ALJANAR FATIMA 13 To 22 HausaNovel

  





   *ALJANAR FATIMA*

   *^^^^^^_______^^^^^*


👺👽👽👽👽👽👽👺 


Page 13-14



NA. 👑 KING BOY ISAH 👑




👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽



THIS PAGE IN DEDICATED TO YOU


☘ *UMMU BASHIR* ☘


 *ZAINAB YUSUF*


*HUSAINI ATK (80K)*





```FOLLOWING US AS:

----

Like us page.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

----

Check us blogger.

Zamaniwriters.blogspot.com

----

 Email us your comment and reports.

Zamaniwritersassociation@gmail.com

----

whatsapp's number 

08096831009

----```


               *KARSHEN PAGEN BAYA*


kafin kace me tuni sun ruga upstairs tana biye da su koda tahau matakala na daya biyu sai sulbi ya kwashe ta ji kake tum ta fado kasa kamar an yarda buhun masara. Kanta ne ya bugu da kasa. Su asmart da suka juyo sukaga abunda ya faru sai suka dora da wata sabuwar dariyar.


»» gidan ALHAJI SALIM S.O kenan babban gida ne dake cike da iyalai. alhaji salim mata hudu gare shi saidai daya ta mutum yanzu uku ke a raye. Asiya uwar gida yaranta biyar biyu mata sune AMEERA DA ASAMA'U. Maza uku SAFIYANU babban danta sai mai mishi YUSIF. Da kuma yayan ameeera ABBA. 



Mai biwa asiya ZUWAIRA 'Ya'yanta hudu FIDDAUSI. NASIMA. ABDUL Sai ALIYU. A yanzu HAUWA'U Ce amarya yaranta biyu kadai kanana ILIYASU ABUBAKAR. 



Shekarar hindatu (Mamar fatima) uku a gidan ta rasu sai dai ta mutu ta bar fatima tana yar shekara biyu. Yarinyar fara kyakyawa a duk gidan tafi kowa kyau domin ita ta dara mahaifiyarta ma kyau. Alhj kamal kuwa ya dauki duk san duniyar nan ya dora a kan fatima domin yana jin tausayinta sosai kasan cewarta karama kuma marainiya hakan yasa ya dauki amanarta yabawa asiya.




Irin san da yake nuna mata shi ya jawo mata ta zama kamar jaba a gidan in aka cire Fiddausi, maza da mata yara da manya baki daya ba mai ragawa fatima a gidan bata samun sauki da farin ciki sai abbanta na gida. 



Hakan yasa ma in baya nan sai ta shiga daki abunta wani lokacin tata barci wani tym din kuma tata kuka abunta. idan ta tuno mahaifiyarta. A labarin da nake baku yanzu fatima takai shekara 9 da rabi a duniya ta iya yiwa kanta komai. Dan ko da tana karama bayi mata ake ba, Asiya da dauda take barinta. Fatima na shan wuya sosai Domin har ta saba da wahalar da yan uwan nata suke bata bama kamar Asmart, da Nasmat. Wadan nan biyu ba irin wuyar da basa bawa fatima. 



*Cigaban labarin* 

Washe gari Fatima ce ta tashi daga barci ta kalli dan agogon dake ajiye a kan mirror dakin nasu firgigit ta zabura ganin karfe 6:10 bata yi sallah ba. Sauran yan uwan nata mata da suke tare a dakin ta kalla. Sai bacci suke abunsu. Fiddausi kawai ta tayar domin ita tace ta dinga tadata. fatima sauran ta kalla ita ba abun ta tashe su ba tasha fada in bataci sa'a bama har duka. Tashi tayi ta nufi ban daki a guje. Tayi alwala ta dawo ta tayar da sallah. Naji muku haushi sosai da baku ji karatun yarinyar nan ba. 




 A hankali bayan tayi fatiha take jan suratul الغا شية ghaashiya. Muryarta na fitowa a hankali. Kamar kar karatun ya kare. Tayi zaman tahiya kafin ta karasa ta sallame. Tun kafin matar ta karaso take kwalla uban kira. "Fatu! Fatutu!" Da karfi. Fatima najin haka ta kama sauri allah-Allah take ta idar da sallah kafin matar ta shigo.





domin tasan halin mama asiya kwarai bata bata dadi kuma tafi kowa musguna mata a gidan. Asiya dingishi take sakamakon double faduwa da tayi jiya. Banko dakin tayi. 



Kamar wacce zata karya shi. Ta tsaya a gurin ta kama baki. "Iyye! Gaga 'yar banza wato sai yanzu ma kike sallah baki tashi da asuba kinyi ba ko?. inji mama asiya. A zuciya kuwa tace "yarinya kina kokari domin kuwa ni banma yi ba tukun". Daidai lokacin fatima ta idar da sallah ta juyo ta dan risina tace, "mama asiya ina kwana". Dan ban kwana ba zaki ganni ne dan ubanki?. Sunkuyar da kai kawai fatima tayi. "Munafuka Kaganta kamar wata salaha. To da ban kwana ba zaki ganni ne?, Tambayarki nake, Maza-maza ki iske ni a kitchen.

 Yau dake zamu hada kayan kari. Saura kuma ki ki zuwa da wuri ta kama kunnan fatima ta murda. "Kinga kunnan nan to sai na cira shi. Ko in ba-ba-laki in yaso in bada kudin dori".




 Faima sai da tayi dan kara domin zafin da taji na murda kunnan gashi har yanzu taki sakinta. Asiya tace. "Bazaki bar yiwa mutane ihu ba sai kin tada mana yara. Maza ki iske ni a kitchen kinji ko?". Gyda kai fatima tayi tace "naji gani nan zuwa mama". Mari ta wanka mata. "Wacece mamarki din?, Allah ya suttura in haifi yarinya kamarki". Ta nuna wasu yan mata dake gefe a gado suna ta sharar barci tace "kinga yarana can ba kamarki ba". Mtseww Ta ja tsaki ta fice.





Nan ta bar fatima tana kuka. Ta zubda hawaye sosai tukun ta tashi taje da sauri ta shiga bedroom tayi brush tukun ta canza kaya ta fito. Dugi-dugi ta nufi kitchen. Fatima tasha wuya sosai a kitchen din dake gaba daya ake haduwa ayi girki a gidan. ba mai tausaya mata a cikin matan baban nata duk su ukun miko wancan kulkula wannan wanke can gyara can. Ba mai tausaya mata ko ganin kankantarta a cikin matan. Bayan an kamala ita suka dinga dorawa kulolin abincin tana kaiwa dinner. Saida aka kamala komai tukun suka korata daki kuma suka ce in ta shiga ta kwanta kmr mai barci kar ta yarda alhj ya gane cewa ta tashi balle ma ya gano tayi aiki. Haka ta tafi tayi yanda sukace ta hau gadanta tayi shiru. Tana ajiyar zuciya. Su kuwa kowacce. Sai ta shigo dakin ta tada ya-nata-ya-nata duk suka yi wanka sukayi brush tukun aka nufi dinner. A nan kwance suka bar fatima. Tana jinsu duk abunda suke.

...................................................


Mujee zuwa.




Autan writers nee king boy













👺👽👽👽👽👽👽👺 


   *^^^^^^^______^^^^^*

    *ALJANAR FATIMA*

   *^^^^^^_______^^^^^*


👺👽👽👽👽👽👽👺 


Page 15-16



NA. 👑 KING BOY ISAH 👑




👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽





😘 Abunda yake raina zana fitar na huce takaici, suyaya ku a raina zana fada bazan boye ba.........



💃🏻 ALAMAR TAMBAYA TANA GA MAI YAWAITA TUNANI, MUSAM DA NASHI CIKIN SOYAYYAR READERS NA. NA KWANA CIKIN TA NA RASA WANDA ZAI FIDDANI SAI KU MASOYA NA WANDA KUKE DA KYAU NA KAMANNI, NA RIKE KAUNAR KU A RAINA TA ZAUNA.. NAYI SHIRINA ZAN BAKU DUKA PAGEN GA😜😜😜😜😝


♥ BANI DA BAKIN GODE MUKU MASOYAN ALJANAR FATIMA, TUN YANZU KAFIN AJE KO'INA MASSAGES DINKU SUN FARA RUTATOWA CIKIN WAYA TA. INA GANIN SAKONNIN KU INA JIN DADI SOSAI, ALLAH YA BARMU TARE. DA MASU KIRANA INA GODIYA, KUNA A HEART NA MUSAMMAN .♥


'YAN PHARIDAH KHAMSHI NOVELS


SAMEE KHAIRAH NOVELS


BIGBOY ISA NOVELS


BIGBOY ISAH FANS


ZAMANIWRITERSASSOCIATION

DA MA SAURAN SU....


BAN MANTA DA KUBA 'YAN WHATSAPP GROUPS INA GANIN SAKONNIN KU INA GODIYA. ANA TARE, ANA TAREN TARE, ANA MUGUN TARE.LOLZ





FOLLOWING US AS:

----

Like us page.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

----

Check us blogger.

Zamaniwriters.blogspot.com

----

 Email us your comment and reports.

Zamaniwritersassociation@gmail.com

----

whatsapp's number 

08096831009

----



               *KARSHEN PAGEN BAYA*


~Su kuwa kowacce. Sai ta shigo dakin ta tada ya-nata-ya-nata duk suka yi wanka sukayi brush tukun aka nufi dinner. A nan kwance suka bar fatima. Tana jinsu duk abunda suke.~


```»»Wajen cin abincin bangare-bangare ne wajen yara mata daban haka maza ma daban. Bangaren uwaye kuma sunsa abincin gaba an zubawa kowa nasa saidai ba damar ci. Sai alhj ya fito. Asiya tayi tsaki tace, "wai ace abincin ma sai an sawa mutane doka a kai, ji dallah yanda ya bar mutane najin yunwa yaje yayi zamansa...". Shiru tayi sakamakon jin yara sun 

Fara hayaniya alamun shigowar alhj kenan. Idan ya shigo duk rashin jin yaro sai ya natsu domin bashi da wasa. Bayan yaje ya zauna. Uwayan wato matansa. Suka fara gaishe sa tukun suma yaran maza da mata masu dan wayo suka biyo layi daya bayan daya suna gaida shi. Yayi mamaki da baiga fatima ba a cikin yan zuwa gaishe shi din ba. Da zai tambaya kuma sai ya kyale. 




Shi ya fara yin bismillah ya fara kai abincin baki tukun kowa ya fara ci. Dokar cin abincin kenan sai ya fara cin indai yana gida tukun kow zaice. Fatima kuwa tana daki ga gajiya ga yunwa kuma sun sata barcin dole. Saidai kwata-kwata barcin yaki zuwa domin yunwar dake kwakwalar ta. Tana jin kwaram niyarsu ana cin abinci kamar ta fito sai dai kuma tana tsoran tayi laifi. Domin tasan in ta saba musu to yau ta shiga uku ko abincin rana baza su bata ba. Haka suke mata idan tayi musu wani laifin. Su sakata aiki mai tsanani kuma su sata azumin dole horo da yunwa. Haka dai ta hakura ta kwanta tana kuka.




 Bayan an gama cin abinci kowa ya kama gabansa dake yau weekend ba makarantar sai islamiya. Alhj ya koma dakinsa amma sai ya kasa natsuwa da ya tino baiga fatima ba. Hakan yasa ya fito ya tambayi matan "wai ina fatima ni ban ganta ba". Asiya tayi farat! Tace "uhmm alhj kai da kasan halin yarinyar nan da shegiyar lalata. Tana can dakin yara tana barci nayi-nayi in tashe ta tayi sallama amma taki tashi". Ta fadi hakan ne domin ta jawa fatima duka. 





cikin fada yace "asiya wace irin banzar magana ne kika fada min kina nufin fatima bata tashi ba har yanzu. me yasa kika zama muguwa maciya amana iyee! asiya. yarinyar nan fa marainiya ce amanarta na baki. amma yanxu dan allah ace duk kin tashi yaranki sunyi wanka har sun karya amma ita dake ba yarki bace shine zaki barta har wannan lokacin bata karya ba. yanzu karfe 9:30 fa". Ta wani marairaice "haba alhj in kuwa kace haka baka min adalci ba. yanzu duk irin tatalin da nake wa wannan yarinyar kana so kace baka gani alhj. Ni ai a ganina rashin tashin ta din ma da nayi duk a cikin gata ne. Na barta ne ta hutawa rant....".



Tsawa ya daka mata. "Ke dallah rufe min baki bana san wannan zakin bakin naki. Maza wuce ki kira wo min ita". Murguda baki tayi ta tashi tana gunguni. Wai irin wannan ai sai yaja a rainata a gaban kishiyoyinta ake mata wannan abun "Dama jiya ka targada ni dan mugunta". Alhj yace "me kikace". Juyowa tayi. "Aa ni banyi magana ba". Ta wani gallo mishi harara. Ta nufi dakin yara. Fatima najin turo kofarta tayi maza ta rufe idanunta kamar mai barci. 








Asiya kuwa tazo ta kama tikarta "fati!-fati!, Tashe munafuka kinzo kin kwanta wato sai barci kike.maza jeki kiyi brush ki zo wannan masifafan mutumin na kiranki". Fati bata ce komai ba ta sauko taje tayi brush ta dawo. Tazo gaban asiya tace nayi. Rigarta ta gyara mata ta kuma dan go goge mata fuska kamar da gaske. Tace "idan kika yarda kika ce kinyi aiki kuma kika gayawa alhj ni nace ki dawo daki ki kwanta to ni dake ne a gidan nan kinsan dai halina sarai".



Fatima tace "bazance ba aunty". Dankwashinta tayi a kai. "Kinci uwaki. Nice aunty wato bama mama ba ko. Wuce muje". Fatima ta shiga gaba asiya na binta baya. Alhj kallo daya yayi wa fatima ya gane tana jin yunwa. Bata karya ba. "Momyna". sunanda yake kiranta da shi kenan. Kinci abinci kuwa. Girgiza kai tayi tace aa ynz na tashi a barci. Barci kuma?, wato bakiyi sallah ba ko?. Bana ce ki dinga kula da sallah ba ki bar wasa da ita". "Dady nayi fa tun da wari nayi sallah sannan na koma barcin". "That good haka nake san ji momyna".  




Juyawa yayi ga matan nasa wanda duk sun Zuro musu ido ba abunda suke sai hararen fatima. A cikin zuciyqrsu kuma tsanarta na kara fadada. "Wace tayi abinci?, Ina abincinta?". Ya tambaya Zuwaira tace, "alhj wane abinci kuma ai gidan nan ba wani sauran abinci duk an cinye tana can tana barci". Alhj yace "Yanzu Dan tsabar mugun hali yarinyar bata ci abinci ba shine kukaki ajiye mata. Ko dan kunsan ba 'ya'yanku bane. Wato ita Marainiya batada uwa ko". Bai tsaya jin abunda zasuce ba yaja hannun fatima yace "zo muje in saya miki abinci mamana". Yaja hannunta suka fita. 




Nan ya bar mata sai surutai suke yi. Har asiya na cewa "wai anya kuwa uwar yarinyar can ba asiri tayiwa alhj ba kuma har yanzu bayan ta mutu yake tasiri a kan yarta ba.nifa abun ya fara bani tsoro". Zuwaira tace "haba aunty barta mana ai gasuwa zatayi a gidan nan domin ko yar aiki sai tafita jin dadi wllh. Yarinya karama sai kini bibin tsiya". Hauwa tace, ai wallah ni kadai nasan muguntar da na shiryawa yarinyar nan, zaku gani da idanku". Yar guda sukayil a tare suka hada hannu. 




Mota suka hau alhj yaja saida suka je wata rumfar mai shayi tukun ya faka ya fito yajawo hannunta suka shiga suka zauna yasa a soyo mata indomei da kwai da kuma zallar wainar kwan da kofin shayi biyu. Kudi ya kashe musu dai sosai a gurin. Fatima saida taji cikinta ya cika nat! Domin kuwa rabanta da ta sama isashen abinci tun waccan juma'ar da taje gidan su wata kawarta ta wasa. Mota suka hau suka nufo gida tafiya ake fatima sai waige-waige take yi ta kalli can ta kalli can. Tana kallan shaguna. "Dady tsaya-dady-tsaya". Bai shirya ba ya take birki. Ya fara tambayarta "miye kika tsaida mu mamana?". "Dady danyi baya, Yi baya dady". Baiyi gardama ba yayi baya da motar. Saida suka zo saitin wani shago tace ya tsaya. Da gudu ta sauko taje tana kokarin dauko wata yar baby. Wacce suke a jere duk na sayarwa ne.



Mai shagon ne ya fito yana neman dukanta alhj ya dakatarda shi. Yace "mamana miye haka kika zo zaki daukar musu abu na sayarwa ne fa ko baki sani ba?". "Na sani dady wannan nake so ka saya min ina santa sosai kaga munyi kama da ita kuma ma dady kaga wannan tafi ta nuratu kyau da girma". Dan Murmushi yayi kadan yace "ke kuwa me zakiyi da wannan katuwar diyar robber ai tayi girma duba karama mn. Wannan tafa kusan kaiki tsayi". "Aa baba ni wannan nake so". Alhj ya kalli mai shagon ya tambayi kudin diyar robar. Mai shago yace "dubu bakwai". Alhj yace ina zuwa. Mota ya koma ya dauko kudi "kash! Ashe na baro kudin a gida". Saura dubu uku ne a hannunsa. Ya dawo cikin yanayin damuwa gashi mutumin baisan shi ba. Balle yace in ya fito zai kawo mishi. Ita kuwa fatima rike take da yar tsanar ta fara wasa da ita. 




Ya dawo yace "malam na manta kudina ne a gida kaga saura dubu uku canjina kayi hakuri ka rike wannan ka bamu yar robar in yaso idan na fito zan kawo maka". Mai shagon yace "ai ina ban sanka ba bazan taba yarda ba. Kaga kawai in bazaka saya bane to". 




Alhj ya kalli yar tasa yace fatima "kinga yanzu bani da canji zo muje gida in dauko kudi sai mu dawo in saya miki". Fatima ta saka kuka ta kankame yar tsanar gam a kirjinta, wai ai ita baza'a rabata da yar babyn ta ba. Alhj yayi-yayi da ita ta bari ya dawo amma taki. Ba yanda ya iya dole wayarsa ya bawa mai shagon ya rike ya basu yar babyn kafin ya dauko mishi kudin. Haka kuwa akayi. Mai shago ya karba yaje shago ya ajiye tukun ya dauko musu wata yar karamar akwati. Ta kayan yar babyn ce. Suka karba fatima sai murna take ta dauki yar babyn wacce ta kusa tsayinta tasa a mota suka tafi gida tunda suka taho a hanya yar babyn ta fara kwai-kwayan fatima. In tayi dariya itama sai yar tsanar tayi, haka in ta bata rai! Sai yar tsanar ma ta tsuke fuska. Fatima dady ta karaji nan tata mata abubuwa har gwallo in faty tayi yar tsanar sai ta rama ............................................... . .........```





Mujee zuwa.



Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION





Autan writers nee king boy















👺👽👽👽👽👽👽👺 


   *^^^^^^^______^^^^^*

    *ALJANAR FATIMA*

   *^^^^^^_______^^^^^*


👺👽👽👽👽👽👽👺 


Page 17-18



NA. 👑 KING BOY ISAH 👑




👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽


😍💃🏻 NA BAKU WANNAN PAGEN NE SABODA NAGA... 


 *TSABAR TSANTSAR TSANANIN TSAGWARAN, TSAYUWA DA TSAIDA TSABAGEN TSAIDADE SO DA YA ZARCE NA TSINTSAYE SAMAN TSAMIYAR TSANGAYAR TSAUNI TSANANIN SO DA KAUNA DA KUKE NUNA WA LITTAFAI NA.*


😍 *INA JI DAKU SABODA HAKA MA NA RUBUTA SUNAN KU A FARFAJIYAR FARAR FAIFAR FATAR FARAR ZUCIYATA DAKE FAFADAR FADAR FADAMA MAI FANFUNAN DA KE FIDA FURUCIN FITARWA MASU FUKAFUKAI DA FANKOKIN.....* 🙊


*SALMAH QUEEN*



*ZEANAV DAWISU*

 

_INA JI DAKU ALLAH YA BAR MIN KU KUNA SAHUN GABA CIKIN MASOYAN LITTAFAINA_



_SAM KALAMAN BAKINA SUNYI KADAN DA SU BAYYANA IRIN TSANTSAR FARIN CIKIN DA NAKE JI YAYIN DA NAGA SAKONIN MASOYANA SUN SHIGO WAYATA._


FOLLOWING US AS:

----

Like us page.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

----

Check us blogger.

Zamaniwriters.blogspot.com

----

 Email us your comment and reports.

Zamaniwritersassociation@gmail.com

----

whatsapp's number 

08096831009

----



               *KARSHEN PAGEN BAYA*

~In tayi dariya itama sai yar tsanar tayi, haka in ta bata rai! Sai yar tsanar ma ta tsuke fuska. Fatima dady ta karaji nan tata mata abubuwa har gwallo in faty tayi yar tsanar sai ta rama~

```»»Tun a mota yar babyn ta fara magana. a cikin wata irin karamar murya. "Sunana safuratu ina tayaki murna da sayana da kikayi". Fatima ta juya domin ganin mai magana bataga kowa ba. tace "abba kaine kayi magana Yanzu?". yace "aa magana kikaji nayi". tace magana naji ko yar babyna ce?. alhj murmushi yayi yace "'yar baby kuma ai ba irin mai magana bace bakiga batada speaker ba...?. Kafin ya rufe baki wata siririyar murya ta kara magana, "Zan dinga saki dariya, zan dinga baki labarai masu dadi, amma ni fa ba'a barina da yunwa, kuma ni kullum sai anyi min wanka an canza min kaya anyi min make-up....." alhj tsurewa yayi domin yaji tabbas yar babyn ce ke magana a tsorace ya fige yar robar yana dudubata wai ko zaiga speaker a jikinta amma bai gani ba. ita kuwa fatima murna kawai take da jindadi yar babynta na magana. alhj yace "fatima 'yar babynki ce fa mai maganar nan to amma ni banga speaker a jikinta ba"

. fatima ta karbe abunta tace "Baba ai itama da baki take yi kamar mu baka gani bane?". 





yace "eh ni ban gani ba, amma bari in na koma zan tambayi mai shagon inji ko tana magana. Domin ni ta bani tsoro fa mamana". Haka dai yaci gaba da tuki cike da mamaki har suka karasa gida. fatima ta sauka da gudu tana murna ta nufi cikin gida rungume da yar babynta a parlo ta iske duk yan gidan yara nata rashin ji masu wasa nayi masu rigima ma hk. ai kuwa yan yaran na ganin yar babyn suka yo kan fatima wannan ya karba wannan ya figa wai ko wane yaro sai ya je gurin uwarsa ya kama kuka wai a kwace a bashi. can wasu yara marar ji guda biyu daya ya kama wajen kan yar babyn daya kuma ya kama kafafun sai jayaya suke wannan yana so ya karbe wannan ma yana so ya karbe fatima kuma sai kuka take zasu karya mata yar baby gashi ba dama tayi mgn. 




lokacin alhj ya shigo. "kai! kai! ku wane irin mararsa jin magana ne. zaku balla mata abu bata kayanta maza". mika mata sukayi. ta karba ta nufi dakinta asiya ta harare ta tace a zuciyarta "munahika ai alhajin zai tafi zaki ci ubanki". alhj yace "yanzu ku kuna gani a gabanku zasu batawq yarinya abu a gabanku amma ko kuyi magana. haba asiya kece babba fa ko sauran basuyi magana ba ai ya kamata ke kiyi mawa yaran magana". "uhm ai ni kullun a wajenka marar adalci ce to amma yanzu kai ga adalci nan a fili ka nuna mana, tunda ga yara nan da yawa a gida kuma duk yayanka ne amma ace ka ware fatima ita kadai ka saya mata abu. wannan shine adalci ko?". Ran alhj ya bace har zaiyi mgn kuma sai ya fasa ya wuce up stairs. yaje dakinsa ya dauko kudi yq fito yayi tafiyarsa. 




su Zuwaira sukayi dariya sukace "aunty asiya kin min daidai ke kadai ce maganin alhj a gidan nan". asiya tace "hmm ku kyale sa ai yau saina toya yar babyn nan muga ta tsiya sai inga me zaiyi haba ya zai dinga fifita wacce kudabukar yarinyar a kan sauran yara bari inje gurinta". su Zuwaira binta kawai sukayi da kallo. ta tashi buzun-buzun ta ta nufi dakin yara. fatima zaune take a kan gadanta ta zaunar da yar babyn tana cin bisket itama tana tura mata a baki. tana ci ci diyata daga bakin. kawai sai taga bakin ya bude. bata wani firgita ba sai ma dadi da taji. ta tura mata bisket din tace "kin koshi.?  




lokacin asiya ta karaso gurin ta kama yar babyn da hannu daya ta wullata jikin bango ta fado tim! ta kuma wanke fatima da mari "shegiya yarinya me kike a nan tun dazu ina can ina jiranki zan aike ki kin wani shigo daki kin zauna. dama nasan wannan yar babyn da kika samu ita zata dinga hanaki aiki amma bari ynz in dauke tq in yayankata in toya muga ta tsiya". fatima ta fashe da kuka tana bawa asiya hakuri karta yanka mata ya' abun mamaki fatima na fara kukan suka jiyo kuka a baya. asiya ta juya baya. yar babyn ta gani a zaune tana kuka harda ruwan hawaye




Abunda yayi mutukar tsorata Asiya kenan, da gudu taje ta shige karkashin gado, fatima na ganin haka ta sauko tuni tama bar kukan ta fara dariya, mama asiya ta bata dariya. Zuwa tayi ta dauka yar babyn tana lalashinta. "Yishiru-Yishiru diyata. Mama asiya ce ta taba min ke ko?" Kunnuwan asiya sunji lokacin da yar babyn tace "Eh itace". Cikin wani karamin voice, "To yi shiri bazata sake ba". Asiya a dan tsorace ta fito daga nesa tace "Au! Fatima dama yar tsanar taki tana magana?". "Eh mama asiya ai tun a mota ta fara magana, babama ya dauka bata magana". Asiya tace "to dan kawo ta mu gani". Amsa tayi ta duduba amma bataga speaker ba. "Fatima ina speaker da wajen sa battery?". Mama ai da baki take magana kuma ba'a saka mata battery, yanzu nayi mata wankq bata bushe ba".  




Abuda ya fadowa asiya a rai shine. Hawayen da ta gani wato ruwan da fati tayi mata wanka ne. Ai kuwa ta maka diyar da kasa tasa katuwar kafarta ta taka tabi ta samanta ta wuce tana hararen Fatima hade da cewa. "Dauki yar iskar yar tsanar ki, ko dan wannan ai tama wuce yar tsana a girm saidai ace *ALJANAR FATIMA*. Fatima bata tanka mataba da sauri taje ta dauki yarta taci gaba da yin wasa da abunta. 



A falo ta iske su Zuwaira suna nan inda suke basu tashi ba. Asiya tana dan dangeshi ta karasa ta zauna ta saki wani gwabran nishi. Wanda yasa su Zuwaira saurin tambayar "Lafiya dai aunty babba, fatan kin yayanka shegiyar yar tsanar nan..." Tarar nunfashinta tayi ta hanyar cewa, "Ina fa 'yar tsana da ta tsoratani. Ashe wai tana magana, ban sani ba ina shiga dakin na karbe ta na maka a bango juyawar da zanyi sai naganta tana kuka harda hawaye. Ai kafin kice me tuni na shige karkashin gado na dauka ai aljana ce, washh! Wllh har yanzu gabana faduwa yake". Su hauwa najin haka suka kwashe da dariya hararar da ta daka musu ita tasa su hadiye dariyar dan dole. "Wai ina su asmart ne ko har yanzu basu dawo daga wajen kitsan ba". Asiya ta tambaya. "Eh wllh kinga har yanzu basu dawo ba, Ni jirama nake su nasan su zasu lalata wannan 'yar tsanar". Zuwaira ta bata amsa. "Ai kinji shiru gidan dake basa nan". 




Su Nasmat kuwa na can gidan kitso gaba daya su hudun harda Fiddausi da ameera. Dake mai kitsan tasan halinsu suna zuwa tace su zata fara yiwa su tafi abunsa.kafin a gamawa asmart kitso saida nasmat ta Zubar da duk ruwan gidan, wai wanke kai take daga ta wanke sai ta shinshina tace wari yake. su Fiddausi dama basuyi magana ba dake sunsan halin ta idan ma sukayi mata magana baji zatayi ba. Da sauri mai kitsan ta burbura tayiwa asmart kitson Nasmat duk ta jike kan, Amma a haka mai kitsan tace tazo a mata dake ya dansha iska. Haka itama asmart tata barna kafin a gamawa nasmat saida tasa yara sunfi biyar kuka a ciki harda wanda ta fasawa kai. Jini na zuba yaran tafi ya gayawa uwarsa. Asmart tazo ta kama nasmat kitsan ma ba'a gama ba sauran layi biyu. Amma a haka suka gudu, basu zame ko'ina ba sai gidan aunty Sakina yayar mamar su ce. (Wato mama asiya.) 





,

Matar yar lukuta wacce itama jikinta ya kai na mama asiya. Nan ta tashi tana musu sannu da suwa. Bayan sun gaidata. Tace, "Asma'u uwayen rashin ji ziyara aka kawo min yanzu da yamman nan?". Bayan sun kalli junane asmart tace "Eh mama asiya ce tace mu zo kuma ma a nan zamu kwana". Sakina tace to madallah ai naji dadin zuwanku dama ga aiki nan kaca-kaca ya min yawa a gida sai ku dan kama man muyi sauri mu gama kan magariba". Cikin daga murya nasmat tace, "Kutumelesi kiji wannan matar wai mu tayata aiki". "Yaseen ni dai bazanyi ba saidai ke ki tayata". Cewar Asmart "Kutt kinga malama yayar mamar ku ce ba yayar mamana ba. Dan haka ko kwano daya bazan wanke mata ba". "Ke zaki tayata". "A'a wallahi ke dai". Garda ma suka hauyi a tsakanin su ko wacce nacewa ita bazatayi aikin ba, abun har ya kaisu ga kunce, ki'kir-ki'kir suka kama wai su da gaske fada zasuyi.....,.............```



Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION


Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn 

https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





Autan writers nee king boy













👺👽👽👽👽👽👽👺 


   *^^^^^^^______^^^^^*

    *ALJANAR FATIMA*

   *^^^^^^_______^^^^^*


👺👽👽👽👽👽👽👺 


Page 19-20



NA. 👑 KING BOY ISAH 👑




👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽




IN DEDICATION TO YOU  

*KHADIJA CANDY* *_ALLAH YA BAR ZUMUNCI, YASA KIFI HAKA NA GODE DA ADDUO'IN DA KIKE MIN. KEMA KUMA ALLAH YA KARQ MIKIN DUMBIN BASIRA DA HIKIMA DA FASAHA, ALLAH YA KARE MANA KE DAGA SHARRIN MAHASSADA DA YAN ADAWA DA MAKIYA. ALLAH YA TSARE MANA KE DAGA SHARRIN DARE. SHARRIN RANA, FATAN KOFOFIN ALKHAIRAI SU BUDE A RAYUWAR KI DUK NA SHARRIN SU GARKAME. AMIN YA ALLAH.*_





_SAM KALAMAN BAKINA SUNYI KADAN DA SU BAYYANA IRIN TSANTSAR FARIN CIKIN DA NAKE JI YAYIN DA NAGA SAKONIN MASOYANA SUN SHIGO WAYATA._


FOLLOWING US AS:

----

Like us page.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

----

Check us blogger.

Zamaniwriters.blogspot.com

----

 Email us your comment and reports.

Zamaniwritersassociation@gmail.com

----

whatsapp's number 

08096831009

----



               *KARSHEN PAGEN BAYA*


~Dan haka ko kwano daya bazan wanke mata ba". "Ke zaki tayata". "A'a wallahi ke dai". Garda ma suka hauyi a tsakanin su ko wacce nacewa ita bazatayi aikin ba, abun har ya kaisu ga kunce, ki'kir-ki'kir suka kama wai su da gaske fada zasuyi.~


```»»Aunty Sakina da ta saki baki tana kallansu ita kallansu take abun yaso ma ya bata dariya kuma sai ta basar. Ta cire takalmin ta ta fara kwada musu da sauri suka saki juna. "Kaji yan iskan yara daga zuwa zaku mayar min da gida kamar gidan dambe?, To wallahi bazan iya ba ku tatara ku koma na gode allah ya baku ladan ziyara". Suna jin ta fadi haka sai suka shiga bata hakuri Da rokonta a kan tayi hakuri ta barsu.



Bacin rai tanuna musu sosai ta murtuke fuska tace, wallahi kafin in futo daga dakin nan ku bar gidan nan in kuwa ba haka ba wallahi sai jikin ku ya gaya muku". Tana gama fadar haka ta shige dakin. Su kuwa kofar dakin sukaje duk su biyun sukayi Neldown kamar wasu mutanan kirki. 



Sanda tayi kamar mintuna biyar tukun ta fito daga dakin sun bata dariya a yanda ta sansu da rashin ji yau sune roko harda durkusawa. Nan dai tace musu ta hakura amma fa aiki ba'a janyewa'. Da sauri sukace "Mun yarda".  



A can kuma gidan mai kitso uwar yaran da aka fasawa kai ce, tazo da wani danta saurayi dauke da wata gora. Da ganin matar kasan jarababa ce, ko yanayin tafiyarta zai iya shedama ba da alkhairi take tafe ba. "Wace yar kutu... Ce ta fasawa yarona kai, ku nuna min ita yanzu itama insa a rotsa mata nata kan". Matar ce ta shigo gidan da wannan furucin lokacin da dan nata kuma ya daga gorar yana shirin makawa duk wacce aka nunu. Da gudu Fiddausi da Ameera suka Ruga dakin mai kitso. Tana shirin binsu Mai kitsan ta shiga gaba ta tare kofar dakin tana "ki saurara basu bane ki saurare ni, kannansu ne basu ba". Tsayawa tayi tana jijiga. "To ai anzo a dai-dai kenan yanzu in nasa aka fasawa daya daga cikin yayyen nasu kai, kinga ai anyi 1-1 ko". Aa dan allah ba haka za'ayi ba kinga nidai kitso suka zo min nan kuma sun tafi gida tun lokacin da sukayi wannan ta'asar. So abunda yafi shine ki bisu can gidan Alhaji salim din". 



"Kutumelesi dama yan gidan alhaji salim ne. Kai zo muje ba zama lafiya yau zasu san sun takali wutar dafa kansu". Fuwww!! Ta wuce yaran na binta bayq da kulki a hannu. Tun daga get suka fara rikici da mai gadi, yaki barinta tq wuce, sanda ta shsmmace shi tukun ta ingiza shi ya fadi da sauri suka shiga. "Asiya! Asiya! Asiya!". Da duk illahirin karfin sautinta take kwalla wannan uban kiran. Ta cire gelen dake makale a kafadarta ta daura a ku'gu. 




Da sauri su asiya da sauran yan gidan suka fito suna tambaya "lafiya-lafiay". Cikin masifa da tsiwa tace, "Ina fa lafiya ai tunda kuka ganni a haka kunsa ba lafiya ce ta kawo ni ba. Wannan bala'eun 'yaran naku ne suka fasawa dana kai dan haka nazo ko dai a fiddosu insa a fasa musu kai. Ko kuwa kuga tashin hankali". Nan ta fara jijiga tana cewa dan saurayin nan ya matso kusa ya shirya. Asiya tace "Innalilahi yanzu su asmart bazasu barmu mu huta ba, Rikicin nasu ba iya gida ya tsaya ba kenan. Kinga mariya zo muyi wata magana". 




Mariya tace itafa ba inda zata sai an fiddo da su asmart ta rama wa yaranta tukun ta tafi daga gidan nan domin har wani hauka-hauka take tana tsalle-tsalle lokacin da Asiyar kecewa suzo su sasanta. Da kyar asiya taja hannunta bayan dakunan su. Basu fi mintuna biyu ba suka fito suna washe hakora. Gaba dayan fishin da Mariya tayi ya zama tarihi ba abunda take sai godiya wa hajiya. Sauran matan sunyi mamaki abun ya daure musu kai. Mariya tayi musu sallama tacewa Dan saurayin "Kai zo mu tafi ai na yafe musu". "Haba mama Najeef fa aka fasa wa kai shikenan munzo a rama kice wai kin yafe". "Kai zanci ubanka fa wai bani nake maka magana ba?". Yana dan gungunin sa ya bita suka fita. Sunje fita mai gadi ya leko ta kofa hade da cewa "Jarababiya kawai allah ya isa turenin da kikayi". Da sauri ta juyo a fusce zatayo kansa "Me kake cewa". Habawa ai da gudu ya shige dakin ya rufo.



Bayan su Asiya sun koma cikin falo Zuwaira tace "wai aunty dukan matar nan kikayi ne ko kusa warning kikayi mata. Naga lokaci daya ta wani saukko". Yar dariya asiyar tayi hade da cewa, "Hmm ba ko daya daga ciki kinsan fa in kikaga mutum na irin haka to in kika bincika harda talauci a ciki, Naira 500N na bata kawai nace taje ayi mishi magani, Shine fa kinji harda su godiya". Dariya sukayi gabaki daya Hauwa'u tace "Gwara da kikayi haka wllh dan da alhaji ya zo ya tarar da ita. Bama su asmart ba mu kanmu bazamuji dadi ba". "Ashe dai kina ganewa gashi yau a dakina yake kinsan yanda muke da shi dama. Ai shiyasa nayi saurin watsawa Wutar nan ruwa". 


************


Kwance take a daki ita kadai tana barci. Wata mahaukaciyar dariya mai gigitarwa ce ta daki dodan kunnan ta. Bata shirya ba ta tashi zumbur! A tsorace, tana waige-waige "Alhaji! Alhaji! Dubawa tayi gefan wajen wayam ba alhaji. Hahahahahaha! Dariyar mace ta jiyo kamar a downstairs a dan tsorace ta tashi ta bude kyaure a hankula ta laleka bataga komai ba, hakan yasa ta idasa fitowa. Da fitowarta Kofar dakin ta taji an banko da karfi kamar za'a balla, dan kara tayi ta zabura kuma. Lokaci ta nema bude kofar amma sai taji kamar an Garkameta da kwado. Abunda yayi mutukar girgizata kenan. A saman dakuna ne guda hudu dakinta ne a can karshe sai na Zuwaira sai na Hindu wanda yanzu alhaji ya mayar nasa. Na karshen kuwa na Hauwa'u ne. Dan lungun dakunan a haske yake fes da fararen Gululuka. Lokaci daya tada wutar ta fara farfari. Kwayayen suna wata irin girgiza dariyar Yarinya ne ya biyo baya dariyar marar dadin ji. Ahhh! Ahhh! Da karfe ta fara ihun itama. Ta durkushe a gurin ta sa hannaye ta rurufe kunnuwanta. Hade da runtse idanu. Dif! Taji komai ya tsaya an bar dariyar haka kwayayin sun daina girgiza da farfarin da suka. Mikewa tayi cikin kuka kuka ta fara tura kofa da karfi tana fadin "na shiga uku ni Asiya me ya fito dani. Gashi sai tsorata ni ake yi". 




Ta baya taji an tabata wata murya yara taji ance "Mama Aciya juyo cigan ni nayi kyau?". A hankali ta fara juyowa dan ganin mai maganar a tsorace. Koda idanunta sukayi tozali da mai maganar Aljanine yazo mata asuffar Iliyasu babban Dan hauwa. Kanshi a rabe yake gida biyu hayaki ne ke fita da wani turiri a ko wanne bare. Aisiya na ganin haka jikinta ya fara bari ta hau kyarma. Dariya taji ya farayi marar dadin saurare. Ya nufo gunta yana fadin "Nayi Ceau (kyau) kuwa mama aciya(Asiya)?". ta kwada ihu! Ta zuba guje ta nufi Downstairs tsabar firgicewa Bata iya kirga iya matatakalan da take tsallakewa. Sabanin 'da, da in zata sauka da Daya-Daya take yi a hakan ma a hankali.




Tana saukowa tayi wata uwar tirjiya a falo nauyin jikinta da kadan ya rinjayeta ta fadi. Ba wani abu yasa ta tsayawa ba. Sai ganin wata yarinya da ke zaune a Falon cikin wasu fararen kaya masu dauke ido. Yarinyar ta juya bayane bata iya gane ko wacce ce. Hakan yasa ta fara matsowa a hankula tana kiran sunayen yaran gidan wanda take tunanin ko daya daga ciki ne. "Dan ubanki fatima me kike yi ne a nan?. Cikin wannan dare?". Shiru bataji amsa ba hakan ya tabbatar mata da ba fatimar bace. A hankali take tafiya tana nufar wajen da yarinyar take. "Ba fatim bace?. Shimsiya ce? Sa'adatu ce?. Ko dai salma ce?". Sunan jikokin ta take ta jerowa wanda take tunanin ko sune. Lokacin ta karasa wajen mika hannu tayi tana karkarwa kamar ta taba kamar karta taba. Tana taba yarinyar tajuyi hade da wani mugun razananen kara da ya daki kunnan ta suman tsaye Asiya tayi a gurin..............,......```




TOFA MUJE ZUWA READERS. YANZU ZAMUGA GWANAYEN TSORO. AN FARA KENAN



Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION


Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn 

https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





Autan writers nee king boy
















👺👽👽👽👽👽👽👺 


   *^^^^^^^______^^^^^*

    *ALJANAR FATIMA*

   *^^^^^^_______^^^^^*


👺👽👽👽👽👽👽👺 


Page 21-22



NA. 👑 KING BOY ISAH 👑




👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽




IN DEDICATED TO ALL ZAMANI WRITERS. *ALLAH SARKI YAN UWANA UBAN GIJI ALLAH YA ALBARKACI RAYUWAR MU. A KULLUM GURINA INGA ZAMANI BA'A BARMU A BAYA BA. ALHMDULILAH KULLUM CIGABA MUKE. ALLAH YA KARA BASIRA, YAN UWANA DOMIN NI KAMAR YAYYAI NA NA DAUKE KU. AUTAN KU NE KING NA AUTAR KU QUEEN. ALLAH YA BARMU TARE YA KARA HADIN KAI. AMIN* ♥



.



               *KARSHEN PAGEN BAYA*

_Tana taba yarinyar tajuyi hade da wani mugun razananen kara da ya daki kunnan ta suman tsaye Asiya tayi a gurin._

»» Aljanar a sufar shamsiya take, jikar Mama asiya hannaye biyu tasa da karfi ta shake wuyan dogayen faracen hannunta masu shegen kaifi. Bakin shamsiya wani bakin abune mai kaure ya fara zuba. Kuma idan ya zubo din a kan mama asiya yake sauka. Mama asiya in banda ihu da neman ceto babu abunda take. Da dai taga ba ko alamun mutane a gida wanda zasu kawo akaji.




Nan ta fara ihu tana kokarin kankare hannun Aljanar da ta makure mata wuya. Aljanar ce ta bude idonu hade da dakawa Mama Asiya tsawa. Ai kuwa fitsari ya fara zubowa harda dan guntun kashi da ya zubo. Fitsarin matseshi take amma zuba yake tsirrr! Duk jikin ta karkarwa yake. Magana na rawa "Haba shamsiya dan allah ki sake ni karki kashe ni me nayi miki ne?, nice fa mahaifiyar babanki". Mama asiya ce ke fadar haka. "Keeeee! Anji ke kika haifi mahaifina to ke kika haife ni ne ni?, Shin a yanzu ni dake waye baba ma?". Muryar mai kamar amsa kuwa aljanar ke magana da shi domin in tana yi dakin har wani jijiga yake yi. "Wallahi kece, kwarai kece baba. Kece uwata ma. Kece ubana, kece yayana, kece yaya ta kece.....". "Keee yimin shiru". Gum Mama asiya tayi ta tsaya da lissafin kafafunta sai rawar karkarwa take fitsari kuwa duk sanda aljanar tayi mata tsawa sai ya subuce ya kwararo. "Hahahhahahjahahhaha!




Aljanar ce ta dake kai sama tana wannan muguwar dariyar. Mama asiya ta dan shammace ta ta ware iya karfin da hannuwa biyu ta tura ta. Can aljanar ta fadi gefe. Tubur-tubur abu ga mai jiki ba gudun kirki, ta nufi hanyar Hawa sama, gaba daya wutar dakin ce ta dauke duf! Mama asiya bata daina gudu ba saida ta hadu da bango kanta ta buda ji kake gum!! Ta kuma zube kasa kamar an yarda buhun gero thom! Kanta ta dafe tana wash! Wash! Aljanar ta gani tazo dai-dai saitin kanta da wata wuka wulshe-shiya a hannunta. "Hahaha- wato ni zaki tserewa ko?. Wukuncin ki kisa ne". Da fadar haka ta daga takobin sama ta caka ma mama asiya a ciki.





Wani Mugun kara ta Saki ta tashi zaune tana nishi daya-daya tana laluba cikin ta jin ko da gaske ne abunda ya faru. Karar da tayi ya tashi alhaji zumbur! Ya fara tambaya "lafiya-lafiya"? Sai yanzu mama asiya ta fahimci cewa mafarki ne take ganin cikinta lafiya lau kuma haka kanta bata jin wani radadi. Alhaji ni kam wallahi bazan yarda ba ashe yarinyar nan mayya ce da wuka fa tazo zata kashe ni a mafarki, wallahi sai na dauki mataki a kanta, to ni kuwa me na tsare mata ne take nema ta cinye kurwata danya". Duk surutun da take alhaji binta yake da tambaya. "Wacece?, wai wace yarinyar". Budar bakin ta tace "Wace yarinya kuwa in ba wannan mayar...". Ta dan dakata tana tunani in fa tace shamsiya abun bazaiyi tsari ba. "Wace"?. "Wannan mayar 'yar taka ce Fatima, duk taimaka mata da nake a rayuwa wai ashe mayya ce ni tazo zata kashe". Tsawa ya daka mata nan da nan ya murtuke fuska, "Asiya bana san iskanci fa, bana san tambadar nan taki, kinje can kin tabo aljanunki sun motso shine zaki likawa marainiya wato. To wallahi kar in sake ji". Gungune kawai tayi, Alhaji kuwa ya kwanta ya juya baya abunsa. Mama asiya na zaune kamar ance ta kalli wajen mirror. Ihu! Ta kwalla ta rukun-kume alhaji kamar wacce zata shige jikinsa. Yarinyar ta gani a cikin mirror tana kiranta. Alhaji yana jinta ya kyale ta, can kuma saj yaji lema a jikinsa wanda yasan wannan ya wuce na gumi. 




Tashi yayi yana "Asiya wai miye a jikinki nake ji sharaf!". Har tashin da yayi a rike take gam da shi idanunta a rufe. Wata mahaukaciyar dariya alhaji ya kwashe da ita, Irin wacce ya jima baiyi ba harda kama ciki. Asiya ido a rufe taki budewa tunani take in ta bude zata sake ganin aljanar, Jin dariyar alhajin taki ci taki karewa, yasata bude ido a hankali bata ko kalli wajen mirror ba. "Alhaji ai dole kamin dariya wannan mayar 'yar taka so take sai ta kashe ni ta huta". "Asiya kalli jikinki fitsari ne fa kika sharara duk kin bata gadon, Hahaha wai duk tsoran ne haka harda fitsarin wando?". 





Sai lokacin Asiya ta lura da jikinta sharkaf take ta jika kayan barci da fitsari. A kunyace ta tashi da sauri ta nufi bandakin da ke cikin dakin domin tayi wanka. Bayan ta shiga ta juya baya tana kokarin Cire riga sai ji tayi wata kalar muryar 'Yan yara tace "Yauwa Shannunki da Juwa". Da gudu ta fito daga bayan dakin taje ta fada kan alhaji ta shishige mishi. Alhaji na niyar tashi yaje ya canza kaya domin ta jika shi amma sam ta hana ta rufe idanu ko budewa batayi. A haka suka kwanta har safe. Tun da safe taje dakin su fatima ta iske ta ta idar da sallah tana barci, nan fa ta hau tikar ta wai tashin ta take a barci, kai da ka gani kasan mugunta ne abun................

Comments