🧟♀️🧟♀️ 🧟♀️🧟♀️
*ALJANAR FATIMA BOOK 2*
🧟♀️🧟♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟♀️🧟♀️
By *Kingboy Isah*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-30-hausa.html
*^ Part 30 ^*
Ba karamin mamaki abun ya basu ba amma sai wasunsu sukayi zargin bata nama ne na kusa da hanta ya bata naman shiyasa yayi dacin. Abincin kuwa sai da ya kusan dahuwa Safuratu taje ta tunkude tukunyar ya bari baki daya har sai da ya toya wasu daga cikin yan ta'adda masu dahuwar. Dariya kawai Safuratu ta kyalkyale da ita ba tare da suna ganinta ko jinta ba, ganin yadda suke ta bata rai domin yunwa ke kwakwalar cikinsu nan take suka sake yunkurin girka wata tukunyar yayin da Safuratu ta ce itama ba zan bari ba yau sai kun dandana kwana da yunwa.
Kwance yake a kan itaciyar kalgo sai sharar baccinsa yake hankali kwance, ya dora bindigarsa a kan ruwan cinkisa. Ji yayi an wanke shi da wani wawan mari wanda saboda karfin marin sai da ya fado kasa daga kan itaciyar da yake, nan take yayi saurin mikewa hade da haƙa bindigarshi yana waige-waige yana fadin "Waye-waye? wane banza ne ya mari Gwaska lalai yau ya tabowa kanshi bala'i". Shiru baiji ance kala ba, a lokacin ne hankalinsa ya dawo jikinshi nan take ya fara dube-dube yana kallon wajen da yake daji ne gaba da baya, domin bai ma san wajen ba kuma bai san ya akayi ya zo wajen ba. Tafiya ya farayi da nufin ya lalleka ko zai gane wajen tunda dajin ba bakonsa bane, ji yayi an kama rigarshi ta baya an jashi baya da karfi ya fadi kasa nan take aka cigaba da janshi kiiii! A kasa, ihu ya fara yi kafin daga bisani yaji an sake shi.
Mikewa yayi hade da daga bindigarshi sama ji kake ratatata! Ya soma harbi kana ya fara magana a fusace, "Uban waye yake jana? Ka bayyana mana ko kai waye yanzu idan ban aikaka garin da ba'a dawowa ba". A gefen kunnensa yaji ance, "Ni ce nan". Tsoro ne ya fara ziyartar zuciyarsa jin muryar mace kuma yana jin lumfashin mutum a kusa da shi, da sauri ya juya hade da dana bindigarsa ya fara harbawa amma sai ya ga wayam ba kowa. Yana nan tsaye yana zage-zage sai ji yayi an kwado masa danyar goriba a kai yayi sauri ya dafe kanshi, kafin yayi wani yunkuri tuni ya ji ana ta jifanshi da danyan kwallon goriba babu shiri ya ara a na kare ya zura da gudu cikin daji kafarshi ko takalmi babu amma bai ko kula da kaƴa ko hakukuwan da yake takawa ba.
Yana cikin gudu yaji an daina jifar amma bai dakata da gudun da yake ba duk da kasancewar bai san inda ya nufa ba cikin dare, a cikin gudun yaji ya ci karo da mutum nan take ya fadi kasa yana dago kai sai ganin mace yayi cikin fararen kaya ta juya masa baya tana gaggaba dariya, yana iya ganin gashi ya zubo gadon bayanta amma lokacin da ta juyo fuskarta sai ya ga iya wuya ne kadai jini na zuba a wuyan amma babu kai a tare da ita kuma a haka take dariya. Yunkurin tashi yayi amma yana dafa hannunsa kasa sai ji yayi ya dafa hannunshi a kan wani abu mai laushi, bai ankara ba sai ji yayi ance, "Ka danne min kai dan ubanka". Nan take ya kai dubansa wajen da ya dafa hannu duk da dare ne amma farin watan da ya haske yana iya ganin kan mutum ne a yanke amma yana jujuya idanu kuma ba makawa wannan kan ne yayi masa magana yanzu.
Bai san lokacin da ya kurma wani uban ihu ba hade da tashi ya sheka a guje cikin daji, yayi gudu mai nisa sai ji yayi an daka masa wata irin tsawa mai rikitarwa hade da cewa, "Dakata a nan, idan ka kara tako daya sai na ciro ma ƴaƴan hanji". Cik! ya tsaya waje daya yana raraba idanu tuni jub'i ya gama keto masa ya jika masa riga. Domin zuwa lokaci ya gane cewa aljannu ne ke faman tsorotashi, ya dan jima yana waige-waige amma bai ga kowa ba nan take ya fara fadin, "Dan Allah aljannu kuyi hakuri ku kyale ni, me nayi muku? Idan laifi nayi muku kuyi hakuri na tuba".
Kukan mace ya ji a gefenshi yayin da ya waiga a hankali, mace ya gani a gindin wata karamar itaciya ta tsugunna ta rufe fuskarta tana kuka, "Wacece? Waye a nan?". Ya fara fada yana matsawa wajen a hankali, karasawa yayi wajen ya mika hannu da nufin ya ɗagota saboda yayi magana har ya gaji amma tayi masa shiru sai kuka take, kafin hannun nashi ya kai gareta ta dago kai ta kalleshi da kwala-kwala idanunta a matukar tsorace ya ja baya har yana faduwa kasa, ya gane fuskarta sarai itace budurwar da ta ce ya taimaka ya samo musu ruwa ko abinci dazu kuma tana daya daga cikin mutanen da suka kamo da yamma. Amma abinda ya kara tsorata shi goshinta a fashe yake ana iya hango cikin kwakwalwarta amma ba jini ko diso daya.
Mikewa tsaye yayi rike da bindiga hade da cewa, "Dama ke aljana ce ban sani ba? To ba aljana ba ko ke mayya ce yanzu zanyi maganinki". Tana jinshi yana magana bata ce kala ba sai kukan da take, nan take ya saita bindigar dake hannunshi saitinta ya sakar mata wuta, ji kake ratatata! Saida ya tabbatar bullet din cikin bindigar ya kare sannan ya tsagaita wuta, bisa mamakinsa maimakon ya ganta a kwance ta mutu, sai ganinta yayi a tsugunne tana kuka kamar yadda ya sameta, kuma sai yaji ta fashe da wata mahaukaciyar dariya wacce karanta yake amsa kuwwa a gaba daya dajin. Tashi tayi tsaye tana zazzage rigarta sai gani yayi bullet din bindigar ya zubo kasa babu wanda ya fasa jikinta balle ya ratse har ya mata illa. A hankali ta fara takowa gabanshi yayin da yaji wani irin bala'in tsoro ya kara ziyartar zuciyarsa juyawa yayi da nufin ya ruga, ba zato ba tsammani sai ji yayi wani hannu ya faso ta cikin kasa ya rike masa kafa, yayi iya kokarinsa amma ya kasa kwace kafar tashi daga jikin hannun da ya rikeshi.
Ganin ta kusa zuwa wajenshi yasa ya zube kasa cike da tsoro hade da hada hannuwansa biyu ya fara fadin, "Ki wa Allah kiwa annabi ki yafe mun wallahi bansan ke aljana bace, nayi miki alkawarin idan kika yafe mun zan tuba in daina garkuwa da mutane da kuma ta'addanci. Dan Allah ki mayar dani gid...". Bai karasa rufe baki ba yaji an dauke shi da lafiyayyen mari wanda saboda karfinsa har sai da ya ga taurarin wahala, Safuratu ta ce, "Yi mana shiru nan ba gidan ubanka bane da za'a mayar da kai gida a lokacin da kake so, a nan sai lokacin da muka ga dama zamu mayar da kai. Idan kana so ka sama yancinka dole sai yan uwanka sun kawo kudin fansa sannan in sakeka". Shiru yayi ya sadda kai kasa cikin tsoro, a ranshi yana mamaki dama aljannu suna garkuwa da mutane su nema kudin fansa ashe.
Ji yayi Safuratu ta bushe da dariya daga bisani kuma ta kallishi hade da cewa, "Yanzu kaji irin abinda na ji dazun ko? Haka mutanen da kuke kamawa suke ji, gashi kaima yau kaji yadda ake ji idan aka yi garkuwa da mutum" Hakuri ya shiga bata yayin da ya ga tayi banza da shi sai dariya take ga hannun da ya rike masa kafa ya matse shi sosai ji yake kamar za'a karya masa kafar. Bayan Safuratu ta bata rai ta ce, "Ya sunanka?". Yace, "Sunana Gwaska". Sai ji yayi an dauke shi da mari ba tare da ya ga Safuratu ta daga hannu ba, "Sunan gaskiya zaka fada min". Da sauri ya ce, "Sunana na gaskiya Muttaka wallahi". "Yaushe ka fara ta'addanci da garkuwa da mutane?". "Shekara uku da suka wuce". Ta ce, "Mutum nawa ka taba kashewa". Ya danyi nazari hade da cewa, "Zasu iya kaiwa goma".
Safuratu ta ce, "Da kyau ashe ko na kasheka banyi laifi ba, dama Allah yace wanda ya kashe a kasheshi". Kuka ya shiga yi harda dora hannu a kai yana fadin ya shiga uku tayi hakuri karta kashe shi. Ta bata rai hade da tambayarshi dalili da kuma amfaninshi a duniya da zai hana ta kasheshi. Ya dade yana tunani amma ya kasa tunano ko abu daya, domin babu alheri ko kadan a zuciyarsa sai sharri dama babu arabi ba boko, sai mugun shaye-shaye da kai wa bayin Allah hare-hare, da ka matsa kusa da shi zaka fara jin kauri na tashi. Hannu kawai Safuratu ta mika a saitin inda yake a tsugunne hade da damke hannunnata nan take yaji tamkar an shake masa wuya da karfi, Safuratu ta juya hannunta kasa zuwa sama da faruwar haka yaji an murde masa wuya nan take ya fadi kasa matacce.
Safuratu ta juya baya hade da cewa, "Saura sauran". Nan take suffarta ta jirkice zuwa ta Gwaska komai da komai har kayan jikinshi, da faruwar hakan taje ta dauki bindigarsa a inda ya jefar da ita ta bace bat ta bar gawar yashe a kasa. Da safe Murja ta nemi Safuratu sama ko kasa ta rasa har tambaya tayi ga mutanen kusa da su wanda aka dauresu tare amma sunce basu ganta ba, nan take Murja ta fara tunanin ko dai Safuratu tayi nasarar tserewa ne tsakar dare, amma kuma bata tunanin Safuratun zata gudu ta barta haka dai tai-ta sake-saken zuci. Safuratu dake cikin suffar Gwaska sai rarraba ido take tana dan zazzagayawa rike da bindigar Gwaska da babu bullet ko daya a ciki.
Kai tsaye wajen madafar abinci ta nufa yayin da ta iske an sauke randa katuwa irin manyan nan cike da koko an jera kofuna da sun kai sittin ana zuzzuba kokon a ciki, ba mamaki tasan su Murja za'a kaiwa shi. Gefe guda kuma ta ga wasu mata na ta tuyar kosai wasu kuma na girka shinkafa dafa duka, daga gani tasan wannan shine abincin yan ta'addan. zuwa tayi ta dauki kofin koko guda daya bayan ta kalli mai zuba kokon hade da cewa, "Baaba bari na dan taba wannan". Ya kalleta hade da cewa, "Kai fa Gwaska rainin wayonka yayi yawa wallahi".
Bata kula shi ba ta dauki kofin kokon ta kai baki ai kuwa tana sawa a baki ta zubo da kokon domin jin wani irin mayen tsami da kokon yake da alamu gasarar ta dade a ajiye kuma ko sugar babu. A zuciyarta ta ce, "kuma wai a haka za'a ba bayin Allah su sha a matsayin abin kari? Lalai yau akwai dirama a wajen nan". Ba tare da ta ce kala ba, nan take masu zuba kokon su kaga Safuratu dake a suffar Gwaska ta kama randar koko guda ta malalar da shi a kasa, nan suka saki baki suna kallo sai gani sukayi ta kama sauran ta malalar sannan ta fara kwallo da kokon dake cikin kofuna wanda aka zuzuba za'a kaiwa wadanda akayi garkuwa da su.....................
😒 Ni dai na gaji
Muje zuwa
Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group
Wa.me/+2348096831009
😍