Sharri Kare Ne Part 8 Littafin Dare Dubu Da Daya

 SHARRI KARE NE 8HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI


Waziri Aku 


Ya sauka daga kan alfadara, ya kutsa kai cikin zauren farko, sai ya ga Abusir zaune a kan kujera. Yayin da Abusir ya ƙyalla ido ya gan shi, sai ya miƙe tsaye, ya tarye shi da murna. 


Amma Marini kuwa sai ya yi tsaye ƙerere kamar wani gunki, ya buɗe baki, wai shi mamaki. Ya dubi Abusir ya ce, "a'aha, ashe rai kan ga rai? Watau da ma haka halin 'yan duniya yake? Yanzu a ce Sarki ya gina mini Marina a garin nan wadda babu kamar ta, na zama babban marini a cikin garin nan, arziki ya lulluɓe ni ta ko'ina, amma ko dai ka zo inda nake, ko kuma ka ce shin wai ina abokina ya shige ne? Duk ba ka yi wannan ba, babu abin da ya dame ka da halin da nake ciki. Ni kuwa babu inda ban neme ka ba, na je gidan baƙin da muka sauka, aka ce ka bar gidan. Na tura bayi gidajen baƙin da ke garin nan duka wajen neman ka, babu ɗaya da ya zo mini da labarinka. Kullum da tunaninka nake kwana da shi nake tashi."


Abusir ya ce, "a'a, ka dai manta ne. Ai na zo marinarka kwanan baya, ka liƙa mini sata har ka yi mini bulala, ka ci zarafina gaban mutane."


Abuƙir ya riƙe haɓa cikin mamaki ya ce, "da ma kai ne na yi wa bulala?"


Abusir ya ce, "I, ni ne."


Abuƙir ya rantse da abin da zai kashe shi wai bai gane shi ba. Ya ce masa, "wani ɓarawo ne ya dame ni da sata, kamarku ɗaya kamar an tsaga kara, to Wallahi na aza shi ne na yi wa bulala, ashe kai ne." Ya yi ta tafa hannuwa yana sallallami yana cewa, "inna Lillahi wa inna ilaihirraji'un! Tabbas na cutar da kai, na zalunce ka ba da sanina ba. To, amma me ya sa ka ƙi ce mini kai ne wane? Ai da sai ka sanar da ni tun da ka ga aiki ya yi man yawa, mutane sun rufe ni, ban tsaya na dube ka da kyau ba, balle in gane ka."


Abusir ya ce, "ai babu komai, ƙaddara ce, limamin gari da rabon giya. Mu shiga ciki ka yi wanka."


Abuƙir ya ƙara marairaicewa yana cewa, "don Allah ka yafe mini wannan babban zunubi da na aikata maka."


Abusir ya ce, "Wallahi na yafe maka, ai ko Ubangiji ba ya kama bawa da laifin abin da bawan ya aikata cikin rashin sani." Ya kama hannun Marini suka shiga cikin gidan. 


Marini ya yi ta raba ido, kamar ɓera a buta, ya saki baki yana kallon abubuwan mamaki da aka ƙawata gidan nan da shi, ko a garinsu, Iskandariya, da suka baro, bai taɓa ganin gidan wankan da aka ƙawata kamar wannan ba. Sai ya tambayi Wanzami, "ya aka yi ka mallaki wannan katafaren gidan wanka haka?"


Abusir ya ce, "wanda ya gina maka marina shi ya gina mini wannan gidan wanka. Na je wajensa ne na bayyana masa alfanun gidan wanka." Ya kwashe labarin abin da ya faru tsakaninsa da Sarki duk ya gaya wa Marini.


Marini ya ce, "ai kuwa Sarki babban aminina ne, bai kuwa san yadda ni ke da kai ba. Lallai ne gobe in je gare shi in faɗa masa cewa kai babban abokina ne, idan ya ji haka kuwa na tabbata zai so ka ya ƙara girmama ka fiye da yadda kake yanzu."


Abusir ya ce, "a'a, kada ma ka wahal da kanka don wannnan. Mai cusa soyayya a cikin zuciyar bayi yana nan koyaushe, kuma ya rigaya ya sanya soyayyata a cikin zuciyar Sarki da fadawansa, duk abin da ka gani nan, daga wurinsu na same shi." Ya faɗa masa duk irin alherin da Sarki da fadawansa suka yi masa. Daga nan ya ce, "tuɓe tufafinka in cuɗa ka."


Abuƙir ya cire tufafinsa ya shiga cikin kwatarniyar wanka, Wanzami ya sa soso da sabulu ya wanke shi tas, dauɗar jikinsa ta fita duka. Ya ɗauraye shi da ruwan wardi. Ya sa 'yan yaran nan kyawawa suka tsane masa jiki, suka taje masa gashin kai, suka yayyafa masa turare, suka dai shirya shi tsaf. Ya ji jikinsa ya koma kamar ba nasa ba.


Abusir ya dafa shayi da hannunsa, ya sa aka shirya musu shimfiɗa, aka jera akussan abinci iri-iri, suka zauna suna ci suna kurɓar shayi. Mutane suka yi ta mamakin yadda Abusir ya girmama wannan mutum, wanda ba su taɓa ganin ya yi wa kowa haka ba.


Da suka gama cin abinci, sai Abuƙir ya ɗauko lalitarsa ya ƙidaya kuɗi ya ba Abusir, shi kuwa ya rantse ba zai karɓa ba. Ya kuma ce, "haba abokina, ka sani fa ni da kai abu ɗaya ne. Ai abin kunya ne a ce na karɓi kuɗi gare ka don na yi maka hidima. Allah dai ya tsari gatari da saran shuka."


Abuƙir ya nisa sa'annan ya ce, "na rantse da Allah abokina, gidan wankan nan naka ya isa abin kwatance, ya kuma fi duk wani gidan wanka da na sani, sai dai abu ɗaya kurum na lura da babu shi."


Abusir ya ce, "wane abu ne wannan?"


Abuƙir ya ce, "maganin kakkaɓe gashin hamata da na mara. Na tabbata idan ka haɗa wannan magani ka ba Sarki, ka kuma faɗa masa yadda zai yi amfani da shi, idan ya jaraba ya ji daɗinsa, to zai ƙara ɗaukaka matsayinka a cikin ransa."


Abusir ya ce, "af, lallai kuwa na sha'afa, an yi tuya an manta da albasa. Ai duk gidan wankan da babu wannan magani to kuwa ba ya zama cikakken gidan wanka. Yau ɗin nan kuwa zan haɗa shi, ba ko wanda zai fara amfani da shi sai Sarki." Suka yi sallama, Abuƙir ya hau alfadararsa ya tafi.


Aka ce wai ɗan banza yashi ne, ko an dunƙula shi sai ya watse! Duk da irin karimcin nan da Abusir ya yi wa Marini bai sa zuciyarsa ta yi sanyi ba, sai ma ya fara tunanin wani sharrin da zai ƙulla wa Wanzami a cikin zuciyarsa. Don haka da ya hau alfadarsa, bai zame ko'ina ba sai gaban Sarki. Ya faɗi ya yi gaisuwa kana ya ce, "Allah ya ba ka nasara na zo ne domin in gargaɗe ka a kan wani tuggu da na hango magauta na shirya maka."


Sarki ya tambaye shi, "wane tuggu ne ka hango?"


Abuƙir ya ce, "wai na ji an ce ka gina gidan wanka a garin nan?"


Sarki ya amsa, "ba wai ba inke, gaskiya ne. Kwanaki wani baƙo ya zo nan, ya zayyana mini amfanin gidan wanka, na kuma gina masa kamar yadda na gina maka karofi." Sarki ya kwashe duk yadda suka yi da Wanzami ya gaya masa, ya ƙara da cewa, "gidan wankan nan kuwa ya haskaka birninmu ga idanun baƙi fiye da yadda muka yi tsammani. Yana ɗaya daga cikin abubuwa masu daraja a garin nan da muke alfahari da shi."


Abuƙir ya duƙar da kai cikin ladabi ya ce, "ranka ya daɗe ka taɓa yin wanka cikinsa?"


Sarki ya ce, "I."


Da jin haka sai Abuƙir ya buga salati ya ce, "tir! To Allah ya fisshe ka sharrin wannan kafiri kuma maƙiyin addinin Islama. Wannan da ka gina wa gidan wankan."


Sarki ya ce, "iye? Wanene shi?"


Abuƙir ya ce, "Allah ya ba ka nasara, sai mu gode wa Allah da wannan kafiri bai yi galaba a kan ka ba har yanzu. To amma ina mai tabbatar maka da cewa, idan ka sake shiga gidan wankan nan, to kai kuma sai dai labari."


Sarki ya gyara zama ya ce, "ta yaya hakan zai faru?"


Abuƙir ya amsa masa da cewa, "wannan mutum da kake gani maƙiyinka ne kuma maƙiyin addinin Musulunci. Ba da niyyar alheri ya sa ka gina masa gidan wanka ba, sai don wata ɓoyayyar manufa da yake da ita cikin zuciyarsa, ta ya hallaka ka ba tare da kowa ya sani ba. Yanzu haka ya shirya wata guba da zai ba ka idan ka ƙara zuwan gidan wankan nan, zai ce maka wai maganin cire gashi ne, ka shafa wa hamatarka da mararka duk gashin wurin zai zube."


Sarki ya dubi Marini yana wasi-wasin abin da ya gaya masa. Sai ya tambaye shi, "ashe dai? to kai ya aka yi ka san da haka?" 


Abuƙir ya gyara zama, ya fara kantara wa Sarki ƙarya.


Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, insha Allah.


Shin Sarki zai yarda da ƙarairayin da Marini zai shara masa ko dai korar sa zai yi?


Ayi SHARE domin wasu ma su amfana.


Bukar Mada 

26/10/2022

Comments