🧟♀️🧟♀️ 🧟♀️🧟♀️
*ALJANAR FATIMA BOOK 2*
🧟♀️🧟♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟♀️🧟♀️
By *Kingboy Isah*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/AMK4CDYUZ54
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-14-hausa.html
*^ Part 15 ^*
Nasmat ta ce, "Mama kwantar da hankalinki kudin napep kawai zaki bamu in mun gama cin abinci mu dauketa a buhu mu kaita can bayan gari mu wullar inda ba zata dawo ba, ko Asmart". "Eh Mama Asiya ki bamu kudin mashin kawai mu je mu wullar miki ita". Tunda naji haka na kama kuka don na san idan magena ta shiga hannun su Asmart sai sun kasheta. Ai kuwa bayan an gama cin abinci wajen karfe tara da rabi Mama Asiya ta basu dari biyar wai su kai magen can nesa inda suka tabbatar ba zata dawo ba.
Suka karba da gudu suka bini har daki suka kwace magen ina kuka suka sakata cikin buhun shinkafa suka fita da ita. Suka hau napep sai da sukayi tafiya mai nisa bayan sannan suka isa wani dan jeji a nan mai napep ya jira su kuma suka kara shiga cikin jejen, Asmart ta kara kulle bakin buhun zata wullar da ita Nasmat ta ce, "Kawo ki ga yadda ake wa mage idan ba'a sonta". Buhun ta karba ta buga magen da kasa sau uku sannan ta wullata da karfi sama suna ji ta fado sai kuka take suja juya suka hau napep sukayi tafiyar su.
Da suka dawo gida suka fadawa Mama Asiya ba karamin dadi taji ba, ni kuma wuni nayi ina kuka ko abinci banci ba saboda naji su Asmart sun ce sun kashe magen, a lokacin bani da abokin hira ko abokin wasa dama daga magena sai yar baby na muke wasa. Da dare muje cin abinci su Asmart na zaune a kan kujerar Dinner suka fara jin hajijiya da ciwon kai, lokaci guda muka ga suna zabura suna cewa gata nan ga ta nan. Ashe wai magen suke gani tana binsu tana kuka.
Sai da suka tayar da hankalin kowa a gida, ita kanta Mama Asiya ranar batayi bacci ba saboda yadda aka rika bata tsoro dole ta sa da safe aka nemo malami yayi musu rukiyya sannan suka sama saukin abun. Bayan kwana biyu da faruwar haka har na manta sai ga magena ta dawo gida, ban kawo komai a raina ba na dauki abuna. Lokacin da su Mama Asiya da su Nasmat suka ganta sai gudu, domin su suka ga abinda suka gani. Amma daga ranar basu kara yunkurin rabani da magen ba domin tsoronta ma suke idan suka ganni da magen sai dai su gudu".
Mairo ta kyalkyale da dariya hade da cewa "Umma dama Allah ya bani irin wannan magen da su Yaya Kubura sun gane kurensu". Fatsuma tayi murmushi hade da cewa, "Ai nima daga karshe magen guduwa tayi bansani ba ko mutuwa tayi ko me ya faru oho". "Aa Mama to ina ce aljana ce ai magen". Fatsuma ta ce, "Aa ai duk abinda ke faruwa Aljanata ce take shiga jikin magen amma ita magen ba Aljana bace, wasu abubuwan ma ita Safuratu da kanta take bani labarinsu wanda ban sani ba".
Mairo ta ce, "Ya Allah kasa Safuratu bata mutu ba, Allah kasa ta dawo ta rama mana zaluncin da ake mana a gidan nan". Fatsuma ta ce, "Ameen baby, amma ina ji a jikina Aljanata bata mutu ba kawai dai tana cikin mummunan hali tunda ina yawan yin mafarkinta a cikin hali mawuyaci".
Mairo ta ce, "To Umma dama suma aljannu akwai abinda ya fi karfinsu ne balle kuma har ya sasu cikin hali mai wahala?". Murmushi tayi hade da cewa, "Baby kenan, ai aljannu ma halittar Allah ne, don haka kamar yanda a cikin mu mutane akwai masu karfi akwai marar karfi to suma haka wani ya fi wani karfi ai". Mairo tayi shiru tana sake-saken zuci a haka har bacci yayi gaba da ita, Fatsuma ta shimfideta itama ta kwanta.
A kwana a tashi sallar azumi ta zo, kowa yayi kwalliya da sabbin kaya a gidan banda Fatsuma da Yarta Mairo, yara suka tafi Idi Salame ma ta biyowa Mairo su tafi tare amma Mairo ta ce ba zata je ba. A nan ta fadawa Salame an kwace mata kayan sallarta da babansu ya dinka mata, don haka Salame taje ta fadawa mamanta ita kuma ta fadawa Baban Salame, bayan an taso daga Sallar Idi tafe yake yana shan rake yaji ana kwala mai kira ta baya don haka ya waiwaya, "Haba Malam Bukar tun daga nesa nake kwalla maka kira amma kaki tsayawa". Rake ya gabtara sanna ya ce, "Haba Malam Lado ai idan mutum yana shan rake uzuri ake masa, domin mutum fita yake daga duniyar nan".
Lado yayi murmushi hade da cewa, "To ba wani abu bane dama dazun kafin na fto daga gida Habiba take fada min wai Salame ta biyawa Mairo su tafi idi Marion take fada mata ba zataje ba domin an kwace kayan sallar da na dinka mata an baiwa Wasila, shine na ce ya za'ayi hakan ta faru amma na ce zan sameka domin inji gaskiyar magana?". Bukar ya gyara tsayuwarsa hade da cewa, "Eh gaskiya haka ne, mantawa nayi ma banyi maka godiya ba, kasan harka ta dangi ni a kullum so nake in ga kan gidana a hade to shine ita abun nan am Kubura ta ga wannan kaya sunyiwa Mairo yawa shiyasa ta ce to bari ta dauka ta bawa ita yayarta wato Wasila ni kuma da naji haka sai ban hana ba saboda kyauta na matukar kara karfafa zumunci a tsakanin yan uwa".
Lado ya ce, "Ban tari hanzarinka ba Malam Bukar amma a zahiri wannan rashin adalci ne kuma abinda kayi banji dadinsa ba. Domin ita Mairo da kunnena naji tana fadawa Salame cewa ita kadai ce ba kayiwa dinkin sallah ba a gidan, wannan dalili ne ma yasa na hada nayi musu dinkin tare, to a name kuma zaka dauki kayan wacce bata da kayan sallah ka karawa wacce take da shi wai sa sunan kara dankon zumunci wannan ai bata zumunci ne ba gyara ba".
Hannu ya daga masa hade da cewa "Dakata Malam Lado, duk wannan doguwar hudu ba da kake ba ita zata sa na canza ra'ayina ba abinda na ga damar yi shi nake yi a gidana babu kuma wanda ya isa ya ce ba haka ba, ni ka ga tafiyata". Yana fadar haka yayi gaba ya bar Lado tsaye yana mamakin rashin adalci irin na Bukar. Ranar sallar yara kowa da sabon kaya ana ta shagwulgula a dandalin a bangaren Mairo kuwa tana daki ita da uwarta don kar kadaici ya wa Mairon yawa ma sai Fatsuma ta sa suka jona da karatu, hatta abincin sallah ba'a basu a gidan ba sai makwabta wanda suke mutunci da Fatsuma suka aiko mata da kuma gidan su Salame da aka kawo. Sai ya kasance har sun fi su Kubura samun abinci mai dadi ma, domin tuwo ne akayi a gidan miyar kubewa...........
Muje zuwa
Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group
https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N