ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 6


🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/ft23GhvuEqc

http://www.bonitomi.com/2023/04/aljanar-fatima-book-2-part-5-hausa.html

*^ Part 6 ^*


Bayan sunyi sallah sunyi addu'o'in da suka saba yi tuni Mairo ta harde kafafu ta zubawa mahaifiyar tata ido, ita kama Fatsuma abun har dariya ya bata amma sai tace ba zata bata labarin ba sai ta biya karatun da sukayi jiya da safe. Ba sanya kuwa Mairo ta kama karatu har zuwa dai-dai inda suka tsaya suna cikin suratul Burooj waje kadan ne Fatsuma ta gyara mata a karin da tayi mata jiya domin kan yarinya na daukar karatu shiyasa ma a ko da yaushe bata mata wasa game da kara karatu. Yanzun ma karin aya uku tayi mata ta ce kuma sai tayi biyawa ashirin kafin ta bata labarin nan da nan kuwa Mairo ta hau biya karatun.


Zuwa can tace "Umma na gama". "kai baby yaushe kika fara da har zaki ce kinyi ashirin aya uku ne fa". Har Mairo zata rantse Fatsuma tace "Kinga ba sai kin rantse ba, kullum ina kokarin hanaki yawan rantsuwan nan amma naga yana son kama bakinki ko". "Yi hakuri Umma insha Allah zan daina". Tace "To Allah yasa". Sannan ta dora da cewa "Safuratu ba yar uwata bace kuma ba kawata bace kamar yanda kike tunani amma a wajena ta zarce matsayinsu baki daya zan iya cewa ta taka matakin uwa a gareni. A takaice Safuratun da kike ji ina ambato a mafarki ba mutum bace Aljanata ce". 


Zaro ido Mairo tayi hade da dan ja baya cikin tsoro game da cewa "Aljanarki kuma Umma?". Murmushi tayi tace "Kwarai Aljanata ce sunan da ma ta fi so a kirata shine Aljanar Fatima. Ta kasance gatana a lokacin da na rasa uwata kuma na hadu da kishiyoyin mahaifiya azzalumai. Baby na sha wahala fiye da wacce kike sha yanzu tun kafin in kai kamarki a hannun kishiyoyin mahaifiyata, amma daga bisani bayyanar Safuratu ya canza komai a cikin rayuwata ya zamto cewa duk wahal-halun da nasha a baya suka zama tarihi. Shiyasa yanzu ma a ko da yaushe nake rokon Allah ya kawo mana mafita ko da kuwa ta hanyar da bamuyi zato bane domin nasan cewa wahala bata dawwama a rayuwar dan adam kamar yadda shima dadi baya dawwama".


Nan fa Fatsuma ta cigaba da ba Mairo labarin Aljanarta wani wajen suyi dariya wani wajen suyi kamar zasuyi kuka, basu ankara ba har rana ta fara yi Fatsuma tace, "To labarin ya isa haka sai wani jikon kuma". Mairo ta bata rai domin labarin ba karamin dadi yake mata ba "Dan Allah Umma dan kara min labarin ko kadan ne". Fatsuma tace "Bana son gardama fa baki ga rana ta fara yi ba dole yanzu mu tashi mu nema abun kari". Mairo tace "To mama yanzu ina Safuratu take?" Nan take fuskan Fatsuma ya sauya hawaye suka zubo mata "Baby bansan inda Safuratu take ba inda nasan inda zan sameta ko ina ne sai naje domin jinta nake a zuciyata tamkar jinin jikina. Karshen tunanina na bani cewa bata raye domin da tana raye dole zata nemeni a cikin wadannan shekaru masu yawa da suka shude, ko da yaushe ina mata addua idan mutuwa tayi Allah ya jikanta" 


Mairo ta zare ido hade da cewa Umma dama aljannu suna mutuwa ne", Fatsuma ta goge hawaye hade da cewa "Nima ko da yaushe tunanina kenan amma in na tuna ayar da take cewa dukkan mai rai zai mutu sai jikina yayi sanyi. Domin hakan na tabbatar min da cewa hatta aljannu ma suna mutuwa tunda suma rai garesu". Shiru Mairo tayi tana nazari ba abinda ke fado mata rai a cikin labarin da mahaifiyar tata ta bata sai ganin da take ina ma ace wannan aljanar ta sake dawowa wajen mamarta da su Kubura da babanta sun gane kuransu. A haka dai suka tashi mamanta tace ta tashi ta je tayo ciyawa wa awaki ita kuma zata je ta nemo surfe ko jan ruwa kafin ta dawo ta sama musu abinci


Haka Mairo ta fito tsakar gidan yaran gida baki daya an zuba musu dumamen tuwo suna ci suma Laure da Kubura a gefe sun zuba nasu suna ci ta gefe ta zo wucewa gaba daya suka bita da harara. Har tayi niyar bada kasa a cikin abincin su Talatu da ta zo wucewa kusa da su sai kuma ta tuno abinda ya faru shekaran jiya ko bata jin kanta ba zata jure wulakancin da za'awa uwarta idan ta jawo rigima ba. Kai tsaye gidan su Salame ta wuce ta kuwa ci sa'a ta iske suma suna cin tuwo ko rabi basuyi ba bayan ta gaida Habiban tace itama Mairo ta sa hannu su ce abincin da su Salame. Har ta nuna cewa ba zataci ba dama sauri take ciyawa zata sai Habiban tace ai itama Salame ciyawar zasu idan suka gama 

Don haka Mairo ta zauna suka gama cin abincin sannan suka fita ita dai Habiba tana jin dadin tarayyar Salame da Mairo domin tuni Salame ta fara dauakan kyawawan hali irin na Mairo ba kamar sauran yaran kauyen ba mararsa tarbiyya. Hakan ne ma yasa suka kulla kawance da Fatsuma itama tana koya mata karatun addini a hankali. Gidan baki daya ya watse su Kubura sun tafi gona ita kuma Fatsuma ta tafi neman garuwa ta kuwa yi sa'a ta sama aikin dari hudu. Wajejen karfe daya Mairo ta dawo gidan mamanta kadai ta tarar a gidan bayan ta zubawa awakinsu guda biyu ciyawa ta nufi daki wajen Fatsuma tana fadin "Umma wallahi yunwa nake". Fatsuma dake zaune tana tunanin duniya tace, "Wato yanzu ma yunwarce ta koroki gida ko nasan dai ba daga ciyawa kuke ba tun da safe kuna can kuna shiririta dai da kuka saba, zo ki dauka ga garin kwaki nan da na jika tun dazu naci na ajiye miki naki". 


Nan take ta zauna ta fara kai loma tana korawa da ruwa, ta kusan gamawa kenan suka ga Kubura ta fado dakin basu ji ko dawowarsu daga gonar bama, kai tsaye kwano garin kwakin dake hannun Mairo ta warce "Kawo nan shegiya acici yan zaman banza ba'a iya komai ba sai ci mu muna gona kuna gida kuna ciye-ciye ku ga ku shafaffu da mai ko". Da fadar haka ta fara hambuda loma da garin kwakin, gaba daya shiru sukayi suka zuba mata ido sai da ta cinye tass sannan ta juyo garesu "Ai ni na rantse da Allah bansan dalilin da yasa Bukar ya hanaki zuwa gona ba anya ba asiri kikayi masa ba? Kamata yayi ace mune zai hana zuwa gona ke kije aiki ko kasheki zaiyi ba ruwan kowa, amma wani wai ya hana fada min gaskiya wajen wane malami kika kai sunanshi?".


Fatsuma kam tama rasa abinda zata ce don haka tayi shiru kawai ta sunkuyar da kai, rankwashi taji a kai "Munafuka ina magana kinyi shiru kin kyaleni ko mahaukaciya kika mayar da ni?" Dafe kai Fatsuma tayi hade da cewa "Yi hakuri yaya Kubura wallahi babu abinda nayi masa kin manta shine da kanshi yace kar na kara zuwa gona wai rashin sa'a gareni...". Laure ce ta fado dakin hade da kallon Kubura tace, "Yaya yau kuma wane munafurcin suke kullawa?". "Me fa suka iya in banda gulma da ci kamar gara zuwa nayi na iske wannan yarinyar mai tulelen ciki tana cin garin kwaki nama rasa daga gidan uwarwa suka samo, wato suna ta nan suna shan dadi mu kuma muna gona muna nema musu abincin da zasuci ba rashin sa'a ba ko farar kafa ce sai nayi yadda nayi Bukar ya sa ta cigaba da zuwa gona". Laure tace "Wallahi da kinyi mun dai-dai Yaya don rashin zuwa gonarta ba karamin ci mun rai yake ba". 

Comments