Zafaffan Kalaman Soyayya Na Ma'aurata Sabuwar Shekara Sabon Salo

 Assalamau alaikum masoya fatan kuna lafiya tare da fatan alkhairi. A yau ma ina dauke da wani sabon samfur na kalaman soyayya musamman gareku maza masu aure. Zaku iya amfani da ko wane bangare na cikin kalaman nan domin faranta ran matanku.shawarata a gareku yayin furta kalmar soyayya ga mace ku sanyayya murya sannan ku fada cikin natsuwa ta yadda maganar zata ratsa har zuciyarta muje zuwa





Tun kafin na aureki nake taya 'ya'yan da zamu haifa murnar samun uwa ta gari. Addini, ilimi, natsuwa, tsafta, kwalliya, da iya zama da mutane. Ba alfahari ba, ba don kar son zuciyata yayi yawa ba da nace na fi kowane namiji sa'ar samun mata. I really love you my queen


Kullum cikin tantama nake, wai mafarki nake ko kuma gaske ne, na mallakeki a matsayin mata. Tabbas in gaske alhamdulillah kawai zan iya cewa. aurenki shine babban burin raina yau gashi Allah ya mallaka min ke a matsayin mata uwar 'ya'yana. Ina miki albishir da samun farin ciki marar yankewa a zamantakewarmu zan zamto miki Aboki, Yaya, Uba, Kuma Miji mai son ganin farin cikinki a ko da yaushe Ina matukar sonki matata


Matata nayi alkawarin zanzo gareki a duk sanda kika bukata. Nayi alkawarin zan rungumeki a jikina a duk lokacin da kika shiga cikin kadaici. Nayi alkawarin ba zan bari hawaye na bakin ciki su zubo daga idanunki ta dalilina ba. Nayi alkawarin killace ki a zuciyata har bayan raina. Ki yarda na fi kowa sonki a cikin masoyanki 🤔


Duk lokacin da na fita daga gida Allah-Allah nake na dawo gareki, musamman in na tuna yadda kike tarbata da kayataccen murmushinki mai yaye damuwa da bacin rai sai inji kasuwancina a gida yake. Ta yadda zan daina fita in zauna kawai ina kallon fuskarki ina jin dadi a raina. Ina kaunarki matata


Matata miye sirrin dake cikin murmushinki? Ina mamakin yadda yake yaye kunci da bacin raina a duk lokacin da nayi fushi. Da duk maza sun zasu auri mata kalarki na tabbata ba za'a taba jin kansu a cikin zamantakewar aurensu ba. Ke farin ciki, ke haske ce. Haka zalika ke tauraruwa ce da ta haskaka gidana, Ina sonki hubbyna 👳🏻‍♀️


Matata ina miki albashir da cewa ke yar aljannace, karkiyi mamakin furcina. Domin aljannar mace na karkashin kafar mijinta ni kuwa tuni na daga miki tun kafin ki karaso. Ko kin san cewa irinku ne matan da ake cewa kunyiwa miji asiri musamman in akaga yadda yake hidimta mata. A kanki na karyata wannan zancen, ba boka ba malam amma kin mallake zuciya, ruhi, da dukkan abinda na mallaka. Ta hanyar so kulawa da biyayya da kike mun. A zahiri da badini ina matukar kaunarki amaryata 😎




Comments