ALJANAR FATIMA BOOK 2 PART 1

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••

*^ Part 1 ^*


 بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu S.A.W da iyalansa da sahabbansa da bayin Allah na kwarai.

*GABATARWA*
Godiya ga Allah da ya sake bani damar sake dawowa gareku dauke da cigaban wannan hakaitaccen labarin mai dauke da tarin darussa na rayuwa. Duk da kasancewar ba labarin da ya faru a gaske bane ina fatan za'a samu darussan da kan iya zamowa izina ga rayuwarmu ta gaske musamman ga masu wasu daga cikin halayyar dake bayyane a cikin labarin na farko da ma wannan na biyun. 

*TUNATARWA*
Ina fatan wadanda suka dauri aniyar bibiyar wannan labarin nawa zasu kasance masu yi mun uzuri a wasu lokutan da labarin bai samu a kan lokaci ba, kasancewar yanzu abubuwa sunyi yawa. Haka zalika idan anga wani kuskure a cikin labarin ko kuma typing error za'ayi mun uzuri, tare da ankarar dani idan da bukatar hakan a game da tafiyar labarin na gode.
 

Tafe take cikin rana sai zufa take, nauyin ciyawar awakin da ta dauko bai hanata gudu-gudu sauri-sauri ba, da alamu dai a hanzarce take. Yarinya ce karama da ba zata haura shekara 8 zuwa 9 ba, dattin da ke jikinta da na kayanta ba zasu hanaka sata sahun farko cikin kyauwawan mutane ba, kasan cewarta fara da ka ganta kaga yarinyar fulani. Ba takalmi a kafarta zanin kuwa dake jikinta duk ya tattare saboda tsabar datti da kuma tsufa da yayi. Rigar kuwa har ta soma cirewa daga wajen wuya. A hanzarce ta karaso garesu yayin da ta cillar da ciyawar da ta daukko ta shaki kwalar rigar wata yar bakar yarinya. Marin da ta wanka mata ne yasa ta saki ciyawar dake kanta hade da fasa kuka

kukan ne ya janyo hankalin dayar yarinyar da suke tare ta juyo da sauri tana kallon abinda ke faruwa. "Dole kiyi kuka barauniya kin dauka cewa bansan ciyawata hannu biyu kika kwashe ba" "Yau za'ayi bur..uba, Mairo Asabe kika mara" Cewar yarinyar da suke tare da Asabe wanda itama dauke take da tsanwar ciyawar dabobbi a kai. A fusace Mairo ta saki Asabe wacce ta fadi a wajen tana birgima da ihu irin na batatun yara kamar wacce aka cire mata wani sashi na jikinta. "An mareta din Lantana ko zaki rama mata ne" Mairo ta fada tana mai fuskantar Lantana cikin masifa, Murguda baki Lantana tayi hade da cewa "Ba zan rama mata ba amma wallahi sai na fada ma mamarta". Da fadar haka tayi hanyar gida da gudu, itama kuwa Asabe ta tashi ta bita baya a guje tana kuka kamar wacce ake cire mata rai. Tsaki Mairo tayi ta tattara ciyawar Asabe da tata ta hade waje guda ta daure ta dora a kai ta nufi gida gabanta na faduwa. 


Ba komai take tsoro ba sai Yaya Kubura mamansu Asabe tasan halin jarabar matar nan. To amma dole ne ta kare mutuncin kanta da na uwarta, ba zata lamunci irin cin kashin da ake musu a gidan ba dan anga hakurin uwarta yayi yawa. Allah-Allah take karfinta ya kawo domin ta rika daukarwa uwarta fansa a kan su Yaya Kubura ko da cizo ne. Tafe take cikin sauri tana sake-saken zuci ga yunwa na kwakwalarta don haka ta fito ciyawar ko karyawa batayi ba. Tun daga nesa ta fara hango Wasila Talatu da Lantana sun yo hanyar da take. A zuciya tace ku kam ba tsoranku nake ji ba gwara ma da kuka biyo ni dajin. Tun kafin sun hade suke aiko mata zagi da ashar tana jinsu bata tanka ba ta zo zata gitta ta gefensu. Wasila ta jawota ta baya hakan yasa ciyawar dake kanta ta fadi kasa, "Gidan uwar wa zaki munafuka yau sai kin gane shayi ruwane sai munyi kasa-kasa dake a dajin nan tunda kika daki Asabe".


 Bata tanka ba sunkuyawa tayi da niyar daukar ciyawarta ta kara gaba, cikin fushi Talatu ta hangizata tayi tangal-tangal saura kadan ta kife a kasa. Talatu tace "Magana muke muke kinyi banza damu uban wa yace ki daki kanwata" Mairo tace "Ciyawata ta daukar min dole na daketa dan gobema kar ta kara". Talatu tace "Ciyawar Banza ciyawar wufi". Wasila tasa kafa tayi kwallo da ciyawar, cikin fusata Mairo tace "Wasila! Ki daina, Wasila ki daina". "Idan naki fa? Ko dukana zakiyi". Cewar Wasila dake rike da kugu tana zarowa Mairo ido, tabbas da niyar dukan Mairo suka zo amma suna shakka duk da kuwa sun girmeta, sun san halinta kamar mage take daga kun fara fada zata cijeka. Talatu wacce itace yayar Wasila ita kuma Wasila yayar Asabe tace



 "Na rantse da Allah idan kika sake dukan asabe sai na ci kut..." "Auzubillahi" Mairo ta fada hade da rufe kunnuwanta bayan jin ashar din da Talatu tayi, nan take kuma ta nufi wajen ciyawar tana kokarin tatarawa ba tare da ta tanka musu ba. "Shikenan shedaniyama ta mayar dake Talatu kina ji Auziyya take" Cewar Lantana 


Da jin hakan Talatu ta nufi Mairo dake sunkuye tana tatara ciyawa tasa hannu ta hangizata, "Uban waye shedan a nan". Sauran kadan Mairo ta kife ba dan tasa hannu ta dafa kasa ba. Shiru tayi ta mike da sauri ta nufi wajen kamar wacce zata daki Talatu sai kuma ta sunkuya ta karasa daure ciyawarta ta dora a kai nan take ta nufi hanyar gida. 


Gaba dayansu kallonta suke "Wallahi mahaukata ta dauke ku" cewar Lantana da ba haka ta so ba, so take kawai taga ana dukan Mairon amma Mairo taki biye musu su kuma suna tsoron tabata saboda cizo da jifa. Biyota baya sukayi suna ta zaginta hade da munanan ashar, tabbas zagin nayi mata zafi musamman in taji sun hado da mahaifiyarta. Sauri Mairo take ta nufi hanyar gida taki kula su ita kadai tasan me take ayyanawa a zuciyarta 


Dai-dai wata marabar hanya suka hade da wasu yaran su 2 Salame da kaninta Kalla sun dawo daga gona hannunta rike da gorar ruwa. Da ganinta Mairo tace "Yauwa Salame dan Allah rike mun ciyawar nan in kuma wani abu ya faru ki kai min gida" Ba gardama Salame ta karba domin Mairo kawarta ce.


Cire yagyal-gyalin dankwalin kanta tayi wanda shi kanshi ya dukunkune saboda tsufa ta daura a kugu, cikin masifa ta nufo Talatu wacce sukaja birki a wajen suke tsaye suna kallonta. Lafiyayyen mari ta wankawa Talatu "Uwata sa'ar wasanki ce da kike zaginta in kin zageni ba laifi amma kika taba uwata sai inda karfina ya kare". "Kika mareni, Ni kika mara!" Talatu tace game da kaiwa Mairo duka a ciki ai kuwa cikin sa'a ta goce dukan bai sameta ba. Talatu ta chakumeta suka fara kokowa.


Ganin Talatu ta kasa kada Mairo Wasila ta shiga fadan yayinda ta fara naushin Mairo ta baya. Zafin dukan ne ya fara shigarta hakan yasa tayi kukan kura ta saki Talatu yayin da ta kamo hannun Wasila ta galla mata cizo. "Ta cije! Ta cije". Wasila ta rushe da kuka, sakin Mairo Talatu tayi ta nufi Wasila tana cewa mu gani ta rike hannun Wasila tana dubawa hade da fadin "Mayya ba abinda ta iya ai sai cizo, shegiya dangin mayu daga gani gadon maita tayi wajen uwart...". Saukar dutsen da taji a kaine yasata kasa karasa maganar. Nan take itama ta dafe kai ta rushe da kuka "Ta fasa mun kai wayyo mamana". Cikin karar kuka take maganar yayin da ta juyo tuni Mairo ta ara a na kare tayi hanyar gida. 


Da gudu Talatu ta bita hannu a kai ta rike wajen da aka jefeta tana kuka. Wasila Asabe da Lantana suka rufa musu baya, Salame da kaninta ma daukar ciyawar tayi suka bisu baya. Zaune take a gindin murhu ta sa wata yar tukunya gaba tana iza wuta sai fama take da iccen yaki cin wuta. Da gudu Mairo ta fado gidan bata zame ko ina ba sai daki. "Innalillahi Mamana! Mamana! Ke dawa kika shigo da gudu haka kamar an biyoki fito gani nan" Mairo da ta fada daki ko kadan bata lura da mutum a tsakar gida ba sai da taji maganar sanan ta ankara, fitowa tayi hade da cewa "Inna Ma'u ina kwana ashe kina tsakar gida ban lura ba na wuce daki". 


"Lafiya kalau Mamana wa kika tabo ne haka kike gudu dubi yanda kike lumfashi". Cewar Inna Ma'u dake kallon Mairo "Inna ba wanda na tsokalo kawai gudu ne nayi, me kike dafawa Inna dama yunwa nake ji" Mairo ta fada game da zuwa tana kokarin daga tukunya "Daga ganin gudun nan nasan ba na banza bane ina nan wanda kika tabo zai zo ya sameni ai ansan wajen boyanki baya wuce gidana dama in kin yo tsokalarki. Yunwa kuma baki karya a gida ba dama kika fito?" Mairo tace "Eh Yaya Kubura ke girki kuma da safe tace dumame ya kare Mamana ma bata samu ba". Tabe baki Inna Ma'u tayi game da cewa mugun halin yan gidan nan naku ai sai su, sai ki zauna idan na gama ki ci, itacen ne ma danye ne yaki kamawa". Nan take Mairo ta kama aikin hura wuta dama ba karamar yunwa take ji ba.



 "Wayyo mamana ta fasa mun kai wayyo kaina zan mutu". Abinda Talatu ke fada kenan ta shiga gidan hannu bibiyu a kai, Wasila da Asabe suna take mata baya suma duk kukan suke. A guje Yaya Kubura ta fito daga daki daga ita sai daurin kirji. A masifance ta fara binsu da kallo "Ku mun shiru shegu kawai ku da wa? waye ya taba ku kuyi mun bayani yau ko waye ya tabowa kansa bala'i" Ta fada yayin da ta kama kan Talatu tana dubawa ita kuwa Talatu har wani kara kakaro kukan take tana dorawa a kan na gaskiya, "Ke dan ubanki kiyi mun shiru ki fada mun waye ya dake ku kin wani rike kai na zata kan naki ya fashe ashe kullutu ne kawai kike ta wannan uban kuka kamar wacce aka cirewa rai". 


Irin tsawar da ta dakawa Talatu ita kanta yarinyar sai da ta zabura nan take ta fara kokarin saisaita kukanta cikin kuka ta fara cewa "Mairo ce ta kwacewa Asabe ciyawa kuma ta gaggaura mata mari, muka hadu da ita a hanya shine muka koma zamu rama mata shine Mairo ta ciji Wasila ni kuma ta buga mun dutse a kai". Tunda ta fara bayanin jikin Kubura ya fara tsuma in banda bala'i a zuciyarta ba abinda ke tafasa "Yau za'ayi bala'i a gidan nan zarrar Mairo har ya kai ta sa hannu ta dakar mana 'ya'ya".


