🧟♀️🧟♀️ 🧟♀️🧟♀️
*ALJANAR FATIMA BOOK 2*
🧟♀️🧟♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟♀️🧟♀️
By *Kingboy Isah*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/IV1i4scamcs
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-26-hausa.html
*^ Part 26 ^*
Safuratu tayi murmushi hade da cewa, "Karkiyi mamakin ganin na mike duk da kin watsa min gubar sankarau, abinda baki sani ba shine a wancan karon ma na farko saboda na yarda dake shiyasa kikayi nasarar shammatata kika watsa min gubar ba tare da na goce ba. Amma a wannan karon ban yarda dake ba haka zalika ko wace irin rantsuwa da alkawari kikayi ba zan yarda da ke ba a wannan karon shiyasa duk wani motsi naki ina ankare dake. Abinda baki sani ba tun lokacin da kikayi yunkurin watsa min gubar cikin sauri irin namu na bace yayin da gubar ta wuce na sake bayyana a waje, abun ya faru cikin yan sekonni ne na tabbata ba lalai kin ankara da bacewa ta ba, shiyasa da na dawo naga baki gane ba nayi kamar gobar ta sameni da gaske na fadi". Kuka Marakisiyya ta fashe da shi, Safuratu ta ce, "Yi kukanki ba zan hanaki ba watakil kuka na karshe kike amma ki sani wannan karon ko kukan jini zakiyi ba zan tausaya miki ba balle kuma kiyi tunanin afuwa daga gareni".
Ko da jin haka sai Aljana Marakisiyya ta kyalkyale da dariya hade da cewa, "Wannan kukan da kikaga inayi ba na komai bane face na takaici na kasa hallaka ki, domin in da gubar sankarau ta shigeki a wannan lokaci ni da kaina zan kasheki na aikaki lahira. Dariyar kuma da kikaga ina yi yanzu, tunawa nayi da cewa ko ban kasheki ba boka kare dangi zai kasheki, domin nasan halinki zaki iya tunkararshi da niyar ki kasheshi kuma a lokacin ne zaki gane wanene shi kuma a lokacin ne zai kasheki kuma ya kashe banza". Da gama fadin haka ta sake fashewa da dariya, a fusace Safuratu ta kalli Marakisiyya nan take wasu irin sarkoki suka bayyana suka daure mata hannuwa da wuya da kuma kafafu yayin da suka rabata da kasa. Wata irin bulala waccan jikinta duk wukake ne ta bayyana a hannun Safuratu inda nan take ta fara zane Marakisiyya da ita, duk inda ta buga mata wannan bulalar sai dai ka ga bakin jini irin na su na aljannu yana zubowa domin kuwa a duk sanda ta buga mata sai wukaken jikin bulalar sun makale a cikin jikin Marakisiyya.
Ita kuwa sai ihu take tana neman agaji a wajen boka kare dangi da sauran shedanun aljannu abokan aikinta amma shiru ba wanda ya bayyana balle ya kawo mata dauki. Sai da Safuratu tayi mata fatata-fata ta tabbatar ta kusan mutuwa sannan ta hada wuta mai yawa ta jefata ciki nan take Marakisiyya ta kama ci da wuta, tana ihu da kururuwa an kai mintuna ashirin Marakisiyya tana ihu jin ta fara yin laushi ne yasa Safuratu ta kashe wutar ta shiga ta dauki Marakisiyya wacce duk sassan jikinta ya kone kurmus amma tana lumfashi sama-sama, nan take ta saki fuka-fukanta ta tashi sama da ita bata zame ko ina ba sai gidan boka kare dangi, tun daga sama ta saki Marakisiyya ta fado kasa tim! A saitin kofar kogon boka, yana jin haka ya taso yana tambaya wanene? A lokacin da ya fito yaga Marakisiyya ce tana gangarar mutuwa nan take ya rungumeta ya fashe da kuka yana ta jijigaga yana tambaya wa yayi mata haka. Ta daga baki tana magana a hankali, "Ka.. Kam... Kasheta... Saf... Safu... ra.. tuu.. ce". Tana gama fadin haka kanta ya langabe lumfashinta ya tsaya nan take ta bace bat a hannun boka.
Da faruwar haka ya gane cewa ta mutu, kuma ta koma siffarta ta asali irin ta aljannu shiyasa ta bace baya ganinta, domin a cikin suffar mutum ko wata dabba ne kadai idanun dan Adam ke iya ganin aljannu sai kuma wanda suka so tsorata mutum dake jirkita halitta ko su bayyana ba wani sashi na jiki domin tsorata mutum. Kai ya daga sama nan take ya kwala ihu mai rikitarwa hade da cewa, "Marakisiyyaaaaaaa". Cikin bakin ciki da takaici domin kuwa yana matukar ji da Marakisiyya don ta kasance muguwa kuma tana yi masa biyayya duk wani aiki na mugunta da ya sakata ba gardama take aiwatarwa. Bata rai yayi tamkar farin ciki ko annashuwa basu taba wanzuwa a fuskarshi ba ya ce, "Safuratu ki jira lokaci tunda har zaki iya kashe min aljana ni kuwa na sha alwashin duk inda zaki buya a duniya sai na kamoki kuma na kasheki, tun farko na so na kasheki amma Marakisiyya ta ce a daureki yanzu gashi kin kubuta kin zama ajalinta amma tabbas haduwarmu ta biyu ranar ce zata zama ranarki ta karshe a duniya kum....".
Kafin ya karasa fadin abinda zai fada ya ji wata iriyar dariya ta karade baki daya dajin, ko da ya daga kai sai ya ga Safuratu ce ta bayyana a sararin samaniya saitin kanshi, nan take ta fara magana da wata irin murya mai amsa kuwwa tana cewa, "Bansan dame kake takama ba da har kake ikirarin zaka kasheni a matsayinka na dan Adam ni kuma Aljana kuma ka kasance kai ba malami wanda ya san ayar Allah ta yakar shedanun aljannu ba, sannan na kasance ni ba shedaniyar aljana ba, hakan na nufin ko da ace kai malami ne ayoyinka na alqurani ba zasu illatani ba domin ni mai imani ce komai na yarda da Allah". Boka kare dangi ya daga baki zaiyi magana kenan Safuratu ta zuro hannunta wanda a nan take ya kara tsayi ya shako wuyan boka ya daga shi sama nan take ya kama hantsila kafafu da kokarin ya kubuce. Safuratu ta ce, "Ka fada min yanzu waye zai hana in kasheka? Na tabbata idan na kasheka har lada sai Allah ya bani domin ka kasance mai kulla makirci kala-kala hade da zaluntar bayan Allah, ka kashe wasu yayin da wasu kuma ka haukata su, kuma ka raba aure bila adadin don haka daga yau karshen zaluncinka ya zo".
Da fadar haka boka kare dangi ya ce, "Don Allah kiyi hakuri ki mun rai na tuba ba zan kara ba idan kika barni da raina zan zama mutumin kirki in daina harkar bokanci". Aljana Safuratu ta kalleshi hade da watsa masa harara ta ce, "Kayi mun shiru babu afuwa ko rangwame a tsakanina da kai yadda baka tausayawa bayin Allah ba haka ba zan tausayama ba". Tana gama fadin haka ta sake shake masa wuya da zankalelen hannunta wanda nan take lumfashinshi ya fara daukewa, bisa mamaki sai ji tayi boka kare dangi ya fashe da wata mahaukaciyar dariya inda nan take ta tsaya tana kallonshi, ya bude idanu hade da cewa, "Kinyi tunanin haka zan rika rokonki da neman afuwarki ko? to ki sani kinyi kadan da ki ga bayan boka kare dangi sai dai ni inga bayanki. Jujuge, duduge, huhuge Ku fito". Ya karashe maganar da karfi.
Bisa mamakin Safuratu sai gani tayi wani irin hayaki ya mamaye illahirin wajen, hayakin yana lafawa sai ga wasu jifga-jifgan ifiritan aljannu guda uku, kallo daya Safuratu tayi musu ta gane cewa lalai wannan aljannu sun fi karfinta nesa ba kusa ba, a zuciyarta ta fara tunani ashe dama boka kare dangi yana da aljannu masu bashi kariya kamar wadannan shiyasa yake tsula tsiyarsa yadda ya ga dama. Boka kare dangi ya bushe da dariya irin ta mugaye sannan ya ce, "Ina tunanin zuwa yanzu ya kamata ace kin yi gaggawar sakina ki janye hannunki daga shakewar da kikayi mun, in ba haka ba kuma yanzu zan sa a cire hannun daga kafadarki. Ko da yake ma ke da zaki mutu ai ba wani abun damuwa bane idan an cire miki hannu". Dariyar ya kara bushewa da ita wacce ta fi ta farko sauti.
Sakinshi Safuratu tayi ta janye hannunta hade da yin murmushi ta ce, "Tabbas nayi alkawarin kasheka amma ga dukkan alamu lokacin da Allah ya daukarma bai cika ba tukun, domin babu wani mai karfi ko wani mahaluki da ya isa ya kashe wani face kwanansa sun kare, don haka ka jira lokaci tabbas idan lokaci yayi zan kasheka da hannayena. Kuma da kake batun zaka kasheni ka sani wadannan aljannun naka malalatan banza basu isa su kasheni ba idan har kwanana bai kare ba". Wani aljani ne daga cikin aljannun ya dakawa Safuratu tsawa hade da cewa, "Ke karamar alhaki ashe rashin kunyarki ya kai har ki kalli kwayar idanunmu ki kiramu da malalata? Tabbas ban cika dan halak ba idan har ban nuna miki lalaci ba yau"
Da jin haka Safuratu ta kyalkyale da dariya hade da cewa, "To su waye ku in ba malalata ba, tunda gashi Allah ya baku baiwa ta karfi da wasu tarin baiwarwakin amma kuka zubda matsayinku kuka zabi ku dawo karkashin boka bokan ma dan adam makaskanci wanda yayi mubaya'a ga shaidan, tabbas ina gargadinku da ku tuba ga Allah ku kama gaskiya idan ba haka ba karshenku da shi kanshi bokan naku ba zaiyi kyau ba". Ko da gama fadin haka nan take kan aljani duduge yayi ja ya kama hayaki alamun yayi matukar fushi kenan, da faruwar hakan sai ga wata bulala ta sarka ta bayyana a hannunshi, a cikin zafin nama irin nasu na ifiritai ya kaiwa Safuratu duka da wannan bulala cikin sa'a Safuratu ta duke kasa bulalar ta wuce ta saman kanta ta sama wani dutse dake bayanta, bisa mamaki sai gani tayi dutsen ya tsage saboda karfin duka na wannan aljani Duduge. Nan take Aljana Safuratu ta jijiga kai a zuciya tana kara tabbatar da cewa karfin wannan aljannu ya fi nata nesa ba kusa ba.
Ba ta ankara ba sai gani tayi wannan aljani ya sake mako wannan bulala tashi gareta, ai kuwa cikin zafin nama itama bulalarta mai wukake a jiki ta bayyana a hannunta nan take ta kai duka saitin bulalar Aljani Duduge ko da haduwar bulalin guda biyu sai gani sukayi wani tartsatsin wuta ya tashi sama bulalin suka nanade juna, cikin fusata Aljani Duduge ya ja bulalarshi da karfi, saboda karfin jan da yayi sai da Aljana Safuratu ta taho baki daya, amma sai ta saki fuka-fukanta cikin iska nan take ta tokare itama ta ja bulalar dake hannunta da karfi sai gashi tana kokarin jawo Aljani Duduge baki daya. Lamarin da ya Boka, aljani Huhuge, aljani Jujuge, da Aljani Duduge matukar mamaki kenan. Domin a tunaninsu wannan yar budurwar aljana fuk! Daya zasuyi mata su kasheta har lahira amma sai gashi karfinta ya kusan dai-daita da na Duduge don haka suka fusata baki daya sunsan cewa idan sukayi wasa ɗan hakin da suka raina zai iya tsokale musu ido.
Shiyasa sukayi nufin hallaka Safuratu ta hanyar kai mata mugun hari baki daya su ukun a tare, aljani Jujuge ya fito da wata kwari da bakarshi ya dana kibiya ya sakarwa Safuratu a saitin ciki, bisa mamaki sai gani yayi ta goce kibiyar ta wuce ta gefenta. Shi kuma aljani Huhuge ya daga gudumarsa ya kaiwa Safuratu wani mummunan duka, nan take ta goce amma cikin rashin sa'a gefen gudumar ta sameta a baya. Saboda karfin dukan sai da Safuratu ta fado kasa cikin ciyayi, suna ganin haka sai suka fashe da dariya ciki kuwa harda boka. Safuratu da ta fado mikewa tayi tsaye cikin galabaita ta bisu da kallo daya bayan daya cikin azababben gudu kuma irin nasu na aljannu ta nufi boka kare dangi ta daga bulalarta ta kai masa duka da karfi da nufin ta rabashi gida biyu, amma sai aljani Duduge ya tare dukan da bulalarshi, amma duk da haka sai da karfin dukan ya sama Boka Kare Dangi inda nan take ya fadi ya wulwula baya hade da yin hajijiya yayin da bakinshi ya daki wani dutse ya fashe, jini ya rika zuba. Ko da ganin jinin sai boka Kare Dangi ya kwala ihu ya kalli aljannun daya bayan daya ya ce, "Idan wannan yarinyar ta kara minti daya a duniya baku kasheta ba sai na muku hukunci mai tsanani".
Da faruwar hakan kamar hadin baki ko wanne daga cikinsu ya nufi Aljana Safuratu da mummunar manufa da nufin su kasheta irin kisa na farat daya, amma sai gani sukayi tana gocewa dukan nasu da wani irin sauri na ban mamaki, duk da wani dukan yana samunta amma wanda take gocewa ya fi yawa, daga karshe sai ya kasance itama tana kokarin maida musu martanin duka . Boka Kare Dangi shi kanshi sai da ya tsorata ganin sun shafe tsawon mintuna ashirin suna fada su uku ita daya amma sun kasa kasheta, daga karshe ma sai suka tsaya sukayi cirko-cirko suna kallon juna suna huci, ita kanta Aljana Safuratu jikinta duk jini ne domin karfin hali da karin zuciya ne kawai yasa take iya kare dukan nasu da kuma kokarin maida musu martanin dukan kasancewar sarkin yawa ya fi sarkin karfi. Boka Kare Dangi ya dakawa aljanunsa tsawa hade da cewa, "Me kuke jira ne da ita bakwa ganin ta gaji kuma ta galabaita? wannan itace dama ta musamman a gareku da zaku kasheta cikin kankanin lokaci".
Ko da jin haka sai aljannun suka sake yunkurin kai wa Safuratu hari, ita kuwa a zuciyarta ta fara tunanin mutanen da take taimako duk da tasan cewa ko babu ita Allah na iya basu taimako daga wani bangaren amma bai kamata ta mutu a nan ba. Domin ta san cewa idan ta tsaya suka cigaba da wannan fada cikin lokaci kankani zasu iya kasheta saboda sarkin yawa ya fi sarkin karfi haka zalika yanzu karfin ta ya kare. Don haka ta rufe idanunta, Boka har ya cika da farin ciki a tunaninsa ta sadaukar cewa ta mutu ne, amma nan take sai gani sukayi wata irin guguwa ta turnuke sararin samaniya wanda su kansu aljannun sai da suka tsaya cik hade da sa hannaye suka kare idonsu saboda kura, shi kuwa boka kare dangin guguwar ce ta dauke shi ta daga sama nan take ya fara ihu yana neman taimako da kyar aljani Duduge ya samu ya cafko kafar boka da guguwa ta warceshi take juyawa da shi. Nan take sukaji wata irin dariya da amonta ya cika ko'ina tana cewa, "Kamar yadda na fada idan kwanana bai kare ba to baku isa ku kasheni ba, don haka yanzu zan tafi amma ku jira dawowata ta biyu tabbas ni zan kasheka boka Kare Dangi, kuma shedanun aljannu idan baku tuba ba ni zan zama ajalinku a dawowota ta biyu". Da gama fadar haka sukaga guguwar ta lula ta yi sama ta shiga cikin gajimare har ta bace suna kallonta. Boka Kare Dange ya ɗaga hannu ya wankawa Duduge dake dauke da shi mari hade da cewa....................
🥱 Na yau baiyi kadan ba ko?
Muje zuwa
Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group
Wa.me/+2348096831009
😍