Sharri Kare Ne Part 3 Hikaya Littafin Dare Dubu Da Daya

 SHARRI KARE NE 3



HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI


(Daga Littafin Dare Dubu Da Ɗaya)


Waziri Aku 


Marini ya sassauta ɗaurin ɗamarar da ta tanke cikinsa, ya gyara zama. Ya jawo kwandon abinci gabansa ya fara wurga loma, kamar ana wurga dutse a cikin rami, yana haɗiyewa kamar giwar da ta yi kwana da kwanaki ba ta haɗiyi komai ba. Kafin lomar ta faɗa har ya yanko wata yana shirin jefawa baka, yana kallon abincin sai ka ce maye na kallon mara lafiya. Wazami dai ya ƙura wa ikon Allah ido. 


Suna cikin haka sai ga wani mutum ya zo daga tantin Madugu ya ce wa Abusir, "Maigida ya ce ka zo kai da ɗan uwanka ku ci abinci."


Abusir ya dubi Marini ya ce, "ko za ka lallaɓa mu tafi?"


Marini ya ce, "ba na iya tafiya."


Wanzami ya miƙe ya bi mutumin har tantin Madugu. Da zuwa ya iske an shirya farantai na abinci iri iri. Madugu ya tambaye shi, "ina ɗan uwan naka?"


Abusir ya ce, "ba ya iya zuwa, yana fama da masassarar teku."


Madugu ya yi dariya ya ce, "babu komai, da ma duk wanda bai saba shiga jirgi ba, sai ya yi fama da wannan zazzaɓi, amma zai wartsake ba da jimawa ba." Ya samu ƙwarya ya jera farantan abinci a ciki, wanda mutum goma za su iya ci su ƙoshi, ya miƙa wa Wanzami ya ce, "ɗauki wannan ka kai masa, ka kuma yi hanzari ka koma domin mu ci namu."


Abusir ya karɓi abinci ya koma wajen Marini, ya same shi yana ta rizgar abinci, sai haƙoransa ke ƙara, ƙararas ƙararas, idan yana tauna abincin kamar karen da ke ragargazar ƙashi. Yana hannu baka hannu akushi kamar wanda aka ce za a kwace abincin daga hannunsa.


Abusir ya ce, "ba na gaya maka kada ka ci wannan abincin ba, za mu samu wanda ya fi shi daɗi a wajen Madugu? Dubi wanda aka ce in kawo maka." Ya miƙa masa ƙwarya.


Marini ya karɓa ya duba, da ya ga lafiyayyen abinci sabo, yana tiriri, sai ya ture busasshen burodi da gurasa gefe guda, ya faɗa wannan da ci kamar mayuwancin zakin da ya fito daga surƙuƙi ya samu wata 'yar dabba ya taushe, ko mayunwacin shahon da ya dirar wa ɗan tsako. Kai, kamar dai mutumin da ya kusa mutuwa don yunwa, aka kawo masa farfesun nama. 


Abusir dai ya tafi ya bar shi nan, yana ta dinarsa shi kaɗai, ya nufi inda Madugu ke jiransa. Suka ci suka sha tare har suka tumbatsa. Ya yi masa godiya, ya dawo inda abokin tafiyarsa. Ya same shi duk ya cinye abincin nan da ya kawo masa, ya jefar da ƙwarya gefe guda mawofanciya. Ya kishingiɗa yana sakatar haƙori, yana nishi don ƙoshi sai ka ce bokalo. Ya ɗauki ƙwarya ya mayar wa Madugu, ya kuma yi masa godiya, ya dawo inda Abuƙir suka kwanta har gari ya waye.


Kashegari Wanzami ya ɗauki zabirarsa ya kewaya cikin jirgi, ya ci gaba da yi wa mutane aski, abin da ya samu duka na abinci ya kawo wa abokin tafiyarsa, shi kuwa ya amshe ya kimsa wa cikinsa, yana daga kan shimfidarsa, ba ya zuwa ko'ina. Idan ka ga ya tashi, to zai je ne ya yi abin nan da wani bai isa ya yi wa wani shi ba. Idan kuma yamma ta yi, sai Abusir ya kawo masa ƙwarya cike da abinci daga tantin Madugu. Haka suka kasance a cikin wannan jirgi tsawon kwana ashirin, har suka isa gaɓar wani babban birni daga cikin birane.