Laure da ke karkashin bishiyar bedi suna daka ita da yarta Halima ta saki dakan "Kambala'i yanzu Mairon ce ta sa su Talatu kuka gandan-gandan da su har su uku". Kubura tayi caraf ta cafe zancen "To ba dole ta sasu kuka ba jikar mayu ta cije Wasila ita kuma wannan ta fasa mata kai. Ai na rantse da Allah ba zan kyale ba ina wannan banzan uwar tata". Nan take ta nufi wani daki mai kyauren langa-langa ta yace labulen da shima duk yayi datti Fatsuma! Fatsuma! Fito! Fito! Yau yarki ta taro fadan da yafi karfinku". 


Shiru ta ji hakan yasa ta leka cikin dakin, kwance take tana baccin da ya zame mata kamar na dole saboda tsabar yunwar da take ji, don ko karyawa batayi ba. Ji tayi an fincikota daga saman dan tsohon gadon da take kwance saura kadan ta kife kasa ba don Allah yasa ta dafe kasa da hannu kuma kafarta ta sauka kasa ba. "Innalillahi wa'inna Illaihir Raji'un" abinda ta furta kenan yayin da ta daka kai ta kalli Yaya Kubura dake huci tamkar mesa. Ga Kubura dama irin matan nan ne masu kamar maza da kaga kirarta ka ga ta katti Allah ne kawai yayota mace ga ta baka ga fuska sai dan karan tayani muni "Yaya Lafiya kuwa". "Au lafiya ma kike tambaya tun dazun ina kwala miki kira wato kin mayar dani mahaukaciya kina nan kina bacci ke gaki yar sarauta yar dadi gida miji fito ki ga abinda yarki ta aikata kuma wallahi ba zan kyale ku ba daga ke har yar taki"


Kiiii ta kama rigar Fatsumar ta jata waje wacce sunanta Fatima amma kauye da batawa mutum suna sai da suka maida mata suna Fatsuma, kan Talatu ta kama "Dubi abinda wannan tsinanniyar 'yar taki Mairo ta aikatawa Talatu ta fasa mata kai, dubi hannun Wasila ta cijeta kamar mayya itama Asabe ta lakada mata duka to wallahi ba zan taba yarda ba dole ne mu dau mataki dan in ba haka ba nan gaba kanmu zata dawo". Laure da take ta gallawa Fatsuma harara tun fitowarta tace "Dubeta munafuka wato ko sannu ba zakiyi musu ba balle ki ba Yaya Kubura hakuri".


Cikin sanyin murya Fatsuma dake tsaye tana dubansu a sanyaye tace "Dan Allah Yaya kiyi hakuri wallahi ina jawa Mairo kunne yarinyar ce bata jin magana a hakan ma Allah yasa tana sauraron maganata da ba'a son abinda zatayi ba amma kiyi hakuri insha Allah ba zata kara ba". "A'a a'a dakata malama zancen ayi hakuri ma a nan bata ta so ba wallahi, Dan buhun ubanta yadda ta sakasu kuka haka zatayi kuka da idanunta. Ke bari kiji wallahi ke ma sai ta shafeki bari Bukar din ya dawo dole a hukunta ki naga alama duk horan da muke miki a gidan nan bai isheki ba". "Allah ya huci zuciyarki" Fatsuma tace yayin da Kubura ta juya kan Talatu "Ku kuma yan kan uba kuyi min shiru dubeki gandan-gandan dake sa'ar kanwarki ta biyu kike wa kuka". "Mama dutse fa..." "Yi mun shiru dan ubanki baki yo halina ba, da halina kika biyo yadda ta kwada miki dutse haka zaki dau murgujeje ki maka mata a kai in ya so ko mutuwa ne tayi kuma ba abinda za'ayi"..........

Comments