💻👩🏻💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼
---------------------------
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร. °°________________________°°
⚔ // *FESHIN JINI* \\ ⚔
_Littafin yak'i_
°°________________________°°
*Babi na daya (1)*
__________________
©
🤴🏻 *KINGBOY ISAH* ✍🏼
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
*GODIYA: Ga Allah subhanahu wata'alah, mai kowa mai komai. Ina dada gode maka ya ubangijina ka dawwamar damu bisa turbar gaskiya. Allah kasa mu cika da imani kuma Allah ka kara mana ilimi da basira. Da sunan ka na fara Allah ka dafa mun*
*TSIRA DA AMINCI: Su kara tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu S.A.W da alayan sa da sahaban sa. Har i zuwa ranar sakamako*
*KULLUM GURINA: Shine in faranta muku masoya. Yau ma ga wani sabon littafi da fatan zaku karbe shi hannu bibiyu. Idan nayi kuskure ni kani ne a gare ku. Ku ja min kunne sannan kuyi min gyara don gaba kar na kuma*.
*SAKON TA'AZIYA GA YAR UWAR MU ZEETTY (MMN HANNAN) NA RASHIN MAHAIFIYAR TA DA TAYI 9/4/2018. ALLAH KA JIKANTA KA GAFARTA MATA. ALLAH KASA TA HUTA AMIN*
Budurwa ce yar kimanin shekara sha biyar wace take sanye da kayan fata. Shiga irin ta jaruman kwarai. Bayan ta kuwa wata zafgegiyar takobi ce doguwa wacce ta kusan rabin yarinyar ma a tsawo. Yarinyar ba a ganin fuskar ta domin ta rufe ta da wani jan kyalle mai duhu, idanun ta kadai kake iya gani farare fes da su. Gashin kanta baki kirin wanda aka kitsa shi guda daya ta jefa shi baya shine har kugunta. A tare da ita akwai maza samari biyu wanda kusan sa'anin juna ne. Dukan su su biyun suna da kira irin ta sadaukai Kai da kaga fuskokin su kasan ba wasa. Na gefan ta na dama mai suna Basim yana rataye da wata irin kwari da baka mai ban mamaki domin kifiyoyin dake cikin kwarin su kansu sun banbanta da irin wanda ka saba gani. Domin ba na itace bane na wani baki karfe ne masu shegen tsini. Dayan saurayin kuwa mai suna Asad yana rataye da wata takobi yana kuma daure da wata irin sarka bak'a mai kama da bulala wacce ya nanada a kugunshi. Kai da ganin wadanna mutane kaga Gawurtatun mayaka madaka karti in ka cire yarinyar nan dake a tsakiyar su yar karama da ita. Abunda zai baka mamaki shine da umarninta suke amfani. Ga dukkan alamu dai farkon shigowar su kasar kenan domin jama'ar gari sai kallon su ake yi. Duk da kuwa yau garin akwai baki amma wadannan sai suka banbanta. Su kuwa basu damuwa ba suka ci gaba da nausawa cikin garin. Basu zame a ko'ina ba sai a wajen wani babban fili wanda ya hada Dubban jama'a sai ihu ake yi ana tafi da alamu dai wata gasar ake yi a gurin. Haka suka ci gaba da ratsawa cikin jama'a har suka matsa gaba-gaba suka kasance a gaban fili. Katoton fili ne dubban jama'a na zagaye da shi. Ga kuma sarakuna dake karkashin wannan masarauta su Ashirin da biyu. Duk suna wannan fili na gasa. Wannan matashiyar budurwar kuwa babu inda idanun ta suka sauka sai a kan basarake wanda ke mulkin gaba daya nahiyar. zaune yake can bisa wata makekiyar kujera ta zinari. Ya hakimce. Hagun da dama na kujerar sadaukan aljannu ne masu muggan makamai sai muzurai suke yi. Suna kallon sama da kasa gabas da yama kudi da arewa. Ko tsuntsu ya gifta kuwa sai kusan guda hamsin daga cikin su sunyi sama sun kamo shi sun gididiba shi. Kai da ganin wannan sarki kasan ba a kawo wargi gaban shi. Idan ka kalli tsakiyar filin kuwa wani zafgegen kato ne rataye da wata makekiyar adda, mai shegen kaifi. Shi kanshi wannan jarumi dake tsaye a filin kallon shi kadai ya isa abun tsoro. Dan jikin shi duk a murmurde Jijiyoyi burda-burda. Idanun shi jawur kamar garwashin wuta, gasu mayan-mayan. Fuskar nan sam ba annuri. Gaban shi wasu samari ne su biyar cikin shigar yaki. Ko wannen su rike da mugun makami sun fuskan ci wannan jarumi mai suna Gunzar bin Jan. Amma duk jikin su rawa yake da alamun tsoro a fuskokin su. Duk da kuwa suma suna da kira irin ta jarumai. Alkalin wasan da ya kasance mai shegen kwarin murya ya fara magana. "A yau filin gasar shekara wanda aka saba yi na wannan gari mai suna Niyaha, babban birnin kasar sin. Wanda sarkin sarakuna Shaddar bin khais ke mulka. Filin zai fara ne da karawar Gunzar bin jan sadauki fasa taro mai tarwatsa rundunar yaki wanda duk birnin nan muke alfarwari da shi. Zasu kara da wasu Sadaukan su biyar wanda aka tabbatar da sadaukan tar su a garuruwan su. Dan haka jama'a a sha kallo lafiya. Gunzar da abokan karawar sa gare ku". Da jin haka filin ya kara kaurewa da shewa. Gunzar ya juya yayi gaisuwa ga sarki Shaddar bin khais. Shaddar ya dago mai hannu tukun ya juya ya fara kallon Abokan karawar nan tasa yana wani irin huci hade da wata irin harara da yake aika musu daya bayan daya. Hararar ta sa kadai ta isa ta firgita mutum har ma ya saki fitsari. Al'amarin da ya kara tsoratar da abokan karawar tasa kenan. Nan take suka fara juyi su biyar din suka karkasu suka saka Gunzar a tsakiya. A can gefan kuwa tuni wannan baki sun gyara tsayuwar su dan ganin yanda wannan gasa zata kaya. Ko da Abokan karawar Gunzar suka ga sun kewaye shi sai suka yo kanshi a tare kamar hadin baki. Wuhuhu In da sun san abunda zai biyo baya da basuyi gangancin tahowa a tare ba, Domin Gunzar tuni ya tsara yanda zai musu fuk! daya. Koda suka ga sauran baifi taku uku ba su karasa gare shi. Sai gabadayan su suka daga tsalle a tare da mugun nufi. Koda ganin haka sai Gunzar yayi wata irin hajijiya wacce ta watsar da su gaba daya kai kace maguna ne suka kai wa giwa hari. Nan fa sukayi sama tukun suka fara zubowa kasa wasu sumamu wasu kuwa a kakarye. Jama'ar gurin kuwa tuni suka cika da tsananin mamaki na ganin irin karfin da Gunzar yake da shi. Nan dai jami'an gasar suka fara shigowa suna janye sumammun mayakan nasu. Filin gasa kuwa in ka dauke bakin jaruman nan guda uku da kuma sauran sarakuna wanda aka kada jaruman nasu. gaba daya kowa murna yake ana ihu hade da kara jinjinawa Gunzar jarumi a kasar ta su. Hatta sarki Dariya yake hade da jinjinawa Gunzar domin Gunzar na gaban goshin shi ne yana matukar ji da shi. Gunzar ya fara daga hannu sama yana wani irin ihu hade da dukan kirji cike da kurara kanshi. Bayan fili ya dan lafa sai mai shelar nan ya sake mike wa yana mai cewa. "Shin akwai wani jarumi kuma wanda zai iya ja da gwarzan mu Gunzar". Ya fadi haka kusan sau uku amma duk irin jarumai da sadaukan da aka tara a filin wanda suka zo daga kasashi daban-daban gaba daya aka kasa samun wanda zai shiga wannan gasar. Domin shiga wannan gasa daya yake da sallama rayuwa. Jin shiru da akayi ba wanda ya tanka zai shiga tasa mutanen kasar Niyaha gaba daya sai suka kama ihu suna murna domin an rasa jarumin da zai tari gwarzan su. Wanda Gunzar a cikin sadaukan kasar shine na Hudu a sadaukan taka. Domin shi mataimakin sarkin yakin sarkin Shaddar ne. A haka kuma ya kasance sadauki dodon maza. Dan a tarihi sau daya ya taba kaiwa kasa tun da ya fara yaki. Kuma ya sha fada da Aljannu dodanni da maridai hade da mugayen dabobbi da kwaruka. Duk girman kato kuwa in Gunzar ya dunkule hannu ya naushe shi sai ya kai kasa. Wani ma daga nan baya ko kara lumfashi. Ana cikin haka wannan bakin sukaga yarinyar nan da ke tare da su ta tsallaka cikin filin gasar cikin tafiyar ta ta jaruman kwarai duk kuwa da kasancewar ta yarinya. Al'amarin da yasa filin yin shiru kenan gaba daya idanun milliyoyin jama'a ya koma kanta ana jira aga abunda zatayi. bata zame a ko'ina ba sai gaban alkalin gasar . Cikin siririyar muryar ta tace, "Ni ina ji da shi". Maganar ta ce ta sa duk illahirin jama'ar wajen suka yi shiru hade da yin sororo suka saki baki suna kallon ta. Hatta sarki Shaddar sai ya tsaya cik yana kallo ta. Zuwa can kuma da sarki yayi wani tunanin sai ya kwashe da dariya da jin haka kuwa jama'ar wajen duk suka barke da dariya wasu harda rike ciki. Cikin masu dariyar kuwa harda Gunzar don shi dariya yake yana rike ciki hannu daya kuma yana nuna yarinyar da yatsa cike da mamaki da takaici wai itace take cewa zatayi fada da shi. bayan sadaukai maza ma sun kasa.Asad ya kalli Basim yace, "Anya kuwa yarinyar nan hankalin ta kalau kuwa?". "Ko dai tana da hankali to fa hankalin nata ragagge ne". Inji Basim. "Kaga kyale ta dai muga iya gudun ruwanta, kuma wallahi ko gani nayi za a hallakata bazan kai mata dauki ba. tunda danyan kanta ya kai ta". Cewar Asad saurayi mai kwari da baka. Basim baice dashi komai ba. Bayan kusan dakika Tisi'in Sarki Shaddar da jama'ar gari na aikin dariya sai Shaddar ya tsuke baki Al'amarin da yasa gaba daya gun akayi shiru ana sauraren Sarki Shaddar. Shaddar ya taso daga kan wannan kasaitaciyar kujerar sa ta mulki ya fara jawabi cike da isgili, da mugunta. "Ya ku jama'ata ta nan kasar Niyaha ku shaida ni Sarki Shaddar sarkin mai mulkin daular sin nayi alkawarin in har yarinyar nan ta sama nasara a kan Gunzar zan raba kasata biyu na bata rabi". Nan take jama'a suka barke da shewa wasu na dariya. In da sarki Shaddar ya san abunda zai biyo baya da baiyi kuskuren yin wannan furuci ba. Nan take sarki ya umarci Alkalin gasar a hada fadan. Ba bata lokaci kuwa Alkalin wasa ya shelanta kamar haka. "Gasa ta biyu a wannan babban fili na mu na gasa ya kasance ne to gashi nan dai. Domin abun zai kasance ne tamkar Bera a gaban mage Kun kuwa san cewa lakuma daya mage zatayi wa bera ta cinye shi. Dan haka jama'a sai a shirya kallon Margayiyar bakuwa da Sadauki Gunzar. Dan a yanzu sunan ta gawa". Nan fa fili ya sake barke wa da dariya. Wannan yarinyar kuwa ba abunda zuciyar ta ke yi sai suya. so take kawai a fara fadan dan ta nuna musu ita wacece. Lokacin da suka fuskanci juna tsakanin bakuwa da Sadauki Gunzar sai ya zamana Yarinyar ta zama kamar kaza a gaban giwa. Dan irinta uku sai su labe a bayan Gunzar ba tare da an gansu ba. Gunzar yayi tilli da takobin hannun sa, Dan shi ba fada ya dauki wannan karawa ba. wasan kwaikwayo kawai ya dauki abun kamar yanda mutane da yawa dake gurin suka dauka haka. Hausawa kan ce rashin sani yafi dare duhu. Ko da ganin yayi wulli da takobin shi itama yarinyar sai ta cire tata takobi dake daure a bayanta tayi jifa da ita gefe. Da ganin haka mutane aka kara kaurewa da dariya. A lokacin kuwa zuciyar sarki ta fara saka mashi wani abu game da yarinya dan ya san cewa ruwa fa baya tsami banza. Gunzar ya fara nuni da hannu yana cewa "Taho mana". Cikin zolaya da raini Ran yariyar nan yayi bala'in baci hakan yasa tace, "Ka sani cewa ba abunda zai hana in murde ma wuya da hannaye na in kashe ka. kai ko kai da ubanka kuka zo nan masga daya ta ishe in hallaka ku ba kari". Maganar ta bata masa rai dan yaki jinin a zagi ubanshi. hakan yasa ya falfalo a guje da nufin ya dan bangaje ta kadan ta fada. dan a tunanin shi in ya bangaje ta da karfi sai ta nutse a kasa. Ko da ya rage sauran baifi taku biyar Gunzar ya kara so gare ta ba sai ta gyara tsayuwar ta ta dunkule hannu. yana zuwa kuwa tayi wani tsalle ta narka mai wani wawan naushi a fuska. Karfi naushin yasa shi wata irin kundunbale yayi baya kanshi ya tafi cikin kasa kamar zai nutsu. kasar wajen da ya bi tayi rami.Kura ta turnuke gun, K'urar na lafawa can aka hangi gawar Gunzar yashe a kasa ko lumfashi bayayi.
Zanci gaba
[7/16, 2:57 PM] αвυє Quyraemey: 👨🏻💻👩🏻💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼
---------------------------
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร. °°________________________°°
⚔ // *FESHIN JINI* \\ ⚔
_Littafin yak'i_
°°________________________°°
*Babi na biyu (2)*
__________________
©
🤴🏻 *KINGBOY ISAH* ✍🏼
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankulan jama'ar wajen kenan. Tsabar mamaki wasu suman zaune sukayi, wasu kuwa idanun su sun kafe ba abunda suke sai kallon wannan bakuwar jarumar. Hatta su kansu Abokan tafiyar nata gaza motsin kirki suke yi dan basu taba sanin cewa tana da wannan karfin ba. Yarinyar cikin daga murya tace, "Kai kuma makaskanci Shaddar kayi sani cewa ba abunda zanyi da sarautar ka. Domin kuwa kasar da nake mulka tafi taka. Abu daya zakiyi mun wanda kuwa dole kayi ko kaki ko kaso. Kai bar jin ana ce ma sadaukin duk duniya in dai ka bijire wa wannan bukata tawa to fa ina mai tabbatar maka da cewa sai na tursasa ka da karfi. Ba wani abu bane Tasawirar zuwa dajin Burbuza zaka bani in kuwa kaki zan murde kanka in kashe ka in nemo ta da kaina a duk fadin gidan ka". Ko da jin wannan jawabi na wannan matashiyar budurwa sai ran sarki shaddar ya baci Ainun jikin shi ya ringa kyarma. Tsigar jikin shi gaba daya ta tashi. cikin fushi ya mike ya nuna yarinyar da hannu ya umarci dakarun shi da suyi gunduwa-gunduwa da namanta. Kafin ya rufe baki Badakare kusan dubu uku suka haura filin rike da muggan makamai suka zagaye Yarinyar kamar zasu cinye ta danya. Nan fa ta kasance tamkar kwayar geru a tsakiyar kaji. A hankali cikin sanda ta Tsuguna ta dauki wukar ta, ta zare ta daga cikin gidan ta. Wani irin haske mai dauke ido. ya fito wanda ya dauke wa duk ilahirin jama'ar dake taron ido. Ciki kuwa har da dakarun nan suka tsugunne suna masu kare hasken da hannu. Wannan ce damar da Yarinyar ta samu ta fara ragargazar su. Abunda zai baka mamaki da wannan wuka shine duk inda yarinyar ta kai sara sai wukar ta kara tsayi kuma duk abunda ta ci karo da shi wuka ko garkuwa ko mashi ko mutum sai ta raba shi biyu ta wuce. Nan fa jini ya fara feshi kamar anawa shuka ban ruwa. Ihun maza kuwa ya cika filin taron. Duk inda yarinyar ta durfafa sai dai kaga sasan jikin maza na zuba kasa kamar ana girbin gero. Tsabar kwarewa har wata katantawa take a sama kamar tsuntsuwa tana sara da kuma dokan dakarun da kafafunta. Kafin cikar dakika Hamsin gaba daya ta gama da dakaru dubu biyu. Tuni saura sun fara juyawa suna ara a na kare. Jama'a yan kallo kuwa gaba daya sun rude wasu sun fara tserewa wasu na fadin wannan ba mutum bace aljana ce. Kaico! basu san sadaukantaka da jarumta hade da karfi sihiri suka hadu gu guda ba aljani ma baya iyawa da mutum. Su kuwa abokan tafiyar nan nata tuni sun cika da tsanani mamaki na irin jarumtakar yarinyar da zafin nama ga shegen karfi. Sarki Shaddar ganin dakarun mutane bazasu iya da yarinyar ba. Nan take ya umarci dakarun sa na aljanu cikin bacin rai yace su kawo masa kan hatsabibiyar yarinyar nan. Aljanu kusan dubu biyu ne suka haura cikin filin. Masu fuka-fukai da marar fuka-fukai. Ba jira aka fara wani irin azababben yaki tsakanin aljannun da yarinyar nan. Domin in tayi sama sai ka zata tsuntsuwa ce mai fuka-fukai. kafin ta dawo kasa kuwa sai ta hallaka kusan aljannu hamsin. In kuwa ta diro kasa sai kaga an rufe ta tamkar zasu cinye ta. Bisa mamaki sai kaga tayi wani irin juye ta watsar da su tana mai ya kar su wani irin bakin jini na feshi. Wuhuhu in jarumta da kwarewa suka hadu da karfin sihiri ba yanda za ayi da mutum sai dai ai masa Allah ya isa. Domin kuwa an shafe kusan rabin sa'a anan wannan bakin gumurzu amma Dakarun aljanun nan sun kasa ko lakutar jikin yarinyar nan. Abunda ya fusata wani jarumin aljani mai suna garzugu kenan. Cikin shammace ya kai wa yarinyar wata wawiyar sara da nufin ya dauke kanta. Kafin wukar taje gare ta kuwa tayi wani irin tsalle kamar wacce aka jefo ta tsinke kan garzugu. Nan take BAKIN JINI YAYI FESHI. 'Yan kallo tuni sun fara cika wandon su da iska. suna neman gun boyo. Don wasu a zatan su yakin duniya ne ya barke. Haka wannan sarakunan suka fara jan ya nasu-ya nasu suna zame wa. Domin ba abunda ke tashi a fili sai ihun aljanu a duk sanda yarinyar ta sare su. Sarki Shaddar ganin Irin barnar da yarinya karama take mishi ya sa ya takarkare ya maka wani uban ihu. Ihun da yasa sauran mutanen gurin sume wa. Jarumai da sadaukai ne kawai ihun nan bai sumar ba. Suma kuwa dole tasa su tsugunnawa suka toshe kunnunwan su.
Cikin masu toshe kunne kuwa har da ita yarinyar nan. Kusan dakika Ashirin ya kwashe yana ihun tukun yayi shiru. Ko da jin yayi shiru sai yarinyar ta dago kai bisa mamaki sai ta hange shi a tsaye gaban ta aljanun nan kuwa ba ko daya duk sun tsere sai gawarwakin su kwance. Sarki Shaddar jikin sa sai karkarwa yake saboda bacin rai. zuciyar sa sai suya take, tun da ya hau karagar mulkin sa ba wani aljani ko dodo da ya taba samun nasarar shigowa har kasar sa ya kashe ko da mutun guda ne. saboda tsabar shakkar sa da ake. Yau kuma sai ga yar karamar yarinya ta zo ta karya wannan alkadari nashi. Kai lalai dole ya nuna wa yarinyar nan akwai maza gaban ta. Tsaye ta mike ta saba takobinta a kafada ta watsa mishi wani kallo irin na raini sannan cikin bacin rai tace, "Kai makaskancin Sarki Shin zaka bani Taswirar nan cikin kwanciyar hankali ko kuwa sai na juya ma fuska ta kalli baya tukun? kafa sani cewa in har na kashe ka ni zan gaje dukiyar ka na kuma dora wakilina a karagarka". Ko da jin haka sai sarki Shaddar ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya ya dade yanayi daga bisani kuma ya murtuke fuska yace, "Shin kin kuwa san wa kike gaya wa wannan maganar? Sadauki Shaddar ne fa sarkin da babu kamar sa a wannan zamani. Shaddar dai wanda shi kadai ne mahalukin da ya taba zuwa baitul jalal Ya dawo a raye. Shi kike tunanin zaki yaka?". Wata dariyar ya kara fashewa da ita al'amarin da yayi matukar batawa yarinyar nan rai kenan. Nan take ta falfala a guje ta nufe shi da niyar ta sa takobinta ta fillen kanshi. Bisa mamaki ko motsi baiyi ba. Tana zuwa kuwa ta daka wani tsalle ta kai mai wata muguwar sara a wuya. Wukar na haduwa da wuyan nashi sai ji kake tassss! Tamkar karfe-da-karfe ne suka hadu tartsatsin wuta ya tashi yayin da wukar ta kwace daga hannun yarinyar tayi sama kwololuwa tukun ta dawo ta caku a kasa. Ita kuwa yarinyar kamar ta daki sifirin can taji anyi tilli da ita ta fadi can gefe a matukar galabaice. Cikin matukar juriya ta mike tsaye tana haki. Cike da matukar mamaki dan a tarihin asirtacciyar wukar ta ta boka ya fada mata wannan wuka ba irin ko wacce irin wuka bace. domin ta shude zamaninika masu dama, Asalin wukar ta wani aljani ne mai suna Burbuza. Duk abunda aka sara da ita kuwa dutse wallau karfe to fa sai ya rabe gida biyu. A karon farko sai gashi yau ta sari mutum bil adama amma wukar ta kasa shigar sa. Sai yanzu ta tabbatar da hatsabibancin Sarki Shaddar da ake fada...........
Zanci gaba
[7/16, 2:57 PM] αвυє Quyraemey: 👨🏻💻👩🏻💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼
---------------------------
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร. °°________________________°°
⚔ // *FESHIN JINI* \\ ⚔
_Littafin yak'i_
°°________________________°°
*Babi na uku (3)*
__________________
©
🤴🏻 *KINGBOY ISAH* ✍🏼
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
Sarki Shaddar yayin da yaga ta cika da mamaki sai ya kyal-kyale da dariyar mugunta. yace, "Kin gwada da makami bakiyi nasara ba. Ko zaki gwada karfin dantsen ki kuma? Domin kuwa naga kina gadara da shi". Ko da jin haka sai yarinyar ta dunkule hannu ta nufe shi a guje. Ko da taga ta kusan isa gare shi sai ta ware iya karfinta dama na sihiri ta kai mai naushi a wuya. kamar dazun haka taji an kara yin wulli da ita kamar ta naushi sifirin. Hannun ta kuwa ya lankwashe hakan yasa ta kwalla ihu dan a tunanin ta hannun ya karye ma. Dan dukan da ta kai mai ji tayi kamar ta naushi dutse. Cikin karfen hali ta mike ta kama hannun ta na dama wanda tayi naushi da shi da na hagun ta ja da karfi yayin da ta kara sakin wani karan. Cikin sa'a kuwa hannun nata ya mike nan ta tabbatar da gocewa hannun yayi. Sarki Shaddar yace, "Tunda ke kin gaza bari in nuna miki yanda ake yi". Da fadar haka yayi kanta . Itama kuwa ta nufe shi cikin zafin nama. ko da ta kai mai naushi sai ya goce dukan nata ya sama iska. ya dunkule hannu ba tare da ganin kankantar ta ba ya gabza mata naushi a baya. nan take ta durkushe tana aman jini. Domin kuwa karfin naushin nashi ba kowa ke iya shanye shi ba. Ko da ganin ta fadi kasa sai ya fara kwallo da ita. Idan ya harbe ta da kafa sai ka zata bata da nauyi ko kadan, dan sai tayi sama kafin ta zo kasa zai bita cikin gudu irin na tsafi ya kara harbata. Tayi iya kokarin ta dan kare wannan hari na sarki Shaddar amma abun ya gagara. Haka yaci gaba da mata sai da yaga ta fara lumfashi sama-sama tukun ya umarci dakarun shi da su daure mishi ita. Domin kuwa yana son sanin wani abu dangane da ita. Mamakin da yake nata shine da ya ganta tare da Saiful sihir. Wato wannan takobin ta ta. wacce ya dade yana neman bai samu ba. Su Asad dake tsaye da ke Tsaye ganin abun da ke faruwa yasa Basim ya yunkura zai nufi filin. Domin ya gama fusata da abunda akawa abokiyar tafiyar ta su. Asad ya ruko shi yana mai cewa. "Ya kai Basim ina hankalin ka ya tafi da kake tunanin tun karar sarki Shaddar. Nasan cewa kai jarumi ne mai tarwatsa maza amma fa ba maza irin su Shaddar da suka kasance gawartattun matsafa ba". Basim yayi murmushin takaici tukun yace, "Abokina ka sani namijin kwarai da juriya akasan shi ba da tsoro ba. Jarumin kwarai ya kashe ko a kashe shi ya sani. Wuya kuma bata sa namiji ya gudu. Shin ina amfanin tafiya tare in har mukaga wani abu da zai cutar da dayan mu kuma muka ki tallafa mishi?. Kuma bari in ma tuni dan naga kamar ka mantan cewa Taswirar da muke nema tana hannun Shaddar kuma a yunkurin amso ta Yarinyar nan ta shiga wannan hali. Dan haka ni dole in shiga fadan nan duk abunda zai same mu to ya same mu tare". Ko da jin wannan jawabi na Basim sai Asad yaji duk wani tsoro ya fita a gare shi. Nan take ya dako tsalle daga inda yake.Tun a sama ya fara dana kibiyoyi yana sakarwa Sarki Shaddar. Basim shima ya dako tsalle ya shigo filin nan fa aka kacame da wani sabon azababben yakin na gaban kwatanci. Sai dai abunda yayi matukar bawa Asad mamaki shine kibiyar na zuwa saitin Shaddar kafin ta taba jikinsa sai yaga ta fadi kasa. Amma duk da haka bai fasa ba yaci gaba da kai hari yana kare kansa. Kwarin tashi ta kasance tana da Wasu irin wukake a gefe-da-gefen ta wanda suke fitowa da zaran a latsa wani waje na jikinta. A haka yaci gaba da gumurzu yana yakar ajlanun nan kuma yana sakar wa shaddar kibiya. Idan kuwa ka juya gurin Basim. Kaico FESHIN JINI kawai zaka ringa ganin yana feshi a duk inda Basim ya durfafa. Da salo biyu yake amfani a fadan nasa. Hannu sa na dama yana amfani da takobin sa. Hannun sa na hagun kuwa wannan sarkar ce itama ta kasance asirtacciya ce domin kuwa duk sanda ya jefata sai kaga ta laulayo kan aljani ta tsinka biyu. Duk wanda ya kai wa duka da ita kuwa sai dai kaga FESHIN JINI wajen ya fashe. Hakika su Basim sun kai sadaukai kuma jarumai madaka kartti. Ko da sarki Shaddar yaga wadan nan takadiran jarumai sun kusan karar da dakarun sa domin sun kashe kashi biyu cikin uku. A abunda bai kai Rabin sa'a ba. Sai ya cika da tsananin fushi nan take ya daka tsalle kamar wani tsuntsu bai tsaya a ko ina ba sai kafaffun sa suka dira a kirjin Asad. Ai kuwa yayi sama ya wulwula kusan sau hudu tsabar karfin dukan. Ya fado kasa magashiyan yana aman jini. Nan da nan dakarun Shaddar suka sa sarka suka daure shi kamar yanda akawa yarinyar nan. Ko da Basim yaga abunda ke faruwa sai ya kwarara wani uban ihu ya burkuce. Ya falfala da gudu ya nufi Shaddar tun kafin ya karasa yayi wani irin tsalle ya harbawa Shaddar wannan bulalar tashi. Bisa mamaki sai gani yayi Sarki Shaddar ya cafke bulalar da hannu daya. Ya jawo shi da karfi ko da ya karaso sai Shaddar ya dunkule hannu ya gabza mai naushi a wuya. Nan take ya sulale kasa summame. Shaddar ya umarci da a daure su a kai mai su kurkukun Burmud. Kurkuku ne mai matukar tsaro domin kaf fadin duniyar mu ta 'yan adam ba kurkukun da ya kai shi tsaro. Mutum uku ne kadai ke iya bude kofar wannan kurkukun, Sune sarki Shaddar sai kanin sa Sharhus. Sai kuma wani katon aljani mai suna Kirmuhu bin Ujbur. Ita dai kofar ta kasance ta farin karfe mai matukar kwari da kauri tsafaffiyar kofa ce domin ku su wadannan mutane masu iya bude ta da wani karatun tsafi mai matukar wahala suke bude ta. Ko da sarki Shaddar yaga an kama su an tafi da su. Sai ya kwashe makaman su ya hau bisa wani tsuntsun sa na tsafi da yake hawa, tsuntsun ya tashi sama bai zame a ko'ina ba sai tsakar gidan sa. Shaddar ya saukko rai a bace ya nufi turakarsa. Duk inda ya gifta sai kaga mutane da aljanu suna zubewa suna mika gaisuwa a gare shi dan tsanannin mulki irin nasa. Yana shiga dakin ya kulle kansa ya zube makaman nan tukun ya nufi wani daki wanda ya kasance akwai wani rami a tsakiyar dakin mai cike da wani tsanwan ruwa Shaddar ya shiga ciki. Kamar yanda ya saba dama in aka bata masa rai sai ya shiga cikin ruwan nan yake samun sukuni. Kuma in ya shiga sai ya share Sa'a biyar ko fiye da haka a ciki haka ka'idar tsafin sa yake. Wannan bakin jaruman kuwa ko da suka farfado sai suka tsinci kawunansu a wannan kurkuku wanda su kansu suna jin labarin shi har yau ba mahalukin da aka taba sawa ciki ya tsere mutum ko aljana ko dodo. Nan take Azad ya dunkule hannu ya naushi bangon bayan shi cike da takaici yace, "Kaicon mu mun fado tarkon da zaiyi wuya mu tsira". Basim ya dube shi yayi murmushi tukun yace, "Karka bada ni mana ya kai abokin tafiya. Ka kalli wannan yar karamar yarinyar mana in ka kalle ta sam ba alamar firgici a tare da ita sai ma fushin ta da ya linka na da". Azad ya kai duban shi ga wannan budurwa duk da baya ganin gaba daya fuskar ta yasan a cikin fushi take. tana kallon gefe. Azad yace "Yake wannan jaruma abokiyar tafiya, ki sani cewa munyi mamakin jarumtar ki matuka. Domin bamu dauka cewa jarumtakar ki ta kai har haka ba. Kasancewar ki mace kuma yarinya karama. Muna son sanin sunan ki ko dan alfarmar tafiya da ta hada mu tare". Sai da ta shafe kusan dakika arba'in bata ce komai ba daga bisani kuma ta juyo cike da izza ta daga baki kamar bata son yin magana. "Sunana Gimbiya Azrah". Da jin haka gaba daya su biyun suka ja da baya cikin furgici. "Da gaske kece Gimbiya Azrah yar sarki Junaid bin Humaid?". Ba tare da ta bashi amsa ba ta kauda kai taci gaba da kallon wani waje. Jin wacece ita yasa suka tsuke bakunan su. Duk da kuwa daya daga cikin su dan sarki ne .Amma ai bindin rakumi yayi nesa da kasa. Azrah tayi musu fice. A can fadar sarki kuwa kwana yayi yana bincike a kan makaman su gimbiya Azrah musamman ma wukar ta mai suna saifu-sahr Wukar sihiri. Takobin da manyan bokaye da manyan sarakuna na duniya suka shafe tsawan shekaru suna nema. Amma an rasa inda take yau sai gata har gida. Wannan ne ma yasa yake cike da farin ciki da murna. Ko da ya nutsa a binciken sa na tsafi sai ya bata rai ya murtuke fuska. Ba wani abu ya sa shi yin haka ba sai ganowa da yayi wato ita wannan takobi a jikinta akwai wani rami wanda yake a zageye kamar makwancin zobe. Ita kuwa wannan wuka sai an saka mata wannan zobe wanda ya kasance shima sihirtacce ne tukun zatayi amafani yanda ya kamata. Zoben kuwa ya kasance a wuyan wani sarkin Ajannu dake can dajin Burbuza, yakin da za'ayi da aljannu kafi a kwato wannan zube kuwa daya yake da yakin duniya sau goma. Domin kuwa wannan aljani mai suna Burbuza ibini Mirginu. Shine ke mulkar wannan daji Kuma wannan wuka ta kasance tashi ce. Tun da kakan Azrah ya je ya raba shi da ita. Aljani Burbuza yake cike da bacin rai yau kusan shekara dari uku kenan amma kullum shirin yaki yake domin a binciken shi yaga cewa akwai zamanin da yan adam zasu sake zuwa da wukar sa domin su kwace zoben wuyansa. Wannan yasa kullum a cikin fushi yake. Shi dai wannan daji ba a cikin wannan duniya ta mu yake ba. Kuma daji ne mai cike da masifu da annuba iri-iri. Ga abubuwan al'ajabi. kai duk wanda ma kaga yaje dajin nan kuma ya dawo a raye to fa tsananin tsawon rai ne kawai zai kai ka can ya dawo da kai. Shaddar na cikin wannan yanayi sai yaji ana kwalla mai kira. Ko da ya fito sai yaga wani hadimi nashi ya rugo a rikice ya zube a gaban shi yana mai cewa. "Ya kai sarkin sarakuna yanzun nan aka zo mana da sakon cewa wannan bakin da aka kama sun tsere kuma an gabza azababben yaki tsakanin su da mutanen mu.Wanda har aljani Kirmuhu mai tsaran gidan kurkukun ya rasa rayuwar sa". Ko da jin haka sai sarki ya kwalla uban ihu wanda yasa duka fadin gidan sarautar yayi girgiza tamkar ana girgizar kasa. Nan take yayi nuni da hannun shi zuwa wannan wanda ya kawo mai wannan mummunan sako. Take wasu irin wukake na tsafi suka fito suka tsarge wuyan wannan dan sakon. Jini yayi tsartuwa. A fusace sarki Shaddar ya fita Yana zuwa fadar tasa ya iske fada ta cika dankan ga sadaukan aljanu bila adadin cikin shigar yaki gefe kuma ga mayaka na mutane. Amma duk sai yaga a banza suke tunda har su Basim suka iya tserewa. gefe ga boka Girbat bini girguz bokan sarki Shaddar ga kuma kanin sa Sharhus a gefe. Sarki Shaddar ya kalli boka Girbat yace, "Yakai bokana ina so in san ta yanda akayi wadan nan hatsabiban mutane suka tsira daga wannan kurkuku wanda ya shude zamuna da dama ba a taba samun wanda ya taba guduwa daga ciki ba". Ko da jin haka sai boka Girbat ya runtse idanu ya fara wani irin karatun tsafi wanda ko kai waye bazaka san abunda yake fada ba. Bayan kwashe yan dakiku yana yi sai yayi nuni da wani bango nan take hotan abubuwan da suka faru bayyana. Wasu bakakken aljannu ne masu girman gaske tsakar dare suka fara dirowa a bakin dutsen da kurkukun yake. Sai da suka gama haduwa su dari biyu tukun suka tasarwa wannan dutsen. Aljanun dake tsaron wannan kurkukun su kimanin dubu biyu ko da sukaga wannan aljanu sun tun karo wajen sai suka zare takubban su suka tare su da yaki. Nan fa wani irin yaki mai ban al'jabi ya kaure domin su wannan aljannu bakake basa jin sara ko suka. Kuma a hannun ko wannen su akwai wata wuka wacce take jawur kamar an fiddo ta daga cikin wuta..................
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/