Jirgi ya tsaya, ya sauke wasu daga cikin 'yan kasuwa. Marini da Wanzami suka sauka tare da su, suka yi sallama da Madugu, jirgi ya yi gaba. Suka sauka gidan baƙi, Abusir ya biya musu kuɗin ɗaki daga ɗan abin da ya samu a cikin jirgi. Ya tafi kasuwa ya sayo musu kayan abinci da nama, ya kuma sayo murhu da tallen dahuwa da akussa da kuma cokullan cin abinci. Da zuwa ya ɗora sanwar abinci.


Shi kuwa Abuƙir tun da suka shiga ɗakin, sai ya bi lafiyar gado, sai barci. Bai farka ba sai da Abusir ya gama shirya abinci da nama, ya tayar da shi domin su ci. Suka ci suka ƙoshi. Abuƙir ya dubi Abusir ya ce, "ɗan uwana kada fa ka zarge ni, har yanzu jiri nake gani." Ya sake haye gado ya yi kwanciyarsa, ba a jima ba ya fara minshari. 


Haka suka kasance tsawon kwanaki arba'in, kullum Wanzami zai shiga gari ya yi sana'arsa, ya sayo kayan abinci da nama, ya dawo masauki ya girka musu, ya shirya abinci cikin akussa sa'annan ya tayar da Marini da ke barci domin su ci. Idan suka fara cin abincin kuwa, sai Marini ya yi loma uku Wanzami bai yi ɗaya ba. Idan suka gama cin abincin, sai ya koma barc abinsa. Aka sake yin wasu kwanaki arba'in, Marini bai ko fita daga gidan baƙi ba, balle ya ce zai shiga gari. Ya yi ƙiba ɓulɓul kamar turkakken maraƙi.


Duk sa'adda Wanzami ya ce masa, "ɗan uwana, ya kamata ka ƙoƙarta ka shiga gari ka miƙe ƙafa ka kuma kashe kwarkwatar ido, da ɗai ban ga birni mai kyawun gine-gine kamar wannan ba, ban ga kuma mutanen da suturarsu ke ba ni mamaki ba kamar na mutanen wannan birni."


Sai Marini ya haye gado ya ce, "abokina kada ka ga laifina, wallahi jiri nake gani."


To, da yake Abusir mutum ne mai haƙuri kamar ƙasa, ga sauƙin hali kamar ruwa, sai ya ƙyale shi, bai taɓa sauya masa fuska ba, balle ya nuna gajiyawarsa. Aka ce jiki ba ice ba ne, yana da jini! A kwana na arba'in da ɗaya sai zazzaɓi ya rufe Wanzami har ya kasa fita wajen aiki. Don haka sai ya samu wani saurayi cikin masu kula da gidan baƙin ya ba shi kuɗi domin ya riƙa sayo musu abinci. Saurayi ya yi kwana huɗu yana sayo abinci yana kawo musu. 


A cikin waɗannan kwanaki rashin lafiyar Wanzami ta yi tsanani ƙwarai, har ya fita daga cikin hayyacinsa. Ashe kuma kuɗin da aka ba saurayi na sayen abinci sun ƙare. To, da Marini ya ga saurayi ya daina kawo musu abinci kamar yadda ya saba, ga kuma yunwa ta fara dafa shi, sai ya tashi daga kan gado, ya tafi inda Wanzami yake kwance magashiyyan, ya birkice shi, ya ƙwaƙule 'yan kuɗin da ke jikinsa duka, ya tarar da sulallan azurfa alfen. Ya fice daga ɗakin ya rufe ƙofa, kamar babu kowa a ciki. Ya sulale daga gidan baƙin ba tare da kowa ya gan shi ba.


Za mu ci gaba.


A yi SHARE domin wasu ma su amfana.


Bukar Mada

08/10/2022

Comments