*ALJANAR FATIMA BOOK 2*
🧟♀️🧟♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟♀️🧟♀️
By *Kingboy Isah*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
*^ Part 4 ^*
Washe gari tun da safe yunwa ta tashi Mairo daga bacci jikin nata yayi sauki ta yunkura ta tashi zaune daga dan karamin gadon da take kwance, duk jikinta ciwo yake amma zazzabin yayi sauki ganin mamarta bata dakin tayi yunkurin tashi ta fita domin yunwa ke kwakwalar cikinta. Ana haka sai ga Fatsuma ta shigo dakin hannunta rike da kwaryar koko dayan hannun kuma kosai ne a langa. Murmushi tayi ganin Mairo ta farka "Sannu yar Umma kin tashi ya jikin naki". A hankali tace "Da sauki mama ina kwana". "lafiya kalau yar Umma saukko ki karya ga koko da kosai na kawo miki". A hankali ta saukko kasan tabarmar kaba dake shimfide a tsakar dakin itama duk ta tsofe.
Ta zauna ta fara cin koko da kosai hade da cewa "Mama nasan ke ma fa baki ci komai ba don Allah ki zo muci". Fatsuma itama yunwar take ci amma tafi so Mairon ta ci tunda bata da lafiya "Kinga yar Umma kiyi maza ki cinye ke nake so ki ci kinga baki da lafiya". Ajiye ludayin tayi hade da bata rai "Ni dai ba zan iya ci idan baki ci ba kokon da yawa fa zai ishemu Umma". Tasan halin gardamar Mairo da gaske sai ta ki ci idan bata zauna susha tare ba, don haka ta zauna suka fara shan koko da kosan. Ko rabi basu sha ba sai ga Kubura ta fado dakin kamar wacce aka tillo.
Da sauri ta dauke kwanan koko da kosan dake gabansu "Iyeeh munafukan Allah ta'alla an barmu da tuwo ana nan ana cin dadi to wallahi kunci rabonku". Sunkuyar da kai kawai Fatsuma tayi hawaye kamar jira suke suka fara zubowa. Ta kalli Kubura da ta cika baki da kosai take kokarin kai kwaryar koko baki tace, "Haba Yaya Kubura ki ji tausayinmu mana ki duba halin da Mairo take ciki bata da lafiya tun jiya ni da ita bamu ci kuma ba, haka yanzu ma naga alama babu kasonmu a cikin tuwo shine na dauki yan sauran kudina na sayo mata wannan kokon dan Allah ki diba ki bata sauran ta ci ni na hakura".
Bakinta cike da kosai da koko ta dallawa Fatsuma harara "Ba za'a ji tausayin ba munafuka ashe kina da kudi shine kike boye wato ke gaki samu kaki dangi, bari Bukar din ya dawo aradu sai kin fiddo su. Kuma bari kiji in fada miki tuwon gidan nan na daren ma da ake baku Bukar yace a daina baku sai bayan kwana uku saboda laifin da wannan tsinanniyar 'yar taki tayi". Fatsuma bata ce komai ba kuka ne kawai ya kwace mata. A hankali Mairo ta mike ta faki idon Kubura dake faman zazaaga masifa tana cika baki da kosai, cikin zafin nama ta dakawa kwanan kosan wawa nan take ta rarumo kusan guda biyar ta watsa baki, sauran na cikin kwanon da basu fi guda hudu ba suka bare
Sororo Kubura tayi tana kallon Mairo daga bisani ta kama Mairo game da shake mata wuya "Shegiya tsinana wacce bata so aci irin arzikinsu amayo kosan nan ko na ci ubanki yanzun nan". Mukul-mukul kake ji tuni Mairo ta zakal-kale kosan cikin abinda baifi hadiya uku ba. Kubura ta dirka mata kulli a baya hade da cewa "Shegiya mai bakin hali ta hadiyesu duk bakin cikinki dai na ci kuma wannan na kasan ma ba bari zanyi ba". Da fadar haka ta tsugunna ta kwashe sauran kosan da ya zube tayi wajen. Kuka Mairo ta fashe da shi ta fada kan cinyar uwarta cikin kuka ta fara magana "Ummana da gaske Baba shine asalin mahaifina don Allah idan ba shi bane ki kaini wajen babana".
Kukan Fatsuma ne ya karu tace "Shine mahaifinki baby kiyi hakuri da kaddarar da kike fuskanta a cikin rayuwarki tun kina karama wataran sai labari". "Umma Baba ya tsaneni baya sona ya fi son su Talatu da su Wasila baya son ganina abu kadan idan na mishi dukana yake kamar zai kasheni ke kadai kike sona Umma". Ita kanta Fatsuma wani lokacin tana mamakin irin wayo na Mairo domin wasu maganganun idan ta fada ko babban mutum sai haka. Shiyasa ma wani lokacin take sakin jiki da ita suyita hira kamar suna hira da wata sa'arta "Kiyi hakuri baby ni kaina nasan irin zaman kuncin da muke a gidan nan to amma bani da mafita ko dabara zabi daya ya rage mana cigaba da rokon Allah ya fitar damu daga cikin wannan ukubar. Shiyasa ko da yaushe nake nuna miki muhimmancin addua".
Mairo ta share hawaye hade da cewa "Umma to dan Allah mu gudu mu bar gidan nan mu tafi wani wajen in ba haka ba kashemu zasuyi". Wani sabon kukan Fatsuma ta saki hade da kallon 'yarta tace "Kiyi hakuri Mairo bani da inda ya fiye mun nan, ni maraya ce ciki da bai bani da uwa bani da uba dangin mahaifiyata sun tsaneni basa sona ko kadan nan da kike gani da Inna Ma'u su kadai suka rage a cikin dangin mahaifina don haka ba inda zanyi nasan cewa Allah yana gani kuma shi zai bamu mafita". Shiru Mairo tayi tana ta tunanin maganganun mahaifiyarta a haka har bacci ya dauketa. Fatsuma ta ajiyeta a gado ita kuma ta tashi ta fita neman wanda zata jawa ruwa ko kuma dakau ko surfau.
Dakyar ta samo dari uku kudin jan ruwa, tun a can ta sayo awara da fanke ta sako cikin hijab, ta zo wucewa ta tsakar gida tana ji suna ta fadin maganganu bata kula su ba kai tsaye ta wuce daki. Har lokacin Mairo bacci take. Ta tasheta sukayi alwala sukayi sallah sannan suka ci awara da wainar. Bayan Magariba kadan Bukar ya dawo gidan ai kuwa Kubura ta fesa mai wai Fatsuma na da kudi. Tana zaune a daki kan tsohuwar sallayarta tana addua bayan ta gama sallah ya fado dakin kamar wanda aka wullo. "Ke inda kudaden da ke hannunki maza-maza bani". Ta dago kai ta kallesa "Wane kudeda". Ya daga hannu "Zan wanka miki mari bana son bata lokaci yanzun nan Kubura tace akwai kudi a wajenki ko karya zata miki?".
Ba yanda ta iya sauran canjin dari da tayi a cikin dari uku na dazo ta ciro daga jikin zaninta ta mika masa. A hautsine ya karba yana dagawa "Dari na gani ina sauran?". Cikin yanayin kuka tace "Wallahi ita kenan itama dazun nayi jan ruwa na samo dari uku canjin kenan da ina son na ba Mairo in ta dawo ta sayo mana wani abu mu ci da dare". "Munafuka karya kike tashi in cajeki". Ba musu ta tashi ya caje ko ina a jikinta da yake tunanin zata boye kudi bai samu ba. Duk ya bincike dakin nan ma bai samu ko ficika ba, ya mangareta da gefen hannu hade da fadin "Matsa ki ban waje ko in ballaki". Da sauri ta ja gefe tare da dafe inda ya daketa a kafada
Ajiyar zuciya kawai tayi ta koma kan sallaya ta cigaba da fadawa Allah kukanta. Sai bayan isha'i Mairo ta dawo gidan kamar munafuka haka ta wuce dakinsu da shiga ta tura kofa ta sa kuba. Fatsuma na zaune a kan sallaya tana gyangyadi bayan ta idar da karatun da take ta ji shigowar mairon, kwanan abinci Mairo ta fito daga cikin hijab dinta "Umma gashi yi sauri ki cinye kafin wannan jarababbun su zo sunga shigowata". "Baby wa ya baki abinci kuma ko daga gidan Inna Ma'u?". Mairo tace "Aa daga gidansu Salame ni munci tare da Salame shine mamansu tace bari ta zubo a kawo miki". Fatsuma tace "Kin dai koshi ke ko?". "Eh wallahi na koshi alhamdulillah yi sauri ki cinye Umma".........