ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 29

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/IV1i4scamcs

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-29-hausa.html


*^ Part 29 ^*



Tafe suke cikin kurkurmin daji lokaci zuwa lokaci yan ta'addan na harba bindigo yayin da wadanda suke kan mashina sukayi gaba wasu kuma a can baya bakin titi suna ta barin wuta da bindigu saboda tsorata ma'aikata ko wasu jami'an tsaro da ka iya kawo dauki. Mutane kuwa babu abinda suke sai innalillahi ciki kuwa harda Murja, Safuratu dake rike da hannun Murja kallonta ta kai gefen hannun hagu da na dama yayinda ta ga mutane kala-kala mata da maza wasu da yara wasu mata da miji ne, wasu kuma iyalai ne baki daya, wata zuciyar ta ce mata ta cecesu amma wata zuciyar ta ce ta bari sai sun karasa can maboyar masu garkuwa da mutanen watakil akwai wasu bayin Allah a hannunsu. Tafiyar da sukayi a cikin daji ta fi ta awa biyu wasu mutanen duk sun gaji amma idan mutum ya tsaya sai dai yaji an kwada masa gindin bindiga dole zai tashi ya cigaba da tafiya wasu kafafunsu ko takalma babu. Sai dare wajen magariba suka karasa sansanin na yan ta'adda, lokacin da yan ta'addan suka hadu ba karamin mamakin yawansu Safuratu tayi ba domin a kala zasu kaiwa su dari uku ko hudu


Wani fili dake bayan kogon dutsen aka nufa da su, duk da kasancewar magariba ta fara yi amma suna iya hango mutane daddaure a jikin sarka da ke zagaye da bishiyoyin wajen. Haka akaje aka daurewa su Safuratu kafafu kamar yan mari. Safuratu ta karewa mutanen wajen wadanda suka tarar a daure kallo, duk sun fita hayyacinsu wasu sun rame sosai saboda yunwa da azaba da suke sha, ta sake kai dubanta ga mutanen da aka kamo su tare duk an gaji, wasu sun kwanta wasu sun a zaune suna kuka saboda halin da suka tsinci kansu a ciki ga yunwa da kishirwa na kwakwalar cikinsu. 


Safuratu ta kalli daya daga cikin samarin dake rike da bindigogi suna zazagayawa a tsakaninsu ta ce, "Dan Allah a samo wa mutane ruwa da abinci mun gaji ga kuma yunwa muna ji". Tsallakowa yayi cikinsu hade da cewa, "Wacece tayi magana?". Safuratu ta ce, "Ni ce". Ai ko yana zuwa wajenta ya daga gindin bindigarsa ya kwada mata a kai, hade da cewa, "Kiyi mana shiru, nan ba gidan ubanki bane balle ki sama abinda kike so a lokacin da kike so, a nan sai lokacin da muka ga dama zamu baku ruwa ko abinci, kuma ko mutuwa zakuyi babu ruwanmu idan kina so ki samu yancinki, dole ki sa iyayenki su kawo mana kudi da wuri sannan mu sallameki". Safuratu har ta bata rai kuma sai ta basar ta rabu da shi ya gama masifarshi sannan ya bar wajen. Wata mata da a nan Safuratu ta sameta a daure da kaca, ta ce, "Yarinya ai mutanen nan basu da imani a wuni abincin da muke samu baifi na cin lokaci guda ba shima sai mai zafin nama yake samu ya ci da dan yawa, domin idan suka tashi rabon abincin hadawa suke kwano daya mutum goma". 


Safuratu ta ce, "Sannu baiwar Allah na ga kin galabaita da yawa gashi har rama ta bayyana karara a jikinki da alamu kin dade a wajen nan, to suna baku ruwa kuwa?". Matar ta danyi murmushi mai cike da tausayawa kanta da kuma sauran wanda aka kamo hade da cewa, "Da safe suna bamu koko dan karamin kofi da ruwa kofi daya shine na karyawa, da rana kuma suna jika mana garin kwaki da kuli-kuli su hada mutane goma faranti daya shima wani baifi yayi loma biyar ba zai kare, sannan sai su bawa kowa kofin ruwa karami. Da dare kuma ba sai na fada miki ba tunda gaki suna gama abincin tuwo ne zaki ga sun kawo shi nan, kuma kamar yadda kika fada na dade a nan don kusan mu talatin aka kamo amma yanzu a cikin wanda aka kamomu tare sauran duk danginsu sun kawo kudi an sakesu cikin wanda aka kamomu tare bamu wuce mu 9 zuwa 8 ba yanzu. Nima dangina na can suna ta fafutukar ganin sun hada kudi million biyu suka ce za'a kawo kafin su sakeni gashi kuma dangina talakawa ne". Safuratu ta ce, "Ayya Allah ubangiji ya kubutar damu baki daya". Ta ce "Ameen". 


Safuratu na nan zaune tana raba ido, wajejen karfe 10 na dare mutane duk sun fara yin baccin dole saboda yunwa, kishirwa, da gajiya dake addabarsu Safuratu ta ga yara sun fara fitowa daga gefen sansanin yan ta'addan dauke da tire-tire na abinci, domin a bayan sansanin yan ta'addan inda aka daure su Safuratu yake. Nan yaran suka rika harbin mutane da kafafu suna tayar da su daga bacci sannan kamar yadda matar ta fada mata haka suka rika hada mutane goma a tire daya wanda tuwo malmala uku ne a ciki tire daya. Haka aka kawo tire daya tsakiyar su Safuratu Murja ma tuni har ta soma bacci saboda yunwa da gajiya, don rabonta da abinci tun wanda Safuratu ta saya mata a mota. 


Kasancewar yan ta'addan sun tayar da babban inji sun kunna kwayayen fitilo wanda suka haske wajen baki daya, watakil don su rika ganin ko ina da kuma motsin kowa. Kallo daya Safuratu tayiwa tuwon ta san cewa irin tuwon nan ne da ake cewa ci karka mutu, duk da kasancewar tuwon masara ne amma miyar tsululu take tamkar an wanke kai a ciki, hannu tasa ta debo kamar yadda kowa ke kokarin dauka ya kai bakinsa saboda yunwa dake kwakwalar cikinsu. Safuratu na kai tuwon baki tayi gaggawar furzar da shi, yayin da su Murja da sauran wanda aka kamo su tare suka wani yatsine fuska bayan sun kai baki, saboda rashin dadin tuwon. Safuratu ji tayi tunda take a rayuwa bata taba cin abinci marar dadin wannan ba, miyar tamkar kuka da gishiri ne kawai aka kada babu mai, sannan tuwon ga dukkan alamu bai dahu ba. Bisa mamaki sai gani tayi wannan mata ta dazu ta dage sai aika loma take, nan take suma su Murja suka daure suka cin tuwon suna bata rai. 


Matar wacce ita kadai ce tsohon zuwa a cikinsu ta ce, "Daurewa zakuyi ku ci tuwon nan, Ko mu nan da farko haka muka sha bakar yunwa da wahala kafin mu saba bama iya cin abincin amma da mu ka ga yunwa na neman hallaka mu dole ta sa muka koyi ci. don in baku ci bama a banza yunwa zata kasheku su kuma ba asara garesu daukar gawar mutum kawai zasuyi suje su wullar a cikin daji inda wari ba zai damesu ba". Haka kawai Safuratu ta ce bari ta je sansanin yan ta'addan ta ga ko suma kalar abincin da suke ci kenan, don haka ta bar gangar jikinta a nan ta nufi wajensu, gaba daya yan ta'addan ne a wani katon fili dake nesa kadan da bukkokinsu da alamu nan ne madafar tasu, Safuratu na karasawa ta ga shanune guda biyar aka bankare ake gasasu a wuta a gefe kuma lafiyayyar shinkafa dafa duka ne ake zubawa a tire ta sha mai ga kuma kayan ciki a saman ko wane faranti. Kallo daya zakayi musu ka gane cewa lalai suna cikin farin ciki, idonta ya kai kan wasu mutane uku dake zazzaune a kan kujerun roba da katon tebur a gabansu irin na roba da alamu sune shugabannin yan ta'addan. 


Daya daga cikinsu ya mike hade da daga bindigarshi sama yayi harbi ji kake ratatata! Nan take gaba daya yan ta'addan suka kwashe da shewa suna fadin "Sai Dodo". Bayan ya dakata daga harbin bindigar ya washe bakinshi da yayi baki kirin saboda shaye-shaye da yake hade da cewa, "Yau rana ce ta farin ciki a garemu bisa kara samun nasarar sato wasu mutanen ba tare da samun matsala irin ta jami'an tsaro ba, sanin kanku ne wannan harka tamu akwai amana a tsakaninmu saboda komai na rayuwa sai da amana ake samun cigaba a ciki, don haka kamar yadda aka saba sanin kowa ne idan munyi aikin hadaka irin wannan daga dabobin nan namu guda uku, wato tawa dabar Dodo, dabar Goje, da kuma dabar Jan Zaki, baki daya kirga mutanen ake kowa ya ja nashi ya nufi dabarshi, to kamar haka wannan karon ma idon Allah ya kaimu safe zamu kirga mutanen da aka kamo a raba kowa ya dauki nashi ya nemi kudin fansa daga hannun danginsu, duk wanda kuma yaga mutanen zasu kawo masa matsala karya bata lokacinsa a kansu yayi gaggawar saita musu hanya. Saboda a irin wannan harka tamu bama bukatar cikar ko kankani. Bisa wannan nasara da muka samu ga shanu nan guda biyar an bankaresu kowa ya sha shagalinshi bayan munci abinci". 


Da gama fadin hakan suka sake kyalkyalewa da dariya game da ihu irin nasu na yan iska. Safuratu dai na kallonsu daya bayan daya, gaba daya babu alamun tausayi ko imani a tare dasu, duk inda ta waiga sai ta ga saurayi na busa tabar wiwi wasu kuma na ta zukar sigari, nan take aka fara rarraba abinci tire-tire bisa mamakin Safuratu sai gani tayi wannan yan ta'adda suna warewa duk mutum uku tire guda sabanin su da aka kama, da ake basu duk mutum goma tire guda. Murmushi tayi hade da cewa, yau zan ga ta yadda zaku ci abincin nan bayan kun hana bayin Allah abincin mai dadi". Da fadar haka ta daga hannayenta biyu nan take wata irin guguwa mai mugun iska ta taso kan kace kwabo tuni guguwar nan ta hargitse wajen baki daya. Guguwar na wucewa suka ga kwanukan abincin nasu sunyi budu-budu da kasa, sai kuma suka shiga zare ido da iface-iface domin ko sauran da ya rage a tukunya da suka duba gani sukayi tukunyar ta bare. 


Nan dai ogannin sukayi umarni da a sake dafa wani abincin, sannan aka ciro wannan bankararrun shanu domin aci, sai dai kuma duk wanda ya kai nama baki sai ka ga ya zubda da sauri, domin ji sukayi nama yayi daci kuma da ka tauna sai kaji tamkar ka tauna kasa.


Tabb na gaji 😥

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments