hakan na iya zama izina ga sauran yan uwansa idan suka zo suka sameshi a haka". 


Da jin hakan Safuratu ta fashe da dariya hade da cewa, "Baki da karfin yin hakan amma ni ina da karfin yin fiye da hakan, don haka nima zan kara da nawa hukuncin gareshi tun yana raye". Da fadar haka Safuratu ta ware hannunta nan take wata wuka mai kaifi ta bayyana a hannunta sai walkiya take, Murja dai ta ga Safuratu ta yanki iska da wukar hannunta, da faruwar hakan ta ji Idi Mugu ya daga kai sama hade da kwalla uban ihu mai rikitarwa, saboda karar ihu sai da duk tsuntsayen dake kusa da wajen na kan bishiya suka tashi. Jini kawai Murja taga yana malala daga cikin gajeran wandon Idi Mugu, cikin sauri da zafin radadi ya cire wando. Nan take Murja tayi saurin sa hannuwaa ta rufe fuskarta ganin azzakarin Idi Mugu a yanke, wai ashe lokacin da Safuratu ta yanki iska azzakarin ne ta yanke, tabbas Murja taji a ranta hukuncin kamar yayi tsauri amma kuma sai ta tuna yadda wannan budurwar ta rika fada mata irin cin mutunci da cin zarafi da su Idi mugu suka rika musu don haka sai ta ji wani farin ciki ya lulubeta. Hannu kawai Safuratu ta mika, nan take Murja ta ga wata doguwar igiya mai kauri ta zuro daga jikin doguwar bishiya ta nannade wuyan Idi mugu ta jashi sama ta rataye yayin da nan take ya fara haure-hauren mutuwa..........................



🙄 Ni dai na gaji, kuma ke Safuratu ahe kema muguwa ce. Idan na ce na daina sonki me zaki mun?


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments