Zafaffan Kalaman Soyayya Na Sabon Salo 2022 Danlove


Assalamu Alaikum Masoya Kamar yanda kuka sani sunana Danlove kuma kunsan zancen gizo bata wuce na koki. Dan haka a yau ma ga wani guzurin kalaman soyayya gareki yan mata da samari


Domin kallon bidiyon latsa kan hoton


1.  Sau da dama nakanyi mafarkin munyi aure, na zama sarki kin zama sarauniya mai juya akalar gidanmu na aure, muna rayuwa irin ta farin ciki wanda ko wane masoyi ke buri da nufin aiwatarwa a zuciyarsa, sai dai kash a irin wannan yanayi ne nake farkawa sannan in an kara mafarki nake ba gaske ba. masoyiya ina fatan wataran mafarkin nan ya zamto gaske Nayi alkawarin cika zuciyarki da farin ciki Ba shakka ina sonki


2. Ko da kuwa so cutane kamar yadda mutane suke fada, na yadda in rayu in mutu a cikin irin wannan cutar, domin kuwa na kamu ta ko wane bangare da cutar sonka na tabbata ba zan warke ba har ranar mutuwa ta. Please ka soni kamar yanda nake sonka dan Allah, tabbas ina kaunarka masoyi



3Sonki ya narkar da zuciyata, mutane sukan kirani zautacce marar zuciya a kan sonki, kwarai na zabi su kirani da mahaukaci a kan sonki, domin malaman tarihi masana soyayya sun tabbatar da cewa so ba zai taba cika so ba sai an hada da hauka, yanzu ne na tabbatarwa da kaina ni cikakken masoyine tunda ina haukan sonki 😍


4. 🥰 Sau da dama nakanji zuciyata tamkar zata fashe, amma sai in kasa daukar ko wane irin mataki. Ya na iya sonka ne ya cika zuciyata yanzu kuma nema yake ya fasata, kaji tausayina dan Allah duk rintsi karka guje ni, idan ka barni nasan ba zan mutu ba amma zan kasance a raye ba tare da zuciya ba, ina masifar sonka 🌹🫣


5. Sau da dama nakanji tamkar in kai kaina asibiti a farka kirjina a ciro zuciyata 💔 a gabanki domin a nuna miki irin yawan so da kaunarki dake cikinta, sai dai kash nasan hakan ba abu ne mai yuyuwa ba. Amma na sadaukar da komai nawa gareki ki yarda ni sadauki ne a cikin masoyanki 😎



6Sau da dama na kanji ina ma ace mutum yana iya rayuwa ba tare da zuciya ba. Da naje an farke kirjina an ciro zuciyata na baka ita domin ka gaskata cewa na mallaka ma komai nawa ciki kuwa harda zuciyata. Ina matukar sonka 💝


Comments