🧟♀️🧟♀️ 🧟♀️🧟♀️
*ALJANAR FATIMA BOOK 2*
🧟♀️🧟♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟♀️🧟♀️
By *Kingboy Isah*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/AMK4CDYUZ54
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-12-hausa.html
*^ Part 13 ^*
( Nima fa jiran Safuratu din nan nake wanda ya ganta ya taimaka ya sanar mata halin da su Mairo ke ciki 🙄 )
Fatsuma ta gyara zama tana mai cewa, "Lokacin ina yarinya kafin su Mama Asiya, su san Safuratu na tare dani, babana ya taba kawo min farar kyanwa mage mai kyau, saboda yaga ina son mage don yasha ganin ina daukko na makwabtanmu ina wasa da su. Nayi farin ciki da murna sosai domin in son mage. Haka na rika kula da mageta ko da yaushe muna tare hatta bacci baya rabamu makaranta ce kawai ke rabani da ita. Ranar nan ina zaune a tsakar gida ina ba magena sauran madarar da babana ya sayo min washe garin ranar da zai tafi kasar waje, Mama Asiya ta zo wucewa ta wajen nan take ta fara min fada tana cewa, "Wato ke Fatima tunda babanki ya kawo mikin wannan tsinanniyar magen baki da aiki sai wasa da ita da jagwalgwalata ko? Nasan abinda zanyi".
Ina jin ta fadi haka na rungume magena ina binta da kallo, jim kadan sai ganinta nayi sun dawo tare da mai gadi, ta ce "Musa maza kama magen nan ka san yadda zakayi da ita bana so na sake ganinta a cikin gidan nan". Da jin Mama Asiya ta fadi haka ni kuwa na fashe da kuka hade da rungume mageta a jiki kamar zan sakata cikin kirjina, na fara rokon Mama Asiya kar ta kwace min mage amma ina. Musa ya kwace magen daga hannuna ina kallo ya fita da ita banda kuka babu abinda nake daga karshe Mama Asiya ta wulla min harara tace in ban mata shiru ba sai ta gaggaura min mari dole ta sa nayi shiru ina ta kukan zuci.
A duk yinin ranar haka na yini babu sukuni har dare, duk sanda na tuna mageta sai inji hawaye na zubo min a zuciya ina tunanin, shikenan an rabani da mageta mai debe min kewa. Tsakar dare Mama Asiya na kwance a dakinta ta fara jin wani abu na taba bayanta, nan take ta bude idanu yayinda ta sa hannu tana lalubawa bataji komai ba, hakan yasa ta rufe ido da niyar komawa baccinta. Wani kara taji ratsam! Tamkar an fasa kwalba a saitin wajen mirror dinta.
Saboda haka ta tashi da sauri, kasancewar dakin da duhu ta kunna wuta tana kunnawa ta ga giccin wani bakin abu ya fita ta tagar dakin nata wanda bata tabbatar da ko miye ba. Ta duba wajen madubi da taji kamar an fasa kwalba bata ga komai ba, don haka bata kawo komai a ranta ba ta ja tsaki hade da kashe wuta ta nufi gadonta domin kwanciya. Kwantawar da zatayi taji ta kwanta a kan wani abu mai laushi da bata tabbatar da ko miye ba, nan take taji wani irin kuka irin wanda mage take yi idan taji wahala 'Myyyww' cikin razana da kaduwa Mama Asiya tayi kundunbala ta fado daga kan gadon ba tare da la'akari da ko taji ciwo ko bataji ba ta ruga a guje ta kunna wutar dakin tana duba saman gado taga wayam ba ko kiyashi.
Ta karasa bakin gadon a tsorace tamkar kice "Arrr" ta zuba a guje, kinsan Mama Asiya mutum ce mai jiki don a kibarta zata kai ukun Kubura". Mairo da ta natsu tana jin labarin ita kanta tsoro ya fara shigarta, zare ido tayi hade da cewa "Ashe lukuta ce". Fatsuma ta ce "Sosai ma domin a nan garin babu wacce zata kai kibar Mama Asiya. A haka ta leka karkashin gado nan ma bata ga komai ba, ta daga filo da bargon dake kan gadon duk dai bata ga komai ba, nan take ta yanke shawarar komawa ta kwanta amma a wannan karon bata yarda ta kashe hasken dakin ba. Har ta kwanta ta fara jiyo kukan mage daga saitin bandakin dake cikin dakin nata.
Murya a raunane tamkar zatayi kuka ta fara cewa "Waye! Waye yake tsoratani?". Shiru bata ji ance kala ba sai kukan magen da yake ta kara karfin sauti. A hankali ta sauka daga ka gadon ta nufi bandakin cikin sanda tamkar munafuka ta sa hannu a hankali ta mura key din bandakin yayin da ta leka haske fayau bata ga komai ba, nan take kuma taji kukan magen ya dauke. Kamar daga sama taji mage ta fado jikinta dai-dai lokacin wutar dakin ta dauke. Wani irin ihu wanda bata taba yin irinsa a rayuwarta ba ta zunduma. Yayin da ta fadi kasa tana birgima hade da kakkabe-kakkabe a jikinta. Ihu take ba ji ba gani tana ambaton sunan duk wanda ya fado mata a baki.
Zuwa can ta ankara da ba komai a jikinta kawai firigita ne tayi, don haka ta tashi da sauri a razane ta lalubo makunar wuta ta sake kunnawa abin ya daure mata kai ta tabbatar da hannunta ta kunna wutar dakin amma gashi ta tarar a kashe. Don haka ta yanke shawarar barin dakin gwara ma ko falo ne ta koma ta kwanta, da sauri ta nufi kofar fita hannunta na karkarwa tamkar suna rige-rigen bude kofar da wani, ta bude kofar hade da yunkurin fita, nan fa taji an rike rigarta ta baya
Ba tare da ta juya ba ta kwada wani irin ihu tana fadin, "Innalillahi wa'inna Illahir Raji'un na mutu na lalace, Aljana jama'a ku ceceni aljana ta kamani. Ameera! Asama'u! Hauwa! Zuwaira! Ku ceceni dan girman iyayenku aljana ta rike ni". Cikin ihu da karfi take maganar tamkar wacce ake zarewa rai, lokaci kankani ta tashi dukkan yan gidan ciki kuwa harda mu. Gaba daya muka fito mukayi cirko-cirko a falo muna kallonta tana ta ihu muje mu ceceta. Kowa tsoro yake ji a lokacin shiyasa aka rasa wanda zai karasa wajenta, hatta mai gadi da yaji ihun ya zo ya kwankwasa an bude masa amma shima jin tana cewa aljana ce ta riketa sai yayi kamar ya ma fi kowa jin tsoron.
Duk da kasancewar falon a haske yake fau da kwayaye muna kallon Mama Asiya kanta waje sauran jikinta a cikin daki amma saboda girman jiki irin nata sai ya kasance ta cika kofar dakin bama iya ganin abinda ke bayanta. Zuwaira ce ta fara isa wajenta cikin tsoro a haka tayi jarumtar kama hannun Mama Asiya da take mikowa tana fadin a ceceta a janyeta daga hannun aljana. Zuwaira ta jata da karfi yayinda mu kaji rigarta na yagewa a lokacin Zuwaira ta hango ashe abin makale labulen daki ne ya rike mata rigar". Mairo ta gagabe da dariya kamar ba itace take kuka yanzu ba...................
🥱 Ayi hakuri dai nima nasan yana kadan din, amma in dai ana samun damar typing din a kullum to da sauki thanks
Muje zuwa
Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group
https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N