ALJANAR FATIMA BOOK 2 PART 2

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️


By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••

*^ Part 2 ^*
Talatu ta ce "Wallahi mama tana kwada min ta ruga a guje kuma kinsanta da gudu..." "Ke ni yi mun shiru ina Mairon take inje in ci ubanta ba zan iya bari har sai ta dawo gida ba yanda zuciyata ke tafasa". Talatu tace "Ba zai wuce taje gidan Inna Ma'u ba don can take guduwa in tayi laifi ta san ko Baba ba zai bita can ya daketa a gaban Inna ba". Cikin fushi Kubura ta nufi hanyar fita daga ita sai daurin kirji ko riga babu jikinta balle ayi maganar mayafi, a irin jahilinci na kauye hakan ba wani abu bane don matar aure ta fita a haka bama batun neman izinin mijinta ake ba tukun. 


Laure tace "Yaya ina zaki kuma", "Gidan Inna Ma'un can zan bita in mata dan banzan duka ko a gaban Inna ne". Kafin Laure ta daga baki tuni Kubura tayi waje Talatu da Wasila suka rufa mata baya. Da fitarsu sai ga Salame da kaninta suka kaiwa Fatsuma ciyawar Mairo, Fatsuma ta amsa taje ta juyewa awakinta guda biyu suma yunwa suke ji dan tun jiya da rana basu ci komai ba. Laure kuwa tsaki tayi ta koma wajen dakan furarta ita kuwa Fatsuma ta koma daki cike da fargabar abinda zaije ya zo ko kadan bata son tashin hankali.


Bagazan-bagazan ta fado gidan ko sallama babu Mairo na ganinta tayi sauri ta zagaya ta boye bayan Inna Ma'u dake zaune bisa tabarmar kaba, "Fito dan ubanki munafuka yau sai na kakkaryaki" Kubura ke fadar haka yayin da ta nufi Mairo gadan-gadan "To marar kunya ai sai ki fara kakkaryani kafin ki karyata". Curus ta tsaya tana huci tare da aikawa Mairo sakonnin harara ta bayan Inna Ita sam shigowarta bata ma lura da Inna Ma'u ba don tsabar masifar dake cinta. Inna tace "Ya kikayi tsaye kuma ki aikata abida kika zo aikatawa mana don da ganin shigowarki ba sallama balle gaisuwa na san da shirin dukana kika zo". Inna Ma'u ta fada a hassale, yatsine baki Kubura tayi hade da cewa "Inna Ma'u ina kwana" "Da ban kwana ba zaki ganni ne? Marar kunya gaisuwar ma sai na roka me ya kawo ki gidan nan".


Kubura ta kamo kan Talatu "Inna dubi kan Talatu yarinyar nan Mairo ce ta dauki murgujejen dutse ta maka mata a kai. Ga hannun Wasila har jini ya kwanta inda ta cijeta sannan Asabe ma bata kyaleta ba haka ta lakada mata dan banzan duka don haka na zo in ci ubanta la'ada waje". Inna Ma'u ta kama baki "Iyee yanzu ke Kubura ko kunyar fadi bakiji ba dubi gandara-gandaran yaran nan naki tubarakallah ace basu isa su tare fadan ga wannan yar yarinya ba har sai kin shigar musu babba dake ki shiga fadan yara kuma dangin juna to ga Mairon a bayana sai ki zo ki daketa a gabana in gani". 


Duk yadda ta zo a firgice tana shakkar yin hauka a gaban Inna Ma'u tasan halin Inna Ma'u in ta mata hauka tana iya daukar ice ta buga mata don haka ta juya a fusace hade da fadin "Zaki fito wallahi yau sai kin gane shayi ruwane ina gida zaki tarar dani". Fuu! Ta fice Inna Ma'u na masifa Mairo ta fito daga bayanta tace Inna ta tafi ba. Dakuwa ta mata da hannu "Ungo nan dan gidanku me ya hadaki da 'Ya'yan wannan jarababbiyar matar kin sani sarai irin zaman da kuke a gidan ba ma sai kun taba su ba". Mairo ta kwashe duk abinda ya faru ta fadawa Inna, Inna Ma'u ta girgiza kai tace, "To ai ga irinta nan yanzu Allah kadai ya san irin masifar da kika jawowa kanki da mahaifiyarki na sha fada miki ki guji abinda zai hadaki da mutanen nan ba kaunarku suke ba ke da mahaifiyarki". Ita kan Mairo ta san abinda Inna Ma'u take fada gaskiya ne yau kam sai ta kwashi kashinta a hannu fatanta dai kar a taba mata ummanta wanda shima tasan abu ne mai wuya. 


