ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 32

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/nxoBNjP_ynY

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-32-hausa.html


*^ Part 32 ^*Wani bakin dan ta'adda ne tsugunne a gaban Murja sai zare mata ido yake yana tambayarta, ita kuwa a matukar tsorace take bashi amsa kala daya, "Ban sani ba, wallahi ban sani ba". Ya daka mata tsawa hade da cewa, "Karki raina mana wayo mana Malama, babbar mace kamarki ace bata rike lambar kowa nata ba, ko dai kin zabi zama a nan ne? Idan bakya son komawa gida kiyi gaggawar fada a cikin mutanenmu ba za'a rasa wanda zai aureki ba, saboda kin hada komai da namiji yake bukata a jikin mace wannan ramar ta jikinki da zarar kin sama hutu zata warware". Ita dai Murja zuwa lokacin ta ma rasa abinda zata fada saboda ita ko a can baya kafin ta haukace lambar mahaifinta kadai ta rike yanzu kuwa baya raye. Tasan cewa a halin yanzu ko da tana da lambar Lami ba zatayi yunkurin kiransu da zummar su kawo makudan kudi su fansheta a wajen masu garkuwa da mutane ba, dan ko kasheta zasuyi Lami ba zata iya bayar da ko sisinta ba. 


Lafiyayyen mari ya wanka mata ganin tana bata masa lokaci hade da kunce sarkar dake kafarta ya jata ya kaita wani bangare na daban inda taga mata ne fiye da goma yan mata da dattijai wadanda a nan ta iskesu. Bayan wanda ya daureta ya tafi wata yar budurwa dake zubda hawaye ta kalleta hade da cewa, "Baiwar Allah kema yan uwanki basu da kudi ne ko kuma baki rike lambar wani naki bane?". Murja ta kalli wacce tayi maganar, ta fita a shekaru amma duk ta rame ta fita hayyacinta ga dukkan alamu akwai tarin firgici a tare da ita saboda hankalinta ba a kwance yake ba, Murja ta ce, "Ban rike lambar kowa nawa ba". Budurwar ta fashe da kuka hade da cewa, "Innalillahi wa'inna Illaihir raji'un shikenan kema zasu lalata miki rayuwa kamar yanda suka lalata mana, domin duk wanda ya kasa biyan kudin fansa har na tsawon lokaci, idan namiji ne kasheshi suke yi, idan kuma macece sai su kawota nan, a cikin yan ta'addan duk wanda yayi ra'ayi haka zai zo ya zabi wacce yake so a cikinmu ya shiga daji ko kuma bukkarsa da ita yayi amfani da ita tamkar ya samu matarsa". Kuka kawai Murja ta fashe da shi hade da cewa, "Innalillahi wa'inna illaihir raji'un ya Allah ka dubemu". Duk abinda suke fada Safuratu na gefe tana sauraronsu amma su basa ganinta, ta girgiza kai hade da cewa lalai wadannan mutanen rayuwarsu bata da amfani dole na dauki tsautsauran mataki a kansu. 


Wata yarinya ce ta fashe da kuka, Safuratu ta kai dubanta gareta budurwa ce yar kimanin shekara 16 Dan ta'addan ya sakata gaba hade da mika mata waya yayin da ta karba cikin kuka ta fara fadin, "Baba dan Allah ka ceceni daga hannunsu basu da mutunci kashemu zasuyi dan Allah baba ko nawa suke so ka basu ni dai ka fitar dani daga hannunsu". Dan ta'addan ne ya karbe wayar hade da cewa, "Idan baka hada kudin nan a cikin kwana biyu ba, zamu kiraka mu fada maka inda zaka tsinci gawar yarka, kuma idan har ka kuskura ka sako ma'aikata a cikin wannan maganar to kamar ka salwantar da rayuwar yarka ne domin kasheta zamuyi farar daya". Dan shiru yayi zuwa can kuma ya kwashe da dariyar mugunta hade da cewa, "Ashe kana son yarka Alhaji to karka damu ka hada kudin anjima da yamma zamu fada maka inda zaka kawo mana kudinmu idan muka dauki kudin kuma zamu fadama inda zaka dauki yarka". Da fadar haka ya kashe wayar ya koma kan wasu mutanen yana cigaba da karbar lambar yan uwansu.


Kusan mutane shida ne danginsu suka amince zasu biya kudin fansa a ranar a dabar Goje, Dabar Zaki da kuma Dabar Dodo. Don haka yamma nayi yan ta'addan suka fito da mashina hade da rataye bindigoginsu, aka daurewa mutanen da za'a tafi dasu idanu da bakin kyalle sannan aka dorasu a kan mashin hade da mutum daya a baya don kar su fado ko kuma yunkurin guduwa. Tsaki yaja hade da cewa, "Kai Alhaji saurara kaji ni fa ba mutumin banza bane duk da na kasance dan ta'adda amma ina cika magana ta, tunda na ce zamu sakar maka yarka yau to zamu sakar maka ita muddun kabi ka'idojinmu wajen kawo kudi kuma ka kawo kudin inda muka ce ba tare da ka sako jami'an tsaro a cikin maganar ba. Kuma wallahi ina gargadinka muna da infomomi masu bamu rahoton duk abinda ke faru don haka da zarar sun sanar mana kana tare da yan sanda to zamu harbe yarka ka zo ka dauki gawarta". Yana gama fadin haka ya kashe wayar hade da tayar da mashin dinsa yayi gaba su kuma suka bishi a baya.


Safuratu na biye da su har suka karasa wajen da suka cewa Alhajin ya kai kudin, tayi mamakin irin tarin mutanen da suke da su a cikin gari, domin tunda Alhajin ya taho duk inda yayi ana kiransu ana fada musu hatta kudin basu suka daukko da kansu ba, suna zuwa saitin wani kangon gida wani saurayi ya fito da jaka a hannunsa da sauri ya hau mashin din suka juya, ashe tuni shi yana tsaya a kusa da wajen da Alhaji ya ajiye kudin ya daukko, bayan Alhaji ya juya a mota. Sai da suka nutsa cikin daji sosai sannan mutumin ya kira ya fadawa Alhaji inda zaije ya dauki yarsa. Safuratu ta juya zuwa wajen da suka ce zasu ajiye yarinyar cikin sauri irin nasu na aljannu ta karasa wajen, su kuma yan ta'addan dake kan mashina guda uku suna zuwa suka jefarda yarinyar a wajen dake bakin gari ne suka juya suka nufi cikin daji, sauke ajiyar zuciya Safuratu tayi hade da cewa ke kam Allah ya tseratar da ke, yayin da ta ga Baban yarinyar ya faka da mota ya dauke ta cikin kuka irin na farin ciki. 


Gudu suke tsalawa a dokar daji cikin duwatsu amma saboda karfin mashinan nasu tamkar a kan kwalta suke tafiya, mashina biyu ne ko wanne dauke da mutum uku a kai kuma suna rike da muggan bindigu, fuskarsu kadai in ka kalla ta isa ta tabbatar ma da cewa wargi kadan zaka musu su aikaka lahira. Suna cikin gudu ba zato ba tsamani wani abu mai kama da saniya ya fito da gudu ya banki mashin din dake gaba, nan take mashin din yayi wata irin katantanwa ya wulwula a kasa nan take ya watsar da mutanen dake kai saboda gudun da suke yi dama yayi yawa. Su ma mashin din dake binsu a baya duk da kokarin taka birki da sukayi amma kan ya lauye nan take suka daki wata katuwar bishiya mashin ya watsar da duk mutanen dake kai, wasu kansu ya bugu da bishiyar wasu kuma sukayi kundun bala a kasa. Safuratu na gefe a cikin iska tana kallonsu ta san cewa irin wannan hadari sai mai tsawon rai ne zai rayu a cikinsu. 


