ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 17

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/LgVOwZek43U


http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-16-hausa.html


*^ Part 17 ^*


Kwana biyu Mairo tana ta sake-saken yadda zata bullowa lamarin ba tare da an ganota ba, don haka ko Mahaifiyarta ba ta yarda ta nuna alamun rashin gaskiya a gabanta, duk da kasancewar kwana biyu Kubura da 'ya'yanta sun matsa lamba wajen gori da habaice-habaice saboda haihuwar tinkiyar. Yau ta kama laraba anyi ruwa irin na karshen damina gari yayi duhu sosai, kasancewar dare yayi kowa ya shiga daki ya kwanta ciki kuwa har da Mairo da itama yau tayi niyar aiwatar da abinda ke mata yawo a zuciyarta da wuri tayi bacci. 


Tsakar dare ta tashi yin fitsari ta fita, bayan tayi fatsarin sai da ta tabbatar bata jin motsin kowa a hankali ta lallaba garken awakin nasu ta kama bakin jinjirin dan tinkiyar da aka haifa ta matse dan kar yayi kuka, sannan ta murde masa wuya sai da ta tabbatar ya mutu ta bar wajen da hanzari jin tinkiyar ta fara kuka kar asirinta ya tonu domin hatta in da ta danne dan akuyan sai da ta tabbatar bata bar wata alama a wajen ba. Har safe tinkiyar na ta rusa kuka amma ba wanda ya fito saboda bacci yayi nauyi. Da safe Kubura tana fitowa idonta yayi mata arba da yar tinkiyarta a kwance kamar bata lumfashi don haka ta karasa wajen a guje ta na zuwa ta daga yar tinkiyar ai kuwa ta ganta a mace, hannu ta dora a kai ta kwala uban ihu wanda yayi kama da kukan mutuwa, don makwabta da dama sai da suka rugo gidan a tunaninsu wanine ya mutu.


Sai dai duk wanda ya shigo ya ga yar akuya ce ta mutu sai yayi tsaki ya juya, Kubura kamar ta yi hauka baki daya ta kidime Laure na ta lalashinta, amma tun a wajen take cewa ta rantse da Allah sai Fatsuma ta biyata yar akuyarta wai ai ta san ita ta cinye mata yar akuya dama tana zarginta da maita. Daga karshe har zuwa tayi ta shake Fatsuma dakyar makwabta suka kwaceta ganin Kubura zata illatata, don haka wasu suka ba Fatsuma shawarar ficewa daga gidan kafin haukan Kubura ya lafa. 


Lokacin da Bukar ya koma gidan Kubura taita mai kuka irin na munafurci ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, wai ita ala dole sai su Fatsuma sun biyata akuyarta a cewarta ko Fatsuma ko yarta Mairo sune zasu cinye mata akuya wai dama ta lura da irin kallon da sukewa yar akuyar tunda aka haifeta. Shi kuma Bukar duk abinda ta fada yarda yake, sai dare Fatsuma ta dawo gidan wanda har lokacin masifa Kubura take, Bukar din kanshi dole ta sa ya bar gidan saboda masifarta da rikici da take masa ita ala dole sai ya sa Fatsuma ta biyata yar tinkiyarta. 


Kwana biyu aka dauka ana dambarwa ba yadda Bukar baiyi da Fatsuma ba a kan ta biya Kubura kudin tinkiyarta ita kuma Fatsuma ta rantse bata da ko sisi haka zalika bata da wani abu da zata sayar ta biyata duk da kuwa ta san ba ita ta kashe akuyar ba kamar yanda suka laka mata sharri. Zaune suke a daki sai lalashin Kubura yake kamar yarinya amma ta ki sauraronsa, "Haba Kuburana sanin kanki ne ina iya jurar fushin kowa ciki kuwa harda Inna amma bana iya jure fushinki kiyi hakuri, na rantse miki inda ace Fatsuma tana da kudi ko kuma wata kaddarar da sai na tilasta mata ta biyaki kudinki".


Tabe baki tayi hade da cewa, "Ni fa ba ruwana in ma bashi zata je ta ci ni dai kawai a biyani in ma kuma kai zaka ciyo bashin ka biyani tunda matarka ce ban damu ba". Jinjina kai Bukar yayi hade da cewa, "Haba Kubura kinfi kowa sanin cewa a garin nan babu wanda zai iya daukar kudinshi ya bani bashi saboda sunyi min shaidar taurin bashi, yanzu haka jari nake nema wanda zan kama wata yar sana'a a garin nan amma abu ya gagara". Tsaki Kubura tayi hade da cewa, "Wannan kuma kai ka so tunda ga awaki nan a hannun matarka duk wanda ka kama ka sayar ba zata ce kala ba". Shiru yayi yana kallonta da alamu bai fahimci me take nufi ba don haka ya ce, "Wace matar tawa kuma wane awaki kike nufi?". "Ita Fatsuma mana ba ga awaki nan da take kiwo ba har biyu in da gaske jarin kake so ka kama daya ka sayar mana in ya so sai a biyani kudin tinkiyata sauran kuma ka kama sana'a in ya so idan kasuwa ta kafu sai ka biyata ka mayar musu da akuyarsu.  


Shiru yayi na dan lokaci kafin ya ce, "Wallahi kanki yana ja Kubura, kinga ni ko kadan wannan tunanin bai zo mini ba yanzu bari ki ga inje in sanar da ita in ya so faduwa ta zo dai-dai da zama yanzu kawai sai in kama Akuyar in kaita kasuwa tunda dama yau kasuwa ke ci". Kubura tana dauke kai ta ce, "Ah to ya fi dai don wallahi a kan kudin tinkiyata ina iya tattara kayana in bar maka gidan idan ba'a biyani ba". "Haba Kubura me ya kawo maganar nan kuma? Ina ce dai kudi ne? To kwantar da hankalinki yau-yau za'a biya ki kudinki". Da fadar haka ya fita ya nufi dakin Fatsuma


A daidai kofar dakin ya fara kwalla mata kira, "Fatsuma! - Fatsuma!". Cikin bacci ta ji kiran nashi ta amsa a firgice hade da ta shi ta yo waje, durkusawa tayi a gabansa, "Don iskanci da rainin wayo kina ji ina kiranki shine kikayi shiru wato rainin da kika min har ya kai haka ko?". "Don Allah kayi hakuri Baban Zubairu wallahi bacci nake shiyasa banji ba". Ya kalleta hade da cewa, "Kinga ba wannan ya kawoni ba zuwa nayi in fada miki zan kama waccan akuyar karama ta wajenki in kai kasuwa". Shiru tayi gabanta na faduwa domin bata ma fahimci inda maganar ta shi ta dosa ba don haka ta ce, "Ita Ladin ce ta ce a kama akuyar a sayar?".


"Ba ita ta ce ba, ni da yayarki Kubura muka zauna mu mukayi wannan tunanin domin kinfi kowa sanin halin da ake ciki, Kubura dai ba yafe miki zatayi ba don sai kin biyata akuyarta ni kuma dama ina neman jari wanda zan kama sana'a a kauyen nan domin zama haka ya isheni, to shine mukayi shawara kuma na ji na gamsu da shawarar kinga idan aka sayar da akuyar sai a zo a biya Kubura kudin yar tinkiyarta sauran kuma sai in rancesu inyi jari, allabishi idan kasuwa ta kafu sai in biya kudin ni gaba daya akuyar ma zan sayI wata a mayar". 


Kuka Fatsuma ta fashe da shi domin tunda ya fara maganar gabanta ke faduwa, musamman da yake zayyano maganganun wanda suke cike da son kai hade da zalunci. "Don Allah Baban Zubairu kayi hakuri karka kama musu akuya ka sayar in sha Allah kudin Kubura ko nawa ne zanyi aiki tukuru kama daga kan daka da wankau ko jan ruwa na hada kudin na biyata. Amma idan ka sayar da akuyar nan Ladi ta zo ta ce ina akuya da wane ido zan kalleta?". Baki ya kama hade da cewa, "Yanzu Fatsuma miye na kuka a cikin maganganuna? Da har zaki wangame baki ki kama kuka sai kace an aiko miki mutuwar iyayenki. Ni a ganina wannan shawara ai taimakon kai da kai ne baki daya, kuma kamata yayi kiyi alfahari zaki taimaki mijinki a kan hakan ma har lada sai kin samu a wajen Allah". 


Cikin kuka Fatsuma ta ce, "Kayi hakuri baban Zubairu na rantse da Allah da akuyata ce zan iya baka kyauta ma amma wannan kayan mutane ne. Idan aro kake so Kubura Akuyoyinta biyu tinkiya daya, ga Laure nan itama Tinkiya biyu gareta mai zai hana kuyi shawara da su, su baka aro ka kama ka saida amma don Allah karka sai da na mutane". Laure dake bakin kofa cikin dakinta tana sauraron abubuwan dake faruwa tsakanin Bukar da Fatsuma tamkar an jefota ta fito waje tana tafa hannun tana salla-lami "Iyeeh yar bakin ciki"..................


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

😍

Comments