Tsigitsila Part 1 Hausa Novel

 πŸ‘Ή *TSIGITSILA* πŸ‘Ή


 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~


{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}


πŸ‘¨πŸ»‍πŸ’» KING BOY ISAH ✍🏼
PART 1

°°°°°°°°°°


 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~Da sunan Allah mai rahma mai jin kai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Shugabanmu gatanmu Annabi Muhammadu S.A.WπŸ‘ Gaisheku Masoya Ko Ba Komai Kun Bani Kwarin Gwiwar Cigaba Da Rubutun. Muje Zuwa Kishi wani abu ne da Allah ya halitta haka zalika ya zama wajibi ga duk dan adam. kamar yadda so ya zama wajibi ga duk talikin da ke dauke da dunkulalliyar zuciya a cikin kirjinsa. Amma kuma ga wasu matan kishiya ya zama wani sinadari dake juyar da kwakwalwarsu, ya gusar da tunaninsu, kana ya mayar da su cikakkun shedanu. Kamar yadda ta kasance ga Kubura. Kishi Hassada Kyashi da rashin yarda da kaddara, game da taimakon malam boka da shedaniyar aljanarta Tsigitsila sun mayar da ita hatsabibiyar shaidaniya, marar tsoro mai kuma iya aikata komai domin biyan bukatarta. Kamar yadda Allah ya hore dare ga yan adam da wasu dabobbin ya zama lokacin hutu a garesu, ita kuwa Kubura lokacin ne garinta ya waye. Domin lokaci ne da take samun damar gudanar da shedancinta cikin sauki ba tare da wani cikas ba. Tafe take cikin duhun dare tsirara haihuwar uwarta tun daga gida ta ratso cikin gari ta nufi wata hanya da ta nufi jeji. Bata zame ko ina ba sai bakin makabartar kauyen nasu. Ba tare da tsoro ko fargaba ba ta kutsa kai cikin makabartar tana tafe tsirara bakinta na fadin wasu kalmomi a hankali cikin rada wanda basuyi kama da larabci ba haka zalika basuyi kama da cananci ba, balle indiyanci. Bata zame ko'ina ba sai bakin wani sabon kabari wanda take da tabbacin shine sabon kabarin da aka binne mamaci da rana. Tana zuwa ta juyawa kabarin baya nan take ta runtse ido tana cigaba da karanto dalasuman tsafi yayin da ta durkusa ta debo kasar kabarin da hannun hagu. Da debowarta ta tahowarta duk daya, yayin da ta canza kalmomin da take karantowa zuwa wasu kala daban a ciki tare da ambaton sunan Rakiya Jafi-Jafi. Bata zame ko'ina ba sai gida, ba tare da fargaba ko tsoron kar wani ya ganta ba ta afka gidan ta kutsa kai cikin dakinta.


Tana isa bakin wani kaskon wuta dake ci ta fara barbada wannan kasar kabari da ta debo tana cigaba da ambaton sunan Rakiya. Ta dakko wani tsumma ta saka a wutar, ta bude wani dan bokiti nan take ta kamo wani bera da ranshi amma an rubuta sunan rakiya a bayanshi ba shakka da jini akayi rubutu. Wuyan beran ta kama da karfi ta fuske nan take ta jefa kan beran a cikin kaskon wutar sannan ta tsiyaya jinin dake zuba a sama. Da faruwar haka nan take wata gigitacciyar dariya ta barke a dakin marar dadin saurare sannan wani jan hayaki ya dunkule waje daya ba jimawa ya jirkice zuwa wata mummunar tsohuwa yakunanna siririya marar kyan kallo. Fatar jikinta tsanwace mai ratsin baki, wasu manyan kuraje masu kama da maruru watse a fuskartata suna motsi sai kace zasu fashe. Hancinta dogo ne da ya gangaro ya kusan rufe bakinta lokaci bayan lokaci wani bakin jini na kwararowa daga ciki. Kwala-kwalon idanunta sunfi kama da idanun mujiya duk da kuwa sunfi na mujiya muni da ban tsoro. Domin kuwa kwayar idon yar karamace wani ruwan dorowa ya zagayeta. Gashin kanta da bai wuce a kirga ba dogone har kasa wanda ya kasance fari fat. Hakoran bakinta basu fi hudu ba, bakake marar kyan gani a bakinta da take faman wangala dariya da shi. Yanayin dage kai da tayi tana kyalkyala dariya irin ta marar imani shi ya kara mata muni gami da ban tsoro. Yanayin halittarta ko a cikin halittun aljannu mummuna ce ta karshe irin wacce gani na farko idan mutum yayi mata nan take zai sume ya fita hayyacinsa in akayi rashin dace ya sume. Amma kubura ko gizau batayi ba saboda ta saba ganinta haka zalika ita kanta yanzu shedaniya ce abar tsoro a cikin shigar bil adama. "Kubura tabbas bukatarki zata biya kinyi dukkan abinda nace kiyi. Ina gashinta da farcenta da na bukaci ki kawo min". Aljanar mai suna Tsigitsila ce tayi wannan furucin yayin da ta mika zankalelen hannunta mai zara-zaran yatsu da farcina dogaye ga Kubura. 


Nan take Kubura ta mika mata wata leda dauke da gashi da kuma farce a ciki. Zuba su tayi a hannu kana ta runtse ido tana karanto wasu kalmomi nan da nan dakin ya rude da hayaniya gami da ihu da kururuwa iri-iri. Watsa gashin da farcen aljanan tayi cikin kaskon wutar nan take wani ihu da sautin kara marar dadi ya tashi hade da bayyanar wani bakin hayaki dake fitowa a hankali daga cikin wutar. Da faruwar haka Aljanar ta fashe da wata rikitacciyar dariya gami da cewa, "Sai ni Aljana Tsigitsila uwar shegu, kanwar shedanu, kakar azzalumai da mugaye. Kubura bukatarki ta biya". Ko da fadin haka wacce aka kira da Kubura ta Fashe da dariyar farin ciki. "Rakiya karshen jin dadinki ya zo, karshen jin dadin yayanki ya zo,karshen haihuwarki ya zo. Tabbas lokacin fara ganin uku bala'i da masifu iri-iri gareki ya zo. Iko mulki da jan ragamar gidan nan daga yau ya dawo hannuna". Hahahahaha! Nan take ta kara fashewa da dariya

Comments