A can gida kuwa Yaya Kubura gaba daya ta hautsuna gidan da masifa takanas take zuwa har kofar dakin Fatsuma tana ta balbalin bala'i zagi da ashariya ba irin wanda baya fitowa a bakinta, Laure na tayata jefi-jefi. Har misalin karfe biyar Kubura na zaune a tsakar gida tana masifa a wannan karon harda jin haushin rashin zuwan Bukar gida da wuri. Zuwa can ta kalli Fatsuma dake kulkula daddawa a dan karamin turminta dake kofar daki dogon tsaki "Matsww Shima wannan tsinannen yaron ko ina ya shiga ko abincin raina bai dawo ci ba yanzu haka yana can tare da shegun abokanansa sun tafi daji yawon shiririta. Ke Talatu maza bi Wasila duk inda yayanku yake ki nemo min shi". "To" Talatu tace hade da mikewa ta nufi waje.


 Fitarta yayi dai-dai da shigowarsa tafe yake yana shan rake cikin zumbula-zumbulan kayansa wanda sun masa yawa gasu sunyi datti ba wanki, Fari ne ba laifi amma baya da jiki ya tara wani dan iskan gashin baki kansa ya sha iski kwalkwali. Da ganinsa Kubura ta dora hannaye biyu a kai ta fashe da kukan munafurci sai kace wacce uwarta ta mutu. Shi kuwa da ganin haka baki daya ya gigice hankalinsa ya tashi baisan lokacin da yayi wulli da raken da yake hannunsa ba ya ruga gareta, "Innalillahi uwar gida- uwar gida me ya faru wa ya taba mun ke me kikewa kuka share hawayen daina kuka dan Allah fada min me ya faru". 


Ita kuwa tamkar yarinya kara kware baki baki tayi hade da fadin "Bukar wallahi ba zan iya ba na gaji kawai ka sakeni na tafi gidanmu ba zan tsaya gidanka a kashe min yara ba kuma a bini da zagi ta wuta ta uba". Hankalin Bukar in yayi dubu ya tashi domin duk lokacin da Kubura ta ambaci kalmar saki a tsakaninsu ji yake zai iya aikata komai domin magance damuwar da ta sa ta fadin haka. "Dan Allah dan annabi Kubura ki daina ambatar saki a tsakaninmu ni Bukar ina zan iya rayuwa ba tare dake ba haba uwar gidana sarautar mata daina kuka ki fada min waye ya taba miki yara a garin nan nasha aradu ko mai gari ne sai inda karfina ya kare".  


Fatsuma tunda ta ga Bukar jikinta ke karkarwa musamman da ta ga yadda Kubura ke kuka domin hatta Laure idan makircin Kubura ya sauka a kanta Bukar baya jiya mata dadi, balle ita kuma da ya tsaneta a zaman da take a gidan ita da yarta ko baiwa ta fita gata. Kubura ta nuna Fatsuma da hannu "Wane irin mai gari kuma ga mayyar da ta hade baki da yarta nan suke son kashe min yara to wallahi ba zan yarda ba dole ka dau mataki in ba haka ba sakina kawai zakayi saboda na lura bani da yanci a gidan nan domin a kan hakan babu irin zagin da Inna Ma'u bata mun ba don naje in daki Mairo".  

Baki daya ran Bukar dake tsugune gaban Kubura ya baci don haka ya mike tsaye hade da fadin "Me sukawa yaran naki fada mun yanzun nan in dau mataki a kanta munafuka daina kallona da idonki kamar na bera". Ya dallawa Fatsuma harara "Mairo ce kana ganinta tamkar karama ashe tayo gadon bakin hali da mugunta wajen uwarta ta lakadawa Asabe dan banzan duka, ta ciji Wasila a hannu sai da jini ya fito bata tsaya iya nan ba ta dauki dargwajejen dutse ta kwalawa Talatu a kai ba don Allah ya kiyaye ba aradu da sai dai a kwaso kwakwalwarta a kwarya". 

Da jin haka Bukar ya dora hannu a kai hade da fadin "Innalillahi na shiga uku ita Mairon ce ta aikata haka yanzu yarinyar nan duk dukan da nake mata da wanda Zubairu yake mata wato ba ji take ba shine take neman kashe mun yara" Ya watsawa Fatsuma wulakantaccen kallo, "Ko dake ba laifinta bane tarbiyar da shegiyar uwar nan tata take koya mata kenan, zo nan dan ubanki yau sai na kakkaryaki a gidan nan". 


Fatsuma da tunda ya fara maganar dama tuni ta daina dakan daddawar ta sunkuyar da kai jikinta na rawa a hankali ta taso don bata isa tayi masa gardama ba ta kara laifi. A gabanshi ta durkusa ta daga baki "Gan.." Bata karasa ba ya ware karfinsa ya wanka mata mari wanda sai da ta fadi kwance daga durkushen da take ta dafe bangaren da ya mara a gigice domin sai da ta ga taurarin wahala. "Ke dan ubanki irin tarbiyar da kikewa yar tawa kenan wato bakin cikin hali irin naki har kin fara goga mata gashi ta fara tayaki kishi tana son kashe yan uwanta wato..." "Don Allah don annabi kayi hakuri ba zata kara ba zan mata fada". 


Da fadar haka a fusace ya rufeta da duka tamkar wanda ya kama barawo naushi da harbi ta ko'ina ita kuma Fatsuma banda kuka da ihu ba abinda take yi. Inda saboda ta saba da wannan dukan laifi kadan zatayi a cikin gidan ya lalasata saboda rashin gata. Ana cikin haka sai ga Mairo ta shigo gidan a guje tana kuka tana sosa baya. Da ganinta Bukar ya bar kan Fatsuma yayi caraf ya cafketa "Zo nan Allah ya kawo ki azzalamu". Hannu ya ware ya dankara mata duka a baya tamkar ba karamar yarinya ba nan take Mairo ta fara tari tuni lumfashinta ya fara kokarin daukewa. 


Fatsuma bata san lokacin da karfi ya zo mata ba da gudu ta yunkura ta fizge Mairo daga hannun Bukar a gigice tana fadin "Mairo! Mairo! Innalilahi wa'inna illahir raji'un Mairo dan Allah karki mutu bani da kowa sai ke kece dan sauran farin cikin rayuwata da ya rage in kika mutu ya zanyi". Ta fashe da kuka tana girgiza Mairo da lumfashinta ke sama-sama Kubura da Lauren da suka zuba ido suna kallo ta dora hannu a kai "Bukar ka kasheta" Bukar ya ja tsaki "Tama mutu mana a wajena da mutuwarta da rayuwarta duk daya". Kamar hadin baki Laure da Kubura suka tuntsire da dariya yayin da Bukar ya juya ya fice a gidan

Fatsuma kuwa kamar tayi hauka Halimatu da ta shigo gidan tana ganin abinda ke faruwa da gudu ta nufi randar ruwa ta debo zata kaiwa Fatsuma wata gigitaciyar tsawa Laure ta daka mata "Intuwa ku..ubanki wa zaki kaiwa ruwa". Cikin firgici tace "Mama Mairo karta mutu". A fusace Laure tace "Kan ubanki idan ta mutu ita din kanwar uwarki ce? Nace ita din kanwar uwarki ce?". Jiki a sanyaye ta koma gefe tana kallon Fatsuma dake rungume da Mairo tana kuka. "Yau na ga iyayi ko miye ruwanta a ciki idan ta mutu harda kokarin dukko ruwa, ke da ma zakiyi fatan ta mutu yaushe rabon mu da cin gumbar sadaka". Cewar Kubura ai kuwa suka sake bushewa da dariya ita da Laure......

Comments