Sharri Kare Ne Part 4 Daga Littafin Dare Dubu Da Daya

 SHARRI KARE NE 4Waziri Aku 


HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI


(Daga Littafin Dare Dubu Da Ɗaya)


To, da Marini ya ga saurayi ya daina kawo musu abinci kamar yadda ya saba, ga kuma yunwa ta fara dafa shi, sai ya tashi daga kan gado, ya tafi inda Wanzami yake kwance magashiyyan, ya birkice shi, ya ƙwaƙule 'yan kuɗin da ke jikinsa duka, ya tarar da sulallan azurfa alfen. Ya fice daga ɗakin ya rufe ƙofa, kamar babu kowa a ciki. Ya sulale daga gidan baƙin ba tare da kowa ya gan shi ba.


Da fitarsa bai zame ko'ina ba sai gaban mai abinci. Ya tsaya ya cika tumbinsa tukuna, domin an ce da ruwan ciki akan ja na rijiya, sa'annan ya nufi kasuwa ya sayi tufafi masu tsada, ya ƙunshe ga takarda. Ya nemi gidan wanka kusa bai samu ba, sai ya gangara wata ƙorama da ya ga mafi yawancin mutane na zuwa don yin wanka.


Ya tulɓa wanka, ya sanya sabbin tufafinsa, ya shiga gari yana hura hanci kamar wani tajiri. Ya riƙa zagayawa cikin garin rariya-rariya yana kashe kwarkwatar ido. Ya tarar ashe dai garin nan gari ne mai tsari da kuma kyawon gine-gine, tun da yake bai taɓa ganin gari mai kyawu kamarsa ba. Nan take kuma ya lura da abu ɗaya da ya ba shi mamaki, mutanen garin duka ba su da wasu launin suturu da suka wuce fari da shuɗi.


Yana cikin tafiya sai ya iso ga wani shago da ya ga an shanya tufafi a gabansa, launin tufafin kuwa duka shuɗi ne. Ashe shagon nan marina ce, dami ya tsinke gindin kaba. Ya tafi ga majirayin shagon ya zaro farin adiko ya miƙa masa ya ce, "rina mini wannan ƙyalle yanzu ka karɓi kuɗinka."


Marini ya karɓi ƙyalle ya jujjuya shi ga hannunsa, sa'annan ya ce wa Abuƙir, "dirhami ashirin za ka biya."


Abuƙir ya dafe baki cikin mamaki ya ce, "wannan ɗan ƙyallen? To, a ƙasarmu dirhami biyu ake rina kamarsa."


Marini ya jefa masa ƙyallensa ya ce, "tafi da shi ƙasarku mana a rina maka. Idan ba dirhami ashirin ba, ba na rina shi."


Abuƙir ya ce, "to wane launi za ka yi mini?"


Marini ya ce, "zan rina maka shi shuɗi."


Abuƙir ya ce, "a'a, ni jan launi nake sha'awa."


Marini ya ce, "ban san yadda ake yin jan launi ba."


Abuƙir ya ce, "to rina mini shi tsanwa.'


Marini ya ce, "ban iya ba."


Abuƙir ya ce, "rawaya fa?"


Marini ya ce, "shi ma ban iya ba."


Abuƙir ya yi ta lissafo masa launuka daban-daban, Marini ya ce duk bai san su ba. Ya kuma ce, "ka sani mu arba'in muke marina a wannan birni, babu ƙari babu ragi. Dukkanmu kuwa mun gaji wannan sana'a ne daga iyayenmu, su ma sun gada daga iyayensu. Idan ɗaya daga cikinmu ya mutu, za mu koya wa ɗansa, domin ya gaje shi. Idan ba shi da ɗa, sai mu koya wa wani daga cikin 'ya'yanmu ya gaje waccan marinar, ba mu taɓa barin wani bare ya shiga wannan sana'a ta mu ba. Ka ga mu arba'in ɗin nan duka, ba mu san wani launi da ya wuce shuɗi ba."


Abuƙir ya cika da mamaki, gayar mamaki. Ya dubi marini ya ce, "ni ma da kake gani na nan, ba ni da wata sana'a da ta wuce rini a ƙasarmu. Na san yadda ake sarrafa baba a fitar da launuka iri iri daga gare shi. Idan ka yarda sai in zauna tare da kai, ka riƙa biya na, ni kuwa in koya maka yadda ake sarrafa launuka daban-daban har ka fi dukkan marinan wannan birni."


Marini ya girgiza kai ya ce, "ina fa za a yi haka, ko ɗan gari ba mu yarda ya raɓe mu ba, balle kai da kake baƙo. Wannan ba shi yiwuwa."


Abuƙir ya ce, "to ai sai in buɗe tawa marinar a cikin gari, tunda ina da 'yan kuɗina. Idan an hana ihu, ai ba a hana aha ba."


Marini ya ce, "wannan ma ba za ta saɓu ba. Ban da mu arba'in ɗin nan da na gaya maka, babu wanda yake da ikon buɗe wata marina."


Da Abuƙir ya ga dai marinin nan ya ƙi ba shi fuska, sai ya rabu da shi ya wuce gaba, ya tambayi inda zai samu wata marinar, aka yi masa kwatance ya nufi can. Shi ma wannan marini ya faɗa masa kamar yadda na farko ya faɗa masa. Bai gushe ba yana bin marinan garin, daga wannan shago zuwa wancan har sai da ya zagaya su duka arba'in. Dukkansu kuwa bakinsu ɗaya, babu wanda ya yarda ya ɗauke shi aiki a marinarsa. Da ya ga haka sai ya yi fushi, fushi mai tsanani. To, in ba rini ba wace sana'a zai yi? Ya tambayi hanyar fada, aka nuna masa, ya tasar wa can domin kai ƙara.


Da zuwa aka yi masa iso. Ya duƙa gaban Sarki ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ni baƙo ne kuma gwanin rini a ƙasar da na fito. Na kawo ƙarar marinan garin nan." 


Ya kwashe labarin abin da ya faru tsakaninsa da marina duka ya faɗa masa. Ya ƙara da cewa, "na san yadda zan rina tufa da duk irin launin da ake bukata. Ina iya sarrafa jan launi ya fitar da launin kowane irin fure ake so a duniya. Zan iya sarrafa tsanwa ya bayar da kowane irin launin ganyen ake bukata. Na san yadda zan sarrafa rawayan launi ya fitar da launin lemu da ruwan ƙwai ko makamantansa. Zan iya sarrafa baƙin launi zuwa baƙi-baƙi ko baƙi wuluk ko launin toka ko launin kwalli. Ina kuma iya sanya wa tufa launuka mabanbanta ta fito kamar launukan da ke jikin ɗawisu ko launukan gashin aku. Na san yadda zan rina zabibi da algashi da makuba da garura da ruwan goro da cincinbale." 


Ya yi ta zayyana wa Sarki launuka dai, wasu ma ko sunansu Sarkin nan bai taɓa ji ba balle ya gan su. Ya ƙarƙare da cewa, "ya Sarki, marinan garin nan duka babu launin da suke iya mayar da tufa sai shuɗi, duk da haka kuma sun ƙi yarda in shiga cikinsu balle in koya musu dabarar sarrafa launuka. Kuma sun hana in buɗe tawa marinar, ga shi kuwa ban iya wata sana'a ba sai rini."


To, Allah ya yi sarkin nan wayayye ne, mai son ci gaban garinsa. Yayin da ya ji abin da Abuƙir ya gaya masa sai ya yi fushi da marinansa. Ya kuma ce wa Abuƙir, "idan dai abin nan da ka faɗa mini gaskiya ne, cewa kai gwanin rini ne, to zan buɗe maka karofi, na kuma ba ka jari ka sayi duk abin da kake bukata ka zuba a ciki. Su kuwa waɗancan marinan, ƙyale ni da lalatattu, duk wanda ya yi maka ko da kallon banza ne, ka zo ka gaya mani, in sa a rataye shi gaban shagonsa."


Nan take Sarki ya kira masu gini ya ce musu, "ku tafi da wannan gwanin rini cikin gari, ya nuna muku duk inda yake so, kada ku kula da gida ne ko shago ko masaukin baƙi, ku rushe ko ma menene, ku zo mini da mamallakinsa a biya shi diyya, ku gina masa marina irin wadda yake so. Kada ku kuskura ku saɓa wa umurninsa."


Sarki ya sa aka ba Abuƙir tufafi na alfarma. Aka je barga kuma aka zaɓo masa ingarman doki. Sarki kuma ya ƙidaya dinari dubu ya damƙa masa ya ce, "riƙe wannan ka riƙa ɓatarwa kafin a kammala gina maka marina." Aka ba shi ƙerarren gida cike da kayan alatu, aka haɗa masa da bayi biyu da za su yi masa hidima. 


Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, insha Allah.


Bukar Mada

12/10/2022

Comments