ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 23

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*AljanaR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/IV1i4scamcs

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-22-hausa.html



*^ Part 23 ^*

Murmushi Safuratu tayi hade da cewa, "Bana tunanin a irin taurin kanki saboda wannan dan horon kawai zai sa ki karya sihirin da kikawa Murja, don haka yanzu ma zuwa nayi na kara zuba miki wasu kwari masu cizo domin nasan na jiya sun fado daga jikinki". Da fadar haka aljana Marakisiyya ta fashe da kuka nan take ta cigaba da rokon Safuratu tana fadin wallahi da gaske ta tuba, amma Safuratu bata saurareta ba ta je ta sake zuba mata sabbin kwari suka cigaba da cizonta ita kuma tana ihu tana rokon Safuratu amma tayi banza da ita ta bace. Kasancewar damuna ce, dare nayi aka sheke da ruwa, dake Murja hankalin yayi gaba haka ruwan nan ya kare a kanta da safe ta tashi da zazzabi duk abinda ke faruwa Safuratu na kallo cike da tausayawa Murja amma ba halin ta taimaketa kasancewar ruhinta na tare da Marakisiyya. 


Abun tausayi ta tashi tana bin mutane da ido duk da zazzabi ne a jikinta, da kyar aka samu wani bawan Allah ya sai mata koko da kosai, amma wasu idan ta je wajensu ma korarta suke musamman masu abincin saidawa. Hakan ba karamin karawa Safuratu tausayin Murja yayi ba don haka ta sake komawa wajen Marakisiyya a karo na biyu. Tana ganin Safuratu ta sake fashewa da kuka tana rokonta game da cewa ta tuba, kallon igiyar kawai Aljana Safuratu tayi nan take igiyoyin da ke daure da Marakisiyya suka kukunce ta fado kasa da karfi, da faruwar haka ta tashi zaune tana sosa jikinta duk yayi kullutu saboda cizon kwari gashi sai kai-kaiyi yake mata, bayan haka har hajijiya take ji saboda yadda tayi kwana uku a rataye kanta na reto a kasa. Tabbas ta sha bakar azaba ga zafin dauri, ta tabbata da mutum ce ita da sai dai gawarta.


Aljana Safuratu ta durkusa a gefe tana kallonta hade da cewa, "A taurin kai irin naki na tabbata wannan horon da na miki ba lalai ya cire tunanin cutar dani a kwakwalwarki ba domin nasan halin taurin kai irin namu na aljannu, amma ina tabbatar miki da cewa dai-dai nake dake, duk abinda kike takama da shi ki bayyana shi ni kuma zan nuna miki ni ba sa'arki ba ce". A dan tsorace Aljana Marakisiyya ta ce, "Dan Allah kiyi hakuri ki yafe mun wallahi na tuba kuma daga yanzu na daina zalunci zan ta rokon Allah ya yafe mun wanda nayi a baya". 


Aljana Safuratu ta ce, "A zahiri da zaki daina da ya fi miki, domin ko da ba zaki daina ba ki sani Murja dai idan ina da rai baki isa ki cutar da ita ba. Don kin ganni nan na san salon mugunta kala-kala idan da ni azzaluma ce to da yan adam sun shiga uku ba ma yan adam kadai ba har aljannu yan uwana sai sun yabawa aya zakinta. Amma sai ya kasance na ta so da tsoron Allah kuma na ta so da tsanar zalunci da duk wani azzalumi, yanzu ina so in san me Murja tayi miki da har kike ikirarin cewa sai kin dai-daita rayuwarta? Wace irin gaba ce a tsakaninku kasancewarta yarinya karama bana tunanin ta cancanci wanan hukunci daga gareki komai munin laifin da ta aikata miki domin na san ba lalai ne ace tana sane ta aikata miki laifi ba idan ma laifin ta miki kenan".


Aljana Marakisiyya ta sake fashewa da kuka hade da cewa, "Labarina mai tsawo ne kuma Murja bata aikata min laifin komai ba, na karbo kwangilar haukatata ne daga hannun Boka kare dangi. Kafin itama nayi masa aiki kala-kala kama daga kan haukata wasu ko kashe wasu ko kashe aure ko kuma yiwa wani kurciya, amma yanzu haduwata dake sai naji ina nadama kuma naji in ban tuba ba zan hallaka in tabbata a cikin shedanun aljannu a lahira kuma Allah yayi mini azaba tare da shedan. Saboda haka nayi miki alkawarin ba zan sake aikata mummunan aiki ba kuma zan bi duk hanyoyin da zanbi domin karya sihirin Murja ba ma ita kadai ba nayi miki alkawarin zan karya wasu asirai da nawa mutane wanda suke cikin wahala har zuwa wannan lokacin". Aljana Safuratu ta kalli cikin idanun Marakisiyya na lokaci mai tsawo domin gano gaskiyar maganar da take fada, ta dai ga kamar akwai lamun da gaske take maganar don haka ta ce, "Idan har da gaske kike ni mai iya yafe miki ce idan har kin cika alkawari kuma zan daukeki a matsayin wace zamu rika yakar mutane bata gari, na tabbata a cikin hakan akwai tarin lada mai yawa". 


Marakisiyya ta ce, "Wallahi na yarda kuma zanyi farin ciki sosai". Tana gama fadin hakan kuma sai fuskarta ta sauya daga alamun farin ciki zuwa alamun damuwa don haka Safuratu ta ce, "Ya na ga kin shiga damuwa lokaci guda haka kuma?". Marakisiyya ta ce, "Wallahi na tuno Boka Kare Dangi ne, domin ni din nan da kike gani kurwata tana hannunsa shiyasa nake tunanin ta yadda za'ayi na tsallake makircinsa har ya yarda ya sakar mun kurwata domin na sama damar fita daga harkar shedanci da yake sani. Ba ma wannan ba shi kanshi makarin cutar hauka na Murja da nake saka mata, dole sai an koma ta hannun Boka Kare Dangi, domin kamar yadda kika tarar dani a jikinta ina kan aikin ne akwai abubuwan da boka bai kammala bani ba wanda zan lalata kwakwalwarta domin in sama wajen zama na din-din-din a jikinta ita kuma zata cigaba da hauka na har abada kenan".
 

Safuratu tayi murmushi hade da cewa, "Marakisiyya na san halin markici irin namu na jinnu, amma duk da kasancewar abubuwa kalilan ne na sani dangane da tsafe-tsafe, karkiyi tunanin zaki raina min wayo ko kuma zakiyi wasa da hankalina domin idan har na gano kina kokarin yi mun wasa da hankali to tabbas na lahira ma sai ya fiki jin dadi". Da jin haka Aljana Marakisiyya cikin tsoro ta hade hannuwanta alamun roko ta ne cewa, "Na rantse miki da Allah ba karya nake miki ba idan muna son karya sihirin jikin Murja dole ne sai na karasa haukatar da ita ya kasance ni nake juya ruhinta sannan ne zamu iya karya sihirin, domin aikin da boka yayi a kan Murja mai karfi ne". 


Safuratu ta ce, "A iya sanina shi boka aikinsa kawai kulle-kulle da hada tsubbu sauran aikin kashewa ko haukatarwa mu aljannu mune muke yi, don haka karkiyi wasa da hankalina ina so kawai ki karya wannan sihiri na jikin Murja domin ko da yaushe tausayinta karuwa yake a raina". Ba yadda Safuratu ba tayi da Aljana Marakisiyya ba a kan ta karya sihirin Murja amma daga karshe dole ta hakuri domin Murja ta ce, lalai-lalai sai ta karasa haukata Murja kafin ta samu damar karya sihirin kuma sai ta jira Boka Kare Dangi ya gama hada abubuwan da take bukata. A cikin sati biyu sai da Safuratu ta sa Marakisiyya ta karya aikin sihirin da tayiwa mutane fiye da talatin. Wasu ta musu kurciya wasu, wasu ta haukata su, wasu ta raba aure hade da sa kiyayya a tsakanin miji da matan. A dan lokacin Safuratu na yiwa Marakisiyya nasiha ba kadan ba, wani lokaci idan tana mata nasihar har kuka Marakisiyya takeyi saboda tsoron Allah da kuma tunanin laifukan da ta aikata a baya. 


Ganin hakan yasa Safuratu ta yarda da Marakisiyya don haka suka cigaba da gudanar da ayyukan taimakon mutane tare duk da haka suna kula da Murja da har zuwa lokacin basu san ko wacece ita ba. Domin Aljana Safuratu ta tambayi Marakisiyya amma ta rantse mata, itama bata san komai a kan Murja ba, ta san dai wata mata ce ta kawowa boka aikin haukata Murja, ta biyashi kudi masu yawa, daga nan ita kuma aka bata aiki amma bata san komai game da ita ba. 


Yau suka shirya domin nufa fadar Boka Kare Dangi Marakisiyya ta karbo duk sauran kayan da take bukata domin karasa aikin haukata Murja, don sun tsara idan Murja ta sama lafiya zasu koma fadar boka domin a ceto Kurwar Aljana Marakisiyya da take wajen bokan, ko da yaushe yana takura mata tare da sakata miyagun ayyuka duk da kasancewar idan ta amso aikin bayi take ba. Hakan ne ma yasa Aljana Safuratu ta kara yarda da cewa lalai ta shiryu. A daren tayi duk abubuwan da zatayi wanda nan take Murja ta karasa haukacewa hauka tuburan, a daidai lokacin kuma Safuratu bata ankara ba Marakisiyya ta watsa mata dafin Sankarau dake bakinta, cikin lokaci kankani ya ratsa fatar Safuratu da faruwar hakan jikinta ya daina motsi sai idanu kawai take iya juyawa.  


Aljana Marakisiyya ta fashe da dariya irin ta mugaye kuma azzaluma kana ta ce "Yau zaki ga ranar yarda da kuma aminci........"...........


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments