ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 16

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/LgVOwZek43U


http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-15-hausa.html



*^ Part 16 ^*


Bayan sallah da kwana biyu da yamma Kubura ta wanke kayan sallar 'ya'yanta gaba daya ta shanya da niyar ta linke ta ajiye musu tunda sallah ta wuce. Mairo ba karamin dadi ta ji ba da ganin Kubura na wanki ita kadai tasan abinda take kullawa a zuciyarta. Don haka kayan basu bushe ba har dare saboda yanayin garin ba iska, da dare Mairo kamar munafuka ta lalaba ta sace kayan sallar Wasila wanda dama na ta ne da aka kwace ta falfala da gudu ta kaiwa Inna Ma'u ajiya. Kubura kam bata kula da babu kayan ba sai da safe bayan sun bushe da ta zo kwashewa, "Kutt... Yau akwai bala'i a gidan nan kowa ya fito na rantse da Allah sai an fito da kayan Wasila". 


Kubura ce ke fadin haka cikin masifa, Fatsuma Da Laure duk suna daki jin irin ashar din da Kubura take ya sa duk suka fito, "Yaya Lafiya kuwa irin wannan zagi haka tun da safe yau kuma da shi muke karyawa?". Cewar Laure dake gyara daurin kirjinta. "Ina kuwa lafiya! kayan Wasila na sallah tare da wadannan na shanya su, yanzu na zo kwashe shanya sun ce na dauke su a inda na ajiye, wato an biyo dare an sace to na rantse da Allah a fito da su ko a ga bala'i harda wasali sama a gidan nan". 


Fatsuma bata ce kala ba, Laure ta ce "To Yaya ni a ganina ai wannan lamari a bayyane yake, masu kayan ne suka dauke abunsu". Duk suka kai dubansu ga Fatsuma, ganin haka ya sa ta ce, "Yaya wallahi ban dauka ba, ni kayan nan tuni sun fita daga lissafina". "To in baki dauka ba ai Mairo na iya daukar kayan". Cewar Laure, Fatsuma ta ce, "Na tabbatar Mairo ma ba zata dauka ba, amma kuma in baku yarda ba kuna iya shiga dakin ku duba ko ina da kuke tunanin za a iya boye kayan". Da fadar haka kamar jira suke suka fada dakin na Fatsuma da babu wani abun a zo a gani a ciki, duk suka bincike shi amma ba su sama kayan ba.


"Na rantse da Allah ba zai yuyu ba, a fito da kayan nan ko ayi bura uba a gidan nan, daga wanke kayan yarinya sai a biyo dare kawai a sace. To duk ma wanda ya dauki kayan nan ya kuka da kanshi ya fiddo su tun muna shaida juna, in ba haka ba ni mai iya biyan kudi ne a zagaya Al'qurani duk wanda ya dauka ya mutu ba ruwana wallahi". Bala'i ya kai bala'i Kubura sai da ta tayar da hankalin kowa a kewayan unguwar ta su, nan mutane suka rika lekowa ta katanga suji ko lafiya, da yawa a tunanin su ma bala'in da Kubura take yi Fatsuma take wa kamar yanda ta sa ba. Abun bai isheta ba har rana tayi Kubura tana bin gidajen makwabta tana cigiyar wanda ya saci kayan Wasila, in ta je gidan da ta raina matar gidan har bincike musu kaya take. Mairo da ta dawo gida tana jin duk abinda ake tayi kamar ba ita ta dauka ba. 


Kubura ta balbaleta da masifa har wuka ta fiddo da barazanar zata yanka Mairo idan bata fiddo kayan ba amma ta ce ita fa ba ita ta dauka ba. Haka Bukar da ya dawo gida shima yayi duk barazanar da zaiyi ga Fatsuma, Mairo kam har da duka ya hada mata amma kayan basu fito ba, haka Kubura ta gama masifarta har dare kaya basu fito ba. Bayan kwana biyu Mairo ta je gidan Inna Ma'u ta karbi kayan ta mayar wa Salame ta fadawa Maman Salame abinda ya faru don haka ta ce da ta barwa Wasila gwara ta kawowa Salame ta hada biyu domin ita ko ta koma da kayan gida sake kwacewa za'ayi.


A bangaren Kubura kuwa anfi sati guda, kullum sai tayi masifa a kan kayan nan. Barazana kuwa tayi kala-kala ga Fatsuma da yan unguwa amma kaya sunki fitowa don dole ta hakura da kayan. 


Zaune suke a karkashin inuwar bedi bayan sun dawo daga gona gaba daya a gajiye suke suna hutawa, Laure ta ce, "Halima tashi zakiyi fa mu tafi debo ruwa kinsan dai a gidan nan ko ruwan sha bamu da shi". Halima tana yamutse fuska ta ce "Laure wallahi na gaji yanzu fa muka dawo daga gona a dan bari mu kara hutawa mana, nasan ana jimawa zaki ce na surfa dawar da za'ayi tuwon dare". Laure zatayi magana kenan suka ji ance "Gafarar ku dai masu gida". Gaba daya suka kai dubansu kofar gidan harda su Kubura baki daya, da sauri Laure ta mike cikin fara'a tana fadin, "Aa wa zan gani yau a gidan Kawata kece kuwa, ashe idan ba'a mutu ba ma ana rabuwa?".


Murmushi matar tayi yayin da suka rungume juna da Laure, nan suka gaisa da Kubura sama-sama Laure tayi mata jagora suka fada daki Kubura ta bisu da kallo ta gane matar sarai, Laraba ce wacce aka kuresu ita da mijinta daga kauyen saboda tsabar makirci da kulle-kulle irin nata, kuma kawar Laure ce ta kut-da-kut tun suna garin ma. Bayan sun shiga dakin sun zauna Laure ta ce, "Laraba manyan gari ashe ana ganinku da sauki haka?". Murmushi tayi hade da cewa "Ai kune manyan gari tunda gashi tunda na bar kauyen nan ko da wasa baki taba kai min ziyara ba anya da amana kuwa?". Laure ta ce, "Yi hakuri kawata wallahi abubuwan ne suke yawa kinsan idan aka ce miki lokacin aikin gona ne to fa mutum baya samun sukuni ko kadan, yanzu haka bamu dade da dawowa daga gona ba dibar ruwa kuma zamu tafi, bayan nan kuma yau ni nake da girki kinga kuwa ina wani lokaci a nan?". 


Laraba tayi murmushi, hade da cewa "Ai wallahi in mutum ya biye ayyukan gida ko kadan ba zaiyi wani abun ba, nima ayyukan suna can gida jibge na tsallakesu na yo nan domin akwai muhimmiyar maganar da na taho miki da ita". Laure ta washe hakora hade da cewa "Allah kawata? To fesa mun da dumi-duminsa kar ya huce". Shewa sukayi hade da tafawa Laraba tayi kasa da murya hade da cewa, "Ke ba wannan ba na ji kina cewa zakiyi girki? Yaushe kuka karbi girkin gidan nan ne daga hannun Fatsuma? da dai nasan ita take muku wani lokaci har dakan fura ma". Laure tayi kwafa hade da cewa, "Bukar ne ya ce ta daina wai sam baya jin dadin girkinta kinsan fa har yanzu a hannun Yaya Kubura yake ita ke juyashi duk yanda ta so". 


"Haba kawata wallahi kin bani kunya kina da kamata amma ace kin tsaya a cikin gida haka kawai wata na juya mijinku! ina kwarewar taki take?". Laure tayi kasa da murya hade da cewa "Ke Laraba raba kanki wallahi duk bin malamai da bokayena Kubura ta damani ta shanye, tilas ne ma ta sa na zubda makamaina na bita don ganin makircinta ya dame nawa ya shanye". Dariya Laraba tayi hade da cewa "To kwantar da hankalinki in dai Kubura ce na rantse miki karamar alhaki ce a gareni, yanzu ma maganar dake tafe dani kenan, munyi sabon kamu wallahi aikinshi kamar yankan wuka na jaraba ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba naga biyan bukata shiyasa na ce ba za'ayi wannan sabgar babu ke ba, don haka idan kina bukatar ragamar gidan nan ta dawo hannunki to ga dama ta samu sai dai fa shi wannan malamin akwai shan mai ah to". Labara ta karasa maganar tana mai dauke kai. 


Shiru Laure tayi tana sake-saken zuci, tabbas abun dadi ne ace ita ke juya gidan nan kamar yanda Kubura ke juya Bukar, amma ita ba karamin tsoron Kubura take ba saboda makircin Kubura ya fi gaban kwatance, don haka ta san cewa idan har Kubura ta gano cewa tana kulla mata wani makircin to fa kashinta ya bushe, don haka ta cewa Laraba sai tayi shawara ko me kenan zata isketa har gida, a haka aka rabu.


  Yau tinkiyar Kubura ta tashi da nakuda ai kuwa unguwar kowa sai da ya sani, don Kubura ta bi gida ya kai goma neman magani hade da neman shawara yadda tinkiya zata haihu lafiya. Daga karshe dai tinkiya ta haihu lafiya, ai kuwa murna da farin ciki a wajen Kubura ba'a magana, Laure ma na tayata don kar ace bakin ciki take. Fatsuma kam har kofar dakinta akaje ana fada mata haihuwar, tayi Allah yasa albarka tare da fatan Allah ya raya amma sai abun ya zama kamar laifi nan fa aka bita da bakaken maganganu da habaice-habaice. 


A bangaren Mairo kuwa tun da ta shigo gidan ta tarar da anyi haihuwar ta shiga sake-saken zuci domin kuwa dama ta dade tana jiran wannan rana. Tayi rantsuwa har a zuciyarta ba zata yafe kashe yar akuyarsu da Yaya Kubura tayi ba...................


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

😍

Comments