ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 14


🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️


By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/AMK4CDYUZ54
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-13.html

*^ Part 14 ^*

Mairo ta ce, "Amma wallahi mama Asiyar nan shegen tsoro yayi mata yawa". Cikin yar dariya wacce bata fito fili sosai ba Fatsuma ta ce, "Ai ko kece ita dole ki tsorata". Mairo tace, "Wallahi kuwa Umma ai labarin ne da tsoro, amai dai ya mun dadi a cigaba Ummana". Ta fada tana kara gyara kwanciyarta a kan cinyar Umman nata, Murmushi Fatsuma tayi ganin yadda Mairo ta saki jiki tuni ta ma manta da matsalolinta hankalinta ya dawo wajen labari, kamar ba ita ta gama kuka yanzu ba sai sauke ajiyar zuciya da take lokaci zuwa lokaci. Fatsuma ta ce "Lokacin da Mama Asiya ta juya taga lalai karfen makale labule ne ya rike mata riga, nan take ta fizge rigar hade da yowa waje da gudu har tana neman banke Zuwaira, da faruwar hakan Ameera, Nasmat, Asmat, Fiddausi da sauransu gaba daya suka kwashe da dariya harda rike ciki. 


Mama Asiya da ta sama kujera ta zauna tana maida lumfashi haushi ya kumeta ta jiyo ta galla musu harara wanda ya tilasta su rufe bakuna suna matse dariyar. Mai gadi zai fita Mama Asiya ta ce "Zo zo Musa ai ba tafiya zakayi ba, shiga zakayi dakin nan ka kamo aljanar magen nan da idona na ganta baka kirin idanunta jawur kamar garwashi". Tsaye yayi a wajen ya juyo yana raba idanuwa jin an ambaci aljanar mage "Hajiya kin tabbatar kuwa akwai mage a dakin ki, ni dai mage daya na sani a gidan nan wacce Alhaji ya kawowa Fatima itama kuma jiya kika bani ita na kaita can wata unguwa na yadda ita, unguwar da na kaita kuwa na tabbatar ko ita aljana ce ba zata iya gane gidan nan ba". 


Da jin ya fadi haka Mama Asiya ta bata fuska hade da cewa "Au kana nufin karya zanyi ma banga magen ba ko? To bari kaji abinda yasa nace aljana ce har wutar dakin na kunna ita kuma ta kashe, in ba aljana ba ya za ayi mage ta kashe wutar daki?". Musa ya ce "Aa Hajiya wallahi ba ina nufin kinyi karya bane amma ina zuwa bari na yo shirin kunar bakin wake na zo na shiga dakin ba aljanar mage ba ko ifiritu ne sai na kamo shi" Da fadar haka ya fita a guje zuwa dakinsa


Mu dai muna tsaye a kofar dakinmu sai gashi ya shigo dauke da adda da katuwar sanda ya rataya wasu layoyi a wuya, "Yauwa Hajiya yanzu na shirya bari inje in kamo magen". Musa mai gadi ya fadi haka yayin da ya nufi kofar dakin mama Asiya kamar zai shige kai tsaye kuma sai ya tsaya a kofar yana lekawa tamakar kace masa arr! Ya yo baya a guje, cikin sanda ya tura kafarsa a cikin dakin yana dube-dube yayinda yake rike da sanda da adda ko wacce hannunta daban. Nan dai ya gama dube-dubensa ko ina ya duba har karkashin gado amma bai ga ko kiyashi ba, don haka ya fito bakin kofar yana cewa "Wallahi Hajiya ko bera ban gani ba balle mage watakil kawai tsorata kikayi amm...". Wutar dakin muka ji an kashe yayin da mukaji kukan mage "Meoooooowwwwww! Meoooooowwwwww!". Da karfi.


Cikin yan sekonni dakin ya hargitse da ihu da guje-guje, ni dai ina tsaye ji nayi kawai an banke ni na fadi kasa saboda duhu bansan waye ya bigeni ba. Ina jin ihun Mama Asiya Zuwaira Mai Gadi da su Fiddausi kowa neman fita yake daga falon amma duhu yayi yawa ko tafin hannu mutum baya iya gani, a cikin guje-gujen Zuwaira da Mama Asiya sukayi karo da juna suka bige nan take suka zube a kasa Mama Asiya ta kurma ihu hade da cewa "Wayyo Allah nayi karo da aljanar Innalillahi, don Allah kiyi min rai bansan abinda nayi miki ba aljana karki kashe ni". A daidai lokacin suka ji an kunna wutar dakin Asmart da Nasmat ne tsaye a wajen makunar wutar, nan take suka bushe da dariya ganin irin halin da mutanen falon suka shiga.


Wai ashe sune suka kashe wutar kuma sukayi kukan magen, Mama Asiya zaune take dirshan a kasa ita da Zuwaira a lokacin ta ga ashe da Zuwaira sukayi karo ba aljana ba, ta kalli su Asmart da suke dariya hade da cewa "Ku kuma uban me kukewa dariya?". Wata dariyar suka kara bushewa da ita irin ta mugunta harda hawaye, Nasmat tace "Na rantse da Allah matsorata sunyi yawa a gidan nan, dubi mai gadi da yake cika baki da zu amma ya makale a waje daya sai karkarwa yake". Asmart cikin dariya tace "Ga Aunty Fiddausi a bayan kujera ita kuma Aunty Ameera ko me take a bayan labule, to wallahi ba wani aljanar mage mune nan muka kashe wuta kuma mukayi kukan mage".



Wani irin ashar Mama Asiya ta rika aika musu, a dakin ni da Fiddausi ne kawai bamu zagi su Nasmat ba Ameera kam binsu tayi da gudu zata dukesu suka fada daki suka kulle. Mai gadi ya fita yana Allah ya isa a nan Mama Asiya tace duk da Mai gadi ya ce babu mage a dakinta wallahi ba zata kwana a dakin ba a nan ta kwana a falo kan kujera batayi baccin kirki ba saboda a tsorace take. Da safe bayan an fito wajen karyawa ina fitowa daga daki naji magena tana bina tana kuka. Wani irin farin ciki naji ya ratsa zuciyata na durkusa na dauketa ina shafata, don a lokacin nayi tunanin Musa kasheta yayi da ya fita da ita. Falon na nufa da abuna kamar yanda na saba tare muke karyawa da magena, Mama Asiya na ganina ta tashi daga inda take zaune a dinner table ta ruga da gudu daki, duk mutanen falon suka bita da kallo


Daga cikin dakin ta leko hade da kallona tace, "Ke Fatima a gidan ubanwa kika sama wata mage kuma banda wacce na kwace jiya?" Gaba daya suka juyo suna kallon magen hannuna Asmart ta ce "Mama Asiya ai wannan dai ita ce magen Fatima da kowa ya sani ba wata ba, nan Mama Asiya ta fito tana zazzare idanu a tsorace ta karaso wajena tana duba magen. "Nasmat maza je ki kirayo min Musa inji dama bai yadda wannan tsinanniyar magen ba ashe". Nasmat ta tafi jim kadan sai ga su Musa na biye da ita a baya, bayan ya shigo falon shi kanshi da ya ga magen sai da yayi mamaki, a nan ya tabbatarwa da Mama Asiya inda ya kai magen in dai ba aljana bace to bata isa ta gane gidan ba har ta dawo da kanta..............


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 
https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

Comments