ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 12

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/f-midB4rvJs
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-11-hausa.html


*^ Part 12 ^*

"Yaya! Yaya! fito-fito". Da sauri ta fito daga daki tana daura dankwali "Laure lafiya kuwa kike kwala min irin wannan kira kamar wacce ta ci bashi bata biya ba". "Yaya ai dole na kwala miki kira zo ki ga dinkin da Fatsuma tayiwa Mairo". Da gudu ta karaso ta fada dakin hade da warcewa "Kambala'i na rantse da Allah ba'a isa ba wannan dinkin ko kadan bai dace da Mairo ba da Wasila ya dace, au ashe dama kina da kudi to bari Bukar ya zo dole ki fiddo su ki bashi a kara ayi awon gero kuma wannan kayan karfi ya kwace".


Kuka Mairo ta saki, cikin tashin hankali Fatsuma tace, "Yaya kiwa Allah kiwa annabi karki kwacewa Mairo wannan kayan kamar yanda kika saba, kuma wallahi bani na dinka mata ba yanzu ta zo tana nuna min babansu Salame ne yayi musu dinki kala daya ita da Salame". Kubura ta tabe baki tana kallon Mairo a banzance, "Ku ji mun yarinya mai mugun hali wacce bata so a ci arzikinsu. Ke dan ubanki da ba'a badawa baban su Salamen zai baki ne? Naga ranar sallah dama ke ba inda kike zuwa a gida kike wuni to don me ma zaki rika kuka dan na amshi kayan sallah zan ba yayarki". Laure ta amshi kayan tana dubawa, Kyakyawar atamfa ce dinkin riga da siket "Rabu da ita dai yaya wannan dinki ai yawa Mairo yawa, watakil ma Wasila akace ta kawowa mugun abu ya sa ta rike tace ita aka bawa". 


Mairo ta kara fashewa da kuka hade da cewa "Mama na rantse da Allah ni aka bawa ba Wasila ba, ki amso min dinkina". Fatsuma da tuni kukan da yar tata take ya fara sakata kwalla amma tasan cewa tunda wannan dinki yaje hannunsu Kubura ko kukan jini Mairo zatayi to fa ba zasu bata ba, "Yaya Dan Allah kuyi hakuri ku bawa Mairo dinkinta, sanin kanku ne ita kadai ce baban Zubairu baiyiwa dinki ba a gidan nan amma Wasila ma anyi mata dinki, dan Allah karku kwace mata". A fusace Kubura tace, "Ba za'a bayar din ba na ce an cinye na karfi ne in kina da karfi ki zo ki kwatar mata".


Shiru Fatsuma tayi ta sadda kai, guntayen hawayen da suke makale a fuskarta suka karasa gangarowa, ko giyar hauka ta sha ba zata tunkari Kubura da sunan fada ba, domin yanayin jikinsu ma ba daya bane ita tun tasowarta ma bata iya fada ba, taya zata iya tunkarar wannan abu mai kamar bauna da fada, ga Kubura rainon tuwon dawa a dire take ta ko'ina. Fucewa sukayi daga dakin Kubura sai wangale baki take tana kara bude kayan sunyi kyau sosai da alamu ba dinkin kauyen bane. Mairo ce ta dawo da Fatsuma daga duniyar tunanin da ta afka bayan ta fada jikinta tana rusa kuka. Ta dafa bayan Mairo cikin lalashi ta ce "Baby kiyi hakuri insha Allah idan babanku ya dawo zan fada mishi idan kika ci sa'a sai ya karbo ya baki". Kara sautin kukan tayi hade da cewa "Umma baba baya sona, yaki dinka mun kayan sallah ya dinka wa kowa yanzu wanda baban Salame ya dinka mun ma an kwace kuma nasan halin baba ba zai karbo min ba".




Maganarsa suka jiyo daga waje, hakan yasan Mairo da Fatsuma suka fito daga dakin, Mairo sai faman kuka take, kwantar da murya tayi cikin sanyi "Baban Zubairu dan Allah kayiwa Yaya Kubura magana ta ba Mairo dinkin sallarta". Yana daddaga kayan da Kubura ke nuna masa wanda baisan ko daga ina ta samo su ba ta dai ce ya kalli kayan Wasila shine ya karba yana dubawa yana fadin yayi kyau "Wane kayan sallah ne kuma nata? Ni dai nasan ban dinka mata kayan sallah ba ko kece kika dinka mata, don na sanki da munafurci yanzu haka kina da kudi a boye". Share kwallar da ta gangaro fuskarta tayi hade da cewa "Ai wannan kayan dake hannunka ne Baban Salame ya dinkawa Mairo shine Yaya ta kwace wai zata bawa Wasila". 


Durkusawa Mairo tayi har kasa ta hade hannayenta alamar roko, "Baba dan Allah a bani kayana wallahi ranar sallah saboda rashin kayan sallah ko fita waje banayi saboda kawayena kowa ta na da kayan sallah banda ni". Tsawa ya daka mata wacce sai da ta sa ta zabura "Ke dallah! Yiwa mutane shiru yar iska kawai, Wasilar ba yayarki bace? Miye a ciki don an dauki kayanki an bata ina ce hakan kara karfafa zumunci ne a tsakaninku. Amma dubi yadda kike kuka kamar uwarki ta mutu, to ba za'a baki kayan ba ni har kullum so nake in ga 'Ya'ya na sun hada kai ba kansu ya rabu ba, don haka dole ku koyi kyauta da taimakon juna, maza bace mun da gani". 


Ya fada cikin tsawa, da sauri Mairo ta tashi ta rungume mahaifiyarta tana kuka Fatsuma bata ce mata komai ba ta jata daki tana lalashinta, shi kuwa Bukar bala'i ya dinga bankawa ta inda yake shiga ba nan yake fita ba, Fatsuma na daga daki tana jinshi bata ce masa kala ba, shafa bayan Mairo tayi hade cewa "Baby kiyi hakuri mana ki daina kukan nan kar kanki yayi ciwo, idan da sabo ai ya kamata ace kin saba sau nawa ina saya miki kayan idan naga ba'a miki kayan sallah ba amma suna kwacewa". Tayi lalashin duniyar nan amma Mairo ta ki daina kuka, don haka tace, "Yi shiru na baki labarin mageta da Mama Asiya". 


Rage sautin kukan tayi tana ajiyar zuciya hade da cewa "To Umma na daina". Kallonta take cike da tausayin yartata, bata san dalili ba amma ita dai Mairo tana son jin labarin yarintarta musamman wanda ya shafi Aljanarta Safuratu, don duk lokacin da zata ba Mairo wani bangare daga cikin labarinta daga karshe tana kasancewa cikin farin ciki, ko da yake shafin da ya kamata ayi dariya take labarta mata ba wanda ya kamata ayi kuka ba a cikin zalunci irin na su Mama Asiya nan take ta soma ba ta labarin da cewa.....



Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 
https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

Comments