Nan take ta fara binsu daya bayan daya tana dubasu hudu daga cikinsu tuni sun mutu, zuwa tayi saitin wajen wanda yake rike da jakar kudi a kan wani ice ya fado ya farke ciki sai jini ke zuba amma har lokacin hannunsa guda na rike da jakar kudin. Kwace jakar kudin tayi daga hannunsa hade da cewa, "Ku kam ba sai na karasa ku ba, na tabbata kafin a kawo muku dauki a wannan dajin kun mutu, sai kuje lahira ku tarar da abinda kuka shuka". Tana fadar haka ta bace bat! Ta barsu kwance suna fidda lumfashi daya-daya. Bata bayyana a ko ina ba sai a cikin motar Alhaji da ya kawo kudin fansar nan take ta ajiye kudin a bayan mota, ko magana bata musu ba ta bace. Suma sauran yan ta'addan suna cikin tafiya a kan mashin kawai sai dai su ga an zuro wani dogon hannu daga sama an dauke mai tukin mashin din wanda kafin suyi wani yunkuri tuni mashin din ya kife ko ya hada su da dutse ko wata bishiyar ya hallakasu. 


A takaice dai sai da Safuratu ta tabbatar duk wadanda aka daukko da niyar a karbi kudin fansa a sakesu sunje hannun iyayensu, sannan ta kashe yan ta'addan kuma ta dauke kudin ta mayar wa wadanda suka kawo kudin. Ganin har dare wadanda suka tafi karbo kudi basu dawo ba hankalin ubannin daba gaba daya ya fara tashi a tunaninsu ko an sama wata matsalar ne, don haka suka bincika ta bangaren infomominsu masu basu bayanai na cikin gari suka shaida musu cewa babu wata matsala da aka samu kuma tun da yamma an karbi kudaden. Ganin hakan yasa suka tashi mutane a mashina domin su bi sawun wadanda suka tafi karbo kudin a tunaninsu ko cin amanar daba zasuyi su cinye kudaden.


Kasancewar hanyoyin da suke bi a cikin dajin suna da yawa ko wanne daga cikin yaran dabobin sai dare sannan suka samo gawarwakin yan uwansu da kuma mashina da sukayi hadari, lokacin da labarin ya kai ga ubannin daban ransu yayi matukar baci ba a kan rasa rayukan yaransu ba, ransu ya fi baci a kan rasa kudaden da aka karbo daga hannun dangin mutanen da aka saka. Don haka duk suka sha alwashin cewa muddun idan suka kama masu hannu a cikin batan kudin da kashe yaransu sai sun aika su lahira komai yawansu. Ai kuwa a cikin sati guda hakan ya faru da dabobin kusan sau uku wasu hudu, don haka suka fara zargin juna a tunaninsu ko wani daga cikin ubannin daban ne yake tura yaransa su kwato abinda aka farauto a wajen dangin wadanda akayi garkuwa da su. Wani yammaci abin yayi matukar fusata Oga Goje ganin an kawo mai gawar yaranshi har mutum biyar wadanda suka fita domin karbo harsasan bindiga a bakin gari, zarginsa bai fada a kan kowa ba sai Dodo saboda yaransa suna yawan kawo mai korafin Gwaska yana yawan zuwa dabar tasu a cikin yan kwanakin wanda suke zargin ko leken asiri yake zuwa. 


Shirin yaki sukayi wajen mashin talatin ko wanne dauke da mutane uku da muggan bindigo a hannunsu, nan take suka durfafi dabar Dodo. Tun daga nesa suka fara kashe mutanen Dodo, da jin haka suma suka daukko nasu bindigun suka fara mayar da martani, sun dade suna azababben yaki da bindigu Safuratu dake cikin suffar Gwaska tana daga gefen mutanen da aka tsare tana kallonsu yayin da take sa ido a kan mutane wadanda akayi garkuwa da su, domin daga ta ga wani ya nufi bangarensu cikin hanzari take harbeshi da bindigar hannunta. Ba dadewa sai ga dabar Zaki suma sun kawowa dabar Dodo farmaki ai kuwa sukayi ta dauki ba dadi suna kashe junansu. 


Safuratu ba karamin jin dadin hakan tayi ba, domin daga karshe kasa fahimtar juna sukayi ko wane uban daba na tunanin dan uwansa uban daba ne ke yi masa zagon kasa yana kwace kudin da aka samo masa, don haka gaba mai karfi ta shiga tsakaninsu ya kasance ba'a zama inuwa daya tsakanin yan kungiyoyin uku, duk inda aka hadu sai kashe juna.........................Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments