ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 25


🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️


By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/IV1i4scamcs

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-25-hausa.html


*^ Part 25 ^*

Da fadar haka Aljana Marakisiyya ta bace bat yayinda ta bar Safuratu a karkashin teku, a tekun ma binne a cikin kasa, Aljana Safuratu tayi iya kokarinta domin ta fita daga cikin kwalbar amma abu ya gagara, ta gwada dukkan baiwarwakin da Allah yayi mata tare da ware karfinta taita dukan wannan kwalba har na tsawon sati guda, amma wannan shu'umar kwalba ko alamun tsagewa batayi ba don haka a lokacin da Aljana Safuratu ta rasa duk wata mafita da take tunani sai ta tattara dukkan tunaninta ta barwa Allah ikonsa. Duk da tana kulle a cikin kwalba ya kasance sallah bata wuceta tana kokari wajen kamanta lokacin sallah kuma tana addu'oi sosai a kan Allah ya kubutar da ita. 


Ikon Allah ya wuce mamaki, amma ita kanta Aljana Safuratu bata san yadda akayi har kwalbar nan ta fito daga cikin kasa dake karkashin teku ba, daga karshe kuma ruwan tekun wanda bata san ko na ina ne ba ma shine ya jawo kwalbar har zuwa kauyen Na'isa inda saurayi Dan Fulani ya sama nasarar fasa kwalbar wanda a nan take asirin ya karye Safuratu ta kubuta.

***** cigaban Labarin *****

Kai kawai Safuratu take jinjinawa yayin da take kallon Marakisiyya abubuwan da suka faru a baya kuma suna dawo mata sabbi fal a kwakwalwa. Safuratu ta kuma kai dubanta ga Murja wacce a wancan lokacin yarinya ce karama amma zuwa yanzu ta lalace tamkar wacce ta tasamma shekaru arba'in saboda tsabar wahalar da ta sha a cikin lalurar ta hauka. Girgiza kai Safuratu tayi hade da kallon Marakisiyya ta ce, "Nasan cewa ko a mafarki baki taba tunanin zan dawo ba saboda in da kika kaini a tunaninki a can zan kare rayuwata ba zan taba kubuta ba, amma kin manta da Allah wanda ikonshi ya wuce gaban mamaki, ko da yake ke da ire-irenku baku san Allah ba domin da kun san Allah da bakuyi wani abun ba". Ta nuna Murja da hannu wacce ita ba ruwanta bata san ma me ke faruwa a wajen ba soshe-soshe kawai take cikin hauka gashin kanta duk yayi datti da kura kasancewar babu dankwali kuma gashin duk ya dukun-kune saboda rashin gyara, hade da cewa.


"Kinga ko hakkin wannan baiwar Allah ba zai bari ki zauna lafiya a rayuwa ba, ni kuma ko saboda kyakykyawar niyata ta nufin cetonta Allah zai iya kubutar dani daga duk halin da na shiga kamar yadda yanzu ya kubutar dani daga cikin kwalbar da kuka daure ni". Kuka Marakisiyya ta saki hade da cewa, "Don Allah don annabi Safuratu karki kashe ni, wallahi bana son in mutu nayi miki alkawarin zan tuba zan canza halayena kuma tuba na har abada wallahi nayi nadam...". Garau taji an dauketa da wani lafiyayyen mari hade da daka mata tsawa, "Yi mun shiru makira maciyiya amana, kin taba ganin inda maciji ya sari mumini sau biyu a rami daya? To tun wuri ki canza tunani domin duk wani salon makirci irin naki wanda kikayi amfani da shi a baya kika cutar dani yanzu ba zaiyi tasiri a kaina ba". 


Kukan Murja ne ya sa Safuratu saurarawa sai a lokacin ta kula ashe cikin tsawa take magana wanda hakan ne ya sa Murja tsorata har ta kama kuka don haka Safuratu ta rungumeta tana lalashinta duk da tana janye jikinta. Daga bisani ta kalli Marakisiyya hade da cewa, "Ba tare da bata lokaci ba ina so kiyi gaggawar karya sihirin da kikayi na haukatar da Murja kuma ina miki albishir da cewa idan kikayi yunkurin raina min hankali na lahirama sai ya fiki jin dadi". Cikin tsoro da fargaba Marakisiyya ta ce, "Wallahi zan karya sihirin amma don Allah karki kashe ni". Tsawa Safuratu ta sake daka mata wacce don karfin tsawar sai da Marakisiyya ta tsorota, don haka ta ce suje ta kai Safuratu wajen da ta binne sihirin, nan take Safuratu ta dauketa suka tafi tana nuna mata hanya har suka je wajen wani katon dutse wanda a karkashinsa Marakisiyya ta binne sihirin, Safuratu ta dage dutsen nan take ta ga kayan sihirin duk tarkace ne irin na kayan tsafi da sunayen aljannu ciki harda sunan Murja da hotonta. Wuta kawai Safuratu ta bankawa kayan sihirin inda nan take suka kone kurmus ta daukko Marakisiyya suka dawo wajen Murja, yayin da suka isketa sai mirgina take a kasa ta rike kanta tana kuka hade da yamutse fuska alamun tana jin azaba. 


Safuratu tayi sauri ta ɗagata tana kallon halin da take ciki duk jijiyoyin kanta sun tashi gashin jikinta ya mimike nan take Murja tayi wata irin kara hade da mika cikin lokaci kankani kuma ta zube a hannun Safuratu a sume. Da faruwar haka Safuratu ta kalli Marakisiyya hade da cewa, "Me yake faruwa da Murja?". Marakisiyya da tuni tayi laushi a ranta tana ta fargabar irin hukuncin da Safuratu zatayi mata, ta ce "Dogon suma ne tayi saboda dai-daituwar kwakwalwarta da dawowar tunaninta kuma kuma ruhinta da nake juyawa ya koma gareta kasancewar sun dade basa tare da ita dole ne zatayi jinya na dan lokaci amma idan ta farka hankalinta zai dawo jikinta".



Safuratu ta ce, "Ina iya ganin wasu ajiya irin na cututuka a jikinta, ga wani a bayanta, wani a gefen zuciya wani kuma a tsakar kanta ina umartarki da kiyi gaggawar ciresu". Da fadar haka Marakisiyya ta ga sarkar da ta daure mata hannu ta kunce da kanta, nan take ta gane abinda ake nufi don haka ta shiga jikin Murja ta cire duk wani abu da ta san ta saka na cuta ko ciwo ta na fitowa ta ce ta gama. Safuratu ta ce, "Da kyau yanzu fada min sauran amfaninki da ya rage a duniya wanda zai hana in kasheki". Da jin haka cikin kuka Marakisiyya ta durkusa ta hade hannayenta biyu tana fadin, "Dan Allah karki kashe ni, wallahi har a zuciyata nayi miki alkawarin na daina munanan ayyuka zan zama mutuniyar kirki kamarki. Kuma idan har kika mun afuwa na rabu da boka na har abada kenan".


 Safuratu ta ce, "Har yanzu banji kin fadi dalili mai karfi da zai sa in rabu dake ba tare da na kashe ki ba". Nan take Marakisiyya ta fara tunani a zuciyarta tasan halin Safuratu tana da matukar tausayi don haka ta fara da cewa, "Akwai mata uku da boka Kare Dangi ya bani aikin haukatar da su, daya ma tana dauke da ciki yanzu haka na kusan haukatar da Ita, sauran biyun ma sun fara zarewa. Kuma akwai aikin raba aure guda biyar a hannuna tuni na fara saka ma'auratan tsanar junansu, sannan nayiwa wani magidanci mai iyalai da yawa kurciya ya shiga duniya ya bar iyalansa, yanzu haka iyalansa suna cikin garari abinda zasu ci ma wahala yake yi musu. Don haka nayi miki alkawarin duk zan bi daya bayan daya in karya wannan ayyuka da na aikata idan kin yafe mun". Safuratu ta girgiza kai hade da cewa, "Tabbas idan da gaske kike duk kin aikata wannan abubuwan kuma zaki karya su, to ina iya kara miki wasu kwanaki a cikin rayuwarki domin ki sama damar lalata ayyukan asirin wadannan mutane da kika zayyano, don haka ta so mu tafi tun yanzu a fara". Da fadar haka Safuratu ta juya baya da nufin tafiya, ai kuwa cikin sauri irin nasu na aljannu Marakisiyya tayi tsalle hade da watsawa Safuratu dafin sankarau a jikinta, nan take Safuratu ta zube a kasa.


Wata iriyar dariya ta mugunta Marakisiyya ta daga kai sama tanayi, kana daga bisani ta dubi Safuratu hade da cewa, "Ke sakarai ce Safuratu kuma a haka zaki kare ba zaki mori komai a duniya ba saboda baki da wayo. Idan da ni ce a matsayin ke, ke kuma a matsayina kika aikata min abinda na aikata miki na sakawa a kwalba to ina mai tabbatar miki da a duk lokacin da na kubuta ko seconds ashirin ba zaki kara yi a duniya ba zan kashe ki. Amma ke saboda wawanci irin naki wai ke gaki mai tausayi wato duk cin amanar da nayi miki a baya basu zama izina a gareni ba yanzu zaki sake bani dama ko? To bari ki ga tunda ke na baki dama kin sake dawowa cikin rayuwata yanzu zan hallaka ki in kasheki har lahira". 


Tana gama fadin haka sai ga wata doguwar takobi ta bayyana a hannunta, nan take ta nufi Safuratu dake kwance ta kasa motsa ko dan yatsanta da nufin ta raba mata wuya da gangar jiki. Sai da ya kasance sauran taku kadan ta karasa wajen sai ji zatayi Safuratu ta ce, "Bawa mutum dama ta biyu ba wawanci ko rashin wayo bane, kokarin kamanta adalci ne, domin hatta Allah idan munyi masa laifi yana bamu tarin damarmarki domin mu tuba, kuma idan mun tuba mu tabbatar bamu koma aikata wannan laifin ba, saboda haka yanzu damarki ta kare kuma na tabbata ko yanzu na kasheki bani da alhaki a kanki ko a wajen Allah domin na baki dama ki tuba amma kin nuna cewa shedanci a cikin jinin jikinki yake kuma ba zai taba fita ba har karshen rayuwarki".


Cikin kaduwa da tashin hankali Marakisiyya ta tsaya cik! A wajen da take nan take ta fara girgiza kai tana fadin "Ba zai yuyu ba, ba zai yuyu ba, babu wanda gubata ta sankarau ta shiga jikinshi kuma ya iya motsa ko da dan yatsa ne balle kuma har yayi magana". Gani tayi Safuratu ta mike tsaye cik tamkar babu abinda ya sameta. Saboda tsabar tsoro wukar dake hannun Marakisiyya sai da ta kubuce ta fadi kasa ba tare da ta sani ba, tana ta kallon Safuratu cikin kaduwa ita kuwa sai murmushi take yayin da ta nufo wajenta...........



